Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
auna wani Abu ya raba
ni dashi nakan ji hankali na ya tashi iya ayyanawa da nayi. Shi din Rabin jikina ne
Wanda na samu solace a tare dashi. Shi din wani bangare ne na rayuwa ta Wanda bazan
iya ba se dashi,ban taba jin son Abu kamar yadda nake son shi ba, how I wish Abbuna
da Mama ta suna raye suga namiji guda daya ya tsaya min a rayuwa. Ni dashi cikin
aminci muke soyayya min riga min fahimci junan mu so deep,nakan Yi mamakin a lokaci
kankani yadda ya fahimce ni Nima na fahimce shi har Haka. No matter what, duk
abinda ya faru zamuyi magana Koda chat ne bana tunanin akwai watarana da tazo ta
tsallake bamui magana dashi ba Wanda ya assassa Kara shakuwar mu dashi. Bangarena
da Yaya Hasher ya daina kulani wani lokacin na Kan duba last seen dinsa and idan
Naga Yana online Bai kulani ba se naji Babu dadi, ko Babu komai ya nuna min kulawa
lokacin da nake bukatar hakan, wani lokacin se na aje pride Dina na Masa magana but
yadda yake replying Dina ke Bata min rai se na tattara shi na watsar dashi Nima, I
know ni ban yaudare shi why will I be accounting for zargin da yake min.
Wani yammaci min kammalla abincin dare na dawo daki Dan returning call din Yaya
Shehu, ya kirani nayi picking nace Masa Zan Kira shi I was a bit busy ne. Dakin
nawa wajen study table Dina duka a hargitse saboda exams da nake, karatu nake ba na
Wasa ba. Na zauna na fara Kiran shi se ya kashe ya kirani yace na kunna data muyi
video call . Na kalla kaina I was clad in skirt da riga na atamfa, ta wajen hips
din ya kamani soosae Wanda ya tabbatar min na fara kiba Nima, Amma saboda yadda
nake son kayan yasa naki cirewa, veil nayi draping saman kafadata ya lullube duk
inda ya kamata sannan na kunna data Wanda immediately Kiran shi ya shigo, Yana
zaune a office he looks tired, nayi murmushi nace
" Somebody is tired!"
Ya shafa Kan shi yace
" Extremely Baby! Ya exams din?'
Na haska Masa study table Dina Ina jin shi Yana dariya kafin na dawo da wayar inda
nake, muka Dan taba Hira se na Mike na fara tattara books din, se kawai naji yace
" Mashaaa Allah! Damsel kiba kikeyi, kin sani?"
Nayi saurin Jan veil din Dan ya rufe min hips dina Ina pouting se yayi dariya
tareda lumshe idanu yace
" I'm sorry zamuyi magana da daddare ko?"
Na gyada kaina har lokacin kunyar yaga abinda nake ta boyewa nake shi Kuma ya Mike
ya tattare kayan shi ya tafi. Muna zaune muna cin abinci wayata Dake cikin pocket
Dina ta fara ringing, nayi saurin hadiyewa na Ciro wayar se Naga Kawu Tijjani ne,
na Kora apple juice din dake cikin tumbler sannan na Kara wayar a kunnena cikeda
farin ciki yace
" Daughter ta"
"Abiey! Ina Basma"
" She's here, Ina Dad dinki?"
Na kalla Dad da ya meda hankalin shi Kan broccoli salad din da yake ci nace
" He's here"
Se da muka gaisa yace na bawa Dad ya kira shi Bai sameshi ba, na Mika Masa wayar
Ina fada Masa Kawu Tijjani ne.
" Man! Wallahi wayar na daki I'm having dinner ne"
" You want to talk to me! Ok..."
