Advertisements
Chapter 18 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 31

51K to 54K   out of 90.3K words

inda yake ban kalla ba na
cigaba da cin abinci na, Yana tsaye Bai motsa ba yau a wuya nake Dan tunda na tashi
a zazzabin na dauki alkawarin Rama duk abinda zaiyi min Koda zai kashe ni ne. Kamar
yasan me nake tunani se ya fita daga kitchen din, na sauke ajiyar zuciya na Gama na
fara wanke wanke se naji Yana kwalla min Kira, na duba kitchen din tas Ina neman
makami, Idanuna Suka sauka akan set of knives da ban taba amfani dasu ba, na dauka
butchers knife na zura cikin sleeve Dina na fito, yana tsaye Yana wurga min harara
kamar idanun shi zasu sakko, na tsaya nesa dashi Ina Masa kallon tsana nace


" Menene?"


I swear seda Naga bakin shi ya bude saboda mamaki, ya nufo ni gadan gadan, na zaro
wukar daga hannun riga ta, ya daga hannu shi zai mare ni nasa wukar na yanki
damtsen shi sannan na wullar da wukar na tsaya Ina huci, hannun ya rike ya saki
ihu, a take jini ya fara zuba, Dan na yanka tundaga rigar har jikin shi, nayi baya
se daki na datse kofar Ina jin ihun shi, se naji me yasa ban ma kashe shi ba yadda
idan yaso Nima se a kashe ni kowa ya huta, na Jima a tsaye se naji an bude gate an
shigo daga baya na daina jin ihun shi, agogo na kalla Naga karfe hudu da rabi,
jakata na dakko na ciro warpper 200 wadda mummy ta bani na saka katon hijab na
dauki wayata na fito ba tareda na kulle dakin ba, Ina zuwa Naga saboda rikicewa a
bude ya bar gidan, ga jini kacakaca tunda ga parlo har waje, na fice daga gidan na
fara tafiya ba tareda nasan inda zanje ba, Ina zuwa Naga napep nace Tasha zai kaini
zanje Kano, Ina Hawa ya kaini har lokacin nayi blocking duk wata channel din tunani
a kwalkwalwata, Ina zuwa Tasha na samu mota baa Jima ba ta tashi se lokacin komai
ya fara dawo mini, what if idan ya mutu kenan na kashe rai Zan mutu kafira, me yasa
banyi hakuri an raba auren a hankali ba. Se na fara kuka Ina jin tsoro Yana ratsa
ni, Ina ganin kamar kamani zaayi. Ta gefena se hakuri take bani tana lallashi na
Dake datijuwa ce. Dake Babu nisa sosae se gashi mun so Kano, na kirga kudin na
bashi sannan na samu guri na zauna Ina tunanin inda zanje, nasan Mummy Bata tafi
ba, Amma sunyi tafiya kamar yadda Rooks tace min, su Ummiey basa nan, shi Kuma Kawu
Tijjani bana son zuwa gurin shi Dan matsoraci be, se kawai na tuna uncle Babawo na
saya airtime na saka na fara Kiran shi kowanne bugu na Kara bugun zuciyata! Seda na
fitar da ran zai dauka sannan ya dauka


" Princess!"


Se na saki kuka jikina na rawa tamkar mazari,


" Me ya faru? Ya akai? Kina Ina nake jin hayaniya?"




Na kasa magana se kuka nake, gaba daya ya tada hankalin shi se roko na yake na fada
masa menene, se can nace


" Na kashe shi! Nasan kasheni zaayi!!"


" Junaidun?"


Ba gyada kaina, hankalin shi ya tashi yace na tsaya yanzun zai taho kazauren, se
nace ai na baro kazaure Ina Tasha a Kano, Allah ya taimaka shima Yana kanon yace
Yana Hanya na jira shi!




AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.39




Koda alkawarin da sukai min Basu cika ba,wannan Abu daya da sukai min se naji duk
wani haushin su day fushi da nake dasu ya yaye, ko Babu komai wannan lokacin shi ne
hardest moment of my life, da ace Bai kawo min dauki ba sede nayi ta watangaririya
a titi tunda nasan Babu Wanda zai kula Dani Kuma. Kawu Tijjani yayi min alamar naje
daki akan zasu Yi magana, na kuwa Mike Ina jin tamkar anyi min bushara da aljanna
na koma dakina, na samu Anty Nafisa tana jera min Kaya cikin wardrobe. Na Isa
gareta nace




"Ki kawo nayi Dan Allah!"


