Advertisements
Chapter 17 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 31

48K to 51K   out of 90.3K words

saka hannun shi ya angaza ni
na fada Kan gadon, kaina ya bugu da katakon gadon wani azababben zafi ya ratsa
kwalkwalwata da dukkan jikina, Babu shiri na saki wani ihu Wanda yasa yayi saurin
sakina alamar ya tsorata, ganin ba wani Abu bane yasa Bayan hannun shi ya buga min
a fuska a take hancina ya fara jini, saboda dukan ya kai. Na saki kuka marar sauti
bani ma da karfin yin me sauti, ya dage skirt din jikina ba tareda wani romance ko
wani Abu ba ya fizge pant din jikina, it's more like a rape than normal marital
affair! Wani ihu na saki Ina kankame jikina, tamkar Zan hadiyi zuciyata Haka naji
lokacin da naji bare skin din shi na gugar nawa bare skin din, ture shi nake Amma
Ina Bai ma ji, se wajen minti uku naji banji komai ba se tsaki da ya saki tareda
ture ni gefe, nayi saurin tashi nayi toilet na kulle na daura kaina kan sink na
saki marayan kuka, kuka nake da karfi zuciyata da dukkan jikina kunci suke, kuka
nake na rashin madafa, na rashin gata, na rashin sanin yadda zanyi, Ina jin
kaddarar tayi min tsauri, a Haka Zan cigaba da rayuwa, I'm been molested, wacce
irin rayuwa ce wannan? Nayi kuka har bansan iyakar lokacin da na dauka a toilet din
ba, se a karshe na fito na samu baya nan. Tun daga nan na rufe kaina a daki na fara
laluben cikin drawer inda nan Rooks tace min ta aje min sako. Wani Dan karamin
diary na dakko daga ciki, na kalla diary take na tuna shi, why did I forgot about
it? Na tambaya kaina da mamaki, na kalla buttons din na tuna a cikin jirgi yake
cemin passcode din date of birth Dina ne, na kankame littafin na saki kuka Ina
fadin


" Abbu I missed you, Abbu ka barni cikin wahala"


Na dinga kuka Ina jin wata irin kewar shi tana Kara mamaye Raina, iyaye sune komai
lokacin da suna da Rai Babu abinda na rasa, kowa Sona yake, kowa kaunata yake, duk
inda naje rubibi na ake Amma kalleni yanzun, ni dinnan dukka gata na cikin kiftawar
idanu komai ya lalace, banida wani gata, banida wanda Zan saka kaina akan kafadar
shi nayi kuka, wannan itace rayuwar? I'm been tortured a hakan yanzun Zan cigaba da
rayuwa? Na Kara sakin kuka na bare bakina wanting to pour out my heart all, Ina son
naji zuciyata tayi wasai, bana son naji Koda digon bacon Rai, nasan na rike da yawa
at this rate Ina jin kamar zuciyata zata fashe kamar bakin ciki zai kasheni. Na
Gama kuka na sannan na Danna code din se gashi ya bude, na fara shafa littafin
rubutun shi ne a ciki, ta gefe pictures Dina ne, title din chapter ARRIVAL OF OUR
PRINCESS! kalamai ne masu Dadi masu sanyaya zuciya Wanda zasu tabbatar maka ko daga
wanne baki ya fito to tabbas ba karamin son Wanda aka rubuta danshi suke ba. Na
saki kuka Ina fadin


" Abbuna!"


Ganin kamar zanyi hauka yasa na rufe na Yi alwala nazo na dauka casbaha na fara ja,
a hanakli naji nutsuwa tana saukar min, se naji kamar an bude zuciyata damuwa ta na
evaporating cikin iska!




Junaidu ya kalla kanshi, ya kalli kofar Dana kulle yana iya juyo ihun kukan da
nake, ya Kara kallon manhood din shi dake a kwance Babu alamar erectile muscles
dinsa na aiki, ya Mike a mugun fusace ya maida wandon da sannan ya fito daga dakin,
hannun shi na rawa ya fara Kiran Safiyyu


" Yane angon Amina?"


Ya buga tsaki yace


" Taki tashi!"


Cikin rashin fahimta Safiyyu yayi dariya yace


" Ka haike ma yar mutane Allah yasa baka kashe ta ba, wa yaga farin Shiga, ko nazo
muje asibiti?"


