Advertisements
Chapter 29 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 31

84K to 87K   out of 90.3K words

wayar Ina murmushi Nima, seda na idar sannan na fito zuwa dakin Mom na
samu suna Hira itada Anty Falmata, na zauna sannan nace Mata


" Wai Daddy ne zai zo"


Ta kalleni tace


" Wanne Daddy?"


Nace


" Daddyn su Nads"


Duka seda suka tambayi lafiya, na girgiza Kai alamar Nima ban sani ba, Anty Falmata
ta mike ta dakko min Kaya ita Kuma Mom ta fita ganin yadda parlon yake. Baa fi
mintina goma ba se sallamar yaro akan suna so ayi musu iso, kafin Anty Falmata ta
fita se gashi sun shigo da Dad da Kuma Abiey. Honey da Yaya Sarki na bayan shi.
Seda Suka zauna Mom ta kawo musu drinks Yana ta dariya Yana fadin


" Haba dai kamar bako? Dan Allah karki da naji kunya"


Sukai dariya sannan suka gaisa da Nanny Yana ta Mata cewar ko ganin ta baayi, ni
Kuma Ina daga daki Ina jiyo su, I never thought Yana Wasa haka, saboda shi Bai Faye
Zama kamar Abban su Rooks ba, duk da dai dama nafi sabawa da Abban Rooks akan shi.
Na fito tare da Anty Falmata, na je har gaban shi na tsugunna na gaishe shi, ya
kalleni sannan ya kalli Shehu yace


" Da ba Haka take gaishe ni ba, she always greet me cheerfully. Me Borno what have
you done?"
Kowa yayi dariya sannan ya dubeni yace


" Uwata tashi ki zauna kinji? I'm still your father"


Na tashi na zauna a kasa kamar yadda Naga Yaya Shehu da Yaya Sarki sukai, na gaida
Abiey sannan Daddy yace


" Nasan duk kunyi mamakin kiranku da nayi ko? Ba wani Abu bane kawai Ina son na Dan
Kara taunasara da Me Borno da uwata akan muhimmancin addua. Nasan wannan yaron
Junaidu ya dawo Neman aurenta kafin Shehu yayi winning, kunsan wannan jarabawar
Allah ce? Allah ya jarabce shi da sonta Dan ya gwada imanin shi da Kuma karfin
shiryuwar da yayi. Abinda mamaki suddenly yaro ya dawo Kan hanya, se Kuma ya dawo
Yana son abinda ya wulakanta, ya daka ya muzguna ma, da kanka Baban Afiyya kace ka
yadda da son da yake Mata, it's boldly in his eyes ko? To wannan yaron zai iya
komawa ruwa yayi duk abinda zai iya Yi Dan aurenta, ko ba Haka ba? To shiyasa nake
son mu hadu muyi addua iya karfin mu, farin ciki ya daure Mana cikin rayuwar mu
Baki daya"


Abiey yace


" Wannan Haka yake Wambai! Tabbas Nima da abinnan nake kwana nake tashi. Muyi addua
sosae saboda komai ya tafi daidai"


Bayan anyi doguwar addua sannan Suka tafi Nima na zauna Abiey da Kuma Dad suka Kara
nuna min muhimmancin abinda Daddy ya fada, na koma daki na cigaba da shirina, se
hakan yasa na zauna na fara lissafo abubuwan da Junaidu zai iya yi.




Saura sati daya biki aka kawo kayan lefena, acan gidan Waziri anan aka karba lefe
na, se yamma sannan aka jibgo su cikin mota aka kawo gida, dakin Mom aka kaishi, ni
dasu Rooks mukaje kalla, komai ka daga kasan bana Wasa bane, kayan sunyi kyau
sosae. Se lokacin na Kara tabbatar wa tabbas da gaske auren zaayi. Bayan min Gama
kalla Mom ta kirani daki anan na same Ammi Maman Basma, Mummy shikenan. Na zauna
aka fara min fada ko nace nasihar aure wadda kusan duk tuni ne akan wadda Anty
Nafisa take min kullum ita da Anty Falmata. Haka na zauna na saurara dukkan abinda
Suka ce making a lot of mental note a cikin kaina, abinda yafi Zama min shi ne
communication part, Ammi tace min Kar na sake muyi fada dashi na Bari mu kwana da
wannan abin a raina, ko Yaya ne muyi magana akan abin, matsalar mu tamu ce mu kadai
kada muyi involving wani har se abin yafi karfin mu. Idan min bar fada ya kwana ko
Kuma muka ki magana akan shi, bayan Yana cin zuciyar mu to tabbas zaiyi drifting
din mu apart. A cikin wannan satin komai na Shirin ya kammalla.


