Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da
Abbu ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji
ba.
" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"
" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake
wahala da yarinya Basu ba"
Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace
" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka
yake, ya kamata ace komai Kai kake kula dashi"
Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace
" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta
Afiyya ce ta makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo
ko takaddu gurin Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace
musu kawai sede duk wata su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da
wani abun fa!"
To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin
shi bayan Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny
ranta ya mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se
ya rike ni, hatta kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya
shi, wannan wanne irin rashin zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai
yayan shi da komai nasu shi ke dawainiya dasu.
" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin
girman ki, ke kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na
Miki alkawarin Zan dinga fitar Miki wani Abu a ciki"
Nanny tace
" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"
Ya Mata godiya se tace Masa
" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin
makarantar ta"
Yayi dariya yace
" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar
makarantar ne ai wannan almubazzaranci ne"
Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga
ciki Yana jin burin shi Yana daf da cika.
Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda
ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar
aiki, yayi aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin
Dan kaida ce duk yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam
da Jarma na zuke zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama
influence din su ne, Amma huzaifa Bai ma taba zuka ba shikam Malam he's always the
lead. Bayan an gama maghrib kowa ya Kama gaban shi. Fatima ce da girki tun karfe
hudu ta kammalla haka take badai kaga tayi Daren girki ba. Ruwa ta tafasa ta shiga
wanka, tana watsa ruwan taji wani kaikayi a duk inda ruwan ya sauka, ta dubi
jikinta gurin yayi jawur tamkar ta kone, a gigice ta dubi ruwan tasa hannunta Amma
shima hannun tana fito dashi se kaikayi yayi jawur, zani ta daura ta fito a guje
tana kwalawa Hajja Huwaila Kira, kafin Hajja ta fito tuni Hasiya ta fito ta same ta
tsakar gida tana faman sose sosen jiki, Hasiya tace
" Fatima ya akai?"
Ta kasa magana se nuna Mata take da hannu, tana Susa, lokacin Hajja ta fito itada
Amarya suka samu Fatima tana Neman cire zanin jikin ta, ga yaran duk sun zagaye ta
wasu a ciki na kuka, hannunta Hajja ta kama Suka shiga daki, Suka fara duba
jikinta, duk inda ta Sosa yayi burdi yayi Kuma kwaf kwaf kamar konuwa. Hajja ta Yi
shiru Dan ita ta rasa abinda zata ce tunda take Bata taba ganin abin ba, ta dauka
hijabi tace da Hasiya
" Ke ki zauna da Yara, ni Kuma da Amarya zamuje general, ki aika a fada ma Malam"
Da hakan Suka Taya Fatima ta shirya,suka samu Keke napep Suka tafi general, kowa
idan aka bude gurin gani suke allergy be hakan yasa focus din maaikatan asibitin,
sede ana administering drugs din kamar bama shiga suke ba, in fact tunda jikin ba
bukatar su yake ba kokarin reacting musu take. Anan Malam yazo ya same su, hankalin
shi ya tashi ganin maaikatan sun ce sede su turasu AKTH suga dermatologist kawai,
Malam ya karba takardar, ga Fatima ciwon se Kara Hawa take, se ihu take tana Kiran
sunan Allah tana su taimaka Mata kaikayi zai kasheta.
A wannan Daren da Junaidu ya dawo ya samu gidan tamkar gidan makokin, yaran na
tsakar gida sunyi jugum, Wanda sukai kuka zuwa lokacin sun hakura, Bai bi ta Kan
kowa ba ya shige dakin abin shi ya zauna Yana ayyana ya kamata ace zuwa yanzun
aikin shi yaci Akan Fatima, tunda kuwa Jarma yace Masa tamkar yankan wuka haka
aikin malamin yake, Yana cikin zaune Sega zainab ta leko, tunda sukai abin kudinnan
yarinyar ke shishigge Masa tana son ganin ta wanke laifin ta. Yana zaune ta shigo
ya dago ya kalleta yace
" Meye?!"
