Advertisements
Chapter 7 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 31

18K to 21K   out of 91.1K words

yana kyalli a ƙasa. Co-pilot ne ya furta, “Speed stable… glide path good.” Ahankali John ya furta “Perfect… keep it steady.” ahankali jirgin ya taɓa runway. “Touchdown!”A natse John ya naɗa tare da amsawa da “Reverse thrust.” Engines suka rage ƙarfi, jirgin yana rage gudu cikin kwanciyar hankali. Jirgin ya juya daga runway zuwa parking bay. “Flight JX-217, welcome to Nigeria.” John ya naɗa tare da amsawa da “Thank you. Safe landing confirmed.” A bayan jirgin kuwa tuni fasinjoji suka fara tafa hannuwansu cike da farin ciki, wasu suna murmushi, wasu suna jin daɗin saukar lafiya.
John ya ɗan jingina bayansa da jikin kujerarsa, yana sauƙe wani numfashi cike da nutsuwa, a bayyane yana me furta “Thanks Jesus....domin sauƙarsu lafiya cikin tsari da farin cikin da shi kansa yake a cikinsa. Bayan jirgin JX-217 ya tsaya a parking bay, ƙofar jirgi ta buɗe a hankali… Iskar Lagos mai ɗumi ta fara kaɗawa zuwa cikin jirgin.
Hasken rana yana bugawa jikin jirgin, yana ba komai wani irin kyalli mai kyau. A waje ma’aikatan filin jirgi suna tsaye cikin tsari, wasu cikin uniform mai tsafta wasu da murmushi a fuskokinsu. Ahankali Captain John da shi ne kusan fitowar karshe ya fito daga cockpit, yana tafiya cikin kwanciyar hankali, yana kallon yadda komai ke tafiya cikin tsari, wani kyakkyawan murmushi ne ya bayyana samar fuskansa me kyau, tare da ambatar.
“This… this is a good landing.” haka passinger's suka ci gaba da fita, wasu na ɗaukar kaya, wasu na yin hotuna, yayinda wasu ke furta Alhamdulillah, cikin yaruka maban banta, Ingilishi, Hausa, Yoruba… duk suna haɗuwa cikin farin ciki... Ga wasu ƙananun ma'aikata masu kula da Airport nata furta musu kalmar... “Welcome! Welcome to Nigeria!” tsaiwa kawai John yayi yana kallon yadda mutane ke cikin farin ciki… yana nan tsaye se ga motar airport ɗin ta ƙaraso har inda yake don kaishi gida, Kai tsaye ya shige motar cikin nutsuwa motar ta fara tafiya, ga hasken titi yana shigowa ta cikin gilashin motan yana ɗan haskaka fuskarsa, yana jingine da jikin kujerar motar, idanunsa lumshe amma gaba ɗaya ita ke wayo a cikin zuciya da ruhinsa gaba ɗaya, be taɓa jin ya ƙaunaci wani abu duk girmansa karon farko irin yasmine ba, sunanta kaɗai idan ya tuna yakan sa yaji zuciyarsa ta ɗan buga, daga lafen da yake a jikin kujerar yake tuno yadda ta tsaya gabansa… yadda idanunta suka kalle shi cikin yanayi na ɓacin ran da bai taɓa mantawa ba, maganganun da ƙaramin bakinta ya dinga yanko masa masu zafi, ƙirjinsa yaji ya sake bugawa shin ta ina ma ya kamaci ace ya fara nemar trouble ɗin nashi nema?, wani munafikin numfashinsa ya fesar, tuno yadda ya kusanto ta, yadda lokaci guda ya tsaya gabanta, kafin bakinta da take masa masifan ya ɗauki hankalinsa har zuwa lokacin da karon farko yaji sha'awan yin kissing wata mace a karonsa na farko, tuno yanayin data shiga yayi na tsoro me girman daya bayyana akan fuskarta, yadda shi kuma a nashi ɓangaren yaji kamar duniyar ce baki ɗaya ta tsaya mishi, da kyau ya wani matse hannunsa a jikin kujeran, yana jin wani abu na ƙoƙarin ɓallo masa, Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa ba dariya ba ce, amma wani abu ne mai cike da nisa da ƙauna ga zuciyar data faɗa tarkonsu, sai kuma nauyin hakan ya biyo baya,domin ya san komai bai gama bayyana ba, yana cikin wannan tunanin har besan lokacin da motar ta tsaya gaban mension nasu ba, se da yaji maganar driver na faɗin “Sir, we’re here.” kana ya iya buɗe lumsassun idanunsa a hankali, yana dawowa daga duniyar tunani zuwa ta gaskiya. Direcly ya fita a motan yana nufar katon get na gidansu, dake anan gida lokacin yammaci ne kuma weekend ce don haka gaba ɗaya ahalin suna zazzaune basu jimawa daga dawowa daga couch ba, don haka da katafanin family ɗin nasu ya fara cin karo, ciki kuwa harda kakansa PATRIARCH, Madam Victoria Osteen ce ta fara ganin tsaiwar yaron nata a kansu...