Ran Junaidu ya Kara baci yace


" Banma shiga jikinta ba, abar Taki tashi kwata kwata..."


" What?!"




Safiyyu yayi exclaiming cikin mamaki yace
" Me ya faru?"


" Da na sani Zan kiraka ne? Fada min zakai yadda zanyi, golden time din na tafiya
fa!"


Safiyyu ya fara tambayar shi yadda akai ya fada Masa shi kaiwa afka min yayi,
Safiyyu ya dinga dariya yace


" Malam ai ba Haka zakai ba, se kayi romancing dinta kafin..."




" Kaga ni fa Banda wannan Saar bana tunanin Zan taba kallon mace naji wani shaawa"


" To Haka zaka Bari lokacin ya wuce, nasan ba sonta kake ba ba zakai shaawarta ba,
to Amma idan ba Kai amfani da ita ba kenan kawai Sa'idu ka cikawa burin shi, kaga
ya samu dukiya sannan ya saka kana bawa yarinyar da Bata ji bata gani ba wahala,
kaci sadakin ka !"


Haka yayi ta zuga shi har ya amince, nikam nayi wanka na fito saboda yunwar da nake
ji, Babu abinci alamar ya shigo yaci kenan, spaghetti na dakko na dafa daidai
cikina Dan bazan bashi abinci ba, alkawari nayi tunda zai iya daga hannu ya dakeni
to tabbas na daina dafa mishi abinci. Ina Gama sauke taliyar na juye cikin
collander, nasa stew din cikin microwave na fara warming, tana gamawa na juye a
plate har lokacin bawai Ina jin ni din farin ciki nake ba Amma dai Babu laifi na
samu sauki. Na fito rike da plate dayan hannuna da ruwa, shi baya sallama Dan Haka
ban maki shigowar shi ba, Yana zuwa tamkar wani dabba ko Dan dabba ne tunda
dabbbobi kawai ke amfani da wannan approach din ga partners dinsu. A tsorace na
saki plate din hannuna ya tarwatse Haka ruwan ya bi nashi gurin, ya janye hijabina
Wanda ya bayyana rigar dake jikina, Bayan nayi wanka Naga Babu amfanin saka Kaya
kawai se na dakko daya daga cikin kayan baccina thigh lenght silky milk, duk kirjin
net ne me Asalin kyan gaske, tayi exposing dukkan boobs Dina a waje, ya keta rigar
wadda ta bayyana jikina take na silale kasa a kokarin Kare kaina ya bini ya fara
exploring jikina, ana cewa wannan abin nada Dadi ko? That's idan zuciyar ka da
gangar jikin ka ta amince, ni din Banda ciwo kunci, bakin ciki, tsoro , bacin Rai
Babu komai a cikin zuciyata, Ina kallo ya raba kanshi da kayan jikin shi, ya daura
bakin shi a nawa duk yadda nake kokarin kaucewa ban iya tserewa wannan awful kiss
din ba, it was a moment da bana son a rayuwata na Kara tunawa, it was the most
hardest moment of my life, Ina ihu Ina komai Ina Kiran sunan Allah, Ina kwalawa
Rooks kira, Ina neman taimako se naji an hankada ni for the second time his manhood
refuse to erect, ya saki wani ihu tareda yin wurgi da wani flower vase dake Kan
center table, yana zuwa bango ya baje Karin aiki kenan, nayi saurin mikewa na nufi
dakina Ina adduar Ina ma na koma gidan Kawu Sa'idu ya fiye min wannan zaman balain
da kuncin!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment through 09063467258.36