Ta juyo ta harareni tace




" Dama haushin ki nake ji.."


Gabana ya fadi na marairaice fuska Ina jin to meye hakan Kuma


"... Wai Kika tashi da sassafe ki kafa shara da wanke wanke bayan nace kiyi bacci
da yawa"


Na sauke ajiyar zuciya nayi tunanin nan dinma wani Abin Zan fuskanta Kuma, nayi
murmushi nace
" Kai Anty ni bazan iya Zama idle ba, bana komai. Lokacin Ina gidan su Yaya tun
asuba nake fara aiki Kuma Haka nake yini Ina Yi, Kinga aiki ya zame min jikina"


Dana fada sunan Yaya se na tuna dashi, Allah kenan komai cikin tsari yake tsara
shi.


" To Banda abin ki ai nan ba gidan Yaya Sa'idu bane gidan favorite Uncle din ki ne,
kede ki huta da kyau Dan zai fara nema Miki admission ba dadewa ba"


Na Kara gyara zamana nace


" To Anty waec din ya fito ne?"


Tace


" Ya fito Mana, printout din ki na gurin Darling bara ya Gama ya Baki, bakiga yadda
Kika ci ba"


Na saki hamdala Ina murmushi me kyau na Jin Dadi, Ina nan zaune ta Gama gyarawa tas
sannan ta zauna gefena tareda bani jaka tace min




" Kinsan me yasa wanann abubuwan duka Suka faru? Kunyi sakaci da addua dukkan ku
daga ke har su Darling din bakwa addua, Dan Haka yanzun addaua zakiyi sosae, duk
dare Zan dinga zuwa Ina tashin ki kiyi sallah ki roki Allah mafita, this is not the
end of it har yanzun akwai aurenki akan Junaidu"


Na gyada kaina tabbas hakane, addua mukai sakaci da ita shiyasa abubuwa da dama
suka lalace cikin rayuwata, dukda nasan kaddara akace ta riga fata Amma wani
lokacin na kanji bamu ma fahimci concept din kaddarar ba, it's prewritten shiyasa
akace muyi addua, wannan adduar can make a great change a cikin rayuwar mu, Idan da
ace Babu abinda yake canja kaddara da bazaa ce muyi addua ba!




JUNAIDU
Kafin yankan da Afiyya ta ma Junaidu, cikin satin abubuwa da dama nashi suka fara
lalacewa, a wañnan safiyar da ya fita, main source din kudin Junaidu wannan garage
ne na gyaran motoci da Saida spare parts, se Kuma shaguna a jere guda biyar da yake
dasu a Kano inda ya zuba Yan haya. Sauran duk yawancin kananan kadaru ne, Amma Kuma
har lokacin Yana drug dealing dukda ba sosae ba kasancewar shi Bai fiya son risking
safety din shi ba, Amma wani lokacin Safiyyu idan yaga chance Yana saka shi Dole se
yayi tunda ba karamin kudi suke samu ba. Yana fitowa ya fara Kiran Safiyyu Dan
sunyi akan zasu je asibiti saboda drugs din aka bashi akan matsalar shi sun Kare,
Doctor yace Masa zai Sha maganin na kimanin sati kamar biyar kafin ya Kara gwadawa
aga ko zaa dace dukda nerves din dake gurin anyi damaging dinsu sosae beyond
repair! Safiyyu ya karaso Suka shiga mota Dan tafiya kamar yadda Suka shirya, se ga
Kira a wayar Junaidu daga manager shi akan gobara baa San daga inda ta taso ba ta
mamaye gaba daya garage din, Kuma ba guri daya ba ta barbazu ne cikin garage, a
take Junaidu ya saki kara cikin tashin hankali yace


" Ku Kuma Kuna me da har hakan ya faru? Dukiyata wallahi baa Isa ba!"


Ya kalla Safiyyu da ya riga ya nufi inda garage yake can farkon gari kafin a kawo
kanti, yace


" Kaji Dan hauka sun bar gurin ya kone! Dukiyata, takama ta !!"


