Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
sanyi, Kar Nima suce aure zasuyi min idan na Gama Olevel
dina, na girgiza Kai nace a raina ai bazai yiwu ba tunda dai ni ba Yar su bace.
" Ni kuwa Kinga Ina son nayi karatu, saboda Abbuna yace Yana son yaga na Zama
medical doctor, Allah sarki Allah ya jikanka Abbuna"
Na fada Ina sunkuyar da kaina na maida hankalina Kan maths din Wai ko na samu abin
ya fita a raina, but the pains is always there, kullum na tuna shi Ina jin kamar
yau Ina zaune aka fitar da gawar shi a idona!
Wannan karatun da muke shi yasa muka Kara shakuwa sosae dashi, na fara damuwa da
alamuran shi, har idan ya fita na Kan tambaye shi Ina yaje ko Kuma idan ya wuni ban
ganshi ba da zarar ya dawo Zan same shi na fara tuhumar shi inda yaje tun safe ban
ganshi ba. Ummaan su duk hankalinta baya kanmu, ta tattara duka hankalin ta wajen
shirye shiryen bikin Mino, Dan haka se Nima na Dan samu a bit of yanci a gidan.
Wata ranar alhamis muna zaune Muna Hira dukkan mu, ranar har Baba, daya dawo daga
port inda anan yake service saboda Yaya ya riga shi hada makaranta, ya zauna Banda
fafa Babu abinda ke fita daga bakin shi, ni Kuma Ina gefe se kallon shi nake yadda
yake zuba karya Dan yasan Wanda yake yiwa karyar ba su San ko Ina ba se ringim.
Mikewa nayi na tafi na dakko books Dina nazo na zauna na fara karatu, ganin hakan
yasa Yaya dawowa gefena ya zauna yace
" Good girl! Gwara muyi karatu ko?"
Na dago na kalle shi Ina sakar Masa murmushi tareda gyada kaina, yayi murmushi
shima kasa kasa yadda ni daya zanji yace
" I love your dimples!"
Nayi saurin yin kasa da kaina Ina murmushi softly Amma bance komai ba, yayi Yar
dariya da ta saka naji wasu knot na warewa a cikin cikina,
" Kunya kike ji? You look really beautiful idan kina jin kunya"
Na rufe fuskata na cuno baki nace
" Kana hanani nayi karatu fa!"
Yadda na shagwabe murya yasa ya shafa Kan shi sannan ya maida hankalin shi akan
littafina Yana min bayani. Se muka ji sallamar Kawu Sa'idu, dukka muka Masa sannu
da zuwa ya amsa sannan ya nufi dakin su, Ummaah dake bakin kofar ta bi Bayan shi.
Ya zauna ya dubeta a kufule ita Kuma tambayar shi take dalilin da yasa ya dawo gida
da wuri, muma duk a waje we were wondering dalilin dawowar shi da wuri. Bai amsa ta
ba yace
" Zinatu me ye wannan nake gani? Nufin ki duk yadda nake kokarin a banza kike so ya
tashi"
" Me ya faru Kuma?"
" Tambayata ma kike? Ke wacce irin mace ce, kullum Ina waje Ina kokarin ganin
rayuwar mu ta inganta Amma ke Ina tufka kina warware min"
" Kaga ni fa ba gane abinda kake fada akai nake ba, ka fito kayi magana Sai zagaye
zagaye kakeyi"
" Au Baki gane ba? Me yasa Kika bar yarinyar can har take karatu, kinsan in har
tayi karatu zata San kanta Kuma zata nemi ja dani, kinsan bazan iya samun komai
akan dukiyar ta ba in har ta Yi karatu, to Dan me yasa Zaki barta take karatu?"
Tayi tsaki Wanda yasa shi Kara harzukuwa yace
" Ni zanyi magana kiyi min tsaki? Meye nufin ki"
Itama cikin daga murya tace
" Ya bazan maka tsaki ba, duk kokarin da nake ganin mun cimma burin mu Amma Kai
baka gani?! Meye zaka dinga tsorata Bayan munyi da Kai aure zaa Mata da Wanda yafi
kowa munin Hali a duniya, yadda ba zata taba fahimtar potentials dinta ba! Ka barta
tayi ta karatu bazai taba Mata amfani ba, Bayan haka aure a shekara goma Sha biyar
zaayi mata, Kai dai Yi kokari kaga ka samu yadda zakai ka juya zuciyar da tunanin
Yan uwan ka!"
