Advertisements
Chapter 9 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 31

24K to 27K   out of 90.3K words

ne?"


Ya kalleta Yana harar ta da Wasa yace


" Shut up my Friend! Tashi anan"


Haka ta Mike Ina Mata dariya tace Masa ita tafi son Sarki tasan da shi ne bazai
taba korar ta ba not ever, yace yaji taje, abinda na lura dashi they're close
gaskiya sun Kuma Saba sosae. Tunda ta tafi se mukai shiru se shi yace


" Ok tell me, me yasa Baki taba Neman Ummiey ba"


Se na kalleshi sannan na dauke kaina daga kanshi nace


" Ta Yaya Zan nema ta bayan ban santa ba!"


" Hakane Kuma! I hope kin yafe musu?"


Nayi dariya nace


" Basuyi min komai ba fa! Stop making it sounds somehow"


Ya gyada Kai. Kwanaki suka cigaba da tafiya kullum Yaya Shehu se yazo Haka Yaya
sede Basu Kara haduwa ba, idan Yaya yazo se yayi ta complain shi baya son yawan
cousins gaskiya, ranar har na Dan ji haushi nace Masa ko baya son na shirya da
dangin Mama ta ne, se ya fara kame kame shi ba Haka yake nufi ba kawai dai shi
tsoro yake ji, banma tambaye shi tsoron me yake ba saboda hankalina baya gurin,
Yana tunanin dalilin da yasa har yanzun Ummin su Bata neme ni ba. Da daddare na
samu Mummy a daki ana gobe zaa fara bikin Mino, tana ta ware Mana kayan da zamu
saka na biki na shigo da sallama, ta aje rigar hannun ta tace




" Afiyya ya akai? Kinci abinci?"


Na gyada Kai na sannan na zauna Dan nesa da ita nace


" Mhmm Mummy...mhm"




" Menene? Fada min"


Nayi kasa da kaina Ina Wasa da fingers Dina nace


" Mummy Ina son naje gurin Ummin su Yaya Shehu"


Ta Dan kalleni for some seconds sannan tace


" Ki Kira Rooks ta raka ki"
Wani dadi naji a raina Amma har na tashi Zan tafi se na dawo nace


" Mummy Amma bakiji haushi ba ko?"


Ta kalleni ta sakar min murmushi tace


" Banji haushi ba, you need to meet her tuntuni. A gaida su"




Tana zaune Kan makeken gadon ta , tayi kwalliyya cikin doguwar riga ta lace,
fuskarta Babu kwalliyya Amma tayi ado da jewelry set masu tsada da daukar hankali.
Hannunta da kafarta yasha kunshi Banda kamshi Babu abinda ke tashi, gefenta sarki
ne se Shehu dake zaune akan bed table.




" Ummiey wannan fa ba dalili bane gaskiya, saboda Kuna fushi da babanta se ku sauke
akanta? Haba Ummiey ke me zumunci ce fa wallahi kunyar yarinyar nakeji, idan Kika
zauna da ita she's so much in pain".


Ta kalleshi sannan ta maida kanta Kan tab din dake hannunta yace


" Kenan ganging kukai kunzo kuyi min fada?"


Shehu yayi saurin dariya Yana daga hannu, yayinda sarki yace


" No Ummiey ba Haka bane ba,kawai munji ya kamata mu fada ne"


Tace


" Naji! Dakko min veil Dina ku rakani na ganta"


Shehu yayi saurin mikewa Yana fadin


" Ko kefa Ummiey!"


Tayi murmushin jin Dadi, sede kafin ya fita Nadia ta shigo tana fadin
" Ummiey ga Afiyya tazo"


Tayi saurin mikewa jikinta har Dan rawa yake tace


" Da gaske?"


Bata jira amsar su ba tayi waje, Shehu ya dubi Sarki yace


" She longs for her Amma saboda dlili marar tushe tana punishing kanta"


Sarki yayi murmushi ya dafa kafadar Shehu Suka fito parlon. Ina tsaye Harith na ta
cemin sufa sunyi fushi dani, se gata ta fito. Rooks ta Kama hannuna muka karasa
ciki, fuskarta da dariya ta bude min hannayenta, Babu musu na shige jikinta ta
rungume ni, Yan kwanakin kam they were one of the happiest days of my life! Bayan
ta sakeni na gaishe ta tana ta kallona tana fadin mamakin girman da nayi takeyi,
time sure flies! Duk yadda take Jana da Hira se na kasa sakin jikina se hirar ta
koma tsakanin ta da Rooks, seda Yaya Shehu yazo sannan na saki jiki mukai ta hira
dashi, se bayan Sha daya na dare aka raka mu gida. Daga nan aka fara bikin Mino,
anyi biki Babu laifi sede son barka, kwana biyu aka daura aure da dare yayi aka
kaita gidan ta anan Sabin fegi.