“My Love…”

Madam Victoria Osteen ta ƙira sunanshi cike da wani irin zumudin da aduk lokacin da zata ganshi take shiga, ko kafin kowa yayi wani motsi tuni har ta isa gabansa ta rungume shi da ƙarfi, irin rungumar da ke tabbatar da cewa tabbas mahaifiyar nashi tayi kewar yaron nata kwarai da gaske, Nan sauran family ɗin ma suka taso, fuskokinsu cike da annuri da farin cikin ganinsa lafiya, don duk hankalinsu a tashe yake, duk da cewan sun ga komai lafiya, amma hankali da nutsuwansu baya tare dasu, yana ga John ɗin ne kawai, shi kuwa John cike da ƙaunar family ɗin ya tsaya a tsakiyarsu, yana jin ɗumin tarɓar daya samu daga su duk da kasancewar har lokacin tunaninta na nan maƙale a ƙasan zuciyarsa daram, har yanzun kuma yana jin dumin rungumar mahaifiyarsa a jikinsa. Kafin ya ɗan ja baya kaɗan yana kallar yadda har yanzun hannunsa ke riƙe cikin nata, tana kallon fuskarsa da kulawa, kafin cikin muryan nuna ƙauna ga yaron nata take tambayar... “Are you okay, John?” tayi tambayar cikin damuwa, kansa kawai ya gyaɗa mata ahankali yana bata amsa da. “I’m okay, Mother… I’m fine.” Deepika ce ta iso da gudunta ta faɗa jikinsa tana basa kyakkyawar rumgumar da haka kawai ya bata ran John, don shi sam ba ma'abocin son ire iren waɗan nan tarin tarkacen nasu yake ba, wata kafuwar hararan gefen ido Madame Victoria Osteen ta mata a fakaice, X-Eashika ma a fakaice ta harara Deepikan wacce mahaifinsa Mr JEF DEEFER PATRIARCH ke son John ɗin ya aura, itama yar ƙanin Papa'n ce yayainda Deepika ta kasance yar gidan ƙanwarsa Oueen Ara, da murmushi me kyau mahaifinsa ya matsa kusa dashi, fuskar sa cike da tsananin ƙaunar yaron nasa shima yake tambayar...
“ Joseph we heard something about the flight… they said there was a problem. What really happened?” se gaba ɗaya parlourn nasu yayi ɗan yi shiru na wani lokaci, kafin a natse John ya sauƙe wani numfashi a hankali, yana kau da idonsa kaɗan yana kuma ja baya ga kowa.
“It was serious… but we handled it.”
“Serious?” X-Eashika tayi saurin taryan numfashinsa. “We’ve been worried sick!” Mahaifiyarsa tayi maganar tana sake riƙe hannunsa. “We couldn’t even sleep… we kept thinking about you.” ta sake faɗi tana kallar John ɗin kai tsaye. Wani laushi na ratsa zuciyarta da ALLAH ya kuɓutar mata da yaron nata mafi soyuwa a cikin duniyarta gaba ɗaya, “I’m here now,” ya faɗa a hankali. “I’m safe.” daga haka suka zauna tare da shi a parlourn suka ci gaba da jero masa tambayoyi ɗaya bayan ɗaya...
“What exactly went wrong?”
“Were you scared?”
“What about the crew?”
“How did you manage it?”
Gaba ɗaya sun fara cika kansa amma haka yake amsa su dole cikin nutsuwa, sedai yana rage wasu wasu bayanan
yayin da suke maganar, yana jikin kakansa Patriarch daya gudu can saboda da Mommah nashi da take wani maƙale masa, daga nan yaci gaba da jinsu yayi shiru yana tafiya ma tunanin Babyn Robar shi, jin shirunsa yayi yawa ne, gashi yana ga masa magana ya saka Mommah nashi ɗan jan ƙafarsa tana me furta... “Joseph … you seem distant. Is something bothering you?” ɗan murmushi kawai yayi, amma murmushin ba cikakke ba ne. Se kawai ya amsa mata da “I’m just tired, Mom… it’s been a long trip.” kallonsa kawai na ɗan lokaci tayi kamar wacce keson son fahimtar wani abu… amma ta barshi.
Wanda ahankali John ya miƙe yana riƙe da p-carp nashi a hannu ya ce. “I think I need some rest,” ya faɗa cikin taushin murya wanda Mother tayi saurin gyaɗa masa kanta tana me furta. “Of course… you need it.” daga haka ya juya ya nufi hanyar ɗakinsa, takunsa a hankali kamar wanda jikinsa yake jin nauyin gajiya da tunani a lokaci guda. Koda ya isa ƙofar ɗakin ahankali ya buɗe ya shige, komai nashi na nan a killace, room ɗin yayi shiru, jacket ɗinsa ya cire kai tsaye ya jefa a kan kujera. Ya zauna a gefen gadonsa, ya ɗan sunkuyar da kansa idanunta na masa gezau,
