Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
Suka rage!
AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, first Bank of Nigeria Aisha Hassan
kwalam, send evidence through 09063467258
Shatttzzzx
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Karfe biyu daidai ya tashi daga baccin da yake,
lokacin da kowanne Dan Adam dake neman dacewa a wajen mahillicin shi Yana ibada, ko
Kuma kowa na kwance na hutawa daga gwagwarmayar da aka Sha da rana, shi Kam Junaidu
lokacin ya fito inda yasa salama tun dare ta hada Masa wuta a Mangal yasan zuwa
Daren ba lallai ta Gama cinyewa ba, Yana zuwa ya tono anan ya samu har lokacin
wutar akwai saura. Ya diba ko tsoro baya ji, baka jin motsin kowa se iska dake
kadawa da Kuma karnuka dake haushi, se wild kukan tsuntsaye dake wucewa, ga garin
yayi duhu kasancewar watan ya Kai karshe. Ya Gama fifita wutar sannan ya dauka ya
shiga dakin sa ya duba lokaci yaga yayi daidai, ya dakko kaso na biyu na maganin ya
fara ambulawa a ciki. Hayaki, tukuki duka Suka gauraye dakin, haka ya Gama yayi
kwanciyar shi. Da safe ya tashi da wurwuri Dan yasa ran shi zaije makaranta, Dan
hakan da wuri ya fita a gidan ba tareda ya nemi kowa ba kamar yadda yasan hajja
Huwaila ce kawai zata nemeshi. Yana zuwa makaranta ya zauna bakin aji, ko Ina ya
canja Dan yafi wata rabon shi da ya shigo cikin makarantar, idan ka kalleshi ba
zaka taba ganin alamar fitina a tare dashi ba, idan ka kalleshi sede ka ga gentle
guy with promising future amma a badini bazaka kawo shi ke tantirancin da yake ba.
Yana nan zaune har mutane suka fara zuwa, Yan ajin su na asali tuni suna ss2 Amma
shi baima San wanne aji yake ba. Yana ta zaune har makamai Suka fara Kora a shiga
aji, shima ya Mike kamar na kirki ya nufi aji. Can karshe ya samu ya zauna, Wanda
suka lura da zuwan shi a ajin suka dinga zuwa suna gaisawa Kuma suna jajen ya Jima
Bai leko ba, sede ya danyi murmushi yace abubuwa ne Suka Masa yawa. Yana zaune
sauran gang din shi Suka karaso,suna hango shi suka fara ihu suna hailing din shi,
shikam Banda murmushi Babu abinda yakeyi, Jarma yace
" Shegen! Amma ko jiya bakace zaka zo makaranta ba"
Ya shafa Kan shi da hannu yace
" Kawai na tashi naji ya kamata nazo"
Malam yayi dariya yace
" Wai baka ga admin block Bari daya ya kone ba? Ko ka tambaya"
Junaidu ya Dan leka da mamaki ya fara binsu da kallo yace
" Guys badai ku..."
Bai karasa ba sukaji shigowar principal, sergeant, senior Master da sauran kuso
shin school din, sergeant rike da zabga zabgan bulali daga bishiyar maina, kowa a
ajin ya tashi in chorus Suka gaishe su sannan, principal yace su zauna, kowa gaban
shi faduwa yake kada ma Malam da Jarma suji labari.
" It's with dismay that I'm announcing to you the expulsion of some of student in
this class. They tempered with the rules and regulations of the school, bullying
junior student, coming to school late and leaving school before closure. With all
this they went ahead and burnt some part of the administrative block to ashes.
Junaidu Ibrahim, Hafizu muhmmad Jarma, Idris yakubu, huzaifa hannafi, I want you
out here!"
Junaidu ya kalle su duka Suka Mike, malam yace
" Guy kace kawai baka nan, Babu yadda zaayi ka karba punishment din mu"
Ya girgiza Kai yace
" A'a komai tare muke Yi Dan hakan wannan ma tare zamuyi"
A tsakiyar makaranta aka saka su sukai lie down flat, sergeant ya dinga dukan su
kamar Allah ya Aiko shi, Banda ihu Babu abinda suke, seda bulalaen suka karye kafin
kowa aka damka Masa expulsion letter dinsu Suka tafi! Kowanne class ka gani zakaga
sun leko suna kallo, Yara da yawa fuskokin su kamar gonar auduga Dan farin ciki.
