Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
To Allah ya Sanya alkhairi, shi Kinga mijin anyi bincike sosae"
Mummy tacr
" Munyi maganar da Sa'idu yace komai steady Kuma Wai baya gari shiyasa Bai zo min
gaisa ba"
Itadai Ummiey kawai kanta take gyadawa Amma dukda Haka idan muka hada Ido se nayi
saurin sauke idanuna Dan gani nake she's seeing through me.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment through 0806346725828
Komai se nake ganin shi tamkar almara, cikin kankanin lokaci Kawu yayi blowing
magana zuwa sauran Yan uwan shi uku. I was so naive then, I was so young then ko
addua ba sosae nake ba gaba daya banyi understanding concept of kaddara ba, saboda
Gani nake kawai duk abinda ya faru da Kai kawai kaddara ce and nothing, absolutely
nothing will change kaddarar. Haka nan na Hana Rooks t fadawa kowa saboda Ina ganin
Dole na karba dukkan abinda yazo cikin rayuwata. Yammacin jumaa Ina kwance se naji
sallamar Kawu Sa'idu, bama sallama zance ba kwala min Kira kawai yake Yi, nayi
saurin mikewa na dauki hijabi na na fito Yana tsaye a kofar dakin har na kusan yin
Karo dashi, na Dan ja baya nace
" Kawu Ina wuni?'
Ya dalla min harara yace
" Ki canja Kaya kizo mijinki yazo"
Idanuna a warwaje nace
" Miji Kuma?"
Nayi saurin janyewa baya saboda dukan da ya kawo min, komawa nayi ciki Ina tausar
zuciyata, Dan na riga na sawa zuciyata I'm accepting aurennan, da dai in cigaba da
Zama gidannan to gwara na aura ko waye, bansan fadar hakan kuskure bane babba.
Skirt da riga na saka, na kalla kaina Anty Nafisa matar uncle Babawo ita ta dinka
min zuwanta na karshe Nigeria, ita kadai tazo wani biki shi ne tazo taga yadda
nake. Yayi min cif cif, na fara budewa ta kasa, dukda shekaru na basuda yawa Amma
Kuma Babu laifi jikina me kyau ne. Mayafin kayan na dakko na yafa na fito, Ummaan
su na zaune ta kalleni ta kyabe Baki, bance komai ba na nufi waje wata kyakyawar
307 sabuwa dal se sheki take da daukar idanu baka wuluk. Yaya na tsaye ya hade Rai,
na kalleshi shima tunda na fito idanun shi akai na yake, fuskar shi tana kunshe da
tashin hankalin da kana kallon shi za ka iya karantawa, se Naga yayi rama a rabuwar
da mukai shekaran jiya, tun da muka Gama wannan maganar ban Kara ganin Shiba. shida
Baba da Kawu Sa'idu suna tsaye se wasu Baki Wanda nake tunanin daya daga cikin su
shi Zan aura Yana tsaye , na karasa na gaishe su, dukkan su idanun su a kaina Kawu
yace
" Tsayuwar me kike ba Zaki karaso ba"
Na tako a hankali har nazo dab dasu idanuna a kasa, ya dube ni yace
" JUNAIDU se kayi hakuri, Haka take kamar Yar kauye, gata nan!"
JUNAIDU na nanata cikin zuciyata, na daga idanuna na kalle su dukkan su shekarun su
baya wuce talatin ba, sun Sha bugaggun shaddodin su, daya ruwan sararin samaniya
dayan Kuma ruwan toka, dukkan si babu me hula a Kan shi and I wonder yadda banji
Kawu yayi korafi ba, na tuna zuwan mijin Siyama na farko Bai zo da hula ba aka ta
ciccira maganar se gashi wannan ma yazo a hakan. Tarkata yaran shi yayi Suka shige
ciki ya barni tsaye Ina Wasa da hannuna cikin mayafi,
" To Bari na Shiga mota se kuyi magana"
Dayan ya fada Wanda ya tabbatar min da bashi bane Junaidun, ya wuce cikin motar, na
dago na kalle shi he's handsome wannan shi ne abinda na fara fahimta Bayan kallon
fuskar shi, he looks decent daga fuskar shi zaka fahimci baya da magana, he looks
innocent and good. Wannan shi ake cewa illusion, what the eyes sees is not always
real! To wannan shi ne abinda nayi idan ka kalle shi ba zaka taba tunanin he's thug
ba, shi da halayen da yake exhibiting sunyi hannun riga, he appears a good man.