Kawu ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta with adoration yace
" Kina da kwakwalwa! Kinsan wannan satin dukka zasu zo saboda kamawar December,
anan Zan samu na Gama kullin da ya kamata nayi!"
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment through 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 18
Babu jimawa Dan ko sati baayi ba na fara exams dita, ana gamawa na daina zuwa, haka
Ummaan su tace mu daina zuwa gwara mu zauna a more mu a gida. A wañnan lokacin Babu
wani aiki na gida da ban iya ba,gaba daya na canja from the butter Afiyya to a
house help, wanki ma da nake ganin wahalar shi shima na iya sosae Dan har nata take
bani nayi Mata, ayyukan dake sani wahala duk na daina jin wahalar su tunda na riga
na sawa Raina sun Zama dole, Dole se nayi Dan hakan Babu amfanin na dinga Bata Rai
na a banza. Rayuwa sosae take canjawa Kuma indai Kai mutum ne dole ka karbi wannan
canjin da yazo maka.
Ranar da zaayi hutu ranar zamuje karbar result din mu Kuma a wañnan ranar Rooks
tace min zasu taho daga NY, Dan hakan fuskata kawai zaka kalla kasan Ina cikin
madaukakin farin ciki. Na Gama shiryawa na fito tana zaune kofar daki kamar yadda
ya Zama kullum nan take zaune, tana bin gidan da kallo, ta kalleni tayi tsaki Wanda
yasa na juyo fuskata dauke da murmushi, tace
" Daina kallo na se kace mayya, da wasu kumatun ki a gurin masu lotsawa"
Maimaikon naji haushi se na Kara sakin murmushi Wanda ya bayyanar da hakorana, ta
mike zata kawo min duka nayi saurin gocewa tayi tsaki ni Kuma nayi saurin ficewa
Ina dariya, Yaya na samu tsaye shi da Mino a kofar gida, idonta yayi ja da alamu
kuka tayi, shi Kuma fuskar shi na nuna lallashi, ganin su a wañnan yanayin se naji
Babu dadi ban Kuma tsaya ba kamar yadda nayi niyya, se Yaya yace min
" Ba magana?"
Na juyo Naga Mino na Mana wani kallo se na dauke kaina nace
" I saw you guys talking shiyasa!"
Ya harareni yace
" Ke na zauna jira, Ina son muyi magana kafin ki tafi, shi ne kin fito zakiyi
tafiyar ki?'
Na tsaya tareda daidaita tsayuwa ta nace
" Yaya! To gani ai"
Ya matso gefena, we were so close da har Ina iya jiyo kamshin turaren shi me sanyi,
kodan saboda idan naji kamshin Ina jin sanyi cikin Raina ne shiyasa nake jin sanyi
ne dashi. Ya fara tambayata ko naci abinci? Saboda yasan ba lallai an bani ba, nayi
murmushi Ina kallon shi nace
" I ate, ka barni naje sauri nakeyi"
For that mean time mun manta Mino na tsaye, ita Kuma se kallon mu take bakin ta a
bude, tasan we're close Amma batayi tunanin closeness din mu yakai haka ba. Nayi
gaba shima ya biyo bayana, haka muka jera Muna tafiya Yana ta min hira se Naga
within shortest of time har mun karasa makaranta, lokacin an baje se kalilan dake
zuwa karbar result din su, Ina karasawa class teacher din mu yace
" Amina Baki zo da wuri ba"
Na langwabar da kaina nace
" Sir kayi hakuri"
Ya gyada Kai na gaishe shi sannan Suka gaisa da Yaya, ya Mika masa result yace
" Tayi kokari sosae na gaske kuwa, idan akwai abinda yafi na daya tabbas Amina zata
dauka, she sure is an asset!"
Nayi murmushi Ina jin dadin praises dinsa, Yaya ya Masa godiya sannan muka juyo, ya
dubeni da idanun shi da Suka washe tas daga Jan da sukai dazun, sunyi haske har
wani maiko maiko suke, he looks so happy Wanda yasa naji kamar banida wata damuwa
se kallon fuskar shi da murmushi yaki daukewa akai!
" I'm proud of you!"
