Advertisements
Chapter 30 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   30 / 31

87K to 90K   out of 91.1K words

maganar.“But stop destroying yourself over people who don’t even understand you.” kalaman da Ibraheem kamar suna shiga zuciyarsa sai dai bai ji zai amince musu. Mommah ce ta matso tana riƙe fuskarsa cikin tausayi ta ce.

“We miss you… The house is empty without you.” Wani irin zafi ne yaji ya taso masa daga ƙasan zuciyarsa, saboda duk yadda yake ƙoƙarin mantawa har yanzu akwai wani ɓangare nasa da ke kewar rayuwarsa ta baya. Rayuwar JOHN…Rayuwar ɗan gata… ɗan mension… ɗan da duniya ke kallon sa da tarin arziki da iko. Sai dai yanzu
shi ne IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL... Wanda a yanzun shi ne wani mutum na daban ɗin da yake neman nutsuwar addini… amma rayuwarsa na ƙara shiga cikin wani irin duhu. PAPA ne ya ɗan katse sa daga ƴar doguwar tunanin daya faɗa.

“Think about it son…”

Sai ya juya zai fita daga haka Madame Victoria na take masa baya cike da wani irin rashin kwarin zuciya dana jiki. Har ya taka zai fita sai kuma ya dakata ba tare da ya juyo ba yace.

“And one more thing…”

Wanda ya saka Ibraheem ɗago kansa,
Papan ya kallesa kafin yace cikin murya mai nauyi.

“Never destroy your soul trying to save someone who doesn’t want to be saved.”
Kalmar… wannan kalmar ta bugi zuciyar Ibraheem kai tsaye.Saboda Abu na farkon da zuciyarsa ta fara hasko masa shi ne fuskar Yasmine. Idon sa a kansu har suka ɓacema ganin sa gaba ɗaya.

JANNEERH
Zaune take a Islamiyya bayan an tashi karatu amma ita ta kasa tashi, Alƙur’ani ne riƙe a hannunta amma yau ko haruffan ma basa shiga cikin zuciyar ta yadda ya kamata. Tun jiya zuciyarta take wani irin bugawa wanda take jin kamar akwai wani abu mai nauyin dake tinkaro rayuwarta, sai dai bata san ko menene ba, ta kuma rasa miye ainihin abinda take ji ɗin. A hankali wasu matan aure biyun dake gefenta daga ɗan nesa kaɗan suka fara magana ƙasa-ƙasa suna kallonta, ba yadda zata gane ko ta ji ba wata daga cikinsu tace.

“Waccan ce ko?”

Da sauri ta gefen nata ta gyada kai tana cewa.

“Eh ita ce mana…”

Ɗan tsaki ɗayar tayi tana cewa.

“To ni wallahi bana ganin akwai namijin da zai iya zaman aure da ita indai waccan guzumar matar ce.”

“Why?”

Ɗayar ta tambaye, wani dan mele baki wacce da ganin ta dama bata sauki tayi, tana cewa.

“To ke Halimah in banda abunki dubi yacce kullum take cikin hijabi da karatu da wa’azi, alhalin mazan yanzun sam ba haka suke bukata daga mace ba, a wannan rayuwar da muke ciki mazanmu na aure sun fi bukata da son mace mai ɗan budaddan ido, ba wacce zata zame musu sumbum buƙumin ba....” wata uwar dariya suka saka wanda take duk kalaman nasu suka shiga kunnen JANNEERH. Sai dai ta sunkuyar da kanta kawai ne kafin ta sake jin sun kuma bushewa da dariya.

“To ni ma dai hakan na gani Naja don naji ance har yanzu babu wanda ya taɓa cewa yana son ta koda kare ne.”

“Hmmm Maybe akwai wata matsala a tare da ita ne Halimah…”

Zuciyar Jannerh ce taji ta sake kamuwa da wani irin rauni sosai, da tsananin tausayin kanta da kanta, amma duk da haka taƙi ɗago kai, saboda tasan wasu kalaman idan mutum ya tsaya kare kansa a kansu… zai rasa darajarsa ne kawai. To don me zata wani damu kanta ma akan kamalan da kullum suke zame mata kamar tuni ne a cikin rayuwarta, amma kuma duk sanda zata ji ɗin tana jin suna mata wani irin ciwo ne kamar bata taɓa jin nauyin kalaman ba sai yau ɗin. Sai dai yau a karo na farko yasa ta fara jin kamar ita ɗin daban ce da sauran mata, kamar akwai wani abu tare da ita da duniya bata fahimta ba.
A hankali ta mike tsaye zata wuce amma wata ta sake faɗar wata maganar da ya saka ƙafafunta suka tsaya cak kafin su soma wata irin rawar dari, wasu ruwan hawaye na kokarin ɓallo mata amma tana hana hakan ta komar da abinta tana shanyewa kamar kullum, kamar ko da yaushe. Sabo da maganar
Ummienta data tuna.

