Advertisements
Chapter 1 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 31

1 to 3K   out of 90.3K words

[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: 💔 AFIYYA 💔




One (Free page)




✍️ Ayshatuuu 💙




RINGIM, JIGAWA STATE.




Taken mu a kullum shi ne " Jinin dabo ringimgim da ka garin karamci" mun amsa
wannan taken Dan mu mutane ne masu karamci da dattako, masu riko da alada, garin me
ruwa, me kifi Wanda suka San kansu a wajen noma. Bari na barku hakan kada kuce na
Koda garin mu da yawa, believe me idan kuka je ringim zaku San ba karya nake ba.


Sunana Amina Abubakar Salihu, Amma anyi min lakani da AFIYYA kasancewar na ci sunan
kakata data haifi babana ne. Kakana Alhaji Salihu shi ne wazirin sarkin ringim
kunga kenan na hada jini da sarauta. Na kanyi tunanin Anya infertility wato rashin
haihuwa baya running cikin zuriar mu? Ko Dan ba hakan ya kamata nace ba , zance
tabbas infertility na yawo cikin familyn mu. Dukda haihuwar ana yinta sede batada
yawa, da anyi daya shikenan, se ta tsaya. Hajiya Amina ita ce kakata, asalinta
mutuniyar Ganjin gebi ce. Ita kadai ce matar daya aura Bai Kara Kuma wani auren ba.
Yaranta su biyar ne. Mahaifina Abubakar shi ne babba se Wanda ke bi Masa kawu
Sa'idu, se Yar tsakiyar su Mummy Maryam, me bi Mata se kawu Ahmad ana ce Masa
Tijjani autansu Uncle Salihu amma Babawo ake Kiran shi, my very own savior.




Kamar yadda muka sani lokacin da westerners Suka kawo karatun boko an fara dauka ne
daga gidajen masarautu Dan a bada misali ga sauran alumma su biyo baya. To mu dinma
hakan ce ta kasance lokacin da yaran sarki zasu tafi se aka hada da Babana da Kuma
Kawu Sa'idu aka kaisu. Hajiya Bata so saboda tana ganin kamar wani Abu ne ake son
koyawa Yara Dan a dauke hankalin su akan turbar musulinci. Da kyar aka samu akai
convincing dinta ta amince Suka tafi makaranta, sede kawu Sa'idu fur yaki idan an
kaishi se ya gudo ya tafi gidan Gwoggon su dake kyarama, duk kuwa da tsakanin
Ringim da kyarama akwai tazara Amma hakan zai gudu. Idan mahaifina ya dawo yayiwa
Hajiya complain tayi fada Amma a banza tunda ita Baso take ba Amma tana ganin Dole
tayiwa waziri biyayya, Kuma ba zata so yayanta Suki Masa biyayya ba. A haka aka
Gama karatun Babu abinda kawu ya tsint, da waziri ya fahimci hakan se kawai ya
kaishi kasuwa yace gwara ya nemi abinyi kada ya ja Masa magana a gari. Nanma Babu
wani abinda yake illa yaje yayi shawagi ya tafi yawon shi, sede a wañnan shekarar
baya ga waccan budurwar baya ga gidan wane, Kuma kowa saboda darajar waziri yake
kyale shi.


Daddy a kings college dake Lagos anan yayi secondary School din shi, Yana gamawa
aka bashi offer Amma se yaki karba akan shi fa se yaje ya Karo karatu. Hajiya Babu
yadda batayi dashi ba Akan yayi aure Amma yaki. Haka ta kaishi Kara wajen fulanin
sarki se ta nuna Mata itama fama take da nata dan maslaha kawai su kyalesu suyi
masu addua.




Mahaifiyata sunanta Halima, ban taba ganin ta ba, asalin ta Yar shehun borno ce,
akai alliance Akan zaa hada auren yayarta da Baba Mustapha Dan sarki Wanda yake
saan Abbuna ne Kuma tare suke karatun acan UK. Yayar ta ita Kuma Mariya, da zasu zo
aka saka mamana ta Mata rakiya, bayan an gama komai se sarki yace ai tunda Halima
tazo se a hadata da da Abbuna tunda Suma Yan uwa ne. Haka akai aka daura aure mazan
na can wata duniya, kowanne se gani yayi an aika Masa da matar shi. Abbu yace min
Bai taba ganin mace kyakyawa kamar mahaifiya ta ba, me hakuri da juriya irinta ba.
Ya fada min zamansu Zama ne sukai Akan fahimtar juna da soyayya.




