Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
ta jigata, tana zaune a babban parlourn gidansu wayarta na hannunta.
A kai akai take kallon screen na wayar,
Ba saƙon, ba kiran. Sai ta lumshe ido a hankali. A hankali kwanaki suka fara wucewa… John ya kiyaye duk wasu kalmanta a kansa na cewar ba ƙira, ba kuma zai nemeta ba...
A gidan su Joseph kuwa wani irin tsaro Papa da Madame Victoria suka sake ninkawa a gidan nasu saboda kawai kada John ya sake fita ko ina, wanda shi kuma dama tun da ya dawo daga asibiti be taɓa koda tunanin fitar bane, amma kuma yau yaji duk duniya babu ubanda ya isa hana mishi fitar nan, don haka ya sakko cikin wasu kananun kaya amma dogon wando har kasa da t-shirt me yalwa ba ire iren irin wacce ya saba sakawaba. Se dai me yana isa security ɗin suka nemi dakatar dashi, wani shegen kallo ya jefa ma securities ɗin yana gyara rikon da yama Pcarp nashi yace. "Duk wanda ya yarda darty hands nashi ya taɓa jikina, ni kuwa sai na kwantar dashi a gadon asibiti kuma ya bar aikin sa kenan har gaban abada a gidan nan, bama a cikin gidan nan ba harma kasar baki daya saina lalata duk wani offer nashi na samun aiki" yay maganar cikin yarensu, wanda ya saka securities ɗin ja baya. Ko kallon inda Mecheal yake bai yi ba ya fita da kafansa, a ƙafa ya dinga yawata duk wurin daya masa. yana tafiya shi kaɗai a wani titi mai natsuwa, ba tare da Mecheal ba. Ahankali yaji wani sauti me sanyi ana furta.
“…ALLAH ya ce…”
muryar wani malami ce ke fita daga wani ƙaramin speaker. John ya tsaya cak ba tare da shiri ba, daga gefen titin kuma wani tsoho ne zaune a kujera
wayarsa a hannunsa yana sauraron wa’azi. Washe gari daya sake fita yana
zaune a café shi kaɗai sai Cup ɗin coffee a gabansa, Wanda bai kai ga sha ba, daga gefe dashi kuma wani matashi ke zaune. Wanda shi bai lura da John ba din ba, ya fitar da wayar sa ya kunna audio na karatun Al-Qur'ani. Sautin ya cika wurin a hankali bada ƙarfi ba, amma irin mai shiga zuciyar nan ne, wanda ya saka John ya ɗago kai kaɗan.
Duk da bai fahimci harshen ba amma
ya ji wata nutsuwa ta musamman.
Wani irin nutsuwar da bai saba da ita ba. Ya lumshe ido na ɗan lokaci kafin ya buɗe su a hankali. “Why does it feel like this…” ya furta a hankali. Haka dai John ya cinye satin yana saurarar ma ban banta ababuwa.
Ranar wata Juma’a da misalin sha biyu ya shirya suka fito shi da Mecheal, garin yi shiru sai motsin mutanen dake wucewa zuwa masallaci.
“Stop here.”
Ya faɗa a hankali wanda ya hakan yasa Mecheal ya ɗan kalleshi da mamaki…
amma bai ce komai ba ya tsaya har zuwa sanda John ya buɗe ƙofar motar
ya fito. Idanunsa suka sauka kan masallacin da ke gabansa, Mutane nata shiga a hankali, wasu cikin natsuwa
wasu cikin gaggawa. Daga ɗan nesa da wurin ya tsaya ba tare daya motsi ba.
Zuciyarsa na bugawa kaɗan ahankali.
“Just watch…” ya faɗa wa kansa.
Sai ya tsaya a gefe yana kallon su suna shiga. Wani tsoho ya wuce kusa da shi.
Ya tsaya kaɗan yana kallon John.
Sai ya yi murmushi. “Dan samari ya ba ka shiga ba?” ya tambaya cikin sauƙi.
John ya ɗan rikice tare da cewa “No… I’m just” Tsohon ya ɗaga hannu yace.
