Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
saboda you've never mentioned it"
" But I showed you all the signs ko? Zakice Baki sani ba, Zaki nuna min Baki gane
cewar Ina sonki ba"
" Yaya Hasher kasan me? I'm thanking you for giving me your shoulders to cry on,
bazan taba manta alkhairin ka ba, Amma Ina son kasan cewar nidin bansan kana sona
ba saboda gaskiya bana daukar signs, for me to understand se idan mutum ya fada
wannan kalmomin daga karkashin zuciyar shi zuwa bakin shi. Yaya Shehu ya fada
tuntuni tun kafin nayi aure. We're just rekindling love din"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki yace
" Amina dama kina da Baki har Haka, what are you trying to tell me, kin zaba Shehu
akaina? Just think about us mana"
Nayi shiru kaina har ya fara ciwo, se nace Masa Zan Kira shi I need to eat, Ina aje
wayar na dago kaina na gan shi tsaye akaina hannunsa cikin aljihun suit din jikin
shi, he looks handsome wallahi, se naji kamar na boye shi kada wasu su kalleshi. Ya
zauna gefena Yana sakar min murmushi yace
" Whatsup? Waye yake Baki hard time a waya?"
Na kalla wayar na kalleshi nace
" Yunwa nake ji"
Ya mike da sauri yace na wuce ya samo min abinci, tare muka ci sannan ya raka ni
class ya tafi akan zamu hadu da daddare, da dukka ba zamu samu yin lunch a gida ba.
AFIYYA is not free, pay 300 to3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 09063467258
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 52
A hankali idanun shi Suka sauka akan mutanen dake zaune gaban massalaci, bawai a
zazzaune suke ba, yawanci butoci ne a hannun su suna yin alwala kasancewar an Kira
sallar laasar, ya kalle su ya dauke Kai tareda kokarin wucewa Amma se ya gagara
wucewar, wani irin abu yaji a cikin zuciyar shi tare da amsa kuwwar maganganun
Afiyya acikin kunnuwan shi, abin ya zame Masa tamkar wani nightmare, kowacce sallah
idan aka Kira Yana zaune se ya dinga Jin tamkar wani nauyi cikin zuciyar shi. Ya
karasa a hankali for the first time a abinda bazai taba tunawa ba ya dauki buta ya
ciko da ruwa ya zauna a wani dakali can gefe ya fara alwala a hankali, kamar yadda
yaga anayu, dukda Babu coordination Amma Yana yi din dai. Yana gamawa aka tada
ikama Dan shiga sallah, wani farin Gaye a gefen shi ya Mika Masa hannu yace
" Zaa Shiga fa"
A hankali Junaidu ya saka hannun shi cikin na gayen suka shiga massalaci, wata irin
nutsuwa yaji tana shigarshi, ya tsaya yaga yadda mutane ke ta hada sawu, suna
jeranta kafafun su tareda hade duga dugunsu, se yaji zuciyar shi tayi taushi har
danshi danshi ya fara bin fuskar shi, a karon farko ya fita
" Astagfurillah!!!"
Ya karasa a hankali ya jera da Yan uwan da musulinci ya hada dasu, suka tad sallah,
kafin raka'o'i hudu su kammalu fuskar shi ta jike da hawaye, Bai taba jin wannan
peace din cikin rayuwar shi ba kamar yadda yaji a wañnan lokacin. Aka idar kowa
yayi addua ya fice, shi Kam kasa Koda tashi yayi se ya zauna ya cigaba da shiru da
zurfi cikin tunani. Dama abinda ya Bari kenan? Dama Haka musulin ci yake d haske?