Shekara na zagayowa Ummin Istanbul kamar yadda muke ce Mata ta haihu Amma mamana
shiru ko Bari babu, wannan haihuwar daidai Gama karatun su Suka dawo Nigeria,
precisely Ringim, sosae aka tarbesu aka nuna jin dadi musamman haihuwar Ummiey ta
dada musu. Anan suka cigaba da rayuwa, Abbuna ya samu aiki a Lagos ga damuwar da
mamana ta saka a ranta na rashin haihuwa se aikin yazo Masa da Dadi yasan zata Dan
ji Dadi idan tayi nisa dukda bawai takura Mata ake ba, Hajiya me tsananin Kara ce
Kuma ta fada min Bata taba suruka ta gari ta kirki me Kara da kawaici who owns a
golden heart irin mahaifiyata ba. Baba Mustapha da Ummiey se Suka bar kasar gaba
daya, a hakan rayuwa ta cigaba da tafiya.


Bangaren Kawu Sa'idu yayi aure matar shi Zinatu, a yawon shi ya samo ta Yar Kano ce
Muna kiranta Ummaah, a yanzun bazan ce muku komai akanta ba Amma nan gaba kadan
zaku gane irin rawar data taka wajen lalata rayuwata, idan Babu Ummaah cikin
labarin AFIYYA to labarin bashi da amfani. Kawu ba karatu yayi ba , shi ba Sanaa
yake ba sede standing order da Abbuna yayi Masa duk wata akwai amounts din da yake
bashi, dukkan yayan shi Abbuna yake daukar nauyin karatun su. Shi ne kadai Wanda ya
haihu da yawa, Ina tunanin kamar ma ya riga Abbuna yin aure. Danshi na farko sunan
sarkin Ringim gareshi shi ne aka Kiran shi Baba, na biyu shi ne Yaya, sunan waziri
gare shi, bazan taba manta Yaya a rayuwa ta ba, mutum me alkhairi Wanda yaci sunan
me sunan shi. Ta uku sunan Hajiya ne da ita ana kiranta Mino, se Siyama se Hafsa.
Banda saa a gidan na girmi Hafsa Siyama ta girmeni. Haka yaran shi suke. Mummy
Maryam tana auren daya daga cikin yayan sarkin Ringim tana zaune a NY yarinyar ta
daya Rukayya muna kiranta Rooks. Kawu Tijjani yana Kano da matar shi Anty Salma,
yarsu daya Basma se Uncle Babawo shi ne a UK precisely a Lancashire yake. Shi Bai
ma tana haihuwa ba.


Abbuna seda sukai shekara ashirin Basu haihu ba, Abbuna yayi kudi,ga ilimi gashi
successful business man Amma Babu haihuwa har ya gaji da zuwa asibiti suka
fawwalawa Allah. Se at the last minute da suka fitar da Rai sannan kamar Wasa mama
ta fara laulayi suna zuwa asibiti akai confirming ciki gareta. Bayan kwana biyu
Suka tafi Germany rainon ciki. Kowa yaji labarin cikin se yayi farin ciki Banda
Wanda suke adduar Allah yasa kada ta haihu idan Abbuna ya mutu gado nasu ne. Saura
sati daya a haifeni waziri ya fara rashin lafiya kamar zai mutu. Dole Abbu ya tafi
Nigeria Dan sadawa dashi, Ashe rashin lafiyar ba ta tashi bace kwanan shi daya da
zuwa ya rasu. Wanann sakon da ya samu Mama se ya sata ta fara labor, dama tasan cs
zaa Mata tunda ta Dade Bata haihu ba. Take aka shiga da ita ot baa fito ba seda
sabuwar halitta wato ni! Seda mukai sati daya sannan Abbuna ya dawo jikinta yayi
sauki muka dawo Nigeria, a wannan dawowar gaba daya Babu wani dadi, Mama taso
waziri ya ganni ya rike no kamar yadda yake Mata nasiha kullum cewar watarana zata
hahihu zata dauki danta a hannunta. Se gashi lokaci yayi Amma baya da Rai. Abbu ya
saka min Amina, Mummy Maryam ta saka min AFIYYA lokacin tanada tsohon cikin Rooks.
Mama Bayan zaman makokin ya lafa ta tafi borno seda ta zubar da wanka sannan ta
dawo. Rasuwar waziri ta girgiza mutane sosae nan akazo tunanin Wanda zaa bawa
sarauta kowa ya nuna Abbuna yake so Amma se wasu suka nuna ai baya Zama balle a
bashi, why not Kawu Sa'idu. Shi dinma so yake a bashi Kuma ace Yana cikin council
members na emirate ai yayi gaba kawai. Hakan Bai kasance ba aka bawa Abby shi Kuma
se ya wakilta kanin waziri kamar yadda Hajiya ta fada Masa. Wannan abin ya Kara
Bata ran Ummaah da kawu Sa'idu.