Ranar Wednesday akai henna party, da farko naki yarda saboda bana son taron ma,
Amma Mummy tace karya nake ban Isa ba Dan wannan shi ne banbancin wancan auren da
wannan. Banyi kwalliyya ba Amma Banda glowing Babu abinda nake, friends Dina
Sheriffa tazo, Maryam da Kuma Farha, Yan class din mu a UCLAN. Se yamma sannan aka
Gama henna party wanda akai a gidan su Basma. Washegari ya tashi a Ladies
gathering, a gidanmu mukai. Se ranar Friday da yamma akai Wushe wushe, tun safe
sukai gaba, Nima wajen 10am yazo Ina daki Anty Falmata tazo ta kirani, Muna cin
abinci da Farha su Kuma sauran suna harhada kayan su, Anty Falmata ta shigo tace


" Shehu yazo ki Gama cin abincin ki fito ku tafi"


Na dubi su Farha nace Mata


" Anty su kuma fa? Duk acan zaayi musu make-up"


Tace ai zaa tafi dasu mu fito Baki daya. Haka na bar abincin muka fito, daga ni
seshi a motar se sauran motocin Kuma cousins dina da friends dina. Seda ya dauki
hanya sannan ya dubeni


" Damsel!"


Na kalleshi sannan nayi murmushi nace


" Honey!"


Ya kalleni sannan ya maida hankalin shi Kan titi yace


" Like play like play we're moving darl! Gobe zuwa zuhr inshallah kin Zama
mallakina"


Na kalleshi sannan na maida kaina gefe nace


" I thought I've lost you duka, se gashi auren zai yiwuwu. I'm very grateful"


Yayi dariya a hankali wadda seda tasa naji tsikar jikina ta tashi yace


" No! Ni Zan gode Miki da Kika zabe ni Akan sauran mazan duniya. Inshallah Zan zame
miki shugaba, aboki, Yaya, kani da Kuma baba. Inshallah Amina zamuyi Zama me dadi.
Our home will be filled with love, laughters. Ina fatan Zaki bani hadin Kai"


Na gyada Kai se ya harareni yace


" Open your mouth and talk, Yara nawa Zaki Haifa?"


Na kalleshi da mamaki yace


" Tell me Mana"
Nayi shiru kafin can nace


" Biyu"


Da mamaki yace


" Biyu Kuma? Ki Kara uku su Zama biyar Mana"


Na kauda Kai nace


" Is not easy in labor room oooo!"


Yayi dariya yace


" Ai tare zamuyi sharing pains din, we're in together ko?"


Na girgiza Kai nace ban yarda ba Amma na yarda mu Haifa uku, se yace zai San yadda
zaiyi yasa muyi biyar din. Munyi Hira sosae a abinda Bai koa awa daya ba. Muna Isa
dutse Sha daya nayi. Straight parlon din me Make up din muka je, ya dubeni yace


" Tell her to be careful with this delicate skin of yours, gani nake ana tabawa
jini zai fito"


Na bude kofa Ina dariya nace


" Kai ko! Waye ya fada maka. Bari ka gani"


Na fada Ina mintsinin hannuna, ya runtse idon shi Wai ji take kamar jikin shi ake
tabawa, nayi Masa dariya na wuce ciki. Karfe hudu I'm clad in asalin kayan bare
bari su Kuma dukkan su sauran kawayena lafaya ce jikin su, wannan kitson gaban na
al'ada anyi min shi tuntuni. Nayi kyau sosae da sosae. Tayi min pictures Haka me
hoton da mukai hiring shima yayi min. Event din ranar yayi kyau ba karya, mummy da
Ummiey sunyi kokarin gayyato friends din Mamana, Kuma sunzo su wajen goma, Banda
matan abokan Abbuna Suma sunzo, ga manyan fans Dina Wanda Anty Azeema ita ce Kan
gaba a kawo su, ko Ina na kalla se naji Dadi nakeji, tabbas wannan Karan nasan nayi
aure da gaske. Se dare muka koma Ringim, a matukar gajiye nake Dan munyi dashi zai
zo Amma yadda yaji muryata faint yasa yace nayi wanka na kwanta, tunda washegari
will also be a busy day. Washegari ranar daurin aure, wajen Sha daya an Gama gyara
min jikina, a wañnan ranar Kuma abokan shi sun hada Mana English dinner da daddare
da zaayi a gidan Uncle din su nan a ringim. Lace na saka champagne color, komai da
na saka champagne ne, ana Gama daura min dankwalin aka yafa min veil akaina naji an
Gama daura aure, kawia se naji idanuna sun ciko da kwalla, wata rayuwar sabuwa Zan
fara Kuma, ai tuni se hawaye ya balle min. Amina Abubakar ce kusa dani, me make up
din tana harhada kayan ta,
" Me ye Haka Afiyya? Kuka Kuma?"