Haka Suka dakko jankunkunan su suka fita daga makarantar jiki duk tsami. Malam ke
ta kuka Dan yasan irin nashi iyayen, irin yadda dama suke cin kaniyar shi akan
rashin jin shi da Kuma bad guys da yake bi. Shikam goga ko a jikin shi Banda jikin
shi dake tsami Amma tun a kofar gate ya faffalla takardar ya yaga, a ranshi yasa
tunda aka koreshi to kuwa ya Gama makaranta har abada. Zama sukai suka saka Malam a
gaba suka dinga lallashin shi tareda nuna Masa is not necessary se ya fada a gida
kawai kullum yayi Shirin makaranta ya taho se suje gareji su koyi aiki, idan time
din waec yayi suje wani garin suyi. Da haka ya Dan kwantar da hankalin shi.
A bangarena Babu abinda ya canja, kullum wahala Kara Sha nake a gidan, kafin wani
lokaci na rame nayi zuruzuru, lokaci zuwa lokaci nakan dauki tab dita idan Babu
kowa nayi chatting Maryam. Seda nayi sati na uku sannan ranar Monday da sassafe min
tashi kamar kullum. Na kwashe shimfida ta, na fito tsakar gida na dauki tsintsiyar
na fara shara, yanzun na iya Babu wannan tsihin, dan Dole ma seda aka saka na koya,
seda ya zamana safiya da yamma ni ke shara saboda na kware, ga dundun da Babu fashi
matsawar nayi messing Kuma tana gurin. Tun inayi Ina hawaye har ya zamana na ma
daina. Na fara shara a hankali kamar yadda yake a jikina, ni ba mutum bace me sauri
and I'm not too slow. Na Gama na hura wuta Siyama ta daura abincin safe seda suka
Gama wanka sannan ni na shiga a karshe, uniform Dina Mino ta Miko min wani Jan
wando farar riga da Kuma Jan hijab, se bakin sandals kwaya daya da stockings daya.
Na kalla na kalleta idanuna sun washe nace
" Makaranta zanje?"
Tana murmushi ta gyada min Kai, na rungume kayan Ina jin Dadi a cikin raina, it
doesn't matter to me ko wacce makaranta aka kaini indai Zan cigaba da karatuna
that's what matters to me. Cikin sauri na shirya, na dakko body mist Dina da ya
rage baifi feshi biyu ba na fesa a hankali sannan na mayar cikin kayana, da tuni na
yiwa Abbu dogon list, komai nawa ya kare, Abbu bama ya jira se Abu ya Kare, da
zarar wata yazo karshe to Nima zai kaini shopping na saya duk abinda nake so. Na
girgiza Kai Ina share hawayen da ya fara min tsartuwa a fuska, na furta
"I've missed you Abbuna, Allah ya Kara rahmarsa gareka"
Na fito na same su suna karyawa, na zauna na gaida Ummaan su ta dubeni ta tabe baki
tace
" Meye kike ta dariya da sassafen nan se kace an Miki albishir"
Nayi murmushi Wanda inaga tunda nazo it was the genuine smile da na Yi, ta tabe
baki ta dangwara min kofin bakin tea din da aka dafa, na karba na fara Sha aka yago
min bread na fara ci a hankali, remembering yadda indai bread ne is either toast ko
akwai spread din mayonnaise, jam ko chocolate spread Amma ni ce nake yagar shi
haka. Har na Saba da abincin da nake ci a gidan, na hakura da komai Dan it's not
changing no one is rescuing me. Mun Gama duka muka tashi Dan tafiya, na dauki bag
Dita me Asalin kyau tun days Dina na Yar gata, books din kwaya Tara ne Wanda nasan
idan js3 ne to tabbas subject din yafi hakan. Kawu ya fito sanye da jallabiyya, na
tsugunna na gaishe shi, Suma suka gaishe shi, ya dubeni yace
" Uwata se makaranta ko?"
Na dago Ina murmushi nace
" Eh Kawu"
Ya gyada kai Yana murmushi dake Bata min Rai, Dan fuska biyu ne dashi Yadda yake
nuna min tamkar Bai masan yadda nake rayuwa a gidan ba Amma ni nasan ya sani, I
might be a little naive girl but am not stupid, kwalkwalwata is very sharp,
kallonka kawai zanyi I can see through you.
