Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
Ina son na ganshi na tabbatar da whether he's
fine or not. Ina zuwa na samu Yan maiduguri aunties Dina sun zo, ana cewa a kirani
mu gaisa, nayi saurin rufe fuskata na fita, dan nasan aka tsaya wannan formalities
din bazan je ba. Kamar yadda ta cemin Yana parking space nan na tarar da motar shi,
Yana hangoni ya bude min gaban seat dake gefen shi, Babu musu na Shiga na kulle, ai
kuwa ya saka central lock ya datse sannan yayi reverse ya fita daga gidan a Dan
guje, a tsorace nace
"Ina zaka kaini? Me za Kai min?"
Ba tareda ya kalleni ba yace
" I'm eloping you! Dole se na Hana aurennan at any cost...."
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258
Talla!
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamakiHakika
✌🏼 babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un
wani kaya sai amale ke d'auka, Fitattu biyu sun shiirya tsaf domin nishad'antar
daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku
cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu
biyu😍✌🏼masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida
rabon ka😘 Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa
da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku
hanzarta neman naku karku bari abaku labari
✍🏽
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA* Nrml 300 Vip 500
✍🏽
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!30
" Eloping?!"
Na mainaita Ina kallon shi da mamaki, Sam ba kallona yake ba hasalima hankalin shi
na kan shi da dukkan hankalin shi suna Kan tukin da yake,
" Me kike tunani? Kina tunanin son da nake Miki kadan ne? Ko Kuma tunanin ki Zan
zuba idanu ayi Miki aure ba tareda son ranki ba, idan kikai wannan tunanin to ba
kiyiwa son da nake Miki adalci ba"
Na sauke ajiyar zuciya me nauyi, sure wannan Yana bashi babban matsayi cikin
zuciyata ba tareda shi kan shi ko Nima na sani ba.
" Yaya Shehu kasan duk abinda hakuri Bai bayar ba rashin shi bazai bayar ba, you
can't just do this. Dan Allah ka maida ni gida"
Ya maka min wata harara wadda nasan tsabar yadda ranshi ke bace ne yasa ba ma zai
iya min magana ba. Na dauke kaina Amma zuciyata Taki aminta da Wai na gudu, why
should I be a coward, I've to accept whatever comes my way! Zuciayata ta tuna min,
se kuwa na fara kici kicin bude kofa dukda yayi locking duka kofofin, wannan
kicinayar da nake Yi yasa hankalin shi ya dawo kaina gaba daya, har ya kasa
controlling brakes din, se ji nayi
" Gab!"
Ya bugawa wani mota. Tuni na sake kofar Ina maida numfashi, yayi saurin parking ya
fito, me motar shima ya riga da ya fito, tuni mutane suka fara taruwa Dan kallon
abinda ya faru, ni dashi Banda mun saka seat belt da Babu abinda zai hana mu bugu.
" Gimbiya wancan kamar motar Shehu nake gani?"
Daddy ya fada Yana duban Ummiey dake amsa waya, tayi saurin kallon gurin tace
" Subhannallah! Wallahi shi ne"
Daddy yayi saurin parking ya fito, Ummiey ma haka, crossing titin sukai zuwa inda
ake ta gutsitsira magana, Shehu na tsaye ya dafe Kan shi ni Kuma Ina cikin motar se
zazzare idanu nake, gabana yayi mummunan faduwa ganin Ummiey da Daddy, na fara
kokarin fita Amma babu halin hakan saboda yadda ko Ina yake a kulle, yasan Zan iya
komawa gida shiyasa ya kulleni, baifi 30 minutes ba Naga mutane na ta tafiya daya
Bayan daya,Ummiey na rike da hannun shi ya zura key ya bude motar, kaina a kansu
nayi tsuru tsuru kamar kace fit in zura a guje, Ummiey da mamaki take kallon
fuskata sannan ta kalla tashi, Daddy yace
" Afiyya!"
Nayi saurin sunkuyar da kaina kasa, Ummiey ta maida kanta Kan Daddy sannan ta dubi
Yaya da yayi shiru yana Kara tamke fuska, cikin sanyin murya Ummiey tace
" Shehu me kukeyi tare? Ina zaka kaita? Me na fada maka?"