Ganin yayi shiru Bai ce komai ba yasa na gaishe shi a karo na biyu, ya kalleni ya
ce
" Lafiya!"
Ban Kara magana ba naji Raina na kokarin baci, a Haka nayi ta tsaye wajen minti
talatin Dan hakan na Kara duban shi nace
" Allah ya kiyaye hanya nagode!"
Ban jira amsar shi ba na wuce cikin gida, Ina jin kaina ya cunkushe da tambayoyi
iri iri sede Babu Wanda Zan iya amsawa a ciki Dan ni na bansan amsar ba, Babu Wanda
na samu tsakar gida Dan haka na wuce daki na kwanta na lumshe idanuna Ina adduar
Allah ya zaba mafi alkhairi. Bayan ishai Suka fita Ummaan su day Kawu se ya rage no
kadai Dan Hafsa anyi hutu ta tafi Kano, Ina nan a kwance naji sallamar Yaya, da
sauri na Mike Ian bin shi da kallo har ya samu guri ya zauna, na tsare shi da idanu
Ina jin yadda ake min tickling a cikina, gaba daya naji farin ciki ya lullubeni,
hakan ya Bata min rai kenan har yanzun Ina son shi.
" Seems kamar kin yadda da wannan auren da zaayi Miki ko?"
Nace
" Eh!"
Da mamaki ya kalleni yace
" Bakya Sona kenan? Kin manta munyi alkawarin zamuyi Aire"
Na mishi banza saboda gaba daya nema yake ya fitar min da nutsuwar da na fara samu,
ganin nayi mishi shiru se ya Mike ya fita. A hankali na Kai hannuna na rike kirjina
dake min zafi,nidai ban cancanci wannan rayuwar ba!
" Me yasa kaki Mata magana?"
Safiyyu ya tambaye shi lokacin da suka dauki hanya, Junaidu yace
" Me zance Mata, nifa kaina mamakin yadda akai na yadda Zan aureta nake"
Safiyyu yayi dariya yace
" Nasan Mata basa gabanka Amma yarinyar nan karama ce Bata San komai ba , Dan Allah
ka rike ta da kyau"
Junaidu ya kalleshi Yana sakin dariya yace
"Kai da bakin ka kake hadani da Allah?"
Ya Kara kwashewa dariya yace
" Kai kanka kasan badan an bani saa da aurenta ba Banga dalilin da zaisa na aureta
ba, Kuma bayan Haka nafi son ta shigo da Shirin cewar uwarta zataci ba Dadi zata ji
ba"
Safiyyu yace
" Tayi kankanta yarinyar, baka ganin kamar shima Sa'idun Yana da wani dalili na
aura maka ita"
" Eh mana dama ban Gaya maka ba? Yarinyar nada dukiya wadda take hannun kannenshi,
yasan idan ya bar yarinyar tayi karatu watarana zata karbi dukiyar ta shiyasa ya
hanata karatu, sannan ya aura min ita, to shi Malam na Dan Issa ya fada Masa idan
ya aura min ita Babu jimawa dukiyar zata dawo hannun shi, ni Kuma idan na aureta
zata zame min kariya daga dukkan sharri, sannan gidan mu da nake son ya tarwatse to
zai tarwatse"
Safiyyu ya jinjina Kai yace
" Akwai samu kenan! Amma dukda Haka banso a saka yarinyar a ciki ba"
Kamar yadda nayi tunani, washegari Sega Mummy da yamma itada Rooks, Kawu Tijjani ma
ya iso. Ina daki na zubawa kayana Dana wanke idanu Amma ko daya na kasa ninkewa
naji sallamar Mummy, nayi saurin sakin hular hannuna na mike, fuskarta dauke da
murmushi ta rungume ni, Nima na rungume ta inajin sanyi cikin raina, ta sakeni ta
zauna Nima na zauna se Kuma na dauki hijabi na fita Ina kallon Rooks da taki
kallona, nayi murmushi na je wani shop kusa damu na siyo ruwa na dawo, Ina Zama
Rooks ta matso nace Mata
" Ni nayi fushi!".
Mummy tana Mana dariya har muka fara Hira, na dubi Mummy nace
" Yanzun na bayar a siyo awara abincin ya Kare"
Tayi min murmushi yace
" To daughter, kawun ki yace min kin fitar da miji ko?"
