Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
ba ya dauki kwanon shi ya fita, na Jima a zaune sannan nace da
Mino dake zaune gefena,
" Zanyi bacci, Ina Zan kwanta?"
Ta kalleni sannan ta kalla gefen Ummaan su tace cikin kasa da murya
" Ko fadawa Ummaan mu"
Nayi shiru Ina tsoron tunkarar ta, anan nayi ta guangyadi sauro ya samu ya cije ni
son ranshi, se Susa nake, can Siyama ta tashe ni tace naje mu kwanta, haka na Mike
nabi bayanta, Ina ayyana yadda zamuyi bacci akan katifa mu hudu, lucky enough Ina
zuwa na tarar an Yar min da Yar karamar katifa irin 6x6 dinnan, net ta Mika min na
daura, na rike net din Ina tunanin to ya Zan daura, Mino ganin Ina tsaye ta min
bayani tana jin motsi tayi shiru, se na fahimci they all want to be nice tsoron
iyar su suke. Wani irin dauri na Masa na Shiga na kwanta, gaba daya ya kwanta a
fuskata Dan haka da asuba na tashi nayi alwala naji fuskata kamar an zuba Mata
barkono, na cije bakina Ina kokarin danne azabar da nake ji, a hakan nayi sallah
duk suna bacci Basu tashi ba, gwara Yaya Ina ban daki naji motsin shi. Anan bacci
ya daukeni se fadan Hafsa da Siyama ya tasheni, na tashi na cire net din fuskata na
azaba kamar zata kwakwabbo, na gaida Mino dake cemin na tashi na kwashe kayan
shimfida ta, nace Mata
" Kinga fuskata zafi take min"
Na fada Ina yatsina fuska, da a gidan mu ne da tuni na tada hankalin kowa kilan se
an kaini asibiti, ta taba fuskar tace
" Net ne, zai warke kinji"
Na gyada kaina, anan ta nuna min yadda Zan saka yau sannan na kwashe kayan muka
fito, ta bani tsintsiya Wai nayi shara, na kalla tsintsiyar na kalla tsakar gidan
na saki ihu a kaina, Ina neman agaji a gurin Allah!
AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam first Bank of
Nigeria, send evidence to 09063467258.
ShatttzzzxDake yan class din sun fara lesson a month ago se ya zamana sunyi nisa a
physics din, motion shi ne topic din da ya rubuta a jikin board, Amma kafin ya fara
bayani Kan motion din seda ya tambayi Yan class Wanda zai iya recapping abinda aka
koyar. Sauda dake kusa Dani ta daga hannu, hakan yasa malamin yayi pointing din ta
ta tashi ta fara bashi amsa, ta Jima tana bayani kafin Kuma yace ta zauna bayan
yasa an tafa Mata. Na kalleta Bayan ta zauna nayi Mata murmushi itama tayimin. Babu
dadewa ya shiga bayani Alan motion, nayi shiru Ina assimilating abinda yake fada,
haka Ina jotting points where necessary. Seda ya Gama sannan ya mikawa class rep
note din yace ta rubuta Mana a board ya fita gaba daya. Na sauke ajiyar zuciya na
kalla Sauda nace
" Sauda Dan Allah naga note book dinki"
Tayi murmushi ta Miko min tace
" Amina kinada kyau!"