“Jinkiri ba yana nufin rashin dacewa bane…haka zalika a duk inda kika tsinta kanki to kuwa ki kasance mai toshe kunnuwanki, daga kalaman da zasu ringa shiga marasa tsarki da ma'anar ji”

A hankali ta lumshe idanunta kafin ta buɗe ta sauƙe a kansu, karon farko cikin rauninta zata taɓa mayar da martani akan ƙaddara da mutane ke kushe mata. Ga wani irin hasken da ya bayyana cikin idanunta. Haske mai cike da ƙaddara ta dasu.

“Wasu zukatan…ALLAH baya haɗasu da kowa ne sai wanda zai gane darajarsu…”

Daga haka ta juya ta fice zuciyarta na wani irin kuka mai zafi amma ta ciki wanda ido basa iya ganinsa. Kuka irin wanda ke gab da buɗe ƙofar wata ƙaddara mai girgiza rayuwa…

Ibrahimul khaleel....

Jingine yake daga jikin gadon su daga kasa, fitilar wajen kaɗai ce ke bada haske mai rauni na dum light. Gaba ɗaya tun bayan tafiyar PAPA da MOMMAH zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa. Maganganunsu ne kawai ke masa yawo cikin kansa kamar ana maimaita masa su ne.

'Come back home…The house is empty without you…!, Never destroy your soul trying to save someone who doesn’t want to be saved…”

Da sauri ya dafe kansa yana runtse idanunsa a bayyane yana mai furta Kalmar.

“Ya ALLAH…”

Ya furta cikin murya mai rauni kafin ya ɗora da faɗin.

“Kada ka mayar dani baya bayan ka nuna min haske…”

Sai yaji wasu hawaye masu zafi sun cika idanunsa, saboda a yau ya fara fahimtar cewa shiriya tana da tsada. Inda wani lokacin sai mutum ya rasa mutane ya rasa farin cikin sa ya kuma rasa komai ciki harda rayuwar da ya saba kafin ya samu ALLAH. A hankali ya ɗago idanunsa zuwa sama tare da hannayensa ya furta.

“Ko duniya gaba ɗaya zata guje ni… ba zan koma rayuwar JOHN dana bari ba.”
Kalmar ta fito daga bakinsa cikin yakini
muryarsa na rawa. Duk wannan abin da yake Yasmine na kwance ruf da ciki tana kallon hotunanta a waya.
Tun daga kama kan Party… club… da duk inda taga damar zuwa. Sai ta tuna yadda Ibraheem yake kallonta idan tana aikata wani abu mara kyau.
Wani irin kallo mai cike da ciwo ba tsana ba…sai dai kamar mutum ne da yake ganin wanda yake so yana nutsewa a hankali. Ɗan tsaki tayi ta ajiye wayar kasa kasa take cewa.

“Why is he making me feel guilty for being myself?”


*AUJARA JIGAWA*
Ƙofar Fada Babban Masallacin juma'a.

Mama Rukayya ce ke ta faman mita saboda ruwan famfo ya ɗauke, ita kuma
Aunty Amarya na nata surutun ne akan tsadar kayan miya.


JANNEERH tun bayan maganganun nan na jiya ta kasa samun sukuni, suna kawai ke mata yawo a rai.

'Maybe akwai matsala a tare da ita
Idan mace ta kai shekarunta babu aure akwai magana…'

Ta runtse idanunta da ƙarfi karo na farkon da taji kalaman mutane sun fara karya wani ɓangare nata. A hankali ta fito tsakar gidan ɗauke da bokitin ruwa zata wanke manyan hijjabanta a tsakar gidan. Ammma muryan mahaifinta ta katse mata tunani ta hanyar ambatar sunanta da yayi.

“HAFSAT…”

Da sauri ta juyo haka nan gabanta YA ɗan faɗi. mai cike da nutsuwa da kwarjini fuskarsa cike da hasken ibada… amma idanunsa ɗauke da wani irin zurfin tunani saurin sunkuyar da kanta tayi tana furta.