Ya bude baki zaiyi magana face
" Oh please Shehu ka manta duk abinda na fada maka. AFIYYA fito!"
Babu musu na fito Ina ta kallon shi he looks defeated and depressed, se naji kamar
kada na tafi Amma iyayen shi dake gurin ba abokan musu na bane, bayan mota na
kwantar da kaina Ina jin sanyi duka na bin jikina, I felt so empty and lost, na Jin
tamkar anyi nesa Dani daga barin jikina. Cikin motar Babu Wanda yayi magana seda
muka Isa gidan mummy sannan muka fito fuskata a rufe da hijabi kamar yadda nayi
Dana fita, Babu Wanda ya lura Dani har na haura sama kamar yadda Ummiey tace min,
na Shiga dakin na samu Mummy na fadin
" Wai ya zaku ce Baku ganta ba, Afiyyan allura ce da zata Bata?"
Nayi sallama jikina a sanyaye na shigo
" Daga Ina kike?"
Na dake nace
" Yaya Shehu ne ya kirani waje"
" Me yasa Zaki fita Baki fada min ba duk kin tayar min da hankali"
Nanny ta dubeni da banma lura da ita ba tace
" Karki Kara fita ko Ina"
Na gyada kaina, wani sabon lace ta dakko min cikin katon akwatin da kayan da nake
fitar biki suke ciki ta bani na saka, sun yimin cif cikin jikina, kudos to me
dinkin, yasan aikin shi, sede dukda abubuwan da yasa da zasu Kara cikani, kallo na
kawai zakai ka kalla zallar yarinta a tare dani, ga jikina ma kawai ka kalla will
tell you my age. Haka muka fita Ina ta zuba kamshi akan kamshi, muka Isa babban
parlon bakin ta, suna zaune sun kusa su biyar koma din hakan, kana kallonsu kasan
Yan gayu ne Kuma a wadace suke, dukkan su Kama suke da Ummiey, Mamana da Kuma ni
kaina Banda mutum biyu da nake tunanin ko su sirikai ne Dan su kamannin su daban ne
da namu. Tsakiyar su Mummy ta aje ni dukkan su suka yo kaina kowa na kokarin hadani
da jikin shi, a raina nace a banza tunda se yanzun sukai niyyar hakan, suka zo
nemana, a daddare na gaishe su kowacce ta min introducing kanta, biyu daga ciki
cousins din Mama ne, biyar sister's dinta se biyu in laws dinta, matan brothers
dinta kenan. Babu jimawa Ummiey ta shigo, Suka sakani a gaba da wasu zantuka da
Suka saka naji tamkar na zura saboda girman su day Kuma nauyin su a kunne na. Ya
zanyi Mummy ko motsi nayi se ta Harare ni, Haka na baza kunnuwa Ina ji, suna gamawa
kuwa na Mike na fice a guje. Anty Bintu tana dariya tace
"Anty Maryam yarinyar ki kunyar auren ma take ji ai"
Mummy ta tabe baki tace
" Allah dai ya kyauta"
Daga nan suka koma hirar nayi kankanta ace an biye min anyi min aure, Ummiey da
Mummy sede su kalli juna kawai Amma Babu me bakin magana. A Haka washegari tayi
Kamar yadda aka saka karfe Sha daya zaa daura min aure. Gidan ya cika sosae da
mutane, mutanen da na dinga bukata duk Basu zo ba se yanzun Wai a Haka boye zancen
auren akeyi Dan kada a zarge su da rashin kula Dani. Tun sassafe Kawu Tijjani yazo
shida Kawu Sa'idu, sun Jima da mummy bansan me suke tattauna wa ba, Kawu Sa'idu ya
fara tafiya sannan Kawu Tijjani, ta shigo dakin da nake an shirya ni fes cikin wani
dakakken lilac lace me adon zare maroon, nayi kyau ba karya, na kalla kaina for an
uncountable number and I wishes I was happy, lokaci na farko naji inama ace Yaya
Shehu ne mijina, may be da tuni Ina nan Baki na kamar zai yage Dan farin ciki.