" Maryam ya akai?"


Kawu Sa'idu ya tambayi Mummy lokacin da suka hadu duka suka je gidan, Bayan an
nutsa da bikin. Ta dago ta kalleshi cikin idanu kamar yadda yake kallonta shima
cikin idanu, gaba daya se taji ta duburburce ta fara stammering, uncle Babawo yace


" Yaya Sa'idu dama zamu ce ne zata tafi da Afiyya can NY!"


Ya Kara dago idanu ya kalli Uncle Babawo yace


" A'a! anan zata zauna"


Gaba daya suka hada Baki duka su ukun sukace to! Ya Mike ya fice ya barsu zaune
tamkar ruwa ya cinye su, Mummy tayi zumbur ta mike tare da Dora hannunta akai tace


" Me ya faru? Menene wannan?"
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Muka zauna mukai jugum jugum mussaman ni da nake
ganin ni ce na Zama silar fadan uncles dina, se lokacin na fahimci maganganun da
Mummy da wannan matar suka dinga exchanging, wato tazo tana Mata fadan sun kasa
rike ni kenan? To idan haka me wannan matar ita ce Yar uwar mamata da akai auren su
tare, na Kara zurfafa tunanin da nake nace tabbas biri yayi Kama da mutum, no
wonder yaranta ke kallona kamar alien, Nima Kuma nake kallonta tamkar an cira
fuskar ta an saka min, shiyasa Mummy ke ce Mata sune Suka ci amanar zumunci kenan!
Ina wannan tunanin naji sallamar Kawu Tijjani da Uncle Babawo, shi banma San da
zuwan shi ba Kuma dama tun asali shi dinne nafi Jin haushin shi, saboda Ina ganin
shi yafi kowa kusa da inda nake Amma bai taba zuwa yaga inda nake ba. Ganin Mummy a
zaune ta hade Kai da gwiwa tana ta kuka yasa duka sukai kanta Basu ma kula da
gaisuwar da muke musu ba, na Mike tsaye na Kama hannun Rooks muka tafi kitchen




" Me ya faru Anty Maryam wallahi kin tayar min da hankali"


" Ta Yaya bazan tayar maka da hanakli ba Tijjani? Kai da Zan tafi bayan rasuwar
Yaya me nace maka? you should be checking on Afiyya lokaci zuwa lokaci, Amma me?
Kayi, bakayi ba, Kai da zaka saka idanu akan yadda take rayuwa baka masan wanne
Hali take ba balle mu da muke wata uwa duniya! Ta Ina zamu sani?"


Uncle da yayi shiru yana sauraron ta yace


" Mom Rooks! Duk tone tone bashida amfani kowa yayi laifi a cikin mu, bamuyi
zunmunci ba Amma yanzun ba lokacin wannan bane ba, kawai let's decide ya zaayi da
Afiyya?"


" Ni Zan tafi da ita wannan Karan Bai Isa ya hanani ba, yasa anzo har gida an
gaggaya min magana, Dan hakan Zan wuce da ita ta koma hannuna"


Kawu Tijjani da se lokacin yayi magana yace


" Mom Rooks kiyi hakuri nasan I've failed you, tabbas banyi abinda Kika cemin ba
Amma Kuma akwai abinda na kasa fahimta, ni bansan yaushe Yaya Sa'idu ya Zama abin
tsoro ba, nazo Ringim say da yawa na Kuma San halin da Afiyya take ciki Amma idan
na sameshi zanyi Masa magana se na kasa...."




" Shirme kenan! Waye shi Sa'idun? Bai Isa ba wallahi yayi kadan daga yau Babawo
kada ka sake tura Masa kudi, idan ya ga dama kada ya ciyar da ita, you've been
sending kudin makaranta, baka taba inquiring makarantar whether Afiyya tana zuwa ko
Bata zuwa, ka dinga tura mishi kudi yarinya ko abinci say uku ba taci. Ka bani
kunya! Duk Ina plans dinka?"