“Ina kwana Baffa…”

A hankali ya amsa yana kallonta sosai.
“Lafiya kalau… Ina son ganinki idan kin gama abinda kike... "

A take Mama Rukayya da Aunty Amarya suka kalli juna. Saboda BAFFA ba kasafai yake kiran Hafsat shi kaɗai ba.

A bayan gidan ƙarƙashin bishiyar mangwaro ta same shi, Iskar safiyar ranar na ɗan kaɗa hijabinta kaɗan.
Ita kuwa kanta a ƙasa cikin girmamawa ta zauna tana saɓunta gaisuwar nasu, amsata yayi kafin ya ɗan dubeta na wani lokaci yana kallonta, yana karanto irin damuwar dake shimfide saman fuskarta. Kallo yake mata, kallo irin na uba mai cike da fahimta. Kafin daga ƙarshe ya sauke numfashi a ɓoye kana yace.

“Kin san me yasa nake yawan kallonki da tausayawa Hafsat?”

A hankali ta girgiza masa kai alamar A Ahh, kafin a bayyanen tace.

“A’ah Baffa…”

Ɗan murmushi yayi mai ciwo yace.
“Saboda kina ɗauke da ƙaddarar da mutane basa fahimta.” zuciyarta taji ta mata wani irin bugu, a hankali ta ɗago idanunta tana kallar Mahaifin nata.

“Wasu mutanen idan ALLAH yana son su…baya barsu su samu komai da wuri.”
Wani shiru kawai JANNEERH tayi tana sauraron mahaifin nata kana ya ɗora da. “Kinga zinare? ba’a samunsa a saman ƙasa, sai an tona da wahala kafin a same shi.” Hawaye suka fara cika idanunta sai BAFFA ya ɗora da magana cikin nutsuwa. “Mutane zasu miki dariya saboda baki yi aure ba…Wasu zasu ce akwai matsala tare dake… wasu kuma zasu raina ƙaddararki saboda basu ga hikimar ALLAH ba.”
Nan take hawayen da take ta kokarin ɓoyewa suka zubo mata duk da wannan ɗin ba sabamun abu bane a wurinta.
BAFFA ya kalleta sosai kafin ya sake ce

“Hafsat…”

TA amsa da “Na’am Baffa…”
“Ki saurare ni da kyau ina son ki sani wata rana…ALLAH zai haɗaki da mutumin da zai sa ki manta dukkan hawayen da kika yi.” A hankali maganganunsa ke ratsa ko ina na jikinta kafin ya ɗora da fadin. “Amma kafin ranar ta zo…Dole sai ƙaddararki ta bi ta cikin DUHU.”Kalmar data bugi zuciyarta kenan kai tsaye sai taji wani irin sanyi da tsoro a lokaci guda.

“Baffa…”

Ya ɗaga hannu ya katseta ahankali ya ɗora da faɗin.

“Kada ki taɓa jin kin makara a rayuwa saboda baki yi aure ba, babban bala’i ba rashin aure bane Hafsat…Babban bala’i shi ne mace ta rasa mutuncinta saboda tana gudun kada ace ta makara.”
Hawayenta da take tarewa suka zubo mata. BAFFA ya miƙa hannu ya share mata hawaye kamar tana yarinya ƙarama. “Kuma ki sani…” Ya ɗan yi shiru kafin yace cikin murya mai nauyi.
“Duk macen da duniya ta kasa fahimta…sau da yawa tana ɗauke da ƙaddara mai girgiza rayuwa ne.” Nan take zuciyar Jannerh tayi wani irin bugawa mai ƙarfi. Har taji kamar bata jin iskar bishiyar mangwaron da suke ƙarƙashinta.

Daga can tsakar gida kuwa Mama Rukayya ce ke ta faman mita.

“To wallahi ni ban fahimci wannan yarinyar ba!, na fara kai wa bango, ya Ƴa kwaya ɗaya saboda san zuciya yasa taki fidda miji tayi aure saboda duniyanci ana mana wariyar launin fata uymmm?.” Tana wanke kayan miyar tana famar mitar nata.

Aunty Amarya ta ɗan taɓe baki tana mai ɗorawa da faɗin. “Yo taya ni gani dai Kullum cikin hijabi kamar wata ta gari ko zaɓaɓɓiyar da aka ce an zaɓa daga sama ba, Shegiya kana kallonta kasan babu namijin da zai iya jure irin wannan rayuwar.” Sadiya wacce take ƴa ta uku ga Aunty Amarya dake zaune gefe tana latsa waya ta bushe da dariya tana mai furta.