Dama Haka sallar take da yayi neglecting iya rayuwar shi? Yana nan zaune har aka
Kira mghrib, gaba daya yayi laushi ya taushi tubus, fuskar shi kawai zaka kalla
kasan cewar akwai babban Abu a tare dashi, he looks pale and down, abubuwa sun Masa
katutu kunya take ji Yana Kuma ganin tamkar dukkan zunuban shi a rubuta shi a Kan
goshin sa shiyasa ya kasa daga idanun shi balle ya kalla wani. Yayi alwala yazo
akai jamin maghrib,Bayan an Gama Malam wato limamin yazo ya fara nasihu kamar yadda
yake duk Bayan sallar mgahrib da ishai, a wañnan ranar yayi nasiha Akan abinda ya
Zama rampant rashin bin iyaye, ya dakko ayoyi da hadisai sahihai Wanda suke
supporting dukkan bayanin shi, Wanda baibi iyaye ba to ya kamar Bai bi Manzon Allah
SAW wanda baibi annabi ba kuwan yasan ya dakko gagurimin rikici tsakanin shi da
Allah! Gaba daya jikin shi yayi sanyi tamkar an sassara Masa jiki Haka yakeji, a
karshe yace shawara ce yake bawa dukkan mutanen dake sauraren shi indai har akwai
rift tsakanin su day iyayen su to suje su daidaita tsakanin su tun kafin lokaci ya
Kure musu. Kafin wani lokaci se tsiraru a cikin massalacin kowa ya Kama gaban shi,
Haka nan ya cigaba da Zama har lokacin da akai sallar Isha wadda ya Kara yin nasiha
akan zamantakewa da alumma, ya nuna cewar Allah yafi kowa sanin menene a zuciyar
bawan shi Amma Dan ya nuna Mana muhimmancin exhibiting halaye masu kyau, shiyasa
idan ka mutu se malaiku su dinga bin chamber chamber ta mutane suji shedar da zasu
maka, Kuma wannan shedar zaayi amfani da ita wajen Yi maka hisabi, shiyasa idan ana
maganar ka to ka dinga duba kanka, A known sociologist Charles Cooley yace looking
Glass self, "The looking-glass self theory suggests that we come to know ourselves
by reflecting on how others see us" Yadda kake daukar kanka ba lallai Haka kake ba,
ya kamata kana duba ya mutane suke kallonka lokuta da dama shi ne ainahin yadda
kake. Yana fitowa a massalacin ya samu napep, Yana Shiga me napep ya tambaye shi
Ina zaije for unknown reason kawai yace a kaishi asalin gidan Malam, me napep ya
kada napep se kofar gidan Malam, ya tsaya a kofar gidan Yana ganin irin mashahurin
canjin da Suka samu, gidan Kan sjo ya canja, shekaru sun tafi Sha biyar tunda ya
baro gidan Kuma Bai Kara komawa ba, ya tsaya Yana tuna lokacin yarinyar su day
jamilu, lokacin da yake cin zalin yaran mutane, lokacin da ake Kai karar shi Hajja
Kan ce suyi hakuri yarin ta ce, yaayinda shi Kuma Malam ke cewa Dan shi jarumi ne,
w Haka ya tashi da zuciyar cewa shi he's superior to everyone he came across, ya
Zama Wanda Babu Wanda zai iya tankwara shi se dai yayi abinda yayi niyya a lokacin
da ya ga dama. Wannan shi yasa da suka zo tankwara shi se Suka kasa. A hankali ya
dinga tuna rayuwar da yayi a wañnan gidan, kamar picture Haka suka dinga wucewa ta
idanun shi, hannunshi ya dunkule in a fist kafin Kuma ya juya Dan he knows he looks
pathetic bazai iya Shiga a Haka ba. Cikin sauri ya juya Dan barin gurin Amma se
yaji wannan muryar me cike da dattako, dijantaka, hakuri da sanyi yace
" Junaidu Ina zaka je Kuma?"
A Haka ya tsaya Bai motsa ba sede dukkan jikin shi a sanyaye yake, har wani rawa
yakeyi. Malam ya karaso tareda saka hannun shi ya ruko na Junaidun Wanda Yana
juyowa ya rungume Malam din, ya saki ajiyar zuciya Malam ya Kashi Suka shiga ciki
Kan shi a kasa kana kallo kasan a takure yake ga Kuma kunya me tsanani data lullube
shi.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 09063467258
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 53
Babu kakkautawa alarm din da aka seta a wayar ya cigaba da ruri Wanda yasa Kara
dunkukunewa cikin quilt din , ganin alarm din bazai kashe Kan shi ba yasa ta zuro
hannunta Wanda yasha artificial nails an painting dinsu da white nail paint da wasu
stones a jiki da a zahiri ita ya kawata ta Amma a gaskiya it looks dirty. Wayar ta
janyo har lokacin bata fito da fuskar ta ba, tsaki ta buga tare da tashi ta zauna
Wanda hakan yasa quilt din yin nashi guri Wanda ya bayyanata, she looks disheveled,
gashinta dukka a barbaje kamar wata bishiya, fuskarta tasha Mai Dan kuwa ba se an
fada maka bleaching take ba. Jikinta sanye da bum short da half vest. Wayar ta
dauka tareda karawa a kunne Ashe bama alarm din bane Husna kawarta ce ke kiranta,
tunda taga lokacin da ta Kira tasan definitely something is up,
" Husna bacci nakeyi"
Ta Dan yatsina fuska tace
" Me zanyi a Whatsapp Kuma? Just tell me"
Ta Dan Kara sakin tsaki tace
" Ok Zan duba, I'll get back to you!"