Nayi murmushi kawai Amma ko godiyar compliment din banyi ba, na bude na fara kwafar
note dinta, dake inada sauri Kuma Yan class din sun tsaya Wasa ko fara rubuta sabon
note din baayi ba yasa na Gama kafin wata period din ta shiga. Nutsuwa nayi inata
going through Dan na samu na iya abinda aka koyar. Ina cikin Yi se ga wani malamin
ya shigo me maths, wani young guy haka, muka gaishe shi yayi abinda zaiyi ya fita,
har lokacin Babu Wanda yayi noticing Dina a ajin, a ranar da aka tashi Sauda ta Ara
min books dinta Dan naje na kwafa. Ana tashi na hada books Dina na saka cikin jaka
na dubi Sauda na Mata sallama, se sauran dake kusa damu da bansan sunan su ba na
musu sallama na fito Ina kallon yadda kowanne dalibi ke kokarin tafiya gidansu, se
na tuna tawa rayuwar a NTIC. Na girgiza Kai kawai na fara tafiya a hankali, ga Rana
ga zafi ga Yunwa, Amma haka na nufi gida bakina ya bushe saboda kishin ruwa. Tun
daga kofar gida na hango Yaya a tsaye Yana magana a waya, cikin sauri na karasa Ina
hango murmushi kwance saman fuskar shi, na karasa kafin yayi min magana ko ni nayi
ya Miko min wayar shi, na karba na Kara a kunne ba tareda na duba me Kiran ba.
" Hello Afeey darling!"
Kadan ne Bata kashe min dodon kunne na ba saboda ihun da tayi, na saki dariya a
hankali Ina kallon Yaya da ya lumshe idanun shi Yana kallona nace
" Rooks! I missed you"
Tace min she missed me too sannan tace
" So fada min ya makaranta? Yau ranar ki ta farko how do you find it"
Tambaya dai a gurin Rooks ba daga nan ba, na zauna kan bencin da Yaya ya janyo min
na fara fada Mata komai akan makarantar, a karshe nace Mata
" Nafi son waccan ta Abuja, saboda idan na dawo gida Ina tarar da Abbu da Nanny a
gida!"
Seda na fada naji idanuna sun ciko da kwalla, itama a yanayin yadda tayi min magana
nasan jikinta yayi sanyi, na danyi murmushi me ciwo nace
" I've to live Rooks ko Dan nayi ma Abbu da Mama addua, I've a reason to live"
" Yawwa Afeey, kiyi addua komai zai zo da sauki. Yanzun kin fini class!"
Nayi dariya na gama tsokanar ta, cewa ya kamata ta fara Kirana senior, I'm not
match for her Dan kuwa na fita aji yanzun. Haka muaki sallama Raina fari Kal, duk
gajiyar Dana kwaso se naji ta Dan tafi. Na Mika masa wayar Ina murmushi nace
" Thank you Yaya!"
Yayi murmushi Yana kallona so intense yace
" Ya makarantar?"
Na amsa da alhamdulillah sannan nace Masa Zan shiga gida bayan na kara Masa godiya,
I felt his eyes trailing on me har na shige gidan. Ina shiga na tarar dukka sun
dawo, da sallama na shiga, Mino ta amsa min tana fadin
" Ina Kika tsaya?"
Na danyi shiru Ina tunanin abinda zanyi cooking, se nace
" Mhmm! A hankali na dinga tahowa"
Ta gyada kanta na shiga ciki na cire kayana sannan na fito nayi wanka, tunda naji
gidan shiru nasan Ummaan su Bata nan, Nima ban tambaye ta ba Dan idan Bata nan
gidan yafi Dadi. Abinci muka ci sannan nayi shara na dawo na fara kwafar note,
sallamar Ummaan su naji, na daga labule na Mata sannu da zuwa, ta amsa sannan tace
na aje littafin nan nazo na Mata wanke wanke, na bude baki da niyyar ce Mata ai
nayi tawa sharar tunda dama shi ne aikina, Amma se nayi sealing bakina kawai na
tattara littatafan na aje na fito, dogon hannun rigar dake jikina na nannade na
hada kayan wanke wanken guri daya na zauna, na fara a hanakli kamar me wanke Raina,
nayi nisa ta leko daga daki ta kwalla min Kira, bafa Afiyya take cemin ba sede tace
min
" Ke!"
Shikenan Kuma Dole na amsa, hannuna na dauraye, kafin na karasa dakin naji sallamar
Yaya Yana kwalla min Kira, na tsaya tareda juyowa kawai se Naga Nanny a Bayan shi,
na cire slippers din kafata na ruga a guje na fada jikinta, na kankame ta kamar Zan
koma cikin ta, ta rungume ni itama, na saki dariya wadda take so genuine and
sincere nace
" Nanny!"