Daga Haka ya Mike ya nufi bedroom dinsu ni Kuma na maida hankalina wajen cin
abinci.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 09063467258.57
Har muka gama cin abinci Babu alamar fitowar Dad, ni Kuma naki tafiya saboda I was
waiting for my phone, na tabbatar Honey will call. Nayi shiru Ina kallon TV Amma ko
kadan bani comprehending abinda ake Yi balle abinda ake fada. Itakam da Nanny Banda
hirar su Babu abinda suke yi, can na Mike na nufi daki na dakko system dinta Dan
washegari inada mental health exams da Rana, na saka slides din a gabana na kura
idanu, yawancin ban Faye son course din ba especially Schiz dinnan dukda Yana da
sauki Amma wannan positive and negative symptoms ke Dan confusing dina, mum ta
dubeni Lokacin I was going through OCD tace
" Karar TV Bai damun ki ne? Ki tafi daki indai karatu kike so kiyi"
Na Dan Yi pouting nace
" Wayana a gurin Dad"
Nanny tace
" Nayi mamakin abinda ya zaunar dake Ashe shalele ce hannun Alhaji"
Duk lokacin da tace Alhaji se Abbu ya fado min , na murza hannuna a idanuna Ina
fadin Allah ya jikanka Abbuna I so much missed you! Mum ta mike Babu jimawa se
gata da wayata ta Mika min na amsa da sauri tareda duba call log dina, na saki
ajiyar zuciya ganin Bai Kira ba, na tattara system Dina na wuce dakina. Ban Dade
Ina karatu ba bacci yayi gaba Dani. Washegari I woke up to calls dinsa da nayi
missing, Ina kuwa idar da sallah na Kira shi Bai dauka ba se kawai na cigaba da
sabgar gabana. Na fito na samu Babu kowa a parlon se na wuce kitchen Dan duk
tuanani na Basu tashi ba, Ina shiga kitchen na hada tea na fara Sha sannan na fara
hada brown yam da tuna sauce, ba jimawa na Gama na fito se Naga Nanny, Mom da Dad
sun fito a tare daga dakin Nanny, Mom fuskarta ta nuna alamar tashin hankali Dake
ita Haka take Bata iya boye damuwa a tattare da ita, Nanny Kuma tana kallona with
my sympathy a idanunta. I was like irin eh! Meye Haka? What are these people doing
together this early morning? Na cigaba da kallon su har suka karaso parlon kafin na
Dan tattaro courage na gaishe su Dad ya fara amsawa sannan sauran biyun. Na juya na
hado komai na karyawa sannan na dawo parlon. Mum na min murmushi ni Kam duk jikina
yayi sanyi, what's happening? Dole akwai wani Abu da zaisa da sassafe su kafa
meeting kamar wasu UN. Na dai zauna Ina yake Dad ya dubeni yace
" When are you writing your last exams for this semester?'
Na aje cup din hannuna nace
" Yau ne!"
Ya gyada Kai tareda fadin
" Se ku Zama cikin shiri we will be flying back to Nigeria cikin satinnan. Ai hutun
ki da yawa ko?"
Na gyada Kai tareda bawa Mom questioning look se ta dauke kanta daga kallona ta
mayar Kan abinci, a take naji abincin ya fita daga raina, naji ko kadan bazan iya
cin komai ba, na karasa shanye tea Dina lokacin takwas da rabi na wuce daki nayi
wanka se school Kuma har lokacin shima Bai kirani ba. Na jima da wayar a hannuna
Ina tunanin what kept him this long baiyi returning call ba se gashi ya kira, na
Dan Bata fuska kamar Yana gabana sannan na dauka nace
" Nayi fushi"
" I'm sorry Damsel! Was a bit busy. How have you been?"
Na Dan yatsina fuska Dan na haddace wannan gaisuwar tamu nace
" I'm fine alhamdulillah! Na Gama exams!"
Yayi Dan karamin squealing na Taya ni murna sannan yayi min addu'oin nasara yace na
tafi gida idan na Isa na kirashi zamuyi magana. Hakan kuwa nayi Ina kashewa nayi
sallama dasu Janet da Maryam na nufi gida, dukda sun so muyi pictures naki nace
musu sauri nakeyi. Ina Isa gida tun a Hanya na hanga Nanny tana Shiga gida, ta fita
strolling na ayyana a raina, bayan na shiga gida na tarar Babu kowa a parlon,
mamaki ya Kama ni ganin ko minti biyu cikakke baiyi da Naga shigarta gida, na cire
veil din na Yar Kan sofa sannan na bishi na danne tareda lumshe idanuna Ina jin
wani ease a jikina, se kawai naji muryar Mom na fadin
" Surprise Afiyya!"