Mu muna daki bamu San abinda take faruwa a parlor ba, Rooks nata kokarin ganin ta
fahimtar Dani akan na dauki zaman mu dashi a matsayin jihadi, nayi kokarin daidaita
rayuwar shi, kilan shi ne dalilin da yasa Allah ya kaddara auren mu, nidai nasan a
kur'ani ance mace ta gari ta miji nagari ce, Dan Haka na sawa Raina ko ba yanzun ba
ko da watarana ne se na rabu dashi, Kuma jikina na bani komai ya kusa zuwa karshe.
Se yamma sannan Suka dauki hanyar tafiya, banyi kuka tunda Banga amfanin kukan ba,
I've cried enough da ace kuka na canja ma mutum rayuwa tabbas da tuni bana cikin
kuncin da nake ciki. Har gate na raka su Ina kallo suka tafi, na maida kofar na
rufe na dawo na zauna a parlor very deep in thought, to Babu abinda zanyi seda suka
gyara min komai da komai sannan Suka tafi. Ina nan zaune har dare yayi se wajen Sha
daya naji motsin shi, ya shigo yadda Bai cemin ci kanki ba Haka Nima bance Masa ba,
na maida hankalina akan kallon da nakeyi. Dakin shi ya wuce na zata bacci zaiyi Dan
Haka na Kara sakin jikina deeply immersed a tunani, Dan ba ma gane abinda akeyi
nake ba, tunani na duka Yana kan maganar da mukai da Rooks, nasan duk maganar da ta
fada gaskiya ce Zan iya Zama silar shiryuwar sa but that's only idan Yana sona, to
nikam kullum kallon da yake min kallon tsana ne da irin Bai taba ganin Abu so
disgusting like me ba. Na sauke ajiyar zuciya Ina jin ta Ina Zan fara? Ya kamata na
saka shi ya fara sallah but ta Yaya? Banma San Wasa nake da bakin wuta ba se
washegari, very early na tashi wannan macaroni da banci ba saboda zuwan su Rooks na
dafa na zuba cikin karamar warmer na aje sannan na danyi gyare gayren da ba zaa
rasa ba na Yi wanka na shirya cikin bakar Abaya gashi na na kalla gaba daya ya
cunkushe Ina bukatar kitso, duk lalacewar zamana a gidan Kawu Sa'idu Ina zuwa
kitso. Na dakko comb na taje na saka band na kulle Kan na daura dankwalin abayar,
Dana fito ya riga da ya fito Yana zaune kana kallon shi kasan Bai wanke fuska ba,
na karasa nace


" Ina kwana?"


Bai cemin komai ba Wanda yasa na fara jin haushin dalilin da yasa na Masa magana ma
in the first place. Kitchen na wuce na zauna na zuba Mai da yaji naci abincin da
duk yadda na Kai da rashin cin abinci da yawa Bai gamshe ni ba. Na Sha ruwa na fito
Yana nan inda na barshi se kawai na shige daki na kwanta Ina juyi Ina jin
matsananciyar Yunwa na addaba ta. Kwalla min Kira yayi yasa na fito, alamar zai
fita Dan yayi wanka ya Kuma canja Kaya, ya dubeni da ga sama har kasa yace


" Ki shirya zakije can gidan'


Na gyada kaina ba tareda nasan wanne gidan yake nufi ba, ciki na koma na canja
kayana zuwa zani da riga na atamfa na dauka babban veil na yafa sannan na Dan
tsinci abinda zanyi tsaraba dashi na fito, yayi gaba na bishi a baya, a kusan
watanni biyu wannan ne Karo na farko Dana saka kafa ta a wajen gate, banma San ya
yanayin unguwar yake ba, duk yadda ya kamata na Shiga makota na Amma ko kadan ban
shiga ba, wa ya Isa ya barni inama Naga fuskar tambayar. Motar shi na Parke kofar
gida se kyalli take, wani yaro a tsaye ya samu kwankwalatin lemu ya fara karto Masa
mota tun daga farkon bomber zuwa karshe, kwankwalatin Nan ya cika Tam da paint din
shi, nayi saurin saka hannuna na rufe bakina tausayin yaron da iyayen shi suka Kama
ni, nasan yau rashin arzikin da Junaidu zaiyi se inda karfin shi ya Kare, ga yaron
ya kusan 10years hakan ya nuna Yana sane yasan abinda yake ba daidai bane. Na kalle
shi na dubi yaron da ya Yar da kwankwalatin ya nufi gidan su a guje, Junaidu ya
cire rigar shi ta bayyana farar singlet din dake jikin shi, ya wullo min rigar a
fuskata ya take kafafun shi yabi yaron nan da already ya riga ya shiga gidan su, na
bishi da sassarfa Dan kada ya Shiga gidan mutane Amma nasan ni wacece, Ina zuwa ya
Kama yaron Yana dukan shi tun karfin shi, ga uwarshi nata balai Amma ba zata iya
kwatar shi ba. Na karasa na ruke hannunshi ba tareda nasan nayi hakan ba, saboda
dukan yadda kuka San saan shi yake yiwa.