Da sauri me make up din ta taho tana rokona Dan Allah Kar na Bata fuskata Amma
kamar zuga ni suke hawaye kawai nakeyi, duka suka tsaya suna kallona har nayi shiru
sannan ta gyara min Amma idanuna yayi ja Haka ko magana bana Yi. Babu jimawa se
gasu sunzo, tun daga nesa na hango shi all clad in white shadda da babbar riga, he
looks Charming se murmushi da dariya yakeyi, har suka karaso mukai hotuna,
Murmushin da yakeyi yasa na manta da wani duk insecurities na fara bude Baki Ina
dariya. Ana gamawa Anty Falmata tasa na canja Kaya sannan aka kaini gidan sarki
chamber kamar shi, ta kalleni ta tsufa se na tuna Hajiya kakata, yadda muke yawan
zuwa wajen ta. Ta riko hannuna kafin a Fara budar Kan tace


" A dakinnan na raini mustapha da Abubakar, saboda amincin su Mata ma Yan uwa Suka
aura,tare sukai karatu. Gashi yau Allah ya nuna min Dan mustapha ya auri Yar
Abubakar. Allah ya albarkaci auren ki ya jikan Dana"


Ta karashe da doguwar addua akai formalities na karba ta sannan da daddare mukai
Shirin dinner, shi kadai ne Wanda mukai tare dashi, suit ya saka kamar peach kamar
nude Haka, shirt din ciki da tie dinsa were all Navy blue, ni Kuma na saka gown ta
material me Dan glitters maroon, munyi kyau, friends dinmu duka sunyi kyau sosae.
Bamu Jima ba sosae muka Gama sannan muka fito rakiya, yawancin Dana nan zasu kwana
tunda dare yayi, hannun shi cikin nawa, seda duka Suka shiga mota suka tafi sannan
ya bude min gefen shi na shiga ya zagayo ya tada motar tare da Kama hannuna ya rike
cikin nashi. Dayan Kuma Yana driving har muka karasa kofar gida. Yayi parking
tareda pecking hannun nawa Dake cikin nashi yace


" I badly wanted holding these hands, I wanted feeling their softness. Da nayi
hakuri gashi na rike"


Na danyi kasa da kaina saboda caressing hannun nawa da yakeyi da thumb dinsa, Jin
na Yi shiru yasa yace


" Nasan kin gaji, the day was very busy kije kiyi bacci Amma ni nasan bazan iya ba,
had it been Zan jiki a kirjina I will have a peaceful night!"


Jin hakan na turo bakina tareda kwace hannuna daga nashi yayi saurin rikeni ya juyo
da fuskata, for the first time naji bakin shi a cikin nawa.




63


Kana kallon yadda yake duba agogo tare da Kuma Jan tsaki lokaci zuwa lokaci kasan
ya kosa motar ta karasa ta sauke su a kazaure, tun biyar na asuba yaje Tasha ya
shiga mota, Dan malamin yace lallai lallai asirin da zaayi sede ya zamana Junaidu
yayi da kanshi ba Safiyyu ba, gashi yau ne daurin auren Kuma Dole se ya kasance ayi
binne binnen da Kuma hayakin Dole se de yayi da Kan shi kafin daurin auren. Yaso
ace tun acan zaayi aikin da yafi kowa farin ciki, dama haushin Afiyya yake ji da
danginta da sanadin su yaje har prison na kusan shekara daya, Dan Haka asirin da ya
karbo ba Wai na fasa auren ne kawai ba, shima Junaid zaiji ya tsaneta bazai aureta
ba sannan rayuwar ta se ta lalace gaba daya. Yayi murmushi Yana Kara kankame jakar
da layoyin da Kuma itatuwan suke ciki, ya sake duba agogo yaga Sha daya da rabi
gashi sun baro daura sun kusa kazaure abada.