" To ayi karatu da kyau"
Na gyada Kai na juya na bi bayan su, makarantar da Dan tafiya daga Ausar haka
mukaje a kafa, kafin mu karasa ba karamar gajiya nayi ba. Ina zuwa mukaje office
din principal ni da Mino, ya dubeni yace
" Amma Malam Sa'idu baice min yarinyar karama bace sosae"
Mino ta dubeni ta kalla principal din Amma batace komai ba, Dan Bata San yadda
sukai da principal da kawu ba. Haka yasa ni a gaba ya kaini class, mutane da yawa a
cikin class din, banbancin dake tsakanin makarantar Dana Bari da wannan abin ba zai
auni ba. Yace nayi introducing kaina ma Yan class din na fada musu, sannan ya Samar
min guri a gaba na zauna, ya Kira wata Sauda yace ta Zama kawata. Na zauna a seat
din Ina rarraba idanu a ajin. Yan kusa dani sunata kallona yawanci mamakin kankanta
ta suke. Ban Jima ba first period ya shiga, wani malami ya shigo, duka muka tashi
Dan gaishe shi ya amsa yace mu zauna, duka muka zauna ya rubuta physics a board,
anan na fara wondering kenan ss1 aka kawo ni, ni js3 Zan Shiga fa!
Shatttzzzx
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Kara runtse idanuna Ina kokarin dadira wukar a
wuyana, many thoughts running through my mind, idan na kashe kaina kowa zai huta,
tunda suna ganina tamkar liability ce gare su to gwara kawai na kashe kaina zaifi
sauki. Ina dirzawa naji wani irin azabar zafi saboda wukar ko yanka albasa seka
dirza balle kashe Kai, na yarda wukar na saki kuka tareda durkusawa a gurin, se
Kuma wani tunanin yazo min, idan na kashe kaina Allah a wuta zai saka ni, Ina kallo
Mama da Abbu zasu tafi aljanna, I can't be able to reunite with them, ko Kuma Kawu
Sa'idu da Ummaan su Mino da ta cuce ni suje aljanna ni da aka cuta saboda na kashe
kaina na tafi wuta! Da sauri na Mike Ina girgiza Ina fadin that's not possible I've
to live, na dauki wukar na fito tsakar gida, akwai wata tsohuwar rijiya a gidan na
jefa wukar ciki, danma kada na cigaba da ganinta suicidal thoughts din Yana zuwa
min. Na koma daki na kalla kayana se Kuma na fara tunanin ko dai na gudu ne? Na
Shiga duniya kilan na samu wani Mai imanin ya dauke ni! What idan na fada mugun
hannu da yafi su Kawu Sa'idu? Na ayyana hakan. Zuciyata se taci galaba a kaina, na
bude trolley karama na dauki necessary na saka hijab, I've made my mind I'm leaving
this house. Na fito Ina zuwa zaure mukai kicibis da Yaya, ya tsaya Yana kallona
Nima Ina kallon shi, hawaye na sauka Kan kuncina, ya kalleni tun daga kasa har
sama, mamaki sosae a fuskar shi, ya bude baki zaiyi magana nayi saurin ketare shi
Zan wuce Dan ya Gama Bata min budget, hannuna ya kamo hakan yasa na tsaya Ina
kicinayar kwacewa,
" Ina Zaki je Afiyya? Me ya faru dake? Me akai Miki?"
Duka a tare ya jero tambayoyin, na kwace hannuna daga tsatsauran rikon da yayi min,
Amma kafin na Kara daga kafata na bar gurin tuni ya rike hijabi na, jawo ni yayi
har cikin gidan, inata turjewa Amma seda ya maida ni, na tsugunna a kofar dakin Ina
jin shima haushin shi nakeji, kaina kamar zai fado saboda kukan da nakeyi, ga
jikina dake ciwo.
" Kina ganin idan kin gudu shikenan kin Gama Shan wahala? How will you even think
of this? Wa Kika sani Ina Zaki je?"
" Ka rabu Dani na tafi, na gaji da wannan rayuwar gwara naje ko Ina ne tunda kowa
baya Sona!"