Ta zauna tace
" Mama ce Bata da lafiya!"
Ya gyara Zama yace
" Me ya sameta?"
Ta zauna tana kuka ta fada mishi komai, maimaikon taga ya canja yanayin fuskar shi
zuwa tausayi, se taga Yana murmushi, yace
" Abin yazo kenan! Kije zata ji sauki"
Zainab jiki a sanyaye ta fito ta dawo tsakar gida tayi shiru tana tunanin halin da
uwar ta ke ciki, Bata Jima ba suka dawo da Fatima dan a wañnan Daren bazasu iya
tafiya Kano ba sede zuwa gobe. Ihun da take yasa Junaidu fitowa kofar daki ya
zauna, Bai ce musu kala ba Amma se smirking yake Yana kallon yadda Fatima ta Zama
Yar bori, sight din kawai dariya yake bashi, ya zauna yaki tafiya Yana hango duk
abinda takeyi, gasu Hajja Huwaila nata karbar jike jiken ayatul shifaa daga gurin
Malam, Suka zaunar da ita suka Bata Tasha, Yana shiga cikin ta ta fara amai
bakikirin, Hajja ta Kira Malam yana zuwa yace wannan sihiri ne Kuma an karya shi,
Hajja ta rike kirji yayinda Hasiya da Amarya suka furta
"Sihiri malam!"
Ya gyada Kai yace
" Tabbas sihiri ne! Allah ya Bata lafiya"
Suka saka ta kuskure bakin ta, ta saki ajiyar zuciya ta lumshe idanu bacci ya dauke
ta. Malam ya gyada Kai ya juya zuwa dakin shi, daidai dakin Junaidu yaji Yana waya
" Man nake fada maka abin yaci fa, dukda dama ba wani tsawon lokaci zai dauka ba
Amma nasan ta karbi wahala"
Ya Jima Yana sauraron magamganun Junaidu Amma ya kasa gane inda zancen ya dosa, shi
yaron tsoro yake bashi tunda Suleiman yace ya ganshi tsakar dare Yana Kona wani Abu
a kasko shikenan ya koma jin tsoron shi. Shidai yasan kullum Yana adduar Allah ya
shirya yaron Amma Kuma har yanzun abubuwan Junaidu Kara gaba suke. Ranar baccin
dadi Junaidu yayi, Dan burin shi ya Gama cika. Da asuba kowa ya tashi yin sallah,
seda ya Bari kowa ya fita massalaci, masu Yi a gida sun tayar, ya fito Dan shi ba
sallar yake ba se jefi jefi idan ya ga dama. Dakin Fatima ya wuce ya sameta tana
kan sallaya tana sallah, ya zauna Kan kujera har ta idar Dan ita Bata lura da
shigowar shi ba. Tana idar da sallar ya sakko ya nufo ta, da sauri ta juyo zatayi
ihu yace
" Junaidu ne!"
" Me kake min a daki? Fitar min daga daki nace"
Yayi dariya yace
" Ba wani Abu nazo nayi Miki ba, daki da kike cewa na fitar Miki daga shi, ai ni
Banga daki anan ba. Kinga sakamakon zagi da sharri da Kika min, ko Baki fahimci
nine nasa aka Miki sihirin da kikai kaikayin jiya, idan Baki fita harka ta ba Zan
saka an Miki wanda Zaki rasa rayuwar ki gaba daya, ko ki haukace, Kuma wallahi
zakiyi kyau da hauka.."
Yayi dariya ita Kuma tuni jikinta ya fara rawa, tsabar yadda ta tsorata da maganar
shi.
" Idan kinji shikenan kin tsira idan..."
