Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
amsawa da.
“Domin zuciya idan ta fara gane Mahaliccinta… Komai yana canzawa fara canzawane daga yadda aka san shi.”
Wani shiru John yayi kafin ya jefa masa tambaya cikin rawar murya ya ce.
“But what if I’m wrong?”
Wani ɗan murmushi Dattijon ya yi yana sake bashi amsa da.
“Saboda da duk mutumin da yake neman gaskiya da zuciya mai tsabta… ALLAH baya taɓa barinsa cikin duhu.”
“DUHU?…”
John ya maimaita kalmar a hankali kamar wanda wani abu ya tsaya masa a rai. Kansa ya gyada masa alamar kwarai kuwa yana ci gaba da faɗin.
“Wasu duhun tsoro ne. Wasu kuma duhun zuciya ne, sai dai mafi haɗarin shi ne duhun da mutum yake rayuwa a ciki alhali yana tunanin yana cikin haske ne.” Wani irin sanyi John yaji kamar yana ratsashi, Kamar kalaman suna warware wani abu ne a ransa.
Ya ɗago idanunsa a hankali bayan ya kalla mutumin yace.
“If I choose this path…”
Ya haɗiye wani yawu tare da sake furta.
“…everything in my life will change.”
Dattijon ya sake gyada masa da bashi amsa da
“Eh.”
Wani shiru ya biyo bayan hakan, kafin mutumin ɗora da maganarsa cikin murya mai cike da nutsuwa.
“Amma ba zaka rasa kanka ba…”
Ya ɗora hannunsa a ƙirjin John yace.
“Zaka same shi.”
Idanun John suka cika da ruwan hawayen da bai san ko na miye ba nan take, numfashinsa kuma ya nemi ɗan rikicewa. Duk kalaman da yake ta gudu daga gare amma gasu yau suna shiga zuciyarsa kai tsaye cikin sauƙi ba tare da yaƙi ba. Idanunsa ya rufe da ɗan ƙarfi yana dafe zuciyarsa cikin raunin murya yace.
“Why am I crying…”
Dattijon ya yi murmushi idonsa zube akan John din yace.
“Saboda zuciyarka tana farkawa ne.”
Kalaman da suka sake karya wani abu a tare da John kenan gaba ɗaya. Ya buɗe idanunsa da sauri yana kallon dattijon.
“What do I do…?”
Dattijon ya ɗan yi shiru kafin ya ce.
“Ka furta abin da zuciyarka ta riga ta gaskata.” Bugun zuciyar John ya ƙaru
Lips ɗinsa suka soma rawa, Idanunsa cike da hawaye. Dattijon ya ɗan janyo shi jikinsa a hankali tare da soma furta kalmar shahada...
“ASHHADU AN LA ILAHA ILLALLAH !.WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH …”
Wani saurin dafe ƙirjinsa John yayi kamar zuciyarsa zata fito woje.
Ga masallacin da ya yi wani irin shiru…
amma ba shiru na yau da kullum ba, A Ahh shiru ne irin mai cike da tsarki mai kuma sama zuciya nutsuwa, amma a lokaci guda yana tare da tsoro. Ya haɗe
hannayensa wuri guda kamar wanda ya zo neman wani abu da ya wuce duniya.
Yana zaune gaban babban malami dake zaune yana fuskantarsa. Fuskar sa cike da natsuwa idanunsa na ɗauke da hikima wanda ya sa John sake kallonsa da zurfi.
“Ka shirya?”
Malamin ya sake tambayarsa a hankali.
Numfashin John ya ɗan rikice yana sake kallon ƙasa zuciyarsa na hasko masa hotunan rayuwarsa na baya, duk
abinda ya taɓa sani, duk abinda ya taɓa yi. Sai ya ɗaga kansa Idanunsa har sun canza launinsu suna cike da tsoro amma suna ɗauke da haske a cikinsu.
“Na shirya…”
Malamin ya ɗan gyada kai yana me furta. “Ka sani wannan hanya ba wasa bace,” ya faɗa a hankali, “amma ita ce hanya ta gaskiya.” Zuciyar naci gaba da bugawa da ƙarfi kamar zata fito waje.
Kamar wani abu na jan shi baya, kamar
tsoron rasa komai tsoron canji da
tsoron sabuwar rayuwar da bai sani ba.
Hannunsa dake rawa ya matse ƙasa sosai wanda ya saka malamin ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa.
“Kar ka ji tsoro ALLAH yana tare da wanda ya zo gare shi.” ya faɗa a natse cikin sanyi kuma. Kalmar ta shiga zuciyarsa wani irin sanyi ya ratsa shi.