" Dan Allah ka rabu dashi, Dan Allah!"


Na fada Ina rike hannun shi, ganin yadda nasa karfina gaba daya na rikeshi, se yasa
hannun shi ya bugeni, nayi baya tamkar Zan Fadi wata budurwa a gidan ta Dan girmeni
ta rikeni seda na tsaya da kafafuna kafin ta sakeni, ya saki yaran Yana karbar ko
nace yana wartar rigar shi a hannuna ya fice, da sauri nabi bayan shi na samu sunyi
kicibis da Wanda nake tunanin shi ne baban yaron,


" Wa yace ka.shigar min gidana? Na Dade da sanin Kai jahili ne Amma bansan abin
naka har ya Kai Haka ba, Dan Haka yau ofishin Yan sanda zaka kwana"


Banyi tunanin zaiyi Masa shiru ba Amma ga mamakina se Naga ya wuce ta gefen shi,
hannun shi ya rike tareda fadin


" Ina zaka je kake tunani? Ka shigar min gida ka Kuma Dakar min Dana sannan kace
zaka tafi, karya kake wallahi!"


Junaidu ya dubeshi ya Kuma dubi hannun shi dake rike hannun mutumin, nasan he's
going to do something stupid, nayi saurin kallon mutumin nace


" Dan Allah ka sake shi, ka bashi hakuri Dan ka ya Karta Masa mota"


Ya min wani mugun kallo da inaga ko Junaidu Bai taba min wannan disgusting look din
da yasa naji ni totally embarrassed irin kallon da mutumin yayi min ba


" Rufe Mana Baki karuwar banza karuwar wofi, mu munyi tunanin babbar mace ce ma
Ashe kece"


Se nayi shiru Ina jin jikina yayi balain sanyi, karuwa? Na tambaya kaina Ashe ban
sani ba kallon da duk Yan unguwar kemin kenan ni din karuwar shi ce, suna ganin
Babu iyayen da zasu dauki Yar su su bawa Junaidu aure, take na ja kafafuna da nake
jin Kamar anyi musu duka na nufi jikin motar shi Ina tsaye, mutane suka taru saboda
police har sunzo, ni ba damuwata abinda suke ba, damuwata kallon da ake min da nuna
da ake Yi shi ne matsalata gashi Kuma ya kulle gidan sannan a yadda temper shi take
high Ina Masa magana zai iya nada min duka cikin mutanen nan ba damuwar shi bace.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 0906346725837




Ina daga can gefe idanuna s unyi ja, a karamar shekara ta na kunshi bakin ciki
kalakala Amma kowanne idan yazo Ina ganin kamar Zan iya coping se na kasa, baa taba
sabo da Shan wahala. Tabbas ance kudi masu gidan Rana, quite sure kowa yasan yaron
ne bashi da gaskiya Amma Junaidu ya dauki hukunci a hannun shi, ya Shiga gidan
mutane sannan ya daki Dan mutane duka irin Wanda zaka yiwa saan ka, yaran duk
fuskar sa tayi kacakaca da jini Amma a haka police officer ya cahrge iyayen shi
akan se sun gyara Masa damages sannan su bashi hakuri Kuma, instead shima ayi
charging dinsa for assault se suka kyale shi. Ina ta kallon ikon Allah, Haka Suka
juya Bayan sunyi musabaha dashi suka tafi su Kuma parent din yaran suka dauki dansu
zuwa asibiti, gashi tunda daga gidan kasan karamin karfi ne dasu Amma ai ya kamata
ace ya biya kudin ko da magani ne. Muatnen gurin se tsine Masa suke suna fadain
daga shi har Wanda ya rabe shi a wuta zasu, ni dai duk a tsorace nake ya dubeni ba
tareda ya min magana ba ya bude gidan ya shiga, na bi Bayan shi cikin sauri jin an
fara cewa ki jefe su, Ina Shiga dutse Yana bugan gate din, na sauke ajiyar zuciya
Ina godewa Allah da Bai sameni ba, na shiga parlon na sameshi yayi daidai da drink
a hannun shi Yana sha, ko Zama banyi ba aka Kira azahar naje nayi alwala na dawo na
samu ko matsawa baiyi ba, nayi sallah na dawo nace Masa


" An Kira sallah gashi har an idar ma!"