Satin Mama biyu da dawowa muka koma Lagos muka fara sabuwar rayuwa, idan ka kallesu
ka kalleni zaka Yi tunanin ni din jikar su ce ba Yar su ba, Dan sunyi girma ace ni
din Yar su ce. Na samu gata na samu tarbiya na Kuma samu jin Dadi sede Bai daure
ba, Allah ya yanke min hakan ya jefo min wata hanyar da zanbi Dan ya gwada imanina.
Shekarata daya Mama tayi rashin lafiya kwananta biyu a asibiti Allah ya Mata
rasuwa.




AFIYYA is not free! Pay through 3091721807, Aisha Hassan kwalam, First bank of
Nigeria (FBN). Send evidence of payment through 09063467258.




Ayshatuuu
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: 💔 AFIYYA 💔


Two (Free)


✍️Ayshatuuu




Junaidu sunan shi, mahaifin shi Malam Ibrahim Wanda yake haifaffe Kuma zaunannen
Kazaure ta jigawa. Mahaifin shi babban malami me Wanda yasan alqur'ani da
litattafai. Ko Ina zakaji anyi kwatance da tsoron Allah irin nashi. Sede bawai a
malimtar ya tsaya ba shi din manomi ne haka Kuma Dan kasuwa ne Wanda yayi karatu
sosae a ilimin zamani, shiyasa malumtar ma take tafiya yadda ya kamata. Allah Yana
da hanyoyi da dama na jarabtar bayin shi, duk imaninka baka wuce kaddara,
Matan auren shi hudu, Babbar wadda ita ce uwargida Yar Roni ce Hajja Huwaila, ita
ta Haifa Junaidu Wanda a yayanta shi ne na uku. Gaba daya yaranta biyar. Me bi Mata
ita ce Hasiya wadda Yar nan cikin garin kazauren ce, se ta uku Yar Daura sunanta
Fatima, amaryar shi Kuma Yar wani abokin shi ce ya bashi ya aura me suna Sadiya.
Gaba daya yaranshi sun tasar ma goma Sha biyar. Yadda aka San gidan malamai gida ne
Wanda zaman lafiya da kwanciyar hankali ya yawaita,nan dinma hakane sede idan Mata
suka taru Dole akwai abubuwa na kishi da Dan rashin jituwa. A alaadar gidan tun
kafin ka Gama primary zakai izu talatin, kana zuwa js3 kayi sauka seka tafi
boarding ka cigaba do littatafia. Karatu ana idar da asuba zaa fara, Bayan sallar
Isha a daura, Dole kowa se yaje ko ya hadu da fushin malam.


Wasu iyayen sun iya banbance yadda yaran su suke tun daga yanayin kukan su suna
jarirai da Kuma yadda suke muamula da Yara sa'o'insu idan sun fara girma. Junaidu
yaro ne me kuka Yana yaro, kukanshi ya baci, Kuma duk abinda Hajja take ya fara
kukan nan se ta katse shi, Yana da zuciya Dan ko an daura shi a po yace ya Gama baa
zo da wuri ba to idan akazo tsarki zai ce bazai tashi ba. Cikin dare idan ya tashi
Shan ruwa kafin a dakko a bashi yayi fushi bazai karba ba. Wannan halayen nashi
yasa ake cewa Hajja tafi son shi saboda gudun zuciyar shi yasa dukkan attention
dinta take Kansa, shima Baban wato malam daya fahimci hakan se kullum kafin ya fita
se yayi rubutu ya kawo a bashi. A hakan ya fara girma har Yana fitowa waje yayi
Wasa da Yara saanin shi dukda ba sosae yake hakan ba Amma duk ranar da ya fita
wasan to se ya daki yayan mutane, a gidan su ma idan kannenshi da yayun shi suna
Wasa Yana zuwa kowa zai kwashe kayan wasan shi idan ba hakan ba ta kansu zai bi ko
Kuma ya dinga wurgi dasu. Kowa tsoron shi yake he's a villain and also a rogue!