Ta Kara rungumeni, bana tunanin Zan manta farin cikin da naji a wannan ranar, da na
sake ta Kuma se na fara Kuka me ciwo, na tuna gida na tuna beautiful moments din da
mukai tare, na tuna Abbuna. Na rike hannun ta na dinga kuka Ina jin tamkar Ina
shading dukkan bakin ciki, da gajiyar Dana kwasa a wannan kwanakin. Ummaan su ta
fito dasu Mino dake daki, ta hade Rai tana hararata da ni bama lura nayi ba.
Lallashina ta shiga Yi sannan na dakko Mata kujera nace ta zauna, se lokacin ta
lura da Ummaan su Suka gaisa ni Kuma na koma kan wanke wanken da nake, Ina wanke
wanken Ina Mata tambayoyi tana amsa ni, su kansu nasan Basu taba sanin inada surutu
har haka ba. Na Gama wanke wanken tana ta Bina da kallo har na Kai kwanukan kitchen
tana zaune, fuskarta na nuna tausayi da Kuma mamakin wata daya yadda na koma wata
daban, tana zaune na hura wuta kafin ta Gama kamawa na leka nace da Ummaan su me
zaa dafa, tace na Kira Mata Mino na tafi gurin Nanny. Ina Shiga daki da Nanny Sega
Yaya, ya shigo hannun shi da Leda ya bani, ruwa ne me sanyi da carbonated drink,
nayi murmushi na Masa godiya, na bude Mata na Bata Amma se kallona take, na riko
hannunta nace
" Nanny naji dadi da Kika zo, kullum se nayi addua ko ke ko Uncle Babawo wani yazo,
Allah ya amsa addua ta"
Se Naga hawaye suna sauka daga fuskarta, nace
" Me yasa kike kuka Nanny, kin tuna Abbuna ko? Ina Masa addua kullum bana mantawa"
Ta riko hannuna tace
" Me yasa Kika rame? Baki cin abinci ne? Ko aiki kike da yafi karfin ki?"
Yarinta ce tsagoro a tare dani, ga wautar Yan fari, ga gabuntar autanci na zauna na
fada Mata duk halin da nake ciki, na Kara cewa
" Nanny Babu dadi anan, komai Babu dadi, rayuwar gaba daya Babu dadi, dama haka
kowa yake komawa idan baban shi ya rasu ko Kuma ni ce Kawu Sa'idu baya so?"
Ta girgiza Kai Amma ta kasa magana, se ta rungume ni a jikin ta, mukai sallah, a
Jakarta ta fito min da foiled kaza, na kalleta na Kara rungume ta, na zauna naci
nayi nak, Dan haka da aka bani jollof din taliya nace na koshi. Guntun lemon da
tayi na shanye, wa yaga komai se da dalili Kuma an Dade Baa hadu ba. Ranar bacci
nayi me dadin gaske, dukda katifar ta matse mu Amma ban damu ba. Da sassafe kamar
kullum na tashi na fita shara na hura wuta sannan na gama nayi wanka na dawo na
tarar ta bude akwatina na, ta dubeni tace
" Ya akai duk kayan datti a ciki?'
Nace
" To Nanny bazan iya wankewa ba"
Ta gyada kanta kawai, ta fito dasu, wankakkun kadan kawai Suka rage!
AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, first Bank of Nigeria Aisha Hassan
kwalam, send evidence through 09063467258
ShatttzzzxNa Gama Shirin makaranta, na kalli Nanny dake juya kayana zuwa daidai
nace
"Zan tafi makaranta, Amma ba yau Zaki tafi ba ko?"
Tace min
" Eh ba yau ba, kije ki karba abinci ki wuce"
Nace
" To Nanny se na dawo!"