A hankali ya ɗaga kansa ya jingina da bango… idanunsa suna ɗan rufen har lokacin, maganar ta _Ta duk kan alamu ma kai arzikin muslunci ma baka da...._ nan take bugun zuciyarsa ya sake tsananta tuna yadda ta kalle shi… yadda idanuwanta suka cika da wani abu da ya kasa fassara, _Kar ka yadda ko a rashin sani ne, wannan ƙazamin hannun naka ya sake yinƙurin taɓa koda hijjabin jiki nane balle hannuwana Malam..._ Gaba ɗaya neman birkicewa ƙwaƙwalwan kansa ke yi, Hannunsa biyu yakai yana riƙe kansa ya ɗan motsasu a hankali...yana jin yadda kan ke nemar dirar masa da ciwon kan nan take, sannu a hankali ya buɗe idanunsa yana kallon samar Pop…
Ahankali ya kama sarƙan Cross ɗin dake maƙale a wuyansa yana ɗan jujjuyawa cike da nauyi, yana jin yadda ciwo ciwon kan nan ke ta kokarin ganin ya taso mishi. Abinci da babu jimawa aka shigo mishi da shi ya kalla, sedai baya jin ci, don shi abknci bai dameshi ba sam sam, rabon dayaci abinci tun kafin ya shiga jirgi, shima kuma coffee. kawai ne yasha. Sake lafewa a kan gadon daya gama amsar amanarsa yayi yana lumshe rinannun idanuwanshi da suka kaɗa sosai a tashin farko. Wani abu me kama da tsananin SO ko ƘAUNA yake ji lokaci ɗaya akan gal ɗin, yanayin dake nemar sake sashi birkicewa nan take, wasu surutai ya fara yana wani lullumshe idonsa har barcin yayi nasarar daukansa na dab da magriba. Ba sosai can yayi baccin ba, don haka lokacin daya farka ahankali ya shiga buɗe sleeping eyes nashi da sukayi masa nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da yake gani acikin su ne ya sashi maida idanun nasa ya rufe ruf, sosai yaji kansa na wani irin bala'in sara masa, dan haka yakejin gaba ɗaya jikinsa yayi weak.... Hannu yasa yana ɗan dafe kansa dake yi masa ciwo kaman zai rabe biyu,still rinannun idanunsa dake a lumshe ya buɗe tare da sauƙe ganinsa akan gadonsa. Kafin kuma ahankali ya ɗan motsa jikinsa tare da soma ƙoƙarin ɗaga kansa da yakejin yayi masa nauyi sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba da tarin tunaninkanta daya ringa yi ba,
jingina bayansa kawai da jikin fuskar gadon yayi, tare da sakin ajiyar zuciya yana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin ɗakinsa. Shower ya sakamar kansa tare da tokare hannuwansa da jikin sink, haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kansa. jin kamar numfashinsa na ƙoƙarin ɗaukewa ne ya sanya shi janye jikinsa da ƙyar. idanunsa jajur alamar har yanzun komai na nan daram a cikin kansa, da bathrube ya fito a jikinsa walking slowly kuma yake tafiya fuskar nan babu alamar annuri ko guda. Kai tsaye kayan shan iska ya saka ya yi waya aka kawo masa dinner nashi, wanda Mother ce ta kawo masa da kanta, amma itama ganin yadda yanayinsa yake ya sakata ficewa salin alin. A natse yayi peeding kansa, bayan ya kammala yaja ɗan madaidaicin plask tare da tsiyanyar coffee a mug , Ahankali yake ɗan sipping coffee ɗin dake left hand nashi, ɗayan kuma yana yana latsa wayarsa daya gaba ɗaya ya gama maida hankali da tunaninsa kanta, yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen wayar kaɗai ya isa baka tabbacin abu mai matukar muhimmanci ne yake yi. Dan sai loƙaci bayan loƙaci ya kan ɗan ɗauka mug na Coffee ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajje mug ɗin, hankalinsa kacokam na kan abinda yake yin ɗin da wayan. Cikin deep down ɗin da yake amsa daga cikin zuciyarsa ya ɗan lumshe idonsa, bayan ya kammala shan coffeen ɗin kuma ahankali ya miƙe tsaye yana nufar hanyar fita, duka ahalin nasu na Zazzaune a parlourn gidan ya musu gaisuwan jam'i a takaice yana nufar hanyar fita, kafin muryan Mommah nashi ya dakatar dashi cak daga fitan da yake kokarin yi wajen fara nemar yasmine.......