" Thank you"
Se Kuma mukai shiru kawai muna tafiya a hankali, iska na kadawa kadan kadan duk
zafin garin Ringim Babu Sabida sanyi ya fara shigowa se bishiyo Yi dake kadawa! A
Haka muka karasa gida zuciyar mu tamkar an Mana bushara saboda kallon mu kawai
zakayi kasan farin ciki na dawainiya damu. Tun daga nesa naga mutum ya juya baya,
gabana ya yanke ya Fadi I can swear tamkar statue din Abbuna ne a tsaye, hatta
tsayuwar jikin da komai tamkar na Abbuna, Yaya ya dubeni yace
" Kinga Uncle Babawo! Let's go to him"
Na dauke kaina na cigaba da tafiya ta a hankali tamkar kwai ya fashe min a ciki,
Bai lura da yanayin da nake ciki ba ya karasa gurin da Uncle Babawo ke tsaye ya
rike hannun sa, Ina hango tsantsar farin cikin da yake ciki na ganin kawun shi.
Yana juyowa muka hada idanu dashi ya saki hannun Yaya ya nufo ni fuskar shi dauke
da farin ciki, he looks so much like my Dad, se naji fushin da nike dashi bazan iya
cigabawa ba, na nufe shi da gudu Amma Kuma se na kasa rungume shi na rike
hannayensa and I found myself crying, yayi shiru yana bubbuga bayana Yana fadin
" Ya Isa! Shiyasa tuntuni naki zuwa saboda banason na ganki kina kuka, ya Isa I'm
sorry kinji?"
Na gyada Kai na, na fara share hawayena se Kuma na fara dariya Ina gaishe shi, ya
dinga kallona daga fuskata da ta canza sosae zuwa kayan dake jikina, ya dubi Yaya
yace
" Daga Ina kuke Haka?"
Nayi sauri nace
" Naje karbar result Dina ne, dama bansan wa Zan nunawa ba, class teacher din yace
nayi kokari sosae"
Ya gyada kan shi ya karba result din Yaya ya shige gida, he went through everything
sannan ya shafa kaina yace
" I'm proud of you my Baby. So bani labarin Ringim"
Nayi shiru bansan me zance Masa ba, zance Masa abincin da zanci ma wahala yake min,
ko Kuma Zan fada Masa tamkar Yar aiki haka nake a gidan riko na. Na girgiza Kai
nace
" Nasan yanzun kazo, idan ka huta I'll gist you"
Ya gyada Kai na Mike na Masa sallama na bar shi da result din a hannu Yana kallona
har na shiga gida, Ina shiga na samu ana gyaran kayan Miya, nasan saboda Baki yau
zaayi Miya
" Gidan uban wa Kika tsaya? Baki San kinada aiki a gida ba ko?"
Naji muryar ta daga gefena, bance Mata komai ba nasan zuwa lokacin ta Saba da
wannan halin nawa tunda akan shirun da nake Mata bazan iya irga sau nawa tana
kaimin hannu jikina ba, Amma anjima idan ta Kara min irin haka ko kallon ta bazan
Yi ba Amma Kuma Zan Yi abinda tace. Kamar lokacin se na shiga daki na cire uniform
Dina nazo na daura shinkafa, kafin ta dahu an kawo markade, nayi Miya Ina jin
kamshin na duka na, se naji yunwar da nake ta dannewa ta taso min, naji Yunwa nake
ji Amma se na daure na koma daki har lokacin da zaa bani nawa. Mino na zaune Itada
Siyama suna hirar bikin da dudduba Kaya, na kwanta Siyama tace min
" Afiyya ke baayi Miki ankon ba? Ki fadawa Uncle Babawo tunda yazo"
Nayi murmushi kawai bance Mata komai ba, to me zance atamfa falle biyu an kasa min
bayan da dukiyata aie cin abinci. Bayan sallar laasar Ina cikin tuka tuwo naji
sallama a bakin kofa, cikin sauri na Mike Dan Babu tantama muryar Rooks ce, tana
ganina ta taho da gudu tana sakin ihu
" Afeey darling!"
Na rungume ta a jikina Ina fadin
" Rooks darling welcome"
Ta sakeni tana Kare min kallo na samo Mata kujera ta zauna gefena ni Kuma Ina tuka
tuwo, ta kalleni tareda matsar da kujerar ta tace
" Baki jin zafi? Bazan iya Zama anan ba"
Ta tashi ta koma can nesa Dani, nayi murmushi Ina tuna da can lokacin da nake da
gata ko suya ake a kitchen bana shiga Wai kada ya fallatso min, gani a gaban murhu
Ina tuka tuwo.