Malam ya bude labulen dakin a zuciye ya Shigo, Fatima da Junaidu lokaci daya Suka
Mike, Fatima tayi saurin matsawa gefen Malam Neman kariya, yayinda Junaidu ya tsaya
sokoko Yana tunanin abinda zaiyi, Wani Mari Malam ya sauke Masa a saman kuncin sa,
yayi baya kamar zai fadi, ya cakumo wuyan shi ya tsayar dashi ya Kara Masa wani,
cikin tsananin bacin Rai yace
" Ni Dana zaije gurin bokan! Malamin tsubbu! A gidana"
Junaidu yayi shiru yana kallon Malam dake janshi har ya kawo shi tsakar gida, dake
fadan malam yasa duk sun firfito Dan ganin meke faruwa, duk suna tsakar gidan yasa
Sukai carko carko suna kallon Malam da Junaidu a hannu, ga Fatima a gefe se hawaye
ke bin fuskarta!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
send evidence to 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 15
Dukkan su lokaci guda suka Isa Kiran da Junaidu yayi musu, ba karamin mamaki sukai
ganin shi zaune da katun katun din jakunkuna, huzaifa ya fara fadin
" Me ye wannan? Se kace zaka bar duniyar"
Yayi Dan tsaki Yana kallon Malam dake zuge jakar da tafi kusa dashi Dan yaga abinda
ke ciki,
" Wai korata akai daga wancan gidan"
Jarma yace
" Wai Malam ya Kore ka kenan? Da gaske?"
Harara Junaidu ya watsa Masa yace
" Da Bai koreni ba ta Yaya Zan dakko uban kayannan"
" Allah ya huci zuciyar ka Man, abinne da bamu kawo ba. Yanzun me zaayi kenan"
Ya fada Yana sassauta murya Dan ya lura Junaidu a fusace yake. Jarma yayi shiru
yana kokarin tunanin mafita, se can yace
" Kai me ka shirya? Meye plan din ka"
Yayi murmushi yace
" Kudi nake son nayi yadda watarana se sunzo sun nemeni sun nemi gafara ta, sun
Kuma nemi kudin abinci daga hannuna"
" Wannan haka yake Man, shi ne hukuncin su na yin watsi da kai, da korar ka da
sukai. To Amma hakan bazai faru ba se mun nema kudi"
Jarma ya gyada Kai yace
" Ni na fara jin watarana zaa koremu muma, Dan haka mu je mu karbo saa sannan se mu
zo mu fara sanaa mu Gina kanmu!'
Da wannan shawarar Suka tafi can shagari Suka sama Masa shago na haya, suka biya
kudi seda yayi settling kafin suka fita Suka barshi Dan sun fahimci Yana son
kebewa. Kwanciya yayi ya lumshe idanun Shi ya fara tunanin yadda zaiyi yayi kudi ya
dauki fansa!
Kwana biyu na daina shiga harkar kowa a cikin gidan, hatta su Mino da muke Dan
magana dasu na daina, aikin duk da nasan nawa ne ni zanyi tun kafin ace nayi na
tashi nayi, duk yadda take kokarin ganin ta dakeni batada wani dalilin dukan,
abinci idan an bani naci idan baa bani ba na hakura Nasha ruwa. Yaya kadai nake ma
magana, Amma shi kanshi Kawu Sa'idu da naji muryar shi Zan koma daki Dan Kar ma mu
hadu, shima Bai tambayi inda nake ba. Na fito daga wanka naji ciwo a marata, na
cigaba da daurewa na saka uniform, na dauki madubi Ina kallon fuskata, Ina cikin
mutane masu doguwar fuska, oval shape, ni ba fara bace fatata me duhu ce dukda
duhun ba can can ba Amma nasan kala biyu Allah ya halitta fari da baki, Babu wani
tarwada Dan hakan ni baka ce, inada gashi Dan banida goshi, kusan gashina har
girata ya hadu, idanuna suna da haske da hakorana, farare ne tas, hakorana Yan
kanana a jere se dimple da nake dashi Wanda ba se nayi dariya ba yake lotsawa ba,
ko magana nayi zakaga ya lotsa, wannan shi kadai ne marabata da Mama, Hajiya tace
min ita batada dimples Amma Ummiey na dashi.