Hawaye suka sake taruwa a idanunsa yana buɗe bakin sa a karon farkon da yaji ya masa nauyi ya kama kalmar da yaji ya Malamin ya faɗi cikin kusan sarkewar murya yace.
“ASHHADU… AN LA ILAHA ILLALLAH …” Se ɗan dakata sakamakon muryan daya kusa sarkewa. Wanda Malamin ya tallafoshi yana sake nanata masa kalmar gaban.
“WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH …”
Da wani irin kwarin gwiwa me cike da tabbaci da kuma zuciya ɗaya john ya sake kama kalmar gaban yana maimaita kamar haka.
“WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH!!!.”
Wani kalan shiru ne ya mamaye wurin, irin shirun nan ne mai cike da rahama.
Wasu hawaye suka zubo daga idanun John, ba na baƙin ciki ba, na samun wani abu da bai taɓa tunanin samu ba.
Malamin ya kalle shi cike da murmushi mai cike da alfahari yace.
“Daga yau…”
Sai ya ɗan dakata zuciyarsa na sake bashi kwarin gwiwwar aiwatar da cewan tabbas wannan suna shine mafi dacewa ga JOHN ɗin, domin da shi yafi chanchanta.
“Kai ba JOHN bane!…”
Wanda ya saka zuciyar John ɗin wani irin bugawa kamar duniya ta tsaya.
Malamin ya sake kallar Idanun John din yaci gaba da fadin.
“Kai IBRAHIMUL- KHALILU NEEEE...
Sunanka… IBRAHEEM…KHALEEL!”
Kalmar data sauƙa a cikin zuciyar John da wani irin zafi da kuma sanyin samun salama da nutsuwa, ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana jin kamar an cire masa wani nauyi ne da ya daɗe yana ɗauke da shi. Kafin a hankali ya shiga maimaita sunan a cikin zuciyarsa.
_IBRAHEEM? IBRAHIMUL KHALEEL…_
Ahankali sunan ya sake amsawa cikin zuciyarsa kamar wani abu da ya daɗe yana nema amma bai taɓa sani ba. Wani irin sanyi mai gauraye da nauyin hawaye ya mamaye shi, yayin da yake jin kamar rayuwarsa gaba ɗaya tana sauyawa a wannan lokaci guda.
Malamin ya zuba masa ido cikin nutsuwa kafin ya furta a hankali.
“Ka san me yasa zuciyarka take jin tsoro yanzu?”
IBRAHEEM ya ɗan girgiza kai alamar a’a.
“Saboda rai idan zai bar duhu zuwa haske… sai ya ji kamar yana rasa wani ɓangare na kansa ne.”
Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin
malamin ya miƙe a hankali yana nuna masa wata ƙofa daga can gefe.
“Zo tare da ni.”
Ba tare da gardama ba IBRAHEEM ya miƙe yana binsa. Ahankali suke tafiya cikin harabar masallacin yayin da sassanyar iska ke bugun fuskarsa, duk mutanen da suke wucewa suna kallonsa da murmushi irin na ƴan’uwa, alhali babu wanda ya san shi, wannan kaɗai ya sake karya wani abu a zuciyarsa.
“Why are they smiling at me like that…?”
Ya tambaya cikin raunanniyar murya,
Malamin ya ɗan yi murmushi.
“Saboda daga yau kai ɗan’uwansu ne musulmi”
Kalaman suka sake ratsashi kai tsaye har suka ƙarasa wajen alwala.
IBRAHEEM ya tsaya yana kallon ruwan dake gudana daga famfon kamar wanda bai taɓa ganin ruwa ba a rayuwarsa. Wani irin nutsuwa ce kawai yake ji tana sake kama sa yake kallon
malamin daya buɗe famfon a hankali sannan ya ce.
“Mutane da yawa suna tsammanin musulunci kalmomi ne kawai…”
Ya ɗan ɗebo ruwan hannunsa.
“Amma musulunci dawowa ne zuwa ga ALLAH.”
Sai ya zuba ruwan a tafin hannun IBRAHEEM. Nan take wani irin sanyi ya ratsa jikinsa har cikin zuciya.
“Ka wanke hannunka…”
Malamin ya faɗa cikin tausasawa.
“…domin akwai abubuwan da suka taɓa rayuwarka da bazaka sake komawa gare su ba.”
IBRAHEEM ya bi umarnin cikin nutsuwa, idanunsa na kallon yadda ruwan ke zuba daga hannunsa zuwa ƙasa.
“Ka kurkure bakinka domin daga yau zaka fara furta kalaman da suka fi dukiyar da abinda ke cikinta daraja.”