Nayi saurin bude idanuna a take na hango cake anyi frosting dinsa, yayi kyau Ina
tunanin 8 inches cake ne. Nayi saurin mikewa bakina wide into a wide grin nace
" Mom"
Ta shafa kaina tare da fadin
" Happy birthday! I wish all the beauties of life!"
Na rungume ta Bayan ta aje cake din se lokacin na lura da pastries din da aka jera
a dining, har Raina na manta da wani birthday dina yau, na sauke ajiyar zuciya na
wuce daki bisa umarnin na canja Kaya. Nan na samu gift Akan gado, na Dan daddaga
Amma Kuma ban bude ba nayi changing zuwa wata flowing gown da tayi min kyau, na
hada kaina in a ponytail sannan na dakko hair band na saka kalar gown din tareda
makala 10 inches pointed high heels. Powder na shafa hade da khol sannan na feshe
jikina da turare na fito, Nanny ta fara rungume ni, tareda riko hannuna tace
" Kamar yau ne aka haifeki, na tuna an aiko Mana Lagos cewar Waziri baya da lafiya
shi ne abinda yasa mamanki ta Shiga labor da baa shirya ba. Gashi yau har kin cika
Sha bakwai! Allah ya raya ki"
N rungume ta Ina Dan goge hawayen dake barazanar Bata min fuska nace
" Nagode sosae Nanny, nagode da Kika tsaya cikin rayuwata! Allah ya jikan Mama da
Abbu"
Ta sharen hawayena tareda fada min nayi farin ciki. I was so happy da Ina yanka
cake din, Mum tasa maid dinmu tayi videos da hotuna, can Naga Mom taje amsa call ba
jimawa ta dawo tace na saka dankwali akaina zatayi Baki, Haka na saka karamin veil
na yafa a take na Kara yin kyau, ga mamakina se kawai Jin sallamar Honey nayi, na
Mike daga zaunen da nake cikin sauri na nufe ahi, kunsan Allah Banda ya kauce
wallahi da rungume shi zanyi, baa taba min surprise me dadi irin wannan ba, na
kalleshi yayi kyau cikin maroon din long sleeve top Amma Kuma ya nade hannun sama
se Kuma wandon pale blue ne. Yayi kyau da wannan Charming smile din nashi, na tsaya
se Kuma na Bata Rai na juya Ina kallon Mom Dake kallona with so much amusement a
idanunta nasan tana weighing kaunar da mukewa juna ne. Na tsaya gefen ta Ina tura
Baki nace
" Kinsan yazo ko?"
Tayi dariya tace
" He wanted surprising you!"
A waje inda wasu wooden chairs suke muka zauna, se kallona yake Yana murmushi
yayinda na hade fuska Amma Kuma cikin zuciyata ji nake kamar nayi ihu na Kuma Yi
rawa. He told me tun jiya ya taho Dan kawai ya kasance Dani a Rana ta Mai
muhimmanci, ban ma Kara fushin ba na hakura da yamma muka fita yawo na manta da duk
wata damuwa da matsala, shi kadai nake gani a duniya, Kai duniyar ma ji nake kamar
daga ni se shi muka rage.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 0906346725858
Bamu dawo gida ba se yamma Dan Muna shigowa ko Zama bamuyi ba aka fara Kiran
sallah, na wuce daki nayi alwala nai sallah na zauna bare gift dina, na Dad da Mom
da Nanny se Kuma nashi, kowanne content din yayi min kyau ba ma kamar nashi. Na
Adana komai sannan na fito Jin Nanny na Kirana, na rungume ta Ina Mata adduar
kyautar da tayi min, tace Mom Dina ke Kirana. Tana Kitchen na sameta tayi packaging
slice cake da sauran finger foods tace na dauka na kaiwa su Sheriffa tunda ban
gayyace su ba, Haka na dauka na fita anan inda muka zauna dazun na ganshi shi da
Dad in a serious conversation kamar yadda fuskokin su ya nuna, na hadiye yawu Dan
kawai jikina na bani something is fishy, akwai Dole abinda yake faruwa a Nigeria,
ban wani maida hankali ba na fadawa Dad inda zanje sannan na wuce, ban Jima ba na
dawo dukda Sheriffa kamar zata yanka ni saboda ban fada Mata ba, nace Mata Nima na
manta gaba daya da hakan. Ina dawowa mukai dinner sannan na zauna kujeran Dake
kallon wadda yake zaune yace
" 2am ne flight dina"
Confusingly nace
" Zuwa Ina kenan?"