Sudai hakuri suka bata, har ta sassauta, Muna daga kitchen Ina jin komai da suke
fada, Mummy ma nada laifi ya kamata ta dinga Kira tana jin yadda nake Amma shiru
itama sede tabbas laifin su yafi nata yawa a nawa ganin kenan. Rooks ta dakko juice
daga cikin fridge ta zuba min cikin glass cup ta aje min, itama ta tsiyayawa kanta
tace


" Ina fata Mummy zatayi nasara mu tafi dake"


Nayi murmushi bance komai ba, Haka kurum jikina ke fada min kada na saka Rai da
yawa akwai sauran lokaci. Daga nan se maganar ta lafa, na cigaba da harkokina gidan
su Rooks, da daddare Abban ta ya dawo yayi murnar ganina, seda suka kebe da Mummy
yake ce Mata


" Afiyya kamar ba ita ba, da farko fa ban gane ta ba"


Mummy sarkin kuka se ta fara matse hawaye ta fara fada Masa duk abinda ya faru
tsakanin ta da Ummin Istanbul, seda ta gama yace


" To kiyi hakuri, tun farko Dana Bai dace ku barta anan ba gaskiya, I'm sorry to
say Sa'idu ko gamawa yaranshi baiyi ba balle yayi shouldering needs din Dan wani.
Se a kiyaye gaba, ita Kuma Hajiya Mariya kada ki Kara kulata har ta Bata Miki rai,
kawai kiyi abinda ya dace."


Washegari da wurwuri kamar yadda na Saba tashi na fito, gidan yayi shiru kowa na
bacci na dakko tsintsiya na fara shara dukda Babu koami a parlon se Dan kura, akwai
lokutan da nake ayyanawa idan har na bar gidan Kawu Sa'idu ko tsintsaiya ba Zan
Kara kalla ba, Amma jikina is groomed da hakan yanzun da na kwanta nayi bacci sosae
se naji jikina ciwo yake min, in no time na Gama gyara gidan nayi wanka na dakko
sabon kayan da Mummy ta bani tun jiya nasa a jikina. Na saka hula na zauna nayi
shiru Ina tunanin yau da gobe, a raina Ina adduar Allah ya zaba min mafi alkhairi,
Zan iya binsu su Rooks din idan akwai kaddarar se na Sha wuya shima gidan su bazan
ji Dadi ba, Allah shi kadai yasan me ya tsara min a rayuwata, Dan haka komai yazo
min Zan karba.


Sosae Mummy tayi mamakin gyaran da nayi, ta kalla Rooks tace


" Ba abinda Kika iya malalaciya"


Abban ta yayi dariya yace


" Itama ba Haka aka so ba"


Ta kalle shi tareda fadin


" Wallahi kua! Allah sarki Yaya Allah ya jikan shi!"


Muka amsa Amin sannan muka bita kitchen Dan yin breakfast, Muna gamawa muka hadu
muka ci, na kalla table din dukda munyi girki Amma seda aka kawo daga fada, na
dauki mug na hada tea me kauri na fara sha, Mummy ta zuba min wajen dishes uku
cikin plate dina, tace


" Ki cinye tas ko zaa samu ki Dan murmure, ramar nan tayi yawa"


Haka mukaci Amma ko rabi kasa ci nayi saboda cikina yanzun ya Saba a bashi abinci
kadan, ni na fara dawowa parlor na zauna Ina kallon wani movie, sallamar Yaya Sarki
da Yaya Shehu tasa na maida dubana kansu, suka shigo Basu zauna parlon ba Suka nufi
dining sukai joining dinsu, seda suka Gama sannan Suka sakko duka Suka fara Hira,
ni bama hi nake ba hankalina Yana kan tab din Mummy dake hannuna Ina surfing
internet. Shehu ya dubi Mummy ya matsa gefen ta yace


" Mummy wacece wannan?"


Ta dubeni sannan ta dubi sarki dake kallon ta with so much curiosity tace


" Ki tambayi baban ku"


Sarki ya matsa gefen Abban Rooks ya maimaita Masa tambayar da Shehu yayi, a take ya
aje wayar shi yace


" Kun tuna Anty dinku ta Lagos, sister Ummin ku?"


Shehu yace


" Of course! Anty Halima ba! Allah ya jikanta, Taya zamu manta ta. Ina yawan
tambayar Ummiey Ina babyn data bari, se tace wai tana Nigeria!"


Abbah ya gyada Kai yace


" She's the Baby! Afiyya is your cousin"


Duka Suka kalloni, intense din kallon yasa na dago se Naga sun sakar min Murmushi,
na danyi yake kadan Zan maida kaina kan tab din Mummy ta dakatar dani, ita tayi min
bayanin su, nayi murmushi bance komai ba saboda banida abinda zance din. Shehu ya
dauki waya ya fita, Sarki Kuma shi ne bashida magana sosae Dan haka duka mukai
shiru, Abbah da Mummy sun koma daki, Ina Rooks na tayi Masa hira muakji sallamar
Harith da Nadia suna bin bayan Shehu, Ashe zuwa yayi ya kirasu. Naji dadi sosae it
was like a mini reunion. Wajen azahar zasu tafi Yaya Sarki yace min nazo muje na
gaida Ummin su, har na Mike Zan bisu se nace da Rooks Bari na gayawa Mummy, Ina
fada Mata ta hade Rai tace


" A'a kiyi zamanki, fita zamuyi"


Cikin rashin jin dadi na fito I wanted meeting her, ko mutum daya da Zan nuna nace
Dan uwan mamata ne, Amma nasan Mummy nada nata dalilin. Ina kallo Suka tafi Rooks
ta bisu zata he gaida kakarsu a fada. Yaya Shehu dake tsaye gefena yace min


" Zan zo da yamma, Zaki bani labari kinji?"