Haka na dauki jakata na fito tsakar gida, wainar gero aka Miko min naci, nasha ruwa
sannan muka tafi cikin ayari. Nanny ta fito da kayan ta fara wanke min, Ummaan su
na zaune tana tabe baki dama tun can bawai su nayi da Nanny bane Dan hakan itama
Bayan gaisawa da sukai Bata Kara bi ta kanta ba. Tayi nisa a wankin Kawu Sa'idu ya
shigo, Dan tun asuba yake fita, yawancin se kowa ya tafi makaranta yake shigowa ya
karya sannan ya Kara fita Kuma se dare. Ni kaina bansan wanne irin aiki yake ba,
zai fita dai ya dawo, su kule a daki su dinga zance da baka San me sukeyi ba. Ta
wanke hannun ta ta zauna kamar yadda ya zauna Yana fadin
" Fanta jiya an fada min kinzo, ban shigo gida da wuri ba"
Ta danyi dariya tace
" Har yanzun anan ana fitar dare kenan?"
Yayi dariya shima saboda Mamana tana da Rai takan ce Masa Wai me yakeyi a waje ya
Dade har cikin dare? Se yace mata shi baya son sa idanu.
" Nazo Naga yata, har an saka ta a makaranta, Allah ya saka da alkhairi ya bar
zumunci!"
Yayi murmushi jin Dadi yace
" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"
Nanny ta gyara Zama tace
" Akan me fa?"
" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta
tunda ni ke rike da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi
na kula da ita..."
Nanny mamaki ya karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da
Abbu ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji
ba.
" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"
" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake
wahala da yarinya Basu ba"
Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace
" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka
yake, ya kamata ace komai Kai kake kula dashi"
Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace
" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta
Afiyya ce ta makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo
ko takaddu gurin Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace
musu kawai sede duk wata su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da
wani abun fa!"
To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin
shi bayan Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny
ranta ya mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se
ya rike ni, hatta kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya
shi, wannan wanne irin rashin zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai
yayan shi da komai nasu shi ke dawainiya dasu.
" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin
girman ki, ke kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na
Miki alkawarin Zan dinga fitar Miki wani Abu a ciki"
Nanny tace
" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"
Ya Mata godiya se tace Masa
" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin
makarantar ta"
Yayi dariya yace
" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar
makarantar ne ai wannan almubazzaranci ne"
Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga
ciki Yana jin burin shi Yana daf da cika.
Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda
ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar
aiki, yayi aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin
Dan kaida ce duk yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam
da Jarma na zuke zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama
influence din su ne, Amma huzaifa Bai ma taba zuka ba shikam Malam he's always the
lead. Bayan an gama maghrib kowa ya Kama gaban shi. Fatima ce da girki tun karfe
hudu ta kammalla haka take badai kaga tayi Daren girki ba. Ruwa ta tafasa ta shiga
wanka, tana watsa ruwan taji wani kaikayi a duk inda ruwan ya sauka, ta dubi
jikinta gurin yayi jawur tamkar ta kone, a gigice ta dubi ruwan tasa hannunta Amma
shima hannun tana fito dashi se kaikayi yayi jawur, zani ta daura ta fito a guje
tana kwalawa Hajja Huwaila Kira, kafin Hajja ta fito tuni Hasiya ta fito ta same ta
tsakar gida tana faman sose sosen jiki, Hasiya tace
" Fatima ya akai?"