Nayi mamakin duk shige da ficen da akeyi Babu Uncle Babawo, har na tambayi Anty
Nafisa lokacin da ta saka ni a gaba da abinci, nace
" Banga Uncle ba"
Ta danyi murmushi tace
" Tun shekaran jiya Yana kazaure, munyi waya dashi Yana Hanya"
Nayi shiru Ina Wondering me ya kaishi Kazaure, ban dai ce komai ba na dauka spoon
din na fara cin dambun shinkafar da nace zanci. Babu jimawa Sha daya ta doka aikuwa
Babu ko Kara minti akan lokacin aka daura min aure ni da Junaidu, what a destiny,
mutumin Dana gani sau daya, ban ma taba jin muryar shi ba, zuciyata tayi min nauyi
Dole na sulale daga cikin cousins Dina Dan kawayena Babu Wanda yazo tun ranar
walima hatta Sauda Bata Kara zuwa gurin bikin ba, daga ni se cousins dina su Rooks
dasu Nads se Wanda sukazo daga Maid da ko Gama rike sunan su banyi ba. Ina nan naji
gidan ya kacame da guda da Kuma kiraye kirayen isowar ango, da sauri nayi toilet na
kulle kofar tareda jingina kaina jikin kofar, a hankali hawaye masu zafin gaske
suka cigaba da sakkowa akan fuskata, na zauna dabar a saman tiles din da suke
malale cikin bandakin bama na tsoron soiling kayana, kawai sanyi nake bukata, so
nake na samu abinda zai saka min naji sanyi a jikina, na Jima Ina kuka seda naji
zuciyata tayi dadi sannan na Kuma daina jin muryoyin mutane nasan ya fita, na saka
wipes nayi wiping fuskata sannan na wanke na fito, Anty Bintu ce kadai dakin alamun
jirana take, na saki Mata Murmushin karya, ta Bata Rai, ta fisu sakin fuska hakan
yasa har na Saba da ita.
" Me kike yi a toilet tun dazun har angon yazo ya tafi?"
Na sauke ajiyar zuciya jin har ya tafi, nace
" Bana jin Dadi"
Se ta tashi ta riko ni ta fara fada min kowacce mace da Haka ta girma, ni nayi saa
na zaba mijina, Amma Mamana rakiyar marriage alliance kawai tayi Bata dawo ba seda
mijinta, ta min nasiha wadda tasa na Dan ji sanyi a raina sannan ta gyara min fuska
na fita aka fara hotuna Dani. Yadda aka saka karfe uku zaa kaini saboda da Dan
tazara tsakanin Ringim da Kazaure. An Gama shirya ni tsaf, a nada min lafayar da ta
jiku da kamshi Sega Ummiey ta shigo tace ba yau zaa kaini ba, till further notice.
Na dago Ina kallon ta da mamaki tace min nasa hijab nazo parlon Baban Rooks. Ina
zuwa na samu Uncle Babawo Yana fadin
" Na hadu da babanka Kuma ya fada min halayen ka Dan hakan se ka saki yarinyar nan,
seda nace a jira na dawo Amma aka daura. Kaji tsoron Allah Sa'idu idan Yar kace ai
ba zaka nata Haka ba"
Duk shi kadai yake maganar, Mummy na gefe se ruwan hawaye take yayinda Kawu Sa'idu
yayi fitinfitin akan aure an daura Babu Wanda ya Isa yasa a kunce. Daddy a nutse
yace
" Kai Junaidu mahaifinka da bakin shi yace ya Kore ka saboda kana bin bokaye, Yan
unguwa sunce baka ma zuwa sallah baa taba ganinka a masallaci ba, kaga baka
cancanci Afiyya ba, Dan hakan ga takadda da biro ka rubuta Mata sakin ta duk abinda
ka kashe no Zan biyaka"
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam, First bank of
Nigeria. Send evidence of payment to 0906346725831
Wani irin kallo yake bin dukkanin su dashi, se a lokacin kamanin shi da yake boyewa