" Ya hanya? Ina Mummy?"
Tayi murmushi tace min
" Mummy da zamu taho tare se tayi bakuwa, matar yayar Abbah ce tazo wannan ta
Istanbul din"
Bansan ta ba Amma Ina jin ta a bakin Rooks, na gyada Kai muka fara Hira har na Gama
kwasar tuwon, ta rkeni idanun ta sun kada tace
" You do all this everyday?"
Na langwabar da Kai nace
" Yeah! And I'm fine our little secret darling"
Na fada Ina Mata wink, ta biyo ni daki hannuna cikin nata, anan taga su Mino Suka
Mata magana ta gaida su sannan tace min
" Me yasa komai se kice it should be secret, you are suffering fa"
Nayi dariya na dauki hijab na fito Dan tun safe Kawu Sa'idu yace idan Mummy tazo na
tafi gidan ta. Na fito Ummaan su ta fito ta dubeni, wani skirt da riga ne a jikina
ya dage saboda jikina ya fara karbar hormonal changes, atamfar tare Uncle Babawo
yayi Mana da Rooks wani zuwa da yayi, Ash ce Kuma kunsan atamfa Ash nada saurin
kodai so duk ta kode,
" Ki wuce ki canja Kaya, ki saka na wannan akwatin naki"
Na juya nace Mata
" Ai duk kin daukar wa hafsa, saura kadan Zan saka da biki"
Ta daka min tsawa Rooks tayi gasping saboda tsorata da tayi ta kalleni taga ki
gezau banyi ba , na koma na dakko wata atamfar blue na saka na fito muka tafi.
" Afeey Dan Allah haka kike rayuwa? Kingan yadda Kika koma kuwa? Nidai gaskiya Zan
Fadi gaskiya"
Na girgiza Mata kaina nace
" Zan daina yadda dake, idan na fada me Zan canja Rooks? Bazai canza komai ba sede
bacon rai, Nanny tace min watarana komai zai wuce and I also believe in that!"
Hakan Dana fada se yasa tayi shiru kawai muka cigaba da tafiya har muka zo gida, a
parlor mukaa samu wasu Yan samari suna zaune, tunda muka shiga hankalin su ya koma
kaina, Rooks ta karasa tana fadin
" Yaya nd Yaya shehu sannun ku da zuwa!"
Suka amsa Mata, ta dubeni sannan ta dube su tace
" My cousin Afiyya"
Na gaishe su Suka amsa da murmushi a fuskar su, dayan ya gyara Zama Yana kallona da
niyyar yimin magana se ya fitowar mummy da bakuwar ta ya katse mu
" Abin kunya ai naku be da Baku San inda yarinya take ba, dangin uwa da aka sansu
da jin Kai Amma ku kuka Yi fatali da yarinya marainiyar kwaya daya, abin kunya
akanki ya Kare Mariya"
Mummy ta fada tana huci
" Nidai na fada Maryam, Kun kasa rike yarinya kwaya daya Kun barta tana
watangaririya a Ringim, kunci amanar zumunci.."
"Ku me kuka ci! Ke kin Isa ma kiyi zancen zumunci, kinada Baki? Ai Baki da bakin
fadar wannan"
Duka muka Yi shiru muna kallon su, ni ba maganar su nakeji ba se kallon matar da ke
ta kumfar Baki nake, so nake na tuna fuskarta, why does she look so much like me?
Babban Wanda shi ne Sarki ya karasa gefen mahaifiyar shi ya rike hannunta Yana
fadin
" Ummiey ku Bari Mana Dan Allah, mu tafi"
Ta kwace hannunta tana fadin
" Zaki San ni Kika fadawa magana Maryam"
Mummy tayi tsaki tace
" Kije da borin kunyar ki dai!"
Ni ban taba ganin manya na fada ba, se Naga scene din banbarakwai, ta juya tana
huci ko lura batayi Dani da nake tsaye ba, tana fita shehu ya bi bayanta, na zauna
Ina gaida Mummy wadda lafiya kawai tace min tana kuka, Rooks ta dawo gefena ta
zauna idanunta sunyi ja itama, waya ta dauka ta fara fadin
" Babawo kazo ka sameni Ina gida, ku taho da Tijjani yanzunnan. Afiyya ta gama Zama
gidan Sa'idu tunda shi Maci amana ne!"