Na danyi Murmushin yake na tuna kashedin da yayi min yau da safe akan kowa yazo
nace ni nake son Junaidu ni na zabe shi, anan yake fada min shi din Dan kazaure ne.
Na gyada Kai Ina sunkuyar da kaina , tayi murmushi tace
" Amma jikina na bani you were forced. Tell me Afiyya gaskiyar magana"
Na dago na kalla Rooks da ta ke Wasa da zoben hannunta Wanda take nuna nervousness
dinta, nace
" Mummy da gaske!"
Se tayi murmushi again tace
" Amma shi ne baki fada Mana ba, se saura sati biyu yake fada Mana. Allah ya Sanya
alkhairi Amma naso ace ba aure Kika zaba ba karatu Kika zaba, dukda auren ma is in
line, But tunda Haka ne ki sani Ina tare da
Ke duk abinda kike so ki fadamin"
Na Share hawayen idanuna nace
" Mummy nagode!"
Aka kawo awara tana ta min nasiha da guda min yadda zamantakewar aure take, se
yamma Suka tafi Kawu yace na bisu saboda Shirin biki. Kwana biyu duk yadda nake son
aiki ta hananin se hutawa kawai da nake tace nayi Rama da yawa kullum girki take
koya min tana bani nutritious food Ina ci, ban Kara ji daga gurin angon ba, tunda
ba waya ce Dani ba Dan ta gurin Yaya Shehu Kawu ya karba tun kafin na hada ta.
Mummy ta Kira Nanny se gata ta taho ta fara guarani, nayi yar kiba nayi kyau. Da
daddare tana mulka min wani yellow abu me azabar kamshi a jikina Rooks na zaune
tana mitar se an shafa Mata tace
" Ku fada min gaskiya meye zancen aurennan?"
Nayi kirikiri nace
" Ai na fada Miki ni na fito dashi"
Tayi dariya kawai tace
" Yara kenan!"
Shirye shirye sosae Mummy keyi,saura sati daya Ina zaune a daki na hada kaina da
gwiwa nayi shiru Kuma ni ba kuka nake ba Rooks ta zauna gefena tace
" Afeey yanzun auren zakiyi? Wanda Baki taba sani ba shi Zaki zauna dashi, Afeey
Ina jin kamar I'm a bad person da nake kallo kina Shan wahala Amma na kasa fadawa
kowa"
Na riko hannunta nace
" Watarana zanji Dadi karki damu"
A wañnan Daren Ummiey ta iso da family dinta, Haka Uncle Babawo Wanda min ringa
munyi waya a wayar Mummy. Ummiey na yin wankan ta taho gidan Mummy ta same ni a
parlor ana turara ni, Mummy nata duba kayan kitchen din da tayi order. Ummiey ta
zauna Suka gaisa, Suka gaisa da Nanny
" Yanzun Maryam yarinyar nan tayi kankanta da aure shekara Sha biyar fa!"
Mummy ta sauke ajiyar zuciya tana kallona tace
" To ya zanyi? Ita ke son shi, da farko nayi tunanin Yaya Sa'idu ke fada kawai Amma
ta tabbatar min da bakinta Haka ne"
Ta girgiza Kai tace
" To Allah ya Sanya alkhairi, shi Kinga mijin anyi bincike sosae"
Mummy tacr
" Munyi maganar da Sa'idu yace komai steady Kuma Wai baya gari shiyasa Bai zo min
gaisa ba"
Itadai Ummiey kawai kanta take gyadawa Amma dukda Haka idan muka hada Ido se nayi
saurin sauke idanuna Dan gani nake she's seeing through me.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment through 08063467258..29
" Ummiey tun tuni nace Miki Ina sonta Zan aureta, Ummiey Kika ki yadda! Ummiey
gashi ina kallo a young age din nata zaayi Mata aure and I'm sure Bata son mijin!"
Ummiey ta dafe kanta, wannan dalilin ta so ace Shehu Bai biyo ta ba, Amma tunda
yaji labarin aurennan gaba daya nutsuwar shi ta tafi, ita gani take kamar Wanda
yake nema ya zautu.
" Me ka sani Shehu? Afiyya da kanta ta zaba mijinta, da bakinta race min ita tace
tana son shi..."