suka fito, tabbas he doesn't look any thing near innocent person, yafi Kama da
takkadiran marasa mutunci, a idanun shi kawai Dana kalla naji wani irin tsoron shi
ya darsar min cikin zuciya ta, nayi saurin sunkuyar da kaina Ina jin yadda gabana
yake wani irin faduwa. Ban karasa ciki ba saboda yadda ake tafka rigima, Dan tun
suna maganar a hankali har ta koma kowa jijiyar wuyan shi ta mike, su sunce lallai
lallai Babu inda zanje se ya sakeni Dan bazasu hada zuria da irin shi ba yayinda
shi Kuma ya dage ba zai sake ni ba, da kowanne yayi insisting akan maganar shi se
kawai Junaidu ya mike, duka Suka bishi da kallo Babu wata wata yayo kaina, Bai jira
komai ba ya daukeni cilak tamkar wata teddy ya Saba a kafadar shi ya fita, Kawu
Sa'idu yayi saurin Mara Masa baya Yana fadin hukuncin da yayi ya burge shi, Haka
Ina doka hannu Wana a bayanshi, kafafuna Ina ta hantsila su Wanda ko takalmi Babu
amma ko gezau baiyi ba seda ya direni cikin wata bakar Corolla LE sannan ya maida
murfin ya rufe, glasses din tinted ne Babu Wanda ke kallona, Amma ni Ina kallon
yadda suke magana kasa kasa shi da Kawu Sa'idu, Basu dauki lokaci ba Sega sauran
mazauna parlon sun fito, Uncle Babawo da Daddy suka nufo gurin Amma kafin su karaso
tuni ya shaiga motar yaja uban reverse yayi Kan titi, na saki matsanancin kuka, a
lokacin ji nake tamkar rayuwata ta Kare, tamkar Babu wani farin ciki da yayi saura,
Banda gudu Babu abinda yake Haka ni Kuma ban fasa kukan da nakeyi ba. Tun baya
kulani har na fara jin tsakin shi lokaci zuwa lokaci. Na saka fuskata cikin palms
Dina Ina kuka Wanda yake fitowa daga karkashin zuciyata.
" Keeeeeee! Dallah rufewa mutane Baki da wata muryar ki kamar ta gyare!"
Babu Wanda ya taba jin muryata Bai so ya kara jinta ba, a hankali nake magana cikin
tattausan lafazi, Haka idan kuka nake bawai bude duka muryar nake Ina kukan ba.
Wani katon Abu da nake ta kokarin ganin ya wuce a makoshi na ya Kara zuwa ya tokare
min, hawayen da kukan memakon su ragu se Kara gudu sukeyi Haka muryata memakon na
rage sautin kukan se na Kara fadawa, nasan Babu mijin da zai daki matar sa Koda shi
din... Ban ma Gama tunanin ba naji saukar Mari a fuskata, nakai second talatin bana
ji, bana gani, sewani dum a kunnena sannan idanuna sun rufe ruf Dan kansu. Nasan
Kawu yasha Marina Amma wannan Marin da ban yake. A hankali coordination Dina ya
dawo, senaji Abu Yana bin hancina Ina Kai hannu naga jini ne, kunsan duk azabar da
nake ciki kasa Koda uhum nayi? Nasa hijab Dina na goge hancin Wanda yasa naji wani
sabbabbin hawaye sun Kare balle min, Amma ko sauri Babu. Tafiya mukai sosae sannan
muka Isa Kazaure wadda ake Mata take da Kazaure ta Dambu kowa Sarki! Ni dai kaina
na a sama saboda na samu jinin ya daina zuba, ban masan iya inda muka ketare ba se
ganina nayi yayi parking gaban wani gida, ya kashe motar sannan ya kalleni tareda
sakar min harara wadda tasa kayan cikina motsawa, na fasa me yasa nake jin tsoron
shi har Haka
" Ke jaka ce? Se ance Miki ki bude ki fita?"