“Ka tsaya ka kalli yadda ake bautar UBANGIJI ma ibada ce idan zuciya na neman gaskiya.” gaban John ne ya sake faɗuwa amma bai ce komai ba, sema gefe da ƙofar masallacin daya samu ya zauna. Daga can cikin masallacin kuwa
Muryar liman
“Bismillah Rahmanir Rahim! Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu,Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillaha, famanyuddul fala hadiyala
waasshadu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kalah, wa asshahadu anna
muhammadan abduhu warasulu! ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum. Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah wattaƙullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum raƙiba,ya haiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asdaƙal hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar." Tun da aka dakko doguwar adda'ar ko mace hudubar zuciyar John tayi wani irin tsalle. Kafin ya dawo daga wannan tunanin ya sake tsinkayo muryan Malam liman yana ci gaba da faɗin.
“Ya ALLAH duk wanda zuciyarsa ke neman gaskiya!… ya ALLAH ka nuna masa hanya bisa tafarkin gaskiya da gaskiyarka...” Aka ci gaba da huduba akan masu neman hanyar gaskiya da gaskiya domin ranar gobe kiyama su rabauta. Kana aka ƙira sallar juma'a duk John na zaune daga gefe, sedai mutanen se sake karuwa suke wanda har seda ya sake komawa ta can baya sosai amma yanajin karatun sallar limamim, daga inda yake zaunen kansa a kasa yana sauraron komai amma bai
fahimci komai ba sosai…Se dai kalmar
“gaskiya” ta tsaya masa a rai ga kyakkyawan karatun dake fitowa cikin suratul _An nisa_ Har aka gabatar da sallar juma'a ɗin raka'a biyu. Aka sake wasu adda'oin masu ratsa zuciya.
Bayan an idar da sallar ne mutane suka fara fita. Har kuma lokacin John bai motsa ba, sema sake matso wa inda yake zaunen ɗazun da yayi, ganin mutanen da suka shimfida abin sallar su sun nade, wasu ma buhu ne suka shimfida. Wannan tsohon na ɗazun ya sake fitowa ganin John zaune har lokacin ya isa gabansa, “Sunanka?” ya tambaya John din cike da hikima da kamala. John ya ɗan ɗago kai ya kallesa.
“…Joseph.”
Tsohon ya ɗan yi murmushi me faɗi da kayatarwa yace. “ALLAH ya shiryar dakai John.” Cak John din kuya ya dakata daga shirin mimewar da yake shirin yi, bawai don ya saba jin irin wannan kalma ba. Cikin zuciyarsa ya tambayi.
“Me yasa kowa ke ce haka…?”
Tsohon ya kalleshi cikin nutsuwa, saboda yaga sauka da hawar mukwallatonsa, kai tsaye ya bashi amsa da.
“Saboda idan mutum ya tsaya a ƙofar gaskiya…toh yana dab da shiga ne.”
Daga haka dattijon ya tafi yabar John da tunani mai nauyi.
Ko da ya koma motarma wani shiru yayi daya saka Mecheal kallonsa ta madubi yace. “Boss… are you okay?” kamar ba zai tanka masa ba, dan kansa ma ya fitar ta woje kafin yana idanunsa ya lumshe yace.
“…I don’t think I’m the same anymore.”
Lokacin da John ke shigowa babban parlourn nasu babu kowa, sai iyaka
Madame Victoria dake tsaye tana kallon shi daga sama har kasa, tana kallon yadda yake tafiya, yadda yay wani shiru, yadda ya shigo kamar mara laka, Kai tsaye wayarta ta fidda ta saka ƙiran Mecheal.
“Where did he go today?”
Mecheal ya yi shiru kaɗan yaƙi cewa komai, don yana tsoron uban gidan nasa sosai. “Answer me.” ta sake faɗa a ɗan tsawace.
“…Masjid.”
Ya faɗa cikin tsinkewar zuciya. Wani irin mugun bugawa kirjin Madame Victoria yayi har tana kusan kwarewa tace.