Na Kara kallon madubin Ina ganin yadda idanuna sukai kwala kwala saboda yadda duk
na rame, hancina ya Kara kankacewa dama ni banida hanci, haka yake Dan dus,
kumatuna duk sun zagwanye. Na lumshe idanuna Ina ayyana abubuwa da dama a cikin
zuciyata. Mino tace min
" Zaki makara fa Afiyya, ki tashi ku tafi"
Ita ta fara neco so ba kullum take fita ba, na Mike bance Mata komai ba na zura
hijab na dauki jakata na fita tsakar gida, na samu suna cin wainar flour da aka
soya da safiyar. Ta kalleni tace
" Kizo ga Taki"
Na Isa gurin na dauka Naga kwaya daya ce kamar ma irin kalen robar ne da ya rage
aka soya min, wani Abu yazo wuyana ya tsaya, kamar na wurgar nace ba zanci ba Amma
se na tuna dukan da naci cikin satin, hakan yasa na zauna na cinye na goge hannuna
sannan nace na gode muka fita. Yaya ma samu a kofar gida Yana zaune Kan wani bench
dake gurin Rai da rai, ya Mike ganin mu. Siyama ya mikawa naira dari yace ta siya
Abu ta siyawa Hafsa, karba tayi ta ja hannun Hafsa suka wuce.
" Have you eaten?"
Ya fada Yana zura hannun shi cikin aljihun wandon jikin shi, nayi murmushi tareda
gyada Kai, ya jinjina Kai yace
" Kinyi azkhar? Amma face dinki looks disturbed"
Nayi saurin shafa fuskata tareda Kara yin murmushi nace
" Yes and I'm fine"
Se yayi shrugging shoulders din shi ya Miko min dari biyu yace
" Karba ki tafi, nasan Baki ci abinci ba, use this to buy something and I won't
take no for an answer!"
Ya zanyi hakan na saka hannuna na karba na mishi godiya, na juya Ina jin wani sanyi
Yana ratsa min jikina, da zuciyata, na saki murmushi daidai jin an Kira sunana,
juyawa nayi na ganshi a tsaye ya harde hannayen shi a kirji Yana kallona a sanyaye
Yana murmushi, na tsaya tareda tsare shi da nawa idanun, ya matso inda nake tsaye
yace
" You're beautiful Afiyya, I love your dimples and..."
Se na rufe fuskata da tafikan hannuna Ina sakin karamar dariya wadda shi dayake
jinta seda ta narkar Masa da zuciya har ya gagara karasa abinda yayi niyyar fada.
Juyawa nayi da sauri na nufi makaranta, Amma kunnuwana se echo muryar shi suke min
na abinda ya fada, lokaci lokaci se na shafa dimples din nawa na saki murmushi. Ina
zuwa gate Naga an fara Taran makara, na karasa Naga su Siyama ne Dan ita tana ss2
Kuma tunda Babu ss3 Dole su zasui taking charge, tsuggunawa nayi kamar yadda
kowanne late comer ya tsugguna, daga can naji Siyama a gefena tana fadin
" Ina Kika tsaya? Yaya ne ya tsayar dake ko?"
Na gyada Mata kai, tuna sunan shi sena fara picturing fuskar shi Yana min murmushi,
nayi saurin runtse idanuna Dan na bar ganin fuskar shi. A cikin prefect din naji
wata tana cewa Siyama
" Har yanzun wadda Kika daukarwa excuse din Bata zo ba?"
Siyama ta kalleni sannan tace
" Gata tazo"
Ta fada tana nuna musu ni, a take akace na wuce class, na kalli Siyama na Mata
Murmushin godiya sannan na wuce class na samu malamin English din Bai riga ya shiga
ba, na sauke ajiyar zuciya na zauna gefen Sauda dake fama da phrasal verb cikin
comprehensive passage,
" Yawwa Amina Abubakar tun dazun nake jiranki, me yasa Kika makara yau?"
Na Mika Mata hannu mukai musabaha nace
" Ki Bari kawai, surutu na zauna Yi"
Tayi dariya tace
" Ke da har surutu kike? Lallai Kam! Kinga duba min wannan kamar adverbial phrase
ko?"