Hannuna na rawa na Kama handle din kofar na fita, Yana tsaye na mayar na rufe
sannan na rufa Masa baya har ya bude kofar ya Shiga, kafata ta dama na saka na
Shiga, Ina karanta adduar da Mummy da Ummiey Suka dinga nanata min, hawaye ya
cigaba da sakko min, wani na korar wani. Babu abinda kake ji se sniffing Dina, ya
juyo ya maka min harara wadda tasa nayi saurin hadiye kukan, gidan safe content ne,
parlor muka fara shiga madaidaici, yayi balain kyau tabbas interior decorator ba
karamin wonderful job tayi ba. Parlon purple ne light da dark Amma light yafi yawa
hakan ya haskaka shi, na shagala Ina kallon parlon, ya shige ciki ni Kuma na rakube
gefe guda, se wajen bayan thirty minutes sannan ya fito ba tareda ya dubeni ba ya
fice abin shi Yana zura makulli cikin aljihu, na Jima a zaune Ina tunanin abinda
bansani ba, naji Kiran sallar laasar, na Mike na nufi inda ke gefe Ina hango kofofi
daya na kallon daya, dama Wanda ya shiga a gefe yake, Kuma ya kulle nasan nashi ne.
Tunda dama Ummiey tace da Suka zo jere se maida kayan dakin shi akai tunda na 3
bedrooms aka siya. Na bude dakin farko, komai na coffee ne se labulayen ne brown
sunyi kyau, Kuma daga gani furniture din sune manya Dan gadon ma abin kallo ne. Na
bude dayan shi Kuma Ash da red ne, very simple yet elegant. Na shiga nayi wanka
sannan na fito da alwala a jikina , na bude wardrobe Ina kallon yadda aka gyara min
kaya, hawaye a hankali ya siraro min, kamar mafarki nake ganin komai, Wai nice me
aure, wannan gidan Wai nawa ne nice matar gidan, I couldn't believe it. Nayi sallah
na shirya cikin dakakkiyar shadda mustard yellow da Lacy edge Baki, na gyara
fuskata kamar yadda aka min nasiha, na daura dankwalin da ba Gama iya daurawa nayi
ba, na koma dayan dakin inata bude bude, Amma bawai kallon content din abun nake ba
gaba daya hankali na baya Kan abinda nake, nayi nisa sosae Ina ayyana anan Kuma
wacce irin rayuwa zanyi? Banga alamar akwai jin Dadi ba, na shafa fuskata da ta Dan
tashi saboda Marin da ya zabga min, na girgiza Kai se na samu kaina da adduar Allah
ya kawo min dauki!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam first Bank of
Nigeria. Send evidence of payment to 09063467258[05/01, 14:34] +227 98 36 59 34: 32
Hajja Huwaila na zaune cikin daki, tayi rama sannan shekaru sun Kara Hawa kanta duk
ta tsufa, balle a yaddaa take jin zuciyata me dauke da mikin kusan shekaru Sha
biyu, tun ranar da Malam ya furta korar da yaiwa Junaidu,Kuma Junaidun ya fita Bai
Kuma Kara waiwayar gidan ba, Babu wnai dare da idan yazo zata kwanta Bata Yi kukan
rashin shi ba, sannan kullum se tayi Masa adduar shiriya sede kullum tana zuba idon
kallon kofar gida taga ko zai shigo Amma har yanzun Babu amo Babu labari, har ta
gaji ta hakura sede dukda hakan kullum se tayi maganar shi, Amma Kuma wani barin na
zuciyar ta na tuhumar ta da rashin tarbiyantar da shi akan daidai shiyasa ma har ya
Zama lalatacce Haka. Sadiya ta shigo dakin bakinta dauke da sallama , Amma Hajja
din Bata amsa ba, ta zauna cikeda rashin kuzari da Kuma sanyin jikin ganin
mahaifiyar tasu a Haka tace
" Hajja! Wai se yaushe Zaki sararawa zuciyar ki ne? Shekara Sha biyu fa, kilan ma
ya manta dake"
Hajja ta saki hannunta tana kallon Sadiya tayi murmushi me ciwo tace
" Da zai iya manta uwar shi Amma Ina me tabbatar Miki ko da ya manta Dani ni din
bazan manta dashi ba, ba Kuma Zan daina Masa addua ba. Baki San dadin da ba"
Tayi kwafa cikeda bacin ran maganganun Hajja tace
" Dukkan mu mu biyar Muna nan, muna Miki biyayya Amma kin kwallafa Rai akan wancan
gantalallen"
" Sadiya! Tashi ki fita min a daki"
Ta mike tana zumbura Baki ta fice, ita kam Babu Wanda ta tsana irin Junaidu a
ganinta shi