Primary aka Kai su Amma baya zuwa se ranar da ya ga dama, shi ne shugaban bad gang
na cikin makarantar kullum rana idan har suna cikin makarantar to tabbas zasu daki
wani ko su sumar da wani. Kullum ana filing complain office din headmaster, har ya
gaji ya fadawa Malam halin da ake ciki. Malam ya dawo gida ya aika a Kira Masa
Junaidu, ya shigo a nutse saboda haka yake, idan ka kalleshi zakaga zallar nutsuwa
a tattare dashi Amma idan ka kalleshi ko ka zauna dashi zaka San Allah ya Masa
hallittar nutsuwa shi Kuma ya bijire. Ya tsaya a tsaye Yana cewa Malam gashi
yazo,yayan shi Suleiman ya kalle shi ya kalla Malam sannan yace Masa ya nemi guri
ya zauna, ko kallon shi baiyi ba balle yasa ran zai zauna hakan ya batawa Suleiman
Rai, Yana tashi ya dauke shi da Mari, Amma ko gezau Junaidu baiyi ba se huci kawai
da yake Wanda ke nuna ranshi yayi mugun baci, seda malam ya Masa magana sannan ya
tsugunna shima yadda tsugunna din kawai se yasa kunyi dariyar takaici.




" An kawo min Kara cewar baka zuwa makaranta, idan Kuma kaje kana dukan yayan
mutane..."




" Inji wanne Dan shegiyar?"
Ya fada Yana Kara Bata Rai tareda mikewa tsaye, Suleiman ya Mike yakai Masa naushi
a take bakin shi ya fara jini, yasa hannun shi ya lakuto Yana ganin jinin yayi Kan
Suleiman ya cakumi wuyan shi ya fara naushin shi, Malam ya Mike da kyar ya raba su,
yana sakin Suleiman ya zube a kasa saboda yadda ya karbi naushi a jikin shi, tabbas
jikin shi ya fada Masa. Malam ya dafe Kan shi ya kwallawa kanin shi sarki Kira,
Babu shiri sukai asibiti da Suleiman. Baa Kara tada maganar ba Amma Malam ya dage
da kaiwa Allah kukan shi.


Tun daga wanann abun gaba me karfi ta shiga tsakanin Suleiman da Junaidu, Kar kuyi
tunanin me sauki basa magana Koda zasu bangaji juna, wannan ya dagawa Hajja Huwaila
hankali ya bar Mata abun Fadi wajen kishiyoyi. Lokacin da ya kusa Gama primary se
ya fara Shan taba, bakin shi ya fara nunawa, ya daina zuwa karatun da suke na Bayan
sallar asuba, ya daina zuwa gaida kowa a gidan, abincin gidan Banda na dare to baya
ci. Can wajen kanti akwai wani garejin gyaran mota nan yake zuwa da yamma anan yake
samun kudi anan Kuma ya fara Shan taba, da Abu yayi gaba we aka fara bashi Wiwi
Yana zuka, baka taba shi da robb da yake shafawa a leben shi da Kuma namijin goro
Dan kada kaji warinta. A hankali Malam ya fara gajiyawa da halayen Junaidu se ya
fara fita daga alamuran shi. Tun ranar da ya daki Suleiman a ranar Malam ya fara
tsoron Junaidu Amma dukda haka yana Masa fada Hajja Huwaila na ma na kokari sosae
Akan shi shiyasa ya daina zuwa gidan. Akwai lokuta da iyaye suke samun matsala,
itace tun Yana karami ake tankwara shi idan ya bushe zai karye, lokacin da Junaidu
ke fatali da kayan wasan Yan uwan shi ya kamata a tsawatar Masa Amma idan yazo ya
nayi se Hasiya ta dinga tafi tana cewa ga gwarzo yazo, yanzun zai baza yaran da
basa son yin karatu se Wasa kawia Suka sani, ko sun Kai kararshi Huwaila ce kawai
zata lallashe su Amma sauran matan se suce ai maganin fitsararru yakeyi. Wannan shi
ne abinda ya bashi lasisin yin duk abinda yakeyi, a unguwa ko ya daki Dan wani
saboda Malam se kauda Kai, a makaranta baya zuwa Amma form teacher batai reporting
ba saboda tana ganin irinsu Junaidu rashin zuwansu yafi zuwan su alkhairi. Kowa ya
taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar shi, tarbiyyar Bata iyaye kawai bace, ni na
yadda cewar tarbiyyar duniya ita ce tarbiyyar, duniya makaranta ce kowa se ta bashi
ilimin da yake bukata.