_Hhhh nace to ya kukaji salon rubutun littafin DUHU na DUKAN duhu ne?, Salon na musamman ne, kamar yadda tafiyar ma take ta daban ce, haka ma littafin DUHU na DUKAN duhu na mai rabo ne, domin bamu sa hannu bama a komai, wasan dai yanzun ne zai fara🤸🤸🤸🤸......_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215




*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 7
Paid book

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

ꨄ “Joseph!!!....“ ta ƙirayi sunan shi kai tsaye tana tashi daga inda take zaune ta iso har inda yake tsaye can, kafin ya juyo a hankali cike da ɓoyayyiyar damuwar dake lulluɓe da fuskarsa, ɗan kallonsa ta shiga da idanunta masu cike da alamar tambaya, ta sake matsowa kusa da shi kaɗan cikin harshen Ingilishi take sake jefa masa tambayar...
“Ina zaka je a wannan lokacin? bayan ko gama hutawa ba kayi ba, bare kuma mu zauna dakai?” ta tambaya cikin ɗan nuna damuwa a muryarta. “Ka san lokaci yayi… dare yayi sosai John.” ta sake faɗi tana ƙoƙarin kamo hannunsa,kansa ya ɗan kau da yana
ƙoƙarin ɓoye abin da ke ransa, cikin silent voice nashi ya ce...
“Zan ɗan fita ne kawai Mother, Ina da buƙatan nasha iska kaɗan.” ya mayar mata shi ma cikin harshen nasara. Bata yarda ma sema sake tsayawa da tayi tana kallonsa na wasu daƙiƙu… kamar tana jin akwai wani abu fiye da hakan ne kawai dai ya ɓoye mata ne, kafinnta sake maimaita kalmar “Iska?” ta sake ɗorawa da cewa. “A irin wannan lokacin kuma?” wani ɗan shiru ne kawai ya ratsa tsakaninsu, tana sake matsawa kusa da shi sosai, ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce... “Love!, me ke damunka?” ɗan lumshe ido kawai John yayi, zuciyarsa na masa nauyi sosai, shi bai san yadda zai bayyana mata ba domin shi bai san kome zai ce mata ba… ba ta san Yasmine ba… ba ta san dalilin da yasa zuciyarsa ke neman fita cikin daren ma ba, “Babu komai, Mom…” ya faɗa a hankali amma muryarsa ta nuna akwai ɓoyayyen abu. Madame Victoria ta ɗan girgiza kanta kaɗan, kafin ta ce “Ni na haife ka John… na san lokacin da kake ɓoye abu, don gaka meke faruwa da kai?....” Wani ɗan murmushin ƙarfin hali kawai yayi idanunsa na sake bayyana damuwar da yake a ciki, kafin a takaice ya ce. “Please… kawai ki barni na fita Mommah zan dawo da wuri I promise!.” duk da haka bata yarda ta sake tare masa hanya, kallonta kawai