Shi dai Safiyyu Bai ce Masa komai ba Dan Bai masan me zaice ba, suna Isa kafin ya
Gama parking Junaidu ya fito a gigice yayi gurin da uban mutane suka taru kowa na
tofa albarkacin bakin shi, Amma abun mamaki duk yadda suka taru Babu Wanda ya dauki
Koda ruwa cikin kofi Dan ya kashe wutar, gaba daya sun zagaye gurin se Allah ya
Kara suke wasu na fadin dama ai dukiyar jinin mutane ce dole zata kone kuwa. Ya
ratsa ta cikin mutanen ya shiaga garage da already inda main heart din garage yake
ta Jima da konewa, yayi wani ihu Yana kallon Safiyyu dake contacting fire service
akan su kawo dauki, Junaidu Allah kadai yasan irin susucewar da yayi kafin zuwan
Yan kwana kwana, Koda suka zo 3/4 na abinda yake ciki ya kone se gini Haka ya dinga
faduwa yif Amma ko sauran da suke makwabtaka dashi wutar Bata taba ba. Safiyyu ya
rike shi saboda fizge fizgen da yakeyi, mutane sunata binsa da Allah ya Kara sauran
ma zasu kone sannu a hankali, da kyar Safiyyu ya tafi dashi daga gurin Amma ba
karamin asara ya tafka ba, abin tashin hankalin ma shi ne akwai motocin mutane,
Kuma yawancin mutane suna Kai Masa gyara ne ba Wai Dan wani Abu ba se Dan Babu
karya sun kware wajen aikin su. Safiyyu ya kaishi gida ya samu ya kwantar dashi
tareda karanta Masa wasu spells a take bacci ya dauke shi, Bai farka ba se wajen
uku anan Safiyyu ya masa bayanin cewar ai akwai damuwa Dan matsawar Afiyya na
rayuwar su Kuma Bai kusance ta ba to abubuwan shi da rayuwar shi Baki daya ta dakko
hanyar tarwatsewa, cikin fushi ya nufo gida da nufin yayi ma Afiyya dukan da ko
Bata mutu ba to se ta nakasa ko ta jigata, ni Kuma na fito da shirina Allah ya bani
saa na yanke shi.


Safiyyu already ya biyo bayan shi Dan yasan definitely zaiyi wani silly Abu ne
tunda ranshi kuwan a bace yake, Yana shigowa ya dinga jin ihun shi, shi ne fa ya
shigo ya dauke shi zuwa asibiti, fada Masa yake ya kulle gidan kada na gudu kafin
ya dawo, yau se ya kashe ni yaga uban da ya tsaya min. Ba karamin jini ya zubar ba,
Dan kafin su karasa har ya Suma, ana zuwa tunda case of assault ne yasa aka Kira
police, yazo ya shaida komai sannan aka dinke gurin it was so deep Dan na taba
Masa artery shiyasa bleeding din yayi yawa. Aka Kara Masa jini duk Safiyyu ke ta
wannan Kai kawon kafin Kuma aka samu ya farfado, da furucin se ya kashe ni shi ne
abinda ya fara fada, dan sandan da case din ke hannun shi ya dubi Safiyyu yace Yana
son magana da Junaidu, Dole Safiyyu ya fita Yana nuna Mai alamar yasan me zai fada.


" Waye ya yanke ka?'


" Mata ta ce"


" Kunyi fada ne?"


Ya gyada Kai, Bai San dalili ba kawai bakin shi yace


" Dukanta nake shi ne a kokarin kare kanta ta yanke ni har Haka"


Shi kanshi Bai San me yasa ya kareni ba dukda a ganina ba kareni bane ba ai
gaskiyar ce, Dana tsaya na Bari ya dakeni kamar yadda ya saba sede Kuma Rooks idan
ta haihu ta tuna tana da Yar uwa me sunana tayimin Kara ta mayar da sunan! Dan
sandan ya fadawa in charge din emergency unit din akan kada suyi discharging
Safiyyu har se an sanar da nan police station din.




AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.40




Tunda na tashi Ina daki ban fito ba, se addua nake Allah yasa komai yazo karshe,
tun karfe uku saura na tashi na dare shi ne har yanzun ban koma ba, Anty Nafisa
tazo ta tasheni da kanta, seda na tashi taga nayi alwala na hau Kan salayya kafin
ta koma dakin su, nayi sallah sosae cikin nutsuwa da Mika Kai, da saka ran cewar
Allah ya riga ya karba addua ta. Ita ta koya min yadda ma zanyi adduar, nayiwa
Allah kirari da dukkan kalmomin da suke nuna girma da Kuma rahma, nayi salatin
annabi yadda Zan iya sannan nayi istigfar, abinda nake bukata ya biyo baya, iyaye
na da sauran alumma. Nayi na Gama sannan na koma karatun kur'ani na Gama na Kara
sallah zuwa lokacin alfijir ya keto nayi rakaatanul fajr sannan nayi sallah abuna.
Na Jima Ina zaune nayi azkhar na karanta suratul Yasin sannan na fada tunanin yadda
abin zai kasance, dukda ban taba jin nutsuwa da sanyi irin Wanda naji ba, Ashe Haka
addua take? Se nake jin tamkar face to face nayi magana da Allah, I felt so much
relieved, naji tamkar lokacin da nake rayuwa ni da Abbuna da Nanny, lokacin banida
wata damuwa ko matsala, Amma kalleni at 16years I'm exposed into abinda wata Yar
shekara arabain din Bata taba fuskanta ba. Na mike nayi wanka na gyara gadon na
shirya cikin skirt da riga na shadda brown, kasancewar ni ba fara bace yasa kayan
Suka min kyau sosae, sede da na kalleni se Naga ramar da nayi ta fito da yawa, na
shafa wuyana Ina turo bakina alamar rashin jin Dadi Amma dukda Haka na danyi kyan
gani akan shekaranjiya. Knocking naji softly jikin kofar hakan yasa na dubi kofar
se naji sallamar Anty, ta shigo har lokacin kayan bacci ne jikinta Bata cire ba se
Dan veil data daura akai, ganina na shirya fes Dani yasa ta saki murmushi tana
fadin


" Kinyi kyau Princess din Darling"


Nayi murmushi me kyau na gaishe ta ta amsa


" Muje kitchen ko?"


Na gyada Kai Ina tambayar ta ko Uncle ya tashi, tace ai tun asuba Bai ma shigo ba
da yaje masjid se yanzun ya kirata akan Yana shigowa kazaure zasu wuce, na gyada
kaina. Kusan karfin hada breakfast dinma ni ce, tunda ita ba ta da sauri, mun kusa
gamawa mukaji sallamar uncle Babawo ya dawo, da sauri ta dauki towel ta goge
hannunta sannan tace min bari ta ganshi, na gyada Kai Ina murmushi, a raina nace
she's so lucky tana zaune cikin farin ciki. Hanzarta gamawa nayi na fito bayan ba
Dan gyara gurin na same su zaune suna magana, Yana kallona ya saki murmushi Yana
fadin


" Princess har kin tashi?"


Nayi murmushi na karasa na gaishe shi, ya amsa da faraar da Yana Kuma bani
reassuring look, a gurin mukai breakfast Yana bani labarin then lokacin Yana karatu
a Lancaster Banda dariya Babu abinda nake, saboda yadda labarin yake so funny, gaba
daya Suka tsaya suna kallona, ganin sunyi shiru yasa na tsagaita dariyar Ina
murmushi na cigaba da tauna plantain din dake bakina, Anty Nafisa tace


" It's nice seeing you smiling again!"


Na Kara sakin murmushi bance komai ba, uncle Babawo ya wuce Dan yin wanka, ni da
Anty muka kwashe kayan muka gyara tsaf kafin muka fara Hira, me aikin ta na ta
gyara gidan. Kamar daga sama naji sallama kofar parlor, wata irin mummunar faduwar
gaba ce ta ziyar ce ni, nayi saurin mikewa hannuna har rawa yakeyi, ta kalleni
sannan ta dubi kofar daidai shigowar Kawu Sa'idu afijajan, na kalleshi kamar yadda
yake kallona, Anty Nafisa tayi saurin zura hijab din da take ajewa standby tana
kallon shi Wanda shi Kam duk hankalin shi Yana kaina, ta rike hannuna tana kallon
shi tace


" Yaya sannu da zuwa"


Ya karaso cikin parlon ya Kai hannun shi zai riko hannuna nayi saurin komawa bayan
Anty Nafisa Ina kankame ta, ya saki hannun ya bude baki zaiyi magana se mukaji
fitowar Uncle daga daki, nayi saurin sakin Anty Nafisa na koma bayan shi Ina rike
hannun shi, Ido cikin Ido suke kallon juna, Uncle ya riko hannuna ya dawo Dani
gefen shi yace
" Sannu da zuwa, dama yanzun nake son zuwa gida na sameka"


Ya dube shi yace


" Dama tana nan? Dama Kai ka boye ta kenan? Kasan me tayi?"