Na gyada Kai daga haka na shiga nuna Mata na time, na place da sauran har malamin
ya shigo.
A tsaye Dana bar Yaya, Bai matsa ba ya cigaba da bin bayana da kallo har na kulle
ya shafa Kan shi tareda Ciro wayar shi dake ringing cikin aljihu, baikai ga picking
ba yaji muryar abokin shi Nuhu Yana fadin
" Naga dalilin palpitations yau"
Yaya ya daga kanshi Yana Sosa Kai ya dubi Nuhu dake dariya kasa kasa yace
" Doctor! Me kake nufi"
Ya samu guri ya zauna, shima Yaya ya zauna Suka gaisa sannan Nuhu ya dubi Yaya yace
" Engr. Kwanaki ka kirani akan kana tuannin kamar heart failure na damun ka?"
Yaya ya shafa Kai yace
" Eh lokacin gaba daya yadda kasan ana farautar rayuwata ne, Ina jin yawan faduwar
gaba matsananciya, wani lokaci har haki nake fa, but yanzun na daina ji"
" Haka kurum kake hakan ko se kaga wani Abu?"
How is he supposed to start saying se ya ganni sannan wannan symptoms din ke zuwa,
Dr Nuhu yace
" I guess waccan yarinyar ita ce dalili ko?"
Ya kalle shi da sauri Yana kokarin musawa Nuhu ya dakatar dashi da fadin
" No! Ita ce. Bari na fada maka gaskiya sonta kakeyi, you're deeply in love with
her sosae, Ina fatan ka fahimci hakan?"
" Yarinya ce bana tunanin tayi 15 yrs ma"
Nuhu yayi dariya yace
" Baka ji ba akace age is just a number ba! Ai ya mafi Dadi gidan ku daya, tana
yarinya se ka kissima Mata sonka cikin zuciyar ta"
Yaya yayi shiru yana ta aunawa a karshe yasan hakane so na yake Amma Yana hango how
possible is it muyi aure?
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 17
Kamar yadda Nuhu ya bashi shawara kawai ya fara yada propaganda din shi akaina,
hakan yayi, ni kaina bazan iya ce muku ga yadda akai ba, kawai dai nasan na ganni
tsumu tsumu a cikin soyayyar shi, bazan ce ga ta inda aka fara ba Dan Nima banyi
aune ba se kawai jina nayi deeply in love with him. Da farko dai nasan ya tsiri Yi
Mana lesson, duk lokacin da aka idar da sallar maghrib lokacin zai dakko past
questions dinsa na neco da waec Wanda suke in a book form, zai Kira mu nida Siyama
mu zauna muyi karatu, yawanci Siyama Bata da interest dukda ita din ce qualifying
exams din ke gabatowa amma Babu wani hankali da take mayarwa duk iya kokarin kuwa
da Yaya yakeyi Dan ganin tana fahimta. Ya bamu wani question ta maths ta 1994 muyi
solving, na dage Ina ta cracking brain dina wajen ganin nayi solving Amma ita wani
littafin hausa ne a hannunta ta saka cikin note book dinta me suna zazzafar kauna
in jita da Fadi. Na Gama na dubeta Naga yadda take murmushi kamar bakinta zai yage
nace
" Siyama Wai ba Zaki zo muyi solving ba har se ya dawo"
Ta ture hannuna daga littafin seda ta Kai karshen page din sannan ta dubeni tana
murmushi tace
" Ke rabu dani, bazan zauna nayi ta Bata lokaci na ba"
Da mamaki na kalleta nace
" Karatun ne Bata lokaci? Lallai Kam!"
Tace
" To meye amfanin shi, kina ganin dai Ina gamawa aure zaayi min meye abin damun
kaina!"
Nace
" Ke Siyama! Ta Ina Kika sani?"
Tayi dariya tace
" To Mino aure zaayi Mata, Baki ga ranar an kawo Kaya gidannan ba, to kayan ta ne
tana gamawa aure zaa mata. Barni nayi karatun soyayya ta ita zata fushe ni"
Nayi Jim jikina duk yayi