AFIYYA is not free, pay 300 into 3091721807, first Bank of Nigeria. A'isha Hassan
kwalam. Send evidence thru 09063467258




Ayshatuuu.
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: 💔 AFIYYA 💔


Three (Free)
✍️Ayshatuuu




Mutuwar Mama ta girgiza mutane da dama saboda rashin lafiyar da tayi ma ba kowa
bane ya San batada lafiya, it was very brief Amma da yake karar kwana ce se gashi
ta rasu ta barmu ni da Abbuna. He was completely shattered beyond imagination, har
ya koma ga Allah Babu ranar da baya cewa " da Halima nada Rai, Allah sarki Halima"
maganar shi kenan, kullum Rana se ya bani labarin ta sede idan baya gari ko bana
nan. A luth ta kwanta aka Gama duk wani cike cike da ya kamata sannan yayi booking
flight within few hours suka dakko gawar zuwa Kano, kafin mu karaso an turo Mana
motoci daga Ringim Emirate council Wanda zasu tafi da gawar zuwa inda dubban mutane
ke jira a sallace ta. Abbuna yana rike Dani a kafadar shi tunda muka taho nayi
bacci bayan Nanny ta bani oat nasha. Muna zuwa danginta da suke nigeria duka sun
biyo flight zuwa Kano sun karasa Ringim, ita mamanta Bata gidan Kuma ita daya ta
Haifa, asalin ta Yar Ethiopia ce, so Bayan sun rabu da shehun borno ta koma
kasarta, acan Bata wani Jima ba ta rasu, so nidin jini da yawa ke bin veins dina.
Ina baccin Nanny ta shiga Dani ta goya ni a wañnan yammacin aka kaita makabarta aka
binne ta. Abbu was devastated, kallon shi kadai zai baka tausayi kowa yabin halayen
kirkinta yake. Mutane da yawa kallon Abbu Dani ke saka su kuka na tausayin mu.
Tunda na farka a baccin aka bani abinci naci se na kankame Nanny dama ni me kowa ce
saboda ban Saba ganin mutane a gidan mu ba. Idan Naga mutane Kuma to se na nanike
mamata ko Abbuna, idan Babu daya se na nanike Nanny. Kwana uku mutane suka baje
yawancin zaman makokin Ina jikin Abbuna a kofar gida Dan naki Zama ciki, kowa se
yaji tausayi na. A Rana ta bakwai Bayan an gama adduaa aka raba gado, a cikin
dangin Mama Babu Wanda yace zai tafi Dani shima Kuma Abbu Bai yiwa kowa tayi ba,
sun tafi suna ta jin rashin dadin rasuwar Yar uwarsu. Duk yadda rayuwa zatayi Dole
mutum ya cigaba da rayuwa, duk wani bakin ciki da zaka dandana akwai ranar da zai
wuce kaji kamar baayi ba. Bayan gidan ya watse Hajiya tayiwa Abbu nasiha sosae Amma
se yace Mata shifa tayi hakuri aure daya ne Kuma yayi Amma baya tunanin zai Kara
wani. Mummy tace to ita zata karbe ni ta hada Rooks Amma yace ya gode zai rike ni
Yana ganina yaji Dadi. Daga nan muka koma Abuja saboda transfer da akai masa zuwa
can. Gidan daga ni se shi se Nanny se Kuma maids din dake Mana aiki, da Nanny ke
Mana komai Amma tunda ita ce sabuwar uwata Abbuna ya maida ita kawai kula Dani su
Kuma sauran suyi aikin gida. Akai akai yake kaini Ringim Dan na Saba dasu, Yan uwan
Mama Babu Wanda ya taba zuwa ya ganni Dan haka Abbu yace shima bazai kaini ba, har
na Isa yaye aka daina feeding Dina da Madara se aka koma solid food. Ban Jima da
yaye ba na cika shekara biyu, Abbu ya kaini creche, so ni dai as far as am concern
tunda nayi wayo a makaranta nake, karatu nake, Dan hakan karatu a cikin Raina yake,
shekarata ta farko bani ma da wayo bazan iya tuna komai ba, seda nayi shekara biyar
sannan na fara sanin kaina, mutum daya na gane matsayin uwata da ubana Abbu, shi
kadai na sani kowa as preliminary nake ganin shi,duk Wanda na Kira da Baba to Kara
ce kawai,Dan Babu Wanda ya yimin abinda Abbu yayi min.




Saboda yadda na Shiga makaranta da wuri yasa kankanin lokaci na gama. Munje Ringim
Ina kwance akan cinyar Hajiya Abbuna ya shigo Dan tun isowar mu fada ya fara zuwa
ya gaishe da sarki sannan ya fito mutane Kuma suka tareshi kowa na fada Masa
financial complain dinsu Dan ya taimaka musu. Da kyar na yadda na shigo gida shima
Yaya na gidan Kawu Sa'idu ne ya lallaba ni muka

1 / 31