" Na sani ta sare shi a hannu, ya Suma an Kara Masa pint of blood, Amma kasan me?
Naso kashe shi tayi. Ba boye ta nayi ba ta dawo gidan ubanta ne kuma no Zan kwatar
Mata yancin da ka tauye Mata"




" Babawo ni kake fadawa Haka?"




" Na fada maka, I'm ashamed to call you a brother, you're a failure. Ka sani da na
Gama dashi Zan dawo kanka, you don't have to waste your time coming, I'll come for
you. Princess jeki daki"


Na saki hannun shi na nufi dakin a guje Anty Nafisa ta bi bayana, sun Jima Ina jin
cecekucen su Amma saboda tashin hankali da nake ciki na kasa fahimtar abinda suke
fada. Anty Nafisa ta sa nata nanata addua " Allahumma la sahla illa ma ja'altahu
sahla..." Se naji uneasiness din Yana sauka.




Uncle Babawo ya leko yace mu fito zai sauke mu gidan Mummy, Dan Bai son barina anan
Baki daya, har mun fito yace na koma na sako hijab Dani zaa tafi kazauren Dan ayu
komai ya Kare, a cikin motar shi muka tafi, mukai branching muka dauki Mummy, se
lokacin Naga Rooks, tana ganina ta taho Mummy ta dalla Mata harara tace


" Ai na raba wannan kawancen, Babu ke Babu ita, she's a bad friend!"


Nayi shiru jikina a sanyaye, ita Kuma ta fara kuka tana fadin


"Uncle kana jin ta ko? Ka Bata hakuri Dan Allah. Wallahi Afeey tace Kar na fadawa
kowa"


Mummy kamar ita take wa magana tace


" Zanci ubanki a gurinnan, da ta fada Miki tace karki fada Mana ke mahaukaciya ce!
Baki San she's indirectly telling you she needs assistance ba. Zaki sani"
Ta rike hannunta tana ta kuka, nayi saurin cewa


"Mummy wallahi..."




" Zan mareki a gurinnan! Kin zata na kyaleki ne? Ina son komai yayi burning down ne
Zan dawo kanki kinji"


Uncle Yana dariya ganin nayi shiru tareda rike hannun. Shi, yace Rooks ta dakko
hijab mu tafi, Mummy ta watsa Masa harara ta karba key din hannun sa ta fice, seda
muka jira ta dakko sannan muka fito Uncle nace Mana


" Ku kyaleta zata sakko da kanta, she's a bully tun muna yara"


Rooks ta saki dariya tana Kara goge hawayen ta, ni Kam murmushi kawai nayi muna
Isa, har ta tada motar, yayi saluting dinta Yana murmushi ta Harare shi, tana
kallona tace


" Daughter zo nan ki zauna"


Gefenta na bude na Shiga na zauna su Kuma suka shiga baya abin su, kallon time tayi
ta fara complain din min kusa makara hakan yasa tunda ta hau titi take gudu,
yayinda suke Hira itada uncle dake fada Mata yadda sukai shida Kawu Sa'idu dazun,
tace how she wish gidan ta yazo da se ta kwada Masa Abu akai. In less than an hour
min shigo Kano, main office din hisba muka wuce, nan muka tarar da Kawu Tijjani
yana jirna mu, muka gaida shi sannan muka shiga ciki, commander muka samu Dan time
din baa fara hisba a jigawa ba, already jiya Uncle da Kawu Tijjani sun filing musu
komai, nan aka Kara min tambayoyi na fada yadda komai ya faru. Sukai filing sannan
muka wuce kazaure, kafin muje already Kawu Sa'idu ya riga mu zuwa tuni Kuma har
yasa an tura case of attempted murder zuwa capital Dutse gadawur!




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 0906346725841
Gaba daya na kasa gane abinda yake faruwa, already komai anyi documenting akan na
yanke shi ne saboda Kare kaina akan Yana duka na, se Kuma report din da aka bayar a
asibiti na yanke shi a hannu, Amma da muka je dutse se muka ga it's a total
different case,

18 / 31