Yace
" Nigeria, Dad yace min jibi zaku taho ko?"
Na gyada Kai trying hard Kar na nuna na damu so kawai muka Shiga hira yau da gobe
Bai ce min komai ba balle Kuma ni da bansan ma abinda ke faruwa ba. A Daren ya wuce
airport banma rakashi ba saboda na gaji ga bacci se kawai na kwanta Bayan munyi
sallama. Washegari ya kasance duk hada Kaya ne, ranar Monday da sassafe karfe shida
jirgin mu ya tashi zuwa Malaysia Dan se mun fara trans in acan kafin Kuma mu wuce
gida wato Nigeria. Abinda yafi min dadi a wañnan tafiyar kasancewar dukka zamu hadu
acan su Rooks ma sun riga da sun wuce.
Agogon hannun shi ya kalla sannan Kuma ya samu guri ya zauna gefen Ummiey wadda ke
kallon duk wani Abu da yake Yi, daga ita se shi a gidan Dan Nads da Harith sun tafi
gidan su Rooks sarki da Daddy Kuma suna fada. Ummiey ta dube shi tace
" Yaushe ne saukar su Afiyya din? Na zata zakaje Kano taho dasu"
Yayi dariya yace
" Ai Kawu Tijjani zai dakko su shiyasa"
Ta gyada Kai tace
" So da kaje Lancaster kayi Mata magana akan Hasher dinne?"
Ya girgiza Kai yace
" Ni ban Mata ba, bana son taji maganar a bakina Amma munyi magana da Mummy da Kuma
Uncle Babawo yace min wai wannan tsohon mijin nata shima yazo Wai da family
dinsa..."
Da sauri Ummiey tace
" Wai Junaidu? Amma ma dai a gaida Tijjani me karfin zuciya shi wannan yaron har ya
Isa ayi Masa second glance."
With lot of humor a muryar Shehu yace
" Ummiey ni nasan afiyy ba zata taba zabar wani miji Bayan ni ba, so shiyasa banma
bi takan maganar ba shi Kuma Hasher yayi contacting Dina akan maganar nace Masa ni
bazan Yi fada da kowa akan ta ba nasan idan har ita zata zaba mijin ta Bata da wani
se ni se Kuma idan Allah ne Bai nufa ba"
Ta Dan bugi kafadar shi kadan tare da gyada Masa Kai tace
" You have so much faith in her"
Yayi murmushi Yace
" I believe in her Ummiey"
Ta musu adduoi sannan ya wuce daki Dan ya huta kafin karasowar su Afiyya.
Karfe Tara na dare muka shigo garin Ringim, tun daga gate din legal nake ta kalle
kalle ko Ina se Ina tuna memory that's lingered a wañnan gurin, har seda muka shigo
cikin gari mukai parking kofar gidan da yake mallakin na uncle Babawo ne. Shekara
biyu kenan da na bar garinnan gashi na Kara dawowa, sede I'm no more that naive
girl wannan din wata sabuwar yarinya ce wadda ta Kara fahimtar rayuwa da Kuma zaman
duniya. Muka fito zuwa ciki a matukar gajiye, Ina shiga nayi daki na fada Kan gado
ko veil Dina ban cire ba, nayi shiru Ina lumshe idanuna a take kuwa bacci yayi gaba
dani, nasan Ina baccin naji shigowar Mom da Nanny Amma banji fitar su ba, se Sha
biyu sannan na farka idanuna har lokacin akwai bacci, na tashi na gyara kwanciyata
na cigaba da bacci.
Washegari da wurwuri mukai gyaran gida komai ya koma muhallin shi sannan nayi wanka
naci abinci na koma daki ko wayata ban nema ba na sake komawa bacci. Wajen daya na
farka nayi sallah sannan na fito parlor nayi kicibis da Nads da Rooks, suka yo
kaina kamar zasu kayar Dani na fara musu ihun su sake ni Zan Fadi kafin Kuma na
zauna
" Mom dinki ta fita tun dazun kema tashi zakiyi mu tafi"
Nace
" Ina zamuje?"