“To ai yanzu Mama maza basa son mace irinsu Aunty Hafsa shi yasa baa son mace ta fiye zurfi a karatun addini sosai, shi yasa Baffa yayi ta fadansa amma yabi ta bayan kunnena wllh.”

Mama Rukayya ta gyada kai da sauri tana amshewa da fadin.

“Wallahi kuwa! haka ne, Namiji ai yana son mai wayewa sosai ba irin su sukumbiya ba…” dariya suka fashe da ita gaba ɗaya daidai nan jannerh ke karasa shigowa tsakar gidan ɗin, cike da wani irin kwarin gwiwar fara maida martanin ga duk mutumin daya faɗa mata ba daidai ba, ko da ba da rashin kunya bane, ko da cike da hikima ne tama kanta alkawarin zata fara wannan yakin maganar koda bata iya ba zata koya. Saboda ta gama gajiya da jinyar ciwon dake a ɓoye. A hankali ta karasa shigowa cikin gidan ɗin daya saka su yin tsit, dadi da kari kuma yau ɗin sunga idanunta cike da wani irin ciwo mai zurfi. Ta kalli Mama Rukayya kai tsaye ta kira sunanta.

“Mama…”

Muryarta tayi magana mai cike da nutsuwa da kuma kamun kai.

“Shin mace bata da wani amfani a rayuwa ne sai aure?”

Duk shiru su kayi kafin Mama Rukayya ta taɓe baki tace.

“To ai idan ba aure ba me kuma?”

Wani irin murmushi JANNEERH tayi…
Murmushi mai ciwo.

“Kenan idan mace bata yi aure ba ta zama marar amfani kenan ku a wurinmu?” kaf ɗin su babu wanda ya bata amsa. Sai ta sake ɗago idanunta masu cike da wani kalan ɓoyayyan rauni kafin tace.

“Shin kun taɓa tunanin yadda kalamanku ke karya zuciyata ne?”

A karo na farko kenan da Mama Rukayya ta rasa bakin magana saboda yau muryar Jannerh bata asalin jannarh'r da suka saba ji bane.

“Wallahi wani lokacin…ni kaina bana fahimtar me yasa wasu aurarrakin ke jinkiri…” Hawaye suka ciko idonta Amma basu subo ba tace. “Amma hakan ba shi ke nufin ALLAH ya tsaneni ba?” Aunty Amarya ta ɗan saki baki saboda bata taɓa ganin JANNEERH tana magana daga zuciya haka ba.

“Kullum kuna kallona kamar ina da wani aibu…” Sai ta girgiza kai da ƙarfi tace. “Alhalin ni ma mace ce…ni ma ina jin ciwo…ina jin kaɗaici…” Kalmar ƙarshe ta fito daga bakinta da wani irin raunin da yasa ko zuciyar dutse sai ta tausaya mata. Sai kuma ta sharce hawayenta da sauri, ta dago Idanunta da suka canza wani irin haske ne mai cike da ƙarfi ya bayyana cikinsu.

“Amma duk da haka…Ba zan taɓa neman soyayya ta hanyar saɓawa ALLAH ba.”
Wani irin shiru ya rufe tsakar gidan gaba daya kafin ta ci gaba da magana.
“Idan ƙaddarata tana zuwa a hankali…to zan jirata cikin aminci da mutunci.”
Har ta juya zata shige ta dakata tace.
“Amma wata rana zaku gane cewa ba kowanne jinkiri bane rashin dacewa…”

TA wuce ta barsu cikin wani irin shiru mai nauyi. Gaba ɗaya jannerh a daren wannan ranar gaza runtsawa tayi, daga bangaren Ibrahim khalil ma hakan ce ke faruwa a wurinsa, Dukansu suna kallon sama kowannensu cikin wani irin duhu. Cikin irin shigen ƙaddara ɗaya gare su wacce ke jan rayuwarsu zuwa hanya ɗaya a hankali. Hanyar da zata haɗa Royalty… da kuma Love…wanda idan suka hade zai zama kamar Love Mystery kenan. Sai dai kafin wannan ranar ta zo dole sai zukata sun sake takura da jin cewar kamar sun gaza ne.