“What Masjid…?” ta maimaita masjid din Idanunta nayin ɗan duhu.
Wayar ce ta zame daga hannunta ta faɗi ta fashe, ta nufi bangaren Papa da gudu tana ihu.
John yana isa bedroom nashi ya isa gaban madubi yana hargitse tulin sumar kansa da tayi tozon rakumi ta gaba, keyar kuma tayi shuwal shuwal haka ya tsaya a gaban madubin yana kallon kansa, sai dai abinda yake gani yanzu a fuskarsa ba wannan fuskar John din bace ta pilot, wannan din fuskar wani mutum yake gani daban, fuskar mutumin da yake shirin karya duniya domin soyayya. Ƙarfin Iko na Family, Family ɗin da suke kamar ba mutane bane na yau da kullum. Saboda su ne Cristina Dynasty. Iyaye masu iko, masu kuɗi, masu tasiri a duniya. Wanda suke da tarin mallakin ababuwa tun daga kan kamfanoni… jiragen sama… siyasa… Kuma abu ɗaya ne dokar su. Ba a taɓa auren wanda bai dace da sunan family nasu ba. Da baya ya koma ya zauna, kamar kuma wanda aka zabura ya mike ya soma hada kayansa domin tafiya Ethiopia. Yana son ganin Almaz. Yana son su sake tattaunawa game da YASMINE da feeling Islam da yake ji...
A lokacin da Madame Victoria ta isa bangaren Papa jikin sa kawai ta faɗa tana sake fasa wani sabon kukan, "Mun shiga uku sweetheart wllh in ba muyi wani abu akan Joseph ba muna da da rasa shi.” tallafarta yayi seda ta gama kukan ta ya share mata kana yake tambayar ta abinda ke faruwa?, nan ta shiga sanar masa da komai, wanda tace a gobe take son a tada maganar aurensa da Deepika bayan ta nuna masa har pictures din nan data tura a wayar wannan security din, take a lokacin Papa ya kira Patriarch mahaifinsa kenan shi kakan John din kuma ya sanar dashi halin da ake ciki, cikin gaggawa yace shi ma yana tafe zuwa gobe. Daga nan ya kira Daddyn India wato Daddyn Deepika ya sanar dashi ya gayyato friends nashi za'a yi baikon John da Deepika, wanda ya saka deepika dake tare da mahaifinta da mahaifiyarka buga ihu tayo bangaren nasu a guje. Kai tsaye bangaren John ta nufa daya mance be rufe kofar bedroom nashi ba, isarta yayi daidai da fitowarsa daga wanka bathrobe sanye a jikinsa Iya gwiwwa fara tas me naski naskin da yake ɗan sirka blue, tana isa babu tsammani yaji ta rungume shi tayi saman gado dashi suka fara juyi, ya bude baki zai yi magana ta kuwa hade bakin nasu ma ta fara bashi wani irin deep kissing ɗin da zai yi wahala in kai cikakken lafiyayye ne ka gaza ke tare tarkon, bare kuma shi da hakan ba komai bane gare su, se dai duk da haka ALLAH ya saka masa wani irin tsentsenin abun har se lokacin da gama tabbatarma da kansa cewar ya gama mallakar mace, Se gashi Yasmine a karon farko itace ta soma fara karya wannan alkadarin nashi. Ita da kanta take kissing nashi tana sake juyi dashi a saman faffadan gadonsa da duk ta gama yamusewa. Jin hannunta na yin inda ba'a aike ta bane ya saka dan sauran hankalin John dawowa ya figeta daga jikinsa yana tsaida kan diga diganta ya ɗauke ta da zafafan maruka a jere har uku kyawawa. Ya jata kiiiiii Kamar wata kayan wanki ya zubar a bakin kofar ya mayar ya rufe.