" Wayace Miki ba a sonki? Muna son ki mana, ni Rooks and your Nanny, you've to stay
for us kinji?"
Ya Jima Yana lallashina seda yaga na hakura sannan ya barni yaje ya siyo min abinci
a wani eatery ya kawo min naci sannan na shiga daki na kwanta wani bacci me nauyin
gaske ya dauke ni.
ISTANBUL, TURKEY
Daddy ya cire glasses din idanun shi, tamkar cire glass din zai Kara Masa karfin
jin sakon da yake amsa ta waya ne, Amma sede maganar da ake Masa tayi Masa nauyi a
cikin Kan shi ya kamata yama bada hankalin shi gaba daya akan maganar.
" So yanzun Kai a Ina kaji wannan labarin da kake fada min?"
Daga dayan bangaren yace
" Ranka ya Dade bazan iya fada maka ba Amma yarinyar tana cikin matsala, Alhaji
Abubakar Bai cancanci jinin shi yasha wahala ba, shiyasa na Kira na fada maka!".
" Wannan hakane na Kuma gode sosae!"
Wayar ya kifar ya Mike daga Kan kujera ya Isa jikin suit holder dake gefen shelf
dinsa, ya dauka ya zura sannan ya rike kugun shi ya fada tunanin Abbuna, haduwar su
ta karshe a ringim ne da sallah yaje gidan shi yake ce Masa
" Abubakar me yasa baka kokarin hada Afiyya da Yan uwan mahaifiyar ta"
Ya gyara Zama yace
"Mariya ta kawo karata kenan?"
Abbu yayi dariya yace
" Halima ta rasu, ta bar yarinya a kaida tunda princess karama ce to ya kamata su
zasu dinga nemanta, Yallabai Babu Wanda ya taba zuwa gidana da sunan sunzo sun
ganta, to yazan musu? Ita Mariya ai tana zuwa hutu Ringim, ko yaranku Bata taba
turowa ba su ganta, me yasa Bata taba cewa na kawo Mata Afiyya ba. Se yanzun zasui
accusing Dina Wai na rabasu da yarsu? Yallabai bazan dinga tura ta gurin su ba suna
ganin kamar liability ce, Zan rike yata duk ranar Dana mutu Allah will take care of
her"
Daddy ya hargitsa kanshi Yana tuna wannan maganar, tabbas Abbu yayi gaskiya laifi
Kam nasu ne bana shi ba, ya tuna yayi ma Ummiey magana tace ita ba yadda zatai, shi
ya kamata ya dinga neman su Basu su neme ni ba. Runtse idanun shi yayi Yana tuno
sakon da aka fada Masa yanzun a waya cewar kwata kwata bana cikin jin dadi, idan ya
ganni bazai gane cewa ni ce ba. Cikin sauri ya tattara kayan da zai wuce dasu gida
ya fito daga office din. Chauffeur din shi na ganin shi ya karaso da sauri ya karba
suitcase din hannun shi, ya bude Masa backseat bayan ya shiga ya rufe, cikin
turanci da accent din can yace
" Sir where are we heading to?"
"Drive me home!"
Daga haka ya karkata akalar motar zuwa hanyar gida, lokaci lokaci Daddy Yana
picking calls mostly office related calls ne. A yard din gidan yayi packing sannan
ya fito ya bude mishi ya fito da wayoyin shi a hannu Yana kashe su Dan kaidar shi
kenan, Yana dawowa zai kashe wayar, baya son stress. A parlor ya samu yaran dukka
suna zaune, su hudu, babban shi ne sarki na biyu me sunan shehun borno, na uku
Harith se autar su Nadia. Gaba daya Babu Wanda yayi aure, sarki ne ma ake zancen
nashi da shehu, Amma Harith ba wani shekaru ne dashi ba balle Nadia shekara biyu ta
bani. Suna ganin shi Suka Mike kowa da murna kamar kullum Suka tare shi, shehu ya
karba suitcase din shi daga hannun chauffeur daya rako shi, bading din su yayi
sannan ya juya,
" Ina Umminku?"