_LAGOS_
*IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL *

IBRAHEEM tsaye yake bakin balcony ɗin gidan yana kallon yadda ruwa ke sauƙa ahankali. Rigar jikinsa ta jike kaɗan saboda feshin ruwan dake ɗan fesowa amma ko motsi bai yi ba, hasali ma tunanin rayuwarsa kawai yake.
Tun daga JOHN… har zuwa IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL. Wani irin murmushin ciwo yayi ahankali yana furta. “Rayuwa kenan…”

“Mutum zai iya mallakar komai amma kuma ya rasa nutsuwar zuciya.”
Ya tuna mansion ɗinsu, ya tuna Papansa, ya tuna Mother Ya tuna rayuwar da yake ciki kafin ya musulunta. Rayuwar party… mata… kuɗi… shaye-shaye… rayuwar da mutane ke kallo suce perfect life.
Sai ya lumshe idanunsa yana sake maimaita kalmar Perfect?… kansa ya dafe domin duk waɗan nan ababuwan babu abinda yake aikatawa. Domin duk cikin hayaniyar rayuwar… zuciyarsa ta kasance babu komai a ciki sai Duhu kawai. Sai bayan kuma da ya gano ALLAH…kana ya fara jin kamar yana numfashi, amma yanzu kuma shin me yasa zuciyarsa ke sake jin wani irin duhu?. Yasmine kawai idan ya tuna sunan wani irin ciwo ne ke ratsa shi. Sakamakon da da idan ya tuna sunan yake jin zuciyarsa kamar ana wanke masa ita da alkausara ne. Tun baya jin gajiya har yanzun yake jin ya fara gajiya. Gajiyar yaƙar zuciyar mutum da baya son canza wa a hankali ya ɗaga kansa sama. “Ya ALLAH…” ya furta muryarsa tayi rauni sosai.

“Idan akwai alkhairi a rayuwa ta kawo min shi cikin sauƙi…” Sai kuma ya ɗan yi shiru karon farko ba tare da ya shirya ba wani suna ya fito daga cikin tsakiyar
zuciyarsa.....

“Who is Hafsat…?”

Ya furta gabansa na faduwa cike kuma da mamaki saboda bai taɓa sanin wata Hafsat ba bai kuma taɓa haɗuwa da ita ba, amma me yasa zuciyarsa ta ambaci sunan?...


Cikin sati biyun da su Ibrahim suka sake yi da Yasmine ya ganoma kansa guma guman ababuwan da bai masan da mai zai musaltasu ba. Duk lokacin da zai yi mata wata magana akan gyara game da rayuwarta, sai tace ita ya bari yana takura rayuwarta ne. Ga kuma wani mayen zazzafan zazzabin dake takura rayuwarta, wanda bayan ya kira wani likita gwajin farko yace tana dauke da cikin One Months ne. Wanda gaba daya ta bi ta ɗaga hankalinta akan cewar ita ba zata taɓa haife wannan cikin ba sai dai a zubar. Idanunsa ya dan lumshe ahankali muryan sa ba ta fita sosai yake tambayar kansa mai yasa matsalolin ke neman fin kafin sane?, mai yasa ababuwan ke nemar masa yawa ne?, mai ya saka ya fara jin kokonto akan kansa addinin Musuluncin ma?, mai yasa haka addinin su nasu su yake kamar baya da alfarma baya da wani sauki ko ramgwame?. Mannuwar da yaji tayi da jikin sane ya saka shi sakin
wani wawan ajiyar zuciya yayi, a ransa yana yin addu'ar ALLAH yasa komai ne ya kusan zuwa ƙarshe. A hankali ya juyo da ita yana zuba mata janyayyun idanunsa da su kayi laushi sosai, fuskanta ya dago yana furta "Why Yas-mine mai yasa kike ƙoƙarin karya kwarin zuciyana?".

Kwacewa tayi daga jikin nasa tana bin sa da wani irin kallon kai mai yasa gaba daya a rayuwa baka da komai sai magana akan addini addini addini dai?, wani irin rauni ne ya ziyarci zuciyarsa mai tafe da fara sarewa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yayin da al'amura ke sake zuwa suna wucewa,wasu masu dadi wasun kuma kishiyar haka,yayin da a ɓangaren family na John sosai rayuwarsu ta sake kunci musamman dai Madame Victoria, inda zuwa yanzun an samu kimanin watanni uku da auren Ibraheem da kuma Yasmine sai

30 / 31