Hawayen dake idanun IBRAHEEM suka sake taruwa sosai.
“Ka wanke fuskarka…”
Sai ya ɗan dakata kafin ya ƙarasa da cewa.
“Domin akwai hasken da ALLAH yake sanyawa a fuskar bayinsa idan suka neme shi da gaskiya.”
A hankali ruwa ya soma gangaro a fuskar IBRAHEEM yayin da yaji kamar numfashinsa ke rawa. Sake kama John yayi suka nufi wani ƙebantaccen wuri, wani matashin balarabe ya nuna ma John yana faɗa masa ya musulumta ne, yaje da shi yayi wankan shiga addinin Musulunci. Shi kuma ya koma inda ya baro, sun jima sosai kafin wannan matashin ya dawo tare da John.
“Alhamdulillah daga yau duk zunuban baya ALLAH ya kankare maka su, ka zama kamar jariri sabon haihuwa Alhamdulillah ya rabb.”
Ahankali aka soma kiran sallah me shiga zuciya.
“Allahu Akbar! Allahu Akbar!! …”
Wani lumshe idonsa IBRAHEEM yayi yana jin wani kwanciyar hankali, nan
Masallacin da mutanen cikinsa suka
sake tarbar sa…
Wani dattijo ya yi masa murmushi dake kusa da Babban Malamin nan ya mika masa hannu tare da furta.
“Assalamu alaikum.”
IBRAHIMUL KHALEEL ya ɗan tsaya kalmar ta tsaya masa a rai don jin yacce kalmar ta so masa kamar sabuwa…
“Wa alaikumus salam,”
Ya amsa a hankali da muryar da ba ta da ƙarfi sosai
Ahankali muryan wani yaro dake karanta “Ayatul Kursiyyu…” da murya me nutsuwa yaja hankalin IBRAHEEM.
Kalmar ta ratsa shi ga wani irin sanyin da yaji ya shiga jikin sa, Sai ya lumshe idanunsa a ransa yana furta kalmar.
_Shin zan iya zama kamar su…?_ ya tambayi kansa, yana tsaka da wannan tunanin wannan Babban malamin ya katse shi, ya kalle shi yace “Ka na kallon duk yacce nayi daga yau haka zaka yi” Ibraheem ya gyada masa kai yana kallon yadda yake motsi… Shi ma ya shiga ƙoƙarin kwaikwayon duk yacce yayi din. Tun daga kan Ruku'u... Sujjada… tare da duk wani motsi
kamar sabon abu ne a gare shi.
A lokacin da goshinsa ya taɓa ƙasa yaji zuciyarsa na samun nutsuwa tare da
wani irin sanyi, wanda bai taɓa ji ba a rayuwarsa. Bayan sun idar suka zauna a ƙasa numfashin Ibraheem na tafiya a hankali.
“Yaya ka ji?”
Malamin ya tambaya. Ibraheem ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce.
“Kamar… na sauke wani abu mai nauyi.”
Malamin ya jinjina kai yana kallon sa cike da nutsuwa da ƙauna.
Ibraheem ya buɗe idanunsa a hankali yana jin yadda duniyarsa ta yanzu ta bambanta data baya. Yana jin kamar an wanke duk wani duhun da ya tara cikin zuciyarsa shekara da shekaru.
Dattijon ya ɗora hannu a kafaɗarsa da murya mai sanyi yace.
“Ka zo da sunan John… Ka tafi da sunan IBRAHEEMUL KHALEEL sunan da ALLAH ke son yaji an ambata .”
*To fa jama’a, Yasmine za ta iya karɓar wannan gaskiyar ne? Ko kuwa wannan shine ƙarshen soyayyarsu?*
*BY AMMEY LAYLERH ✍️
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 25
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
Two Months later.
ꨄ Ƙaton jirgin private jet ɗin daya taso daga kasar Saudi Arabia yayi dirar mikiya a garin Lagos da misalin goma da rabi na dare. A wani irin natse
fuskar mutumin da ya fito daga cikin jirgin ɗauke da farin jalabiya mai sauƙi da ɗan hularsa a kansa, ta fi komai ɗaukar hankali. John kenan wanda yake amsa sunan _IBRAHEEMUL KHALEEL_ Cike da wata irin nutsuwa yake takunsa
irin wacce ba’a taɓa gani tattare da shi ba. Babu hayaniyar bodyguards ɗinsa kamar da, babu ɗaga murya, babu girman kai irin na tsohon JOHN.
Sai dai wani irin kwarjini mai cike da salama me ɗauke da wata irin kamewar kai. Wani ɗan ƙaramin tasbaha ne riƙe a hannunsa yayin da lips ɗinsa ke motsi a hankali kamar mai ambaton ALLAH.