Lumshe idanun shi yayi Yana kiyasto yadda zaiyi fata fata da rayuwar Afiyya, Allah
dai ya kaisu kawai ya ayyana a zuciyar shi. Suna Dan da Isa cikin gari wata Mata ta
fara fadin driver ya tsaya yarinyar ta da Bata saka Mata diaper ba tayi Bayan gida,
Kuma ya Bata har na kusa da ita. Dole driver ya tsaya Yana ta fadan ta Bata musu
lokaci. Gashi acan extreme take seda kusan kowa na motar ya sakko sannan ta fito
dan gyara yarinyar. Safiyyu ya bude idanun shi tare da kallon agogon wayar shi ya
saki tsaki Wanda kowa ya gaji daji. Sauran passengers masu bukatar stretching
kafafun su day Wanda zasu zagaya duka suka sauka se Safiyyu kawai ya rage cikin
mota. Kamar bayan mintina biyar Babu wani Wanda ya Isa ya Fadi abinda ya faru, ko
shi Safiyyu Bai Isa fadar yadda wuta ta fara daga jikin shi ba, shidai yasan ya
fara jin burning sensation a jikin shi, ya bude murfin motar ya fito Amma wuta
sosae ta kankama a jikin shi tun daga wandon jikin shi har zuwa rigar shi se ci
suke tamkar Wanda aka zuba Masa fuel aka kyasta Masa ashana Haka yake ci, wani
passenger dashi ya fara ganin shi ya saki ihu Yana fadin


" Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!! Kuzo jamaa kuga ni"


Safiyyu se ihun Neman taimako yake Yana kokarin yage kayan jikin shi Wanda hakan ke
exposing jikin shi Yana Kara konewa. Ruwa Suka Nemo masu kasa ana ta zuba Masa Amma
ko gezau wutar ba tayi ba, Haka suka tsaya kallon ayar Allah Dan kanta ta mutu ya
zube a gurin jikin shi Babu kyan gani.


NDLEA OFFICE, ABUJA.


Files ne guda uku Wanda aka saka igiya aka daure su wani officer yake dauke dasu ya
fito daga ofishin babban sashen zuwa nashi ofishin. Yana shiga nashi ya zauna
tareda sake kallon sunayen da Kuma address din su duk da Suka Gama samu, ya dauki
wayar landline dake aje Akan desk dinsa ya fara Kira. Bai wani Jima ba ya fara
magana cikin turanci Wanda accent din barebari ke fitowa a ciki. A jikin desk din
akwai sunan shi Muhammad Ali. A cikin magangun shi ya bada order Akan suspect din
da ake nema masu trading hard drugs. Yana maganar Yana Kara bubbude files din
sannan ya aje wayar tareda shafa fuskar shi, it was sure a hard job sunfi shekara
uku suna Neman mutanen nan se yanzun aka samu aka San inda dukkan su suke.


Junaidu na zaune kofar gida da wayar shi a hannu sunyi magana tun sassafe da
Safiyyu Akan ya taho, dukda a lokacin da suke wayar seda ya fada Masa cewar shi ya
fasa kawai ya barwa Allah ya zaba Masa abinda yafi alkhairi Amma Safiyyu yace Babu
wannan maganar, aure se ya aura Afiyya ya jira shi Yana Hanya. Shi yasa ya fito
kofar gida ya zauna, se wayar shi ta fara ringing a tunanin shi Safiyyu ne se yaga
Malam ne abokin shi, ya dauka Yana fadin


" Malam ka buya"


Malam ya danyi murmushi yace


" Gaba daya ka Bata ya maganar cocaine da mukai dakai zaa samu?"
Junaidu yayi tsaki yace


" Suna nan fa, akwai wajen 1kg a gidana ni so nake na daina harkar wallahi"


Malam yace


" Bari kawai zamuyi maganar yanzun kazo gidan Zan Aiko Yara su karba min"


Daga Haka sukai sallama ya wuce gidan da se yayi sati Bai leka ba, Yana zuwa ya
saka mukulli ya bude sannan ya Shiga inda shi kadai yasan gurin, ya fara Ciro
cocaine din da wasu daga cikin hard drugs da yake dealing kawai se Jin alamar kyas
din camera yayi, Yana dagowa yaji bindiga a forehead din shi, cikin sauri ya saki
ledar tareda daga hannun shi sama in surrender, camera man din yayi snapping scene
din Suka saka gloves suka kwashi kayan sannan suka handcuffing dinsa seda aka saka
shi bayan motar su sannan yaga Malam a zaune ya zabga tagumi da tashi handcuff din,
ya dube shi yace


" Setup ne?"