Shehu ya Kara Shiga damuwa yace
" Se kuka yarda da ita Ummiey? Kina ganin gaskiyaa ta Fadi maki? That girl has
already giving up! Ko Baku lura ba Ummiey? Ta riga ta cire tsamannni daga afuwar
rayuwa, tana ganin rayuwa ba wajen da zaka samu sauki bane Ummiey! Why are you all
blind Ummiey, ta Yaya zaku barta tayi ta Shan wahala a hannun wancan azaalumin..."
" Shehu!"
Ummiey ta daka Masa tsawa, ya dago idanun shi da sukai ja ya dubi Ummiey da take
kallon shi a bace
" Ya zanyi? Shehu Yan uwan babanta ne, shi ne marikin ta Shehu. Ya zanyi Kuma
banida wani kwakwaran shaidar cewar auren Dole ne, Afiyya tayi testifying cewar ita
take son shi. What else do you want me to do!"
" Duk laifin ku ne Ummiey, da Kun riketa da kyau Kun jata a jiki how'll that animal
in human form zai dinga wahalar da ita"
Yana Gama fadar haka ya saka kanshi ya bar parlon ya bar Ummiey zaune da tagumi.
Sarki ya karaso ciki ya zauna gefen Ummiey sede baiyi magana ba
" Na sani munyi kuskure babba, min watsar da Yar Halima. Halima ta fiye min dukkan
Yan uwana Amma bansan me yasa da ta rasu na kasa daukar Yar ta ba, bansan me yasa
na dinga fushi da ita ba, I never imagined Yar Halima cikin wannan mess din. Sarki
I'm a bad sister"
Ta fada tana riko hannun shi, ya gyada kanshi yace
" Haka ne Ummiey, the worst thing shi ne babu lokacin gyara, lokaci ya rigada ya
Kure"
Se ta fara kuka tana Kara kankame hannun shi cikin nata. Babu jimawa se ga Yaya
Shehu ya karaso gidan Mummy. Ina can bedroom din Mummy Ina Shan fruit, nayi kyau
jikina yayi kyau se glowing yake irin na asalin amaren nan, ko raba ta kazo Yi
zakaji kamshi me dadi dake tashi daga jikina, tabbas idan da ace Wanda na aura
mutumin arziki ne ko Kuma ace dukkan mu muna son juna to Babu tantama da yayi saa,
Nanny tayi kokari sosae. Duk wannan abin da ake Yi Kuma Banda Rama Babu abinda nake
Kara Yi, Rooks dake zaune tana kallona yadda nayi shiru very deep in thought, I'm
very stupid I know Amma Nima baa wannan lokacin nasan I was stupid din ba se daga
baya idan na tuna abubuwan da Kuma shirmen da duk nayi se naji haushin kaina nake
ji, naji Ina tuhumar kaina da rashin trusting Allah, da Kuma rashin trusting
rayuwa, Dan da ace nayi trusting din rayuwa na Kuma game menene concept na kaddara
I would have prayed. But I was so reluctant, na saka a raina Babu inda sauki zai
zo, na sawa Raina duniya ba gurin jin Dadi bace na Kuma saka a raina Babu me zuwa
kawo min dauki.
" Keeee tunanin me kikeyi Haka?"
Rooks ta tambaya tana bubbuga kafada ta, na girgiza Kai Ina sakin fork din hannuna
cikin bowl din nace
" Ba komai, just some few thoughts!"
Tayi murmushi tace
" Ina Miki fatan alkhairi Afiyya,ke Kuma path din da Zaki bi kenan Haka Allah ya
tsara Miki. Make this relationship work, ki bashi hadin Kai Allah kadai yasan me ya
tanada Miki a ciki"
Nayi murmushi kafin nayi magana naki muryar Nanny na Kirana, nayi saurin saka
hijabi na fito, ta dubeni tace min naje Mummy na Kirana a parlon kasa. Cikin
nutsuwa na dinga tattaka stairs har na sauka kasa, na nufi parlon da Babu kowa a
ciki, idanuna cigaba da cillawa se da nazo tsakiyar parlon sannan na lura da Yaya
Shehu dake zaune ya hada kanshi da gwiwa, nayi saurin Zama Dan nesa dashi nace
" Yaya!"
Da sauri ya dago idanun shi ya sauke kaina, cikin sauri na kawar da nawa saboda
yadda sukai jawur, ga Kuma bacin Rai da ya kwanta cikin idanun ya fito kurkuru.
Cikin wata murya da take a hargitse kamar yadda shi dinma a hargitse yake, fuskar
shi looks pale yace
" Are you stupid?"