Washegari ƙarfe duk yanda John yaso barin gidan be sama ba, don sun ce masa ya tsaya masu baikon jelly ne zasu zo, kuma yasan dole ze dashi tun da kamar al'adan sune hakan. Ƙarfe goma na dare kowa ya gama hallara a babban hall na gidan nasu, gashi an huhhura huta wa abin bautar su ya sakawa wannan aure albarka, duk wasu friends na kusa dana nesa sun gama hallara. Saboda an san baya son kide kide yasa ka babu kidan da yawa, abu na farkon daya fara bashi mamaki ne shi ne ganin manyan friends nashi a wurin, musamman ma dai babban amininsa Joshua. Amma se ya maze suma duk sukayi fuska. Bayan an zaune wurin ya dauki shiru sega shigowar wasu manyan mata biyu sun sako deepika tsakiyansu wacce fuskar ta ke rufe, don har yanzu bata sabe ba daga uban marukan data amsa daga John ɗin. Sedai taki fadin ma kowa abinda ya faru tace zamewa tayi a bayi. Ana shigo da ita cikin babban hall din aka saki wasu haske…Mahaifin John ya zauna cikin girma da iko, Daddyn India ma ya zaune deepika na daga kafafun John, Kafin Mahaifiyarsa Madame Victoria dake sanye cikin wata irin shiga ta mike, ta amshi zobe daga hannun Patriarch dare da wani abu nade ta isa ga Papan ta mika masa. Wanda yayi gyaran murya ya amsa ya ce.
“An gama shirya komai.” Yay maganar yana mikawa John zoben yace ya saka ma deepika ita ma daidai nan Lady Rebecca ke mika mata natan.
“Me ake nufi?”
Mahaifiyarsa ta yi murmushi mai sanyi.
“Za ka auri Deepika ne baiko za kuyi.”
Ai a wani irin tsiyace ya mike yana fatali da wutar dake gabansa me hasken da suka sa mata launi yace.
“Ƙarya ne!!!....”
Kalmar ta fito daga bakin John cikin ihu da tsananin fusatar daya saka duka hall din ɗauka. Papa ne ya mike tsayen shi ma a fusace yace.
“Me ka ce?”
“Ba zan aure ta ba.”
Ya bashi amsa kai tsaye ba tare da shakkun komai ba.
“A kan wanne dalili ?”
Papan da Mom suka furta kusan tare.
John ya kalli cikin idanuwansu su duka biyun kafin kai tsaye.
“Saboda Yas-mine.”
Gaba daya jin saukar kalmar sukayi kamar gashewar bam. Kowa a wurin babu wanda be girgiza ko ya gigice ba. Da ƙarfi mahaifinsa ya buga masa wata uwar tsawar da tin da yazo duniyar ko me kama da irinta be taɓa masa ba yace.
“HE DISGRACED US!”
Mahaifinsa yay Maganar yana buga tebur din da yake zaune da ƙarfi.
Mahaifiyarsa kuka kai tsaye kuka ta sanya tana fadin.
“Mun rasa ɗa… ba shi bane wannan!”
Amma shi John bai damu ba kuma ko a jikinsa sema kuwa da yayi ya soma tafiya yana me sake ce dasu.
“Zan aure ta.”
_Hhhhhhhh shi yasa nake ce muku duk wanda ya bari aka yi wannan zazzafar tafiyar ba tare dashi ba to ya bar dadi wllh. _
# JANNERH +IBRAHIMUL KHALEEL
# YASMINE +JOHN
# DEEPIKA JOSEPH
# X_ESHIKA JOSEPH
# AKA AMMEY LAYLERH ✍️
*BY AMMEY LAYLERH ✍️
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 22
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
ꨄ Gaba ɗaya a wannan daren mutane da yawa basu runtsa ba, daren da suka ga ya ƙara musu zurfi ba. Madame Victoria kuwa ko rufe ido kasawa tayi saboda tsananin tashin hankalin da take a ciki wanda tunaninta ya kasa samun nutsuwa wuri guda. “Not my son…” ta faɗa da ƙarfi tana ɗaukar wayar ta ta saka kira, “Arrange emergency meeting with the families. Tonight or tomorrow morning. I don’t care.” Ta katse kiran da tsananin fushi. “Wannan aure se ya daru.” A wannan lokaci shi kuwa JOHN ya na zaune a gefen gadonsa wayarsa riƙe a hannunsa yana dan jujjuyata sega ƙiran Mecheal ya shigo masa.