Ta kasa magana se nuna Mata take da hannu, tana Susa, lokacin Hajja ta fito itada
Amarya suka samu Fatima tana Neman cire zanin jikin ta, ga yaran duk sun zagaye ta
wasu a ciki na kuka, hannunta Hajja ta kama Suka shiga daki, Suka fara duba
jikinta, duk inda ta Sosa yayi burdi yayi Kuma kwaf kwaf kamar konuwa. Hajja ta Yi
shiru Dan ita ta rasa abinda zata ce tunda take Bata taba ganin abin ba, ta dauka
hijabi tace da Hasiya
" Ke ki zauna da Yara, ni Kuma da Amarya zamuje general, ki aika a fada ma Malam"
Da hakan Suka Taya Fatima ta shirya,suka samu Keke napep Suka tafi general, kowa
idan aka bude gurin gani suke allergy be hakan yasa focus din maaikatan asibitin,
sede ana administering drugs din kamar bama shiga suke ba, in fact tunda jikin ba
bukatar su yake ba kokarin reacting musu take. Anan Malam yazo ya same su, hankalin
shi ya tashi ganin maaikatan sun ce sede su turasu AKTH suga dermatologist kawai,
Malam ya karba takardar, ga Fatima ciwon se Kara Hawa take, se ihu take tana Kiran
sunan Allah tana su taimaka Mata kaikayi zai kasheta.
A wannan Daren da Junaidu ya dawo ya samu gidan tamkar gidan makokin, yaran na
tsakar gida sunyi jugum, Wanda sukai kuka zuwa lokacin sun hakura, Bai bi ta Kan
kowa ba ya shige dakin abin shi ya zauna Yana ayyana ya kamata ace zuwa yanzun
aikin shi yaci Akan Fatima, tunda kuwa Jarma yace Masa tamkar yankan wuka haka
aikin malamin yake, Yana cikin zaune Sega zainab ta leko, tunda sukai abin kudinnan
yarinyar ke shishigge Masa tana son ganin ta wanke laifin ta. Yana zaune ta shigo
ya dago ya kalleta yace
" Meye?!"
Ta zauna tace
" Mama ce Bata da lafiya!"
Ya gyara Zama yace
" Me ya sameta?"
Ta zauna tana kuka ta fada mishi komai, maimaikon taga ya canja yanayin fuskar shi
zuwa tausayi, se taga Yana murmushi, yace
" Abin yazo kenan! Kije zata ji sauki"
Zainab jiki a sanyaye ta fito ta dawo tsakar gida tayi shiru tana tunanin halin da
uwar ta ke ciki, Bata Jima ba suka dawo da Fatima dan a wañnan Daren bazasu iya
tafiya Kano ba sede zuwa gobe. Ihun da take yasa Junaidu fitowa kofar daki ya
zauna, Bai ce musu kala ba Amma se smirking yake Yana kallon yadda Fatima ta Zama
Yar bori, sight din kawai dariya yake bashi, ya zauna yaki tafiya Yana hango duk
abinda takeyi, gasu Hajja Huwaila nata karbar jike jiken ayatul shifaa daga gurin
Malam, Suka zaunar da ita suka Bata Tasha, Yana shiga cikin ta ta fara amai
bakikirin, Hajja ta Kira Malam yana zuwa yace wannan sihiri ne Kuma an karya shi,
Hajja ta rike kirji yayinda Hasiya da Amarya suka furta
"Sihiri malam!"
Ya gyada Kai yace
" Tabbas sihiri ne! Allah ya Bata lafiya"
Suka saka ta kuskure bakin ta, ta saki ajiyar zuciya ta lumshe idanu bacci ya dauke
ta. Malam ya gyada Kai ya juya zuwa dakin shi, daidai dakin Junaidu yaji Yana waya
" Man nake fada maka abin yaci fa, dukda dama ba wani tsawon lokaci zai dauka ba
Amma nasan ta karbi wahala"
Ya Jima Yana sauraron magamganun Junaidu Amma ya kasa gane inda zancen ya dosa, shi
yaron tsoro yake bashi tunda Suleiman yace ya ganshi tsakar dare Yana Kona wani Abu
a kasko shikenan ya koma jin tsoron shi. Shidai yasan kullum Yana adduar Allah ya
shirya yaron Amma Kuma har yanzun abubuwan Junaidu Kara gaba suke. Ranar baccin
dadi Junaidu yayi, Dan burin shi ya Gama