Nads race
" Gidan Ummiey mana!"
" Ummiey fa? A'a wallahi bazan je ba"
"Kunyar surukai!"
Na wuce daki na canja Kaya sannan na fito muka fita, iska na kadawa a hankali muka
nufi gidan Mummy kamar yadda nace musu sede da mukaje Bata gidan, na Ciro wayata na
saka Sim Dina na Nigeria sannan muka fara Hira se tsokana ta suke Wai jikin su na
Basu kafin a Gama hutunnan zaayi min aure. Nayi dariya nace
" Da an rage min wahala wallahi dama so nake na kasance da Honey kullum"
.
Rooks bakin ta kamar zai yage Dan mamaki yayinda Nads ke fadin
" Lallai in law kice a matse kike"
Na Harare ta
" Ke Nads I'm your elder sister yanzun stop teasing me"
Kafin ta bani amsa wayatta tayi ringing ta dauka Babu jimawa ta dubeni tace
" Dad dinki na Neman ki acan gidan Waziri"
Nace
" Toooo!"
Na mike Ina musu kashedin su jirani na dawo sannan su sayo Mana Dan malili muci
idan na dawo se suka ce kawai idan na Gama na same su a gidan mu can zasu koma. A
hankali na cigaba da tafiya har nazo kofar gidan Kawu Sa'idu, na tsaya ba tareda na
shiga ba Amma se kallon zauren gidan nake rayuwa kenan. Komai ya wuce se tashin
labari,na tuna lokacin da nake ganin rayuwa ba zata taba komawa daidai ba, na tuna
lokacin da nake ganin Babu wani Jin Dadi a rayuwa , lokacin da nayi giving up akan
rayuwar ma Baki daya lokacin gani nake banida wani hope na kara samun yancin but
Allah ya nunamin shike da iko bani ba. Na juya na cigaba da tafiya nayi niyya Zan
Shiga Amma ba yanzun ba se na dawo daga Kiran Dad. Na danyi nisa kadan naji muryar
Hafsisi tana kwala min Kira, a sukwane na juya ita din ce kuwan da Sahib a hannun
ta yaron Siyama, na saki murmushi lokacin da ta karaso tana fadin
" Afiyya kin ganki kuwa?"
Nace
" Me nayi?"
Tace
" Innanlillahi se wani haskawa kike kin Kara kyau"
Nayi dariya nace taje gida zanzo yanzun jirana ake, ta ruko hannuna tana tambayata
kp da gaske zanzo nace Mata ai alkawari nayi.sannan na samu ta tafi ni Kuma na
hanzarta naje. Shima gidan an gyara shi sede Ina iya hango guraren da mukai wasan
kasa, guje gujen da komai, Allah sarki Hajiya kakata. Kofar parlon takalma me sunfi
biyar hakan yasa gabana faduwa Amma na daure bakina dauke da sallama kaina Kuma a
kasa na shiga, Mummy ta fara fadin
" Mashaaa Allah Afiy xo nan"
Na saki murmushi na Isa gareta tare da rungumar ta nace
" Mummy Ashe kina nan? Ina wuni?"
Ta amsa sannan na gaida Dad da Kawu Tijjani, Ina daga kaina Naga Kawu Sa'idu a
zaune ya zuba min idanun shi, nayi saurin janye nawa na gaishe shi a ciki ciki
kafin Kuma na Kai idanuna kan sauran occupant din, subhannallah! Kadan ne zuciayata
Bata fito ba ganin Junaidu wani dattijo da Kuma wasu su biyu da ban San su ba.
Gaban ya Fadi na dubi Mummy se Naga ta min alamar na gaishe su, bakina na Dan rawa
na gaishe su, dattijon yace
" Amina kece?"
Na Dan gyada kaina kadan sannan Kuma na sunkuyar da kaina. Kawu Sa'idu Dake gefe
yace
" Tunda tazo se mu Basu guri Dan su sasanta kansu ko?"
Da mamaki na dago cikin sauri na kalla Kawu Sa'idu, na kalla Junaidu da yaki dauke
idanun shi daga kaina, se lokacin na lura da sauyi a tattare dashi, Naga wata irin
nutsuwa da ban taba gami a tare dashi ba Amma duk ba wannan