Muryar Mecheal na rawa kaɗan yace.
“Boss… akwai sabon update.”
John ya ɗan lumshe ido yana furzar da wani huci yace. “What now?”
“Family meeting has been called. Your mother… and Yasmine’s family.”
Da kamar alamar tambaya JOHN ɗin yace.
“Meeting?”
“Yes Boss. It’s about… marriage arrangement.” Mecheal ya sake bashi cikakken tabbaci daga cikin wayar, wanda ya saka take idanun John suka yi duhu nan take tare da yanke kiran.
A tsakiyar ɗakin ya mike ya ɗan fara zagawa yana fitar da hucin wani numfashi mai nauyi. “Marriage…” ya sake maimaita kalmar, Kafin wata irin dariya mai ɗaci ya biyo baya.
“Without my permission?”
A can gidan su Yasmine kuwa babu wanda yasan abinda ke faruwa, ko nuna musu cewar kawunnan John sun zo masa da wata magana tun a daren, don haka yau ko shirin fita aiki be yiba, kwata kwata ma ko parlourn kasan be sakko ba se yanzun da yake fitowar. A natse Ambassador Kabeer Usman Maina ya zauna a kujerar parlourn cike da nutsuwa amma fuskarsa cike da damuwa. A natse ya ke sanarma da Mamy komai wacce tayi zuru abar tausayi, don abar a tausaya mata ce mana. Cikin sanyin murya amma a zahirin gaskiya cike take da tashin hankali tace. “Wannan magana ba karama ba ce…” Tayi maganar tana sauke ajiyar zuciya me nauyi sosai mara nutsuwa, Gyara zamansa Ambassador yayi ya ɗaga hannu yace. “I know.”
Sai ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce,
“Family of that boy… they are powerful. Too powerful.” Cikin kwantar da murya Mamy tace. “Amma ka duba labarin kawai ace Yasmine tana son wani…”
Sai da ya sauƙe numfashi.
“Love is not enough when politics enters.” daga haka suka ci gaba da tattaunawa akan maganar.
Mecheal na zaune tare da sauran Guards na gidan suka ga fitowan John, yayi saurin mikewa da nufin binsa amma kan ya karasa har ya figi motar da wani irin gudun tashin hankali bana wasa ba. Don haka Mecheal cike da tashin hankali ya mara masa baya a mota ta biyu. “Boss! Where are you going?!” Mecheal ɗaya ƙira shi a waya yake tambayar John ɗin, “To the source of this madness.” Suna zaune harkokin a parlourn suka jiyo karar mahaukacin Hong ɗin daya saka dukkan su mikewa tsaye babu shiri. Ko kafin suyi wani yunkuri ma sega security ɗaya ya fado parlourn yana cewa.
“Sir… wani mutum ne a waje duk da mun hana shi shigowa amma seda ya shigo.” tun kafin ya sake cewa komai sega shigowar John ya bayyana a parlourn gidan, directly kuma idonsa akan Ambassador Kabeer suka fara sauƙa. Wani ɗan shiru ne ya ratsa wurin na ɗan lokaci kafin cikin ƙarfin hali da dauriya Ambassador ya yi magana a hankali. “Mr. John… this is unexpected.”
John ya tsaya kai tsaye tare da bashi amsa da. “I came for one thing.”
Sai ya ɗan juyo kaɗan, kamar yana jin duk duniya na kallonsa. “I heard there is a marriage being arranged.” kafin ya fesar da wani dan numfashi ya ɗaga kansa ya kalla sama inda yake jin Yasmine na nan. “Between me…” ya ce a hankali. Ya kuma nuna kansa “and her.”
Daidai lokacin da Yasmine ke sakkowa amma bata karasa sakkowarba ta tsaya a bakin stairs tana kallonsa . Idanunsu