Yayi min banza kamar yadda ya saba, maimaikon na kyaleshi se nace


" Ba kyau abinda kake Yi, abinda yake raba Arne da musulmi sallah ce kawai, tunda
Suma a cewar su ai suna azumi Amma sallah ce basayi, Kuma idan kana sallah in har
ta karbu ko sauran ayyukan ka baa dubawa..."




" Keeeeeee! Ni saan ki ne?"




Naga karfin halina nima, nace


" Ai waazi ba se saa ne yakeyi ba, baka ganin malamai nayiwa shugaban kasa waazi
ba? Hakkina ne na fada maka gaskiya Dan idan ka mutu a Haka Allah kadai yasan me
zai ma..."
Ban ma karasa ba naji saukar kyakyawan Mari a saman kuncina, na Mike tsaye idanuna
Suka ciko da hawaye Amma har lokacin bakina yaki yin shiru na cigaba da fada Masa
abinda ya kamata a fada masa aka ki fada masan, ni kaina nayi mamakin daga Ina na
samu wannan confidence din? Ban taba ganin bacin ran shi irin wannan ranar ba, ya
dakeni kuwa ranar, Dan duk jikina seda yayi birdin dukan da yayi min, nayi ta kuka
a daki ni daya Ina jin duniyar gaba daya tayimin zafi but I still have to pick
myself up, tunda Allah yasa ba mutuwa zanyi ba to ya kamata nasan abinyi, bazan
cigaba da Zama cikin wannan rayuwar ba, Dole na nemawa kaina mafita.




Watanni biyu suka Kara Hawa akan Wanda nayi a gidan shi, ya tsiri wasu halaye Kuma
na daban kullum se ya dakeni ko nayi Abu ko banyi ba, idan zai fita se ya daina
barin gidan a bude se de ya rufe ni ta waje, gaba daya na hargitse banida wani aiki
se kuka se plotting yadda zanyi na bar gidan, Babu Wanda ya Kara zuwa gurina se
mummy da Rooks shima har kofar gidan suka zo Suka kirani se kawai nace ai bama nan
munyi tafiya to ta Ina Zan fada musu cewar ya kulleni ne a gidan, lokuta da dama
Ina jin ana knocking Wanda nasan Yan gidan su ne Amma Babu halin shigowa,zancen
abinci sau daya ne a Rana yake bani, I remembered na taba jin suna waya da Kawu
Sa'idu kafin ya fara bude min wuta sosae


" To Kai me kake tunani? Ni kaina bansamu abinda nake so ba, ai cewa akai se na
kusance ta kafin burina zai cika, ni banyi ba Banda asara me auren ta ya tsinana
min?"


Daga dayan bangaren Kawu Sa'idu yace


" Ni kaina bansamu abinda nake so ba Sabida Kai dinne madaogara, Amma ya zaayi kace
min ka kasa kusantar ta Bayan na aura maka ita"


Junaidu ya dunkule hannun shi yace


" Zancen banza kenan! Idan Haka ne Zan sake ta Dan na gaji da ajiyar ta tunda ba
amfani take dashi ba"


" Baka amsa tambaya ta ba, me ya hanaka ka kusance ta, Kuma ya zaka saketa bamu
cika burin mu ba"


Se lokacin Junaidu ya Masa bayanin Ashe Erectile dysfunction or damun shi, an samu
hakan bayan dogon bincike da akai a asibiti suka fahimci trauma ne na dukan da Yan
sanda Suka ta Masa lokacin samar takar sa, ranar yini nayi Ina farin ciki a ganina
Allah ne ya fara saka min duk zalincin da yayi min. Nafi tunanin a wañnan wayar
Kawu Sa'idu ya fada Masa yayi ta duka na Dan nasan zaiyi abinda yafi Haka.


Ranar wata lahadi na tashi da zazzabi da azababben ciwo Ciki Wanda nasan Yunwa ce
ta saka hakan, nayi kuka nayi juyin har bacci ya daukeni, se wajen asr na tashi
nayi wanka sannan na fito Dan daura abinci, na samu shinkafar ba tafi gwangwani
daya ba, na dafa sannan na zauna naci, Ina cikin ci naji muryar shi alamar Yana
waya, ya shigo kitchen din ya tsaya Yana kallona, ko

17 / 31