Cab ya tara zuwa gida don babu wanda yasan da zuwan sa bare azo tarbansa, tun da taxi ɗin ta fara tafiya Ibrahimul khaleel ya koma ya jingina da kujerar motar yana tasbihi a cikin zuciyarsa, yana kuma hasaso garin daya baro ba don ya so ba sai dan saboda cilastawan Dattijon Arziki Sheik IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL WAXER. Bayan motar ta tsaya a bakin mension nasu John yaja ajiyar zuciyar da bai san ko ta menene ita ba. A hankali driver ɗin ya zagayo ya buɗe masa ƙofar motar. Fararen kyawawan ƙafafunsa ne suka fara bayyana, wanda suke sanye cikin wasu luxury leather sandals masu taushi. Kafin daga bisani shi kansa ya fito gaba dayansa, tsaye kawai yayi a wurin idanunsa a lumshe kamar mai jin daɗin wani abu da duniya bata fahimta ba. Ahankali ahankali kuma yana jan wani ɗan ƙaramin tasbaha dake rike
a hannunsa. Lips ɗinsa kuma na motsi a hankali suna me ambatar.
“Subhanallah!…” ƙasa-ƙasa Mecheal ne ya fara lura da tsaiwar uban gidan nasa, don da da farko ma be gane shi bane kwata kwata, se daga baya aikuwa yayo wurinsa cike da wani irin murna da farin ciki yana ambatar.
_Boss!,Voss!!._
Sai dai ya ƙame ƙam a inda yake ne sakamakon dago kan da John ɗin yayi, inda Mecheal ke kallon zallar tsananin nutsuwar dake tattare da John ɗin kaɗai ta isa razana mutum. A hankali ya ɗaga kansa yana ci gaba da kallon katafaren gidan daya taɓa ɗauka a matsayin duniya baki ɗaya, wanda sai yanzu yake jin duk wannan rayuwar bata taɓa cika masa zuciya ba can dama. Cikin nutsuwa yaci gaba da takawa zuwa cikin ainihin gidan bayan ya ɗaga ma Mecheal tare ma da saurin security na gidan hannu. Wanda duk suma suka yi mutuwar tsayen irin ta Mecheal, a ransu suna ayyana me ya haɗa uban gida da kalan wannan sutura ɗin?. Sanya kansa tsakiyar parlournsu yayi daidai lokacin da Madame Victoria ke sakkowa daga samanta zuwa parlourn. Se dai itama ta kame kam ne gabanta na wani irin yankewa ya faɗi rass.
“JOHN!,JOSEPH!! MY LOVE!!!”
Ta kira sunan nashi cikin tsananin tashin hankali tana ƙarasawa gabansa tana binsa da wani irin kallonsa. Tun daga kan fararen kayan dake jikinsa, tasbahar dake hannunsa, sai kuma idanunsa.. Idanun nan da suka rasa hayaniyar JOHN ɗin data sani ta baya da ihu idan an ɓata masa ransa.
“Mom!…”
Ya furta cikin taushin muryan daya saka
Madame Victoria haɗiye wani yawu.
“Me… meke faruwa da kai…?”
“I’m asking you a question, give me John’s answer.” Ta sake faɗa a tsawace tana sake matsowa kusa dashi sosai.
Wani ɓata fuska Ibraheem yayi kafin a hankali ya furta.
“Not JOHN!, IBRAHEEM!! IBRAHIMUL KHALEEL!!!...”
Wani irin ƙara Madame Victoria ta saki tana ja da baya, tare da sakin glass cup ɗin dake hannunta ya faɗi ƙasa ya
tarwatse a wurin ya baje. A dai-dai kuma lokacin Mr. Jeff Deefer ya fito daga saman stairs ɗin gidan cikin sauri shima, don yaji karar madame Victoria ɗin, don haka ya sakko cikin sassarfa yana me tambayar.
“Victoria meke far...
Se dai shima kalaman nasa sun makale masa ne sakamakon ido biyun da yayi da John ɗin. Wani irin canzawa shima tashi fuskar tayi kamar wanda yaga fatalwa. Idanunsa sauƙa kan hannun IBRAHEEM dake rike da tasbaha.
“JO... JOSEPH!!!....”
Ya furta sunan cikin wata irin murya mai cike da ruɗani da tsoro.
Da nutsuwa John ya ɗago idanunsa gare shi, bai ma fahimci dalilin wannan firgicin ba, sai dai duk da hakan cikin ƙarfi da kwanciyar hankali ya gyara tsayuwarsa sannan ya furta.