Yace


" Ya zanyi?"


A take ya mikawa Junaidu waya akan ya Kira abokin harkallar tasu.


Gari ya waye tun asuba ban koma bacci ba Ina gurin Dad Yana Kara nausar Dani abinda
ya kamata dukkan Wanda nauyi irin wannan ya hau kanshi abinda ya kamata yayi, nayi
shiru Ina sauraren shi yace


" Kiyi hakuri wannan gidan ba kamar wannan gidan bane, wancen you've every freedom
Amma watarana zakiji kamar ke din captive ce, kamar a prison kike, nasan zaman da
kikai damu Kinga yadda muke zaman mu lafiya da antyn ki, bawai bama fada ba munayi,
but we face it together, kema Haka nake son kiyi. Ki sani nine babanki, ni din
kullum Zan saurareki duk lokacin da kike bukatar hakan. Ina farin ciki da hannu na
gida Zaki Shiga I'm sure of waye shi. Kada ki bani kunya, be the person I know you
were. Please Afiyya"


Na gyada kaina siraran hawaye na bin kuncina yayi min addua sosae sannan yace naje
na tafi. Na dawo daki na tarar kowa na hada kayan shi Dan ranar kowa zai tafi. Na
zauna Ina fadin


" Meye kuke ta hada Kaya se kace korarku akeyi"


Amina tace
" Allah ya Baki hakuri"


Na Mata banza na fita gurin Anty Falmata da Anty Yana Suka karasa gyara min jikina
sannan nayi wanka na saka Kaya, wani lace ne me balain kyau , aka saka min sarka da
dukkan wasu abinda ya dace Amma fuskata Babu ko powder Dan na tashi kuraje sun fito
min Wanda Anty tace saboda makeup din da akai min ne, fuskata Bata Saba ba. Mom ta
dakko wani set din sabulu, bridal set ta bani tace


" Ki fara using dasu friend dita take siyarwa Nima dashi nake amfani ba karamin
kyau ne dashi ba"


Na kyabe Baki Ina kallon sunan Fattyjet 3D bridal set a jiki. Na amsa da to sannan
aka saka min a kayana. Wajen Sha daya motocin da zasu kaimu airport mu tafi
maiduguri Suka zo, ai se na fara kuka na kankame Mummy dukda duk tare zamu tafi, ta
rike hannu na muka fito inata kuka har ta saka ni mota sannan ta zauna gefena, se
babbar yayar su Mamana Ammiey ta Dan tallafo kaina jikin ta tana cemin nayi shiru
muka dauka hanya, bansan min bar Ringim ba hold up da muka fara shiga a Kano yasa
na farka na gyara zamana, ta dubeni da murmushi a fuskarta tace


" Kin tashi?"


Na gyada kaina tareda sake kallon kasa mummy ta rike hannuna se wayatta ta fara
ringing, ta Ciro daga handbag ta Kara a kunnen ta tana fadin


" Baban Basma bamu karasa ba ma... innanlillahi wa inna ilaihil rajiun! Drug
dealing? Ya hayyu ya kayyum! Bari Zan dawo kawai"


Na kalleta tana aje wayar nace


" Mummy me ya faru?"


Tace cikin sanyin murya


" Yaya Sa'idu aka kama, Wai Yana drug trading"


Seda kaina ya Sara saboda nasan menene a kamaka da drug dealing, nayi shiru Ina
tunanin to kenan harda Junaidu in har an Kama Kawu Sa'idu Dan ni na San Yana harkar
drugs na taba jin Yana waya Amma ban taba kawowa da Kawu sukeyi ba Kuma ban fadawa
kowa ba. Ina jin itada Ammiey suna jajantawa har muka Isa airport Nasha kuka da
zata juya Ringim. Nida Rooks da Nads se aunties Dina muka tafi. Dama wasu tun jiya
sun wuce Shirin tarbata, shi Honey ne ma bansan inda yake ba tun asuba mukai waya
bamu Kara ba. Fadar tayi, ginin kanshi abin kallo ne Haka aka lullube kaina aka
Shiga Dani zuwa dakin wadda ta Riki Mama, tana zaune ta manyanta sosae da mutane ko
Ina se kamshi ke tashi har seda hancina ya daina jin kamshi. Aka zaunar Dani Akan
shimfidar da akai min

29 / 31