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 20
Kamar yadda yayi min alkawarin cewar zai zo da yamma hakan ce ta faru,sede shi
kafin yazo Yaya ya riga shi zuwa. Muna daki ni da Rooks ni Ina kwance Ina kallon
frozen cikin system ita Kuma tana ta ciye ciye. Me aikin su ta kwankwaso sannan ta
shigo tace Mana a parlor Yaya yazo. Nayi saurin mikewa Wanda yasa Rooks kallona
tace
" Meye abin sauri kamar Zaki Fadi?"
Nayi murmushi nace
" Ba Dadi jira"
Ta tabe baki ta cigaba da tauna popcorn din da take ci, na zauna Ina yarda hijab
din hannuna nace
" Rooks naaa! Muje Mana"
Ta kalleni tana murmushi tareda fadin
" Ban taba ganin kina gaggawa akan Abu ba"
Ban ce d ita komai ba na zura hijab dina na nufi kofar fita a bedroom din, tayi
saurin mikewa ta biyo bayana, a parlor muka same shi an jera Masa drinks kamar wani
bako, Mummy dama ta fita tun dazun ta Shiga fada, kamar yaji footsteps Dina ya juyo
ya zuba min idanun shi , na Dan kalleshi briefly Ina murmushi sede idanun nashi
bazan iya kalla na tsawon lokaci ba, Zama nayi har lokacin I felt his eyes akaina
nace
" Yaya tun jiya baka zo ba?"
Ya danyi murmushi yace
" Haba dama kina nemana ne?"
Na tura bakina Wanda yasa shi dauke Kai ya maida Kan Rooks dake faman tambayar Ina
yaje tunda tazo Bata ganshi ba. Nan muka hadu munata Hira wadda mostly ma shida
Rooks dinne, se shi ne yake sako ni a ciki. Mun fi minti talatin se ga sallamar
Yaya shehu, na daga idanuna Ina kallon shi, he looks so much like baban su Rooks,
kana kallon shi ba se an fada ba kasan he's a royalty, tafiyar shi ma kawai cikeda
Isa yake yinta, a fuska zakaga tamkar Yana da girman Kai Amma idan ka zauna dashi
zakaga ko kadan he's simple as what you can't imagine, kyakyawa ne musamman idanun
shi Dan ni dai su suka fi burgeni dashi, se Kuma leben shi. Kullum idan Yana magana
lips dinsa kawai nake kallo yadda yake motsa su a hankali. Yana da tsawo kana
kallon shi zakasan Yana zuwa gym yadda abs dinsa ke fitowa musamman idan kayan
jikin shi sun Kama shi, he's a man to kowanne gaba. Muna hada idanu ya sakar min
murmushi, na mayar masa har ya zauna ya bawa Yaya hannu suka gaisa, Rooks tace
" Ya shehu wannan sunan shi Yaya, gidan su Afiyya yake Kuma cousin dinmu ne"
Ya Shehu ya saki fuska ya Kara Mika Masa hannu a Karo na biyu suka gaisa, Rooks ta
dubi Yaya tace
" Yaya Shehu, Afeeys' cousin and also my cousin!"
Yaya ya tsira Masa idanu kamar zai ce wani Abu kawai se ya Mike, Ina ganin hakan
Nima na tashi Ina fadin
" Yaya tafiya zakai?"
Ya gyada min Kai yace
" Ai Naga kunyi bako, Zan dawo anjima"
Banji dadi ba Sabida ganin shi ma ko bazan Yi magana ba nutsuwa yake saukar min,
Haka Ina kallo ya tafi na dawo na zauna Ina duban Ya Shehu da yake kallona
admiringly yace
" Afeey Babu magana! Ko na tafi I'm not welcome?"
Na girgiza Kai na zauna na gaida shi, ya Bata fuska yace
" Seda ma na roka"
Na danyi shiru Ina kyabe fuskata kamar zanyi kuka, yayi dariya wadda tasa na
shagala Ina kallon shi yace
" I got you exactly where I wanted to! Wasa nake come on bani labari"
Nima se nayi dariya na gyara zamana nace Masa ni banida labari, se yace min zai
bani Mai dadi, Rooks dake gefe tace
" A'a ya kamar Kun manta Dani