“IBRAHEEMUL KHALEEL... not Joseph, Papa....”
Kamar an danna ma Papa wani maɓallin tashin hankali haka yaji, ya ɗan shiga jan Jikinsa baya kamar wanda ƙafafunsa suka kasa ɗaukar nauyin jikinsa. Idanunsa suka ƙara buɗewa cikin tsantsar firgici, leɓɓansa na rawa tamkar wanda aka zarewa rai yake sake nanata kalmar _IBRAHIMUL KHALEEL?... _ Saurin damƙe railing ɗin staircase ɗin yayi da ƙarfi saboda firgicin daya ratsashi.
“IBRAHEEMUL... KHALEEL...?”
Wannan karon kam ya maimaita sunan a bayyanen daya saka ƙafarsa zamewa gaba ɗaya yayi baya kamar zai faɗi saboda gigicewa, domin jin sunan nan kadai yay jinsa yay kamar daidai yake da rabuwar numfashinsa. Da sauri Jelly dake sakkowa daga staircase ɗin benen ta hangi yadda yake tangal-tangal kamar zai zube ƙasa.
“Papa!!”
Ta faɗa cikin firgici tana saurin ƙarasa isowa da gudu ta tare shi kafin ya faɗi, hannayenta na riƙe da shi sosai take tambayar.
“Papa lafiya? Me yake faruwa?”
Take tambayarsa cikin tashin hankali, amma Papa ko kallonta bai yi ba sai idanunsa daya kafe akan John tamkar wanda yake kallon wani abu daya gagare shi tun da jimawa. Numfashinsa ya fara fita da ƙarfi wani gumi na keto masa a goshinsa na tsantsan tashin hankali da rudun daya shiga. Shi kuwa John tsayawa yay cak cike da mamaki, idanunsa na yawo tsakanin Madame Victoria da Papan nasu. Saboda shi kansa bai fahimci dalilin da yasa sunan “IBRAHEEMUL KHALEEL” ɗin ya firgita su har haka ba.
“Wa ya baka wannan sunan?! And ama ina uban ya ka hadu dashi da yaja mana ra'ayinka akan wani can addininsu na karya?....”
Ya tambaya cikin tsananin firici da wani sabon tashin hankalin da yake jin kamar yana dirar masa. IBRAHEEM ya ɗan haɗe girarsa jin suna nemar taɓa addininsa, addinin da yake da cikakken tabbaci da kuma yakinin cewa shi ne addinin gaskiya.
“Wani babban malami ne a Saudi Arabia…”
Ai tun kan ya ƙarasa furta wa Mr. Jeef Deefer dake jingina da jikin jelly yay wata bahaguwar mikewa da ƙarfi yana sake jefa masa tambayar.
“Ka ce a wacce ƙasa ka musulunta?”
“Saudi Arabia .”
Kamar walƙiya haka Papa yaga shudewar wani abun daya jima mantawa dashi ya gitta masa.
Madame Victoria kuwa cike da wani irin rudewa ta dafe baki cikin tsoro tana ambatar.
“…Shikenan.”
Cikin rawar muryan daya saka IBRAHEEM ya sake kallonsu.
“Me... ya... sa dukanku kuka firgita haka?”
Sai dai babu wanda ya amsa masa
sabofada a wannan lokacin… Saboda duk gani suke wani sirri ne na shekaru da shekaru ke neman farkawa daga cikin duhun da suka jima bisnewa.
“Saudi Arabia…?”
Kusan a tare suka hade baki wajen nanata wannan kalmar. Wacce jin sunan kasar kawai jinsa suke tamkar sauƙar mashi a cikin zuciyoyinsu.
Madame Victoria ta matsa kusa da Papa cikin rawar murya da tashin hankali ta riko hannunsa cike da tsoro tace.
“Jeff…”
Stop ya mata da hannunsa yana me furta.
“Kar ki cemin komai... shiru!”
Ya katseta da sauri idanunsa cike da tashin hankali.
IBRAHEEM ya tsaya kallonsu zuciyarsa na bugawa yana jin kamar akwai wani abu da ake ɓoyewa game da rayuwarsa.
Game da sunan nan da kawai ya dawo dashi game da Saudi Arabia. Game da dalilin da yasa zuciyarsa ta amsa musulunci kamar wanda ya daɗe yana jiransa dama.
Mr. Jeff Deefer ya sake kallonsa kamar a tsorace yace.
“Ka ce min…” amma duk da haka seda ya gaza mai kalmar duka har se da ya haɗiye wani yawu kana ya ɗora da.
“…wa ya saka maka sunan na