Daga Haka Nusaiba ta kashe wayar tare da sakko kafafunta ta zura cikin wani soft
bedroom slippers, toilet ta Shiga ta wanke fuskarta tayi alwala tayi brushing, tana
fitowa ta samu har an canja spread din gadon, sallayya ta shimfida ta hau Bayan ta
saka jilbab Wanda ya rufe duka jikinta, agogo ta kalla har Tara saura, hakan yasa
ta yatsina fuska ta tada sallar asubar da batayi ba akan lokaci. Seda ta idar ta
dauki coffee din da aka aje Mata a gefe, ta juya tana ta hura hanci ta dauki tea
spoon tana juyawa ta fara Sha a hankali sannan ta cewa me Mata gayran dakin ta Bata
wayar, ta Miko Mata cikin ladabi, ta karba ta kunna data sannan ta jira komai yayi
settling kafin ta duba message din Husna da ya shigo, tana dubawa taga pictures ne
da yawa se videos Haka, ta shiga budawa tana jin ko menene tabbas Yana da
muhimmanci da Husna zata Mata sharing. Yana Gama budewa da wannan video namu na
swing ta fara cin Karo, idanun ta ta ware sosae tana kallo har ya Gama cikin sauri
ta Kara kunnawa tana zooming fuskata, ganin bazai Yi ba ta bude sauran pictures
din, wani Wanda Janet ta Mana a bakin mota ranar da ya raka ni tutorials school,
tayi zooming tana kallon fuskata da wani farin ciki da yake a kwance bama ya
bukatar se an fada. Aje login coffee din tayi ta bar wayar a gurin ta Shiga toilet,
har ita Shehu zai ciwa mutunci? Yayi karya Bai Isa ba wallahi, wannan karya ne ta
dinga ayyanawa bayan ta sakar ma kanta ruwa me dumi, cikin hanzari ta Gama wankan
ta fito ta shirya a gaggauce cikin wando da riga ta daura jacket wadda iya karta
kugunta, ta yafa wani firirin mayafi hade da saka takalmi wani high wedged sandals.
Fitowa tayi rike da wayatta saboda yadda ranta ke bace Bata ma ga alamar Kiran da
Husna tayi Mata ba. A parlor ta tadda wata dattijuwar mace, itama kana kallonta
kasan Yar duniya ce, fuskarta is wrinkled Amma alamar shafe shafe Yana nan tattare
da ita.
" Mama zanje Law firm din Usman"
Maman ta kalleta tace
" Meye Kuma hadin ki da Usman? Ina ce maganar ku ta tashi"
Ta girgiza Kai tace
" Idan na dawo Zan Miki bayani, I need to go"
Daga Haka ta finciki Jakarta tayi waje, maman tayi murmushi tace
" Banda wauta ki samu miji kamar yaronnan lokaci daya ki juye kice ba Haka ba.
Allah ya kyauta"
Nusaiba na fita office din Shehu ta nufa, tun da ta Isa Secretariat shi tace Mata
ai baya nan, kwana biyu Bai zo ba Yana hutu. Ko amsa Bata Bata ba ta juya tana
fadin
" Yau har gidan su zanje, ta Yaya zance na bar Abu sannan wani ya dauka, ai idan na
bar Abu bazai cigaba ba sede ya lalace!"