yayi yana rasa me kuma zai ce mata, shi fa wannan takura da rashin son fitan da ba'a son aga yana yi akai akai kan takura rayuwansa suke, wani numfashi ya fesar Zuciyarsa na faɗa masa kawai yace mata... _Wajen Hausa gal ɗin sa zai je, saboda yana son ya sake kissing nata irin na ranar?...._ ko kuma cewa ze mata _Ya sama wacce yake so?..._ yana tsaka da wannan tunanin kuma yaga ta bashi hanya tamkar ta karanto zuciyarsa bata son ya furta mata kalaman ne don haka ta bashi hanyar, da murmushin yaƙen dolen data ƙaƙalo a fuskanta ta ce...
“Before you go, let’s pray“ ɗan sunkuyar da kansa kawai John yayi cikin yanayin girmamawa, Ita kuma ta wani rufe idanuwanta a hankali, tana fara masa adda’a cikin nutsuwa “Heavenly Father,
I commit my son into Your hands as he goes out today. Please guide his steps and order his path. Protect him from every danger and evil. Surround him with Your grace and bring him back
home safely. In Jesus’ name, Amen.”
Bayan ta gama ta gama masa adda'an
ta buɗe idanuwanta tana murmushi mai cike da ƙauna ta sake ce dashi. “Go, my son… God is with you.” John ya kalli mahaifiyarsa da girmamawa zuciyarsa cike da kwanciyar hankali dajin daɗin adda'an data masa ya ce “Thank you, Mom.” ya juya, har ze fita ta sace dashi.
“Go in peace, God is with you.”
“I will, Mommh…” daga haka ya buɗe ƙofar a hankali ya fita, Mecheal na ganin fitowarsa wanda shi ne dawwamammen driver nashi in yana gari yayi hanzarin nufar wata Black Bentley ya buɗe masa. A tsanake John ya shiga motan a hankali, driver ɗinsa ya kunna motar tare da tambayar....
“Where to, Boss?” ɗan shiru John yayi don shi kansa be san inda suka nufa ɗin ba takamaimai, sema shiru kawai da yayi yana kallon titi ta cikin gilashin motar, zuciyarsa cike da rashin tabbas ya ce da Mecheal ɗin kawai.. “Just… drive,” hakan kuwa akayi Mecheal tafiya kawai yake yi, shi kuma idonsa na waje yana kallar hasken streetline, da mutanen dake tai da komo wasu a ƙafa, wasu abin hawa motace ,keke ne, mashin ne, wasu shaguna suke rufewa bayan dogon yini. duk daga inda John ke zaune lafe a bayan motar yake kallar komai, hannunsa riƙe da wayansa amma kuma babu abinda yake da ita, har lokacin kansa na waje yana kallon kowanne fuska da suke wucewa, kamar yana fatan ganin wacce yake nema ne, haka motarsu ta dinga yawo daga

7 / 31