" I'm here Darling! Welcome home"
Ta fada tayi kyau cikin gown da akai Mata ado da stones, fuskar ta tamkar an Ciro
tata an saka min, dama ance min Kama take da Mamana, Dan wasu Basu ma gane su
saboda Kama, Nima na yadda da hakan Dan akwai hoton su na biki a parlon mu da Kuma
na ranar sunan shehu Dana suna na. Fuskarta dauke da murmushi tace
" Ya aikin you look tired and worried"
Ya nufi hanyar dakin shi ta mara Masa baya yace
" Ganin ki ya warware gajiyar, lemme have a quick shower"
Ta gyada Kai tace ita Kuma zata dakko Masa Kaya kfin ya fito. Bayan sun Gama dinner
sunyi Hira da yaran Suka koma daki sukai Shirin bacci, ta zauna gefen gado hannunta
dauke da water bottle Tasha wasu pills sannan ta dube shi bayan ta Mata masauki
akan bedside drawer ta dube shi ya lumshe idanu ya daura hannun shi akan goshin sa,
tasan mijin ta tasan idan yayi hakan Yana cikin damuwa ne, hannunta ta daura akan
hannun da ya daura akan goshin tace
" Darling how can I help you!"
Ya bude idanun shi ya tashi zaune ya dubeta, she looks disturbed also yace
" Mariya kin taba tunanin makomar yaran mu Bayan mun rasu kuwa?"
Da rashin fahimta tace
" Me ya kawo wannan maganar darling?"
" Kawai ki bani amsa"
Tayi shiru na Dan lokaci kafin tace
" Yanzun Babu zumunnci, ba kowa zai rike maka danka ba idan Babu ranka, gata da
zaka ma danka shi ne tarbiyya da ilimin addini da zamani"
Ya gyada Kai yace
" Akwai wayanda sun so suyi hakan Amma Allah Bai Basu dama ba. Kin taba tunanin Ina
Afiyya take?"
" Wacece Afiyya?"
Ya girgiza Kai wani haushi Yana Kara Kama shi yace
" Afiyya Yar Halima da Abubakar"
Tace
" Ooh ai Maryam ta tafi da ita NY ba?"
" You failed me Ummin Yara, Baki masan inda Yar Yar uwarki take ba, why? Kin manta
tsakanin ki da Halima ne? Afiyya Kun yadda ita Babu me nementa, wallahi Baku kyauta
ba"
Tayi shiru ta kasa cewa komai itama once in a while hakan Yana damunta, takan tuno
yarinyar Amma ta rasa meye yake hanata nemanta.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence to 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Gama Shirin makaranta, na kalli Nanny dake juya
kayana zuwa daidai nace
"Zan tafi makaranta, Amma ba yau Zaki tafi ba ko?"
Tace min
" Eh ba yau ba, kije ki karba abinci ki wuce"
Nace
" To Nanny se na dawo!"
Haka na dauki jakata na fito tsakar gida, wainar gero aka Miko min naci, nasha ruwa
sannan muka tafi cikin ayari. Nanny ta fito da kayan ta fara wanke min, Ummaan su
na zaune tana tabe baki dama tun can bawai su nayi da Nanny bane Dan hakan itama
Bayan gaisawa da sukai Bata Kara bi ta kanta ba. Tayi nisa a wankin Kawu Sa'idu ya
shigo, Dan tun asuba yake fita, yawancin se kowa ya tafi makaranta yake shigowa ya
karya sannan ya Kara fita Kuma se dare. Ni kaina bansan wanne irin aiki yake ba,
zai fita dai ya dawo, su kule a daki su dinga zance da baka San me sukeyi ba. Ta
wanke hannun ta ta zauna kamar yadda ya zauna Yana fadin
" Fanta jiya an fada min kinzo, ban shigo gida da wuri ba"
Ta danyi dariya tace
" Har yanzun anan ana fitar dare kenan?"
Yayi dariya shima saboda Mamana tana da Rai takan ce Masa Wai me yakeyi a waje ya
Dade har cikin dare? Se yace mata shi baya son sa idanu.
" Nazo Naga yata, har an saka ta a makaranta, Allah ya saka da alkhairi ya bar
zumunci!"
Yayi murmushi jin Dadi yace
" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"
Nanny ta gyara Zama tace
" Akan me fa?"
" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta
tunda ni ke rike da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi
na kula da ita..."
Nanny mamaki ya