Lokacin da ta Isa kofar parlon, sarki na kokarin fitowa daga gidan, ya kalleta ya
Kuma kalli kayan jikinta ya matsa ya Bata guri ba tareda ya Mata magana ba, he
hates yarinyar to the square of infinity, ya ga wautar Shehu da ya kalleta yace
Yana sonta, the girl is so artificial, komai nata jabu ne. He was so happy lokacin
da ya fara ganin hankalin shehun ya fara rinjaya wajen Afiyya yasan definitely zai
bar Nusaiba ya koma can, se kuma aka samu akasin wannan auren Amma dukda Haka
yasan Dan uwanshi Bai hakura ba, yasan a zuciyar shi burin shi auren Afiyya ne. Ya
ficewar shi Bai koma ba Dan yasan Ummiey will handle everything squarely, tana
shiga ta samu Daddy da Ummiey na karyawa, tunda Ummiey ta amsa Mata sallama taji
kamar ta koma, dama Basu taba haduwa da juna in person ba, sede kowa Yana da
labarin kowa, Ummiey ta dubeta tace
" Zauna Bari a Kira Miki Nadia"
Ta girgiza Kai tace
" Gurin Usman nazo"
Ummiey tayi shiruu tana tunanin waye Kuma Usman se ta tuna Ashe ubanta ne Usman
din, ta Kara kallonta kafin Kuma ta tura kujerar ta baya ta dawo parlon tana Kare
Mata kallo, Daddy shidai Bai ce komai ba se abincin shi da yake ci Yana Kuma
sauraron su,
" How are you two related keda Usman Dina?"
Nusaiba ta kalli Ummiey sannan ta Dan fara Wasa da hannunta ba tace komai ba
" Bakiji ba? Meye tsakanin ku keda Shehu? I mean Usman"
Ummiey ta Kara maimaita Mata, Nusaiba ta dubi Ummiey tace
" Ni budurwar shi ce"
Ummiey ta zaro idanun waje yayinda Daddy dake cin abinci ya kware, cikin sauri ya
tsiyaya ruwa ya fara sha, Ummiey ta dubeshi sannn ta maida hankalin ta Kan Nusaiba
tace
" Are you Nusaiba? Kece?"
Ta gyada Kai tana jin dama wannan ce uwar Shehu, ai ita Bata taba tsayawa gaban
wani ba ta kasa yin abinda tayi niyya ba, sewannan matar ta kasa Koda kwakwarran
motsi. Ummiey ta Kara kallonta tace
" Look! Duk ranar da Kika koyi descent dressing you can come back here, wuce ki
tafi!"
Nusaiba kamar ta hantsila Haka ta fice ranta a mugun bace, Allah wadaran wannan
matar, tana zuwa gate suka hadu da Nads da Harith. Nads ta tsaya suka gaisa sannan
ta fada Mata Shehu na London, Nusaiba ta dinga rokon ta seda ta samu contact din
shi na can kafin ta tafi tana jin abinda Ummiey ya Mata ba komai bane indai har ta
samu contact din da zata sameshi ta ci Masa mutunci.
Afiyya is not free pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 09063467258
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 54
Tunda na sakko akan gado nake jin zuciyata Babu dadi, na dai daure nayi wanka Amma
Ina Zama akan gado Dan fara shiri se na fara kuka, a hankali sautin kukan ke fita,
inama inada dama na ayyana a raina da bazan Bari ya tafi ba, wannan satin biyun da
yayi a tare damu ba karamin farin ciki ya saka ni a ciki ba, ya saka na tuna lokuta
da dama na rayuwata ta baya, yasa ya Kara samun babban matsayi cikin zuciyata. Na
share hawayena Ina murza Mai a jikina har lokacin ban daina kukan ba, how I wish he
will stay with me and be my one, to Babu yadda zanyi Dole zai tafi Dan kuwa komai
is not formalize. Na Kara goge fuskata Ina jin kamar na Hana shi tafiyar, na saka
Kaya na wuce toilet na wanke fuskata sannan na fito parlor Amma dukda Haka Dana
hango fuskata a jikin mirror se Naga idanuna sun danyi ja alamar kuka, na samu
Nanny da Mom suna zaune, Nima na zauna Mom tace min da Bata lura da yanayi na ba
" Yau Shirin ya dade, muje Kar yayi missing flight dinsa"
Ba tareda na amsa ba na Mike tsaye da wayata a hannu na nufi kofa, se lokacin ta
fahimci kuka nake yasa ta mike ta biyo bayana,
" Menene abin kukan Kuma? Naga zaku dinga waya"
Na gyada Mata Kai, tace
" Jeki dakko shade ki saka sannan ki wanke fuskar ki, idan yaga kina kuka he'll be
disturbed"
Haka na koma nayi yadda tace sannan na fito shima lokacin ya shigo, clad in black
trouser da Kuma turtled neck top me long sleeve ta ciki black ya daura suit a sama
saboda har lokacin yanayin sanyin Bai Gama saki ba. Yayi kyau sosae na kalle shi
Dan tunda na fito hankalin shi na kaina, ya karba key din motar hannun Mom muka
fita bayan sunyi sallama da Nanny, na bi Bayan shi ni ya fara budewa seat din gefen
shi na zauna ya rufe min sannan ya zagaya ya shiga ya zauna ya tada engine. Mom ta
tuna Masa akan zamuje office din Dad suyi sallama Dan shi ba zai samu damar yin
rakiyar ba. Tunda muka tafi motar shiru Babu me yin magana har mukai parking gaban
katon building din, Yana kokarin fita Mom ta dakatar dashi da fadin
" Zauna kawai Bari na same shi mu fito"
Yayi murmushi Dan ya fahimci she's giving us some space muyi magana, tana fita ya
dube ni all worried yace
" Damsel! Me yake damunki?"