Na kalleshi da mamaki idanuna a warwaje Amma ni din Afiyya ce indai wajen share
mutum ne na Masa banza Ummaan su Yaya ma ta buga ta barni.
" Bakiji tambaya nayi Miki ba? Kina haukana zakice ke Kika ce kina son a Miki aure?
Come on Afiyya Baki ce min karatu kike so kiyi a Oxford University ba? Didn't I
promise you to stand for you and make all your dreams true? What does it takes ki
ce musu auren Dole zaayi miki, why are you doing this?"
Nayi shiru dukkan kalmomin da take fada na dukan kunnena Haka hearing nerves Dina
na dauka suna kaiwa kwalkwalwata tana interpreting Ina fahimtar me yake cewa. Na
taba fada muku son da Yaya Shehu yake minis immeasurable? Ko ni bansan yawan son da
yake min ba, bansan how much Zan fada muku irin son da take min ba, a wasu lokutan
a rayuwar mu we always go for the wrong person kamar yadda Sofy tayi akan Alby
dinta.
" Afiyya kiyi hakuri just tell them wannan animal in human form dinne yayi forcing
din ki, kinada chance Amina ki fada yadda zaa San abinyi"
" Ni Ina son shi!"
Na fada Ina kawar da kaina, I dunno why I was so adamant, I really don't know, Ina
furta hakan Naga gaba daya jijiyoyin dake wuyan shi da kanshi Wanda Zan iya gani
sun tashi,idanun shi ya runtse tare da naushi sofar da yake Kai ya furta
" Damn it! See Afiyya, ba Dole se kin kula ni ba, ba Dole se kinyi reciprocating
feelings Dina ba, Dan Allah ki Fadi gaskiya for once kiyi farin ciki cikin zuciyar
ki, it's so obvious aurennan na Dole ne, duka shekaran ki nawa , yaushe Kika San
meye so?"
Yafi mintinann da bazan iya lissafawa ba Yana persuading da ni ba, Amma Haka na ki
Koda cewa komai. Karshe na Mike na tafi na barshi a gurin , why did I done that?
Nima bansani ba, kawai na koma kawai auren nake son ayimin. Na koma daki na dinga
kuka Ina Jim zuciyata na yimin zafi, Haka na hakura Dan kaina. Da daddare Ina
kundundune cikin blanket se naji sallamar Mummy da Uncle Babawo, na Yi saurin
mikewa na zauna Ina kirkiro murmushi nace
" Uncle"
Ya zauna yace
" Princess!"
Se idanuna suka ciko da kwalla, Abbuna he always call me Princess, Allah ya
rahmushe shi ya jikan shi har da Mama da dukkan musulmi. Mummy tafita hakan ya
tabbatar min magana zamuyi , na gyara zamana yace
" A Ina kuka hadu da wannan guy din Junaidu?"
Wani gumi a take ya karyo min, na fara fidgeting da fingers dina, kana kallona
kasan banida gaskiya, shi Kuma se Bina yakeda kallo, se can nace
" I lied! Kawu ne yace na aureshi"
" You ok with that? Wait meyasa kika mana karya in the first place?"
Na share kaina nace
" He threatened me, Dan Allah Uncle kayi hakuri da na muku karya bansan yadda zanyi
ba"
Ya danyi murmushi yace
" I know we failed you, mu ba iyayen arziki bane, but Afiyya ya kamata duk halin da
kike ciki ki fada Mana. Though na Kara bincike sede wasu sunce ba mutumin arziki
bane wasu sun Fadi akasin hakan. So far Zan Kara bincike kafin zuwa asabar din. Ki
dinga cin abinci"
Se naji dadi har bansan hawaye ya sakko min ba, se naji wani hope yazowa zuciyata,
har ma da ya fita se na kwanta na fara bacci cikin jin Dadi, sede cikin dare na
farka maganganun Yaya Shehu suka tayimin echo a kaina se naji na damu sosae, naji
fuskar shi da idanun shi sun kasa gushewa a idanuna. Shirye shiryen ya cigaba da
tafiya ban Kara saka Yaya ko Yaya Shehu a idanuna ba se ranar saka lalle ko nace
walima Dan a Ringim abinda Suka go kiranta dashi kenan. Da daddare Ina ciccire
kayan jikina Nads tazo tace min nazo Yaya Shehu na Kirana, na saka hijab na nufi
waje Ina jin kamar zanyi gudu saboda