Na girgiza kaina bayan na Dan bashi brief kallo he looks worried and disturbed. Na
juyar da kaina jin hawayen na Kara taruwa a idanuna, ya saka hannun shi ya janyo
fuskata tareda zare shades din Dana saka, ai tuni se hawaye ya balle min, na daura
fuskata akan Bayan hannun shi Ina kuka a hankali, ya Dan saki siririn tsaki yace
" Look Damsel ki daina kuka, Nima kaina I wish Zan iya Yun kukan saboda na nuna
Miki zanyi kewar ki idan na tafi, but at least idan na tafi na barki kina kuka
hankalina bazai kwanta ba Zan ta tuna yadda muka rabu"
Na saki ajiyar zuciya Ina jin dukkan kalaman shi, na dago da jajayen idanuna da
Kuma fuskata da tayi kacakaca da hawaye nace
" I'm going to miss you terribly"
Ya danyi murmushi me ciwo yace
" It's same here, I promise you I'll be coming often zamu dinga magana kullum
kinji? Know that Ina sonki, a gurina you're irreplaceable kinji?"
Ya fada Yana sakar min tattausan murmushi tareda bani karamin yatsan shi Dan yaga
Ina kallon shi irin Are you sure dinnan, ya gyada min Kan shi, na bashi yatsan nawa
muka kulla yace
" Deal sealed!"
Nayi saurin sakin hannun saboda nasan abinda nayi ko nace mukai Babu kyau, na saki
murmushi na maida hankalina Kan shi nace
" To kaima kayi kukan Naga da gaske zakai missing Dina".
Ya fara min dariya da tafa hannun shi yace
" Idan maza sukai kuka ai Babu kanta, know that I'm gonna miss you"
Na gyada kaina Ina Dan Kara jin Babu dadi. Mom ta karaso tare da Dad sukai sallama
sosae Yana ta Masa godiyar zuwan da yayi. Daga Haka mukai sallama muka wuce airport
shi Kuma ya koma ciki, mom Bata fito ba tayi Masa sallamar daga ciki sannan
tayi.min alamar na bishi, tare muka dauki luggage din har zamuyi gaba tace mu tsaya
tayi Mana hoto sannan Kuma muka wuce, seda aka Gama dukkan wasu formalities da Zan
iya tsayawa tare dashi kafin Kuma yazo ya tsaya gabana yace
" Zan tafi, I love you!"
Na Dan Yi kasa da kaina Ina Kara jin ba Dadi nace
" I love you too"
Ya saki wani murmushi me taushi gaske so Charming nake fada muku yace
" You finally said the L word!"
Na rufe fuskata Ina dariya se Kuma wauan shi ta fara ringing, ya Dan Jima Yana
kallon wayar kafin ya Kara kunnen sjhi Yana min alamar nayi excusing dinsa
" Nusaiba?! Ina Kika samu contact Dina"
Bansan ta ba Amma a family banji ance munada Nusaiba ba, hakan yasa a wayance na
tattara dukkan hankalina Kan sauraron abinda yake fada, yeah sure I'm eavesdropping
Amma ba zaka ce ba
" Har ka Isa ma? Why will you be happy bayan nayi dumping