Na gyada kaina, Nadia ta Dan rungume ni Suka tafi abinsu.




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 First bank of Nigeria Aisha Hassan
kwalam, send evidence of payment to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 22




" Mom Rooks, Anty Mariya karku manta kokarin karbar Afiyya daga hannun Yaya Sa'idu
ma ya gagare mu, balle mu kawo zancen auren ta. Ya kamata kowannne Abu muyi solving
din shi one at a time. Amma bamu Gama fita daga wani ba kada mu saka kanmu a cikin
wani."


Uncle Babawo ya fada cikin nutsuwa, dukka suka Yi shiru Dan sure he has made a
point, Amma Kuma dukda haka suna bukatar abinda zai kubutar damu.


" Yanzun haka yarinyar zata cigaba da Zama a hannun shi kenan"


Ummiey ta dubi Shehu da yayi kalar tausayi tace


" Oya tashi ka fita, manya na magana kana saka musu Baki, bansan Ina kabar manners
dinka ba"


Ya mike sumsum ya nufi karamin parlon da muke ciki, kana kallona kasan I was not
ok! Gefena ya zauna Yana kirkiro murmushi yace


" Haeee! Tunanin me kike Yi?"


Na girgiza Kai bayna nayi firgigit nace


" Nothing!"


Ya Dan tsira min idanu sannan yace
" Afeey wani ya taba ce Miki Yana son ki?"


Na kalleshi da sauri Ina zaro idanuna waje, na kalli gefena yasan Rooks nake nema,
ya danyi murmushi yace


" Tana daki ni dake ne kawai, nasan you're too young for love words Amma Ina ganin
su kadai zasui saving din ki da wannan rayuwar da kike ciki.."


Bai Gama ba nace


" Anan Zan cigaba da Zama ko? Kawu Bai yarda ba ko?"


Ya girgiza Kai yace


" No...!"


Nayi saurin katse shi Ina Murmushin takaici nace


" You don't have to lie, nasan Bai yarda ba, dama bana expecting ya yarda, wannan
itace rayuwar da Allah ya tsara min"


Yayi shiru yana sauraro na, idanun shi sun tashi da asalin milky color dinsu Dan
dama idanun shi ba fararare bane irin nawa, sunyi ja Amma ba jajawur ba, I can see
tsagoran tausayina a ciki, he looks helpless yace


" I'm sorry!"


Na Mike tsaye saboda Ina jin gurin yayi min zafi I'm suffocating, na kalleshi nace


" Why? Bakai min komai ba, karka manta ance duk abinda yazowa bawa ya karba, nasan
watarana I'll be happy, nasan watarana komai zai Kare, kilan sede labari. I've to
live tunda haka Allah ya kaddara min."


" AFIYYA I love you!"


Zan iya rantsewa cewa hatta dogon hannun dake jikin agogo wato second hand ya daina
juyawa, tamkar lokaci ya tsaya Haka na gani, komai ya tsaya cak se bugun zuciyata
kawai da ya karu, idanun shi cikin nawa, wasu molecules ke fita a nashi suna Shiga
cikin nawa, a wañnan shekarun I couldn't comprehend abinda nakeji, se de da muka
cigaba yiwa juna kallon kurilla se naji tamkar jiri zai daukeni, cikin sauri nayi
shutting idanuna tareda Jan dogon numfashi na koma sofar Dana tashi na zauna
jagwab! Nafi mintina biyar kafin a hankali na bude idanuna sede ni daya ce a zaune
a parlon, shi din baya nan. Cikin sauri na Mike na bude kofar da zata hada ka da
main parlor Amma Babu kowa cikin parlon, na lumshe idanuna na koma parlon na zauna,
Rooks ta shigo tana cemin naje Mummy tana Kirana, na Mike tamkar wadda kwai ya
fashewa a ciki na sameta a bedroom dinta. Na zauna gefenta kamar yadda ta nuna min,
ta Jima tana min tambayoyi akan makaranta da Kuma yanayin zaman da nake gidan Kawu
Sa'idu, Amma mirsisi na ki fada Mata, a ganina Babu wani amfani da zaiyi, tunda dai
komawa gidan ya zame min dole se nayi, tace


" Kiyi hakuri da duk yadda rayuwa take zuwa Miki, Allah shi yasan me yake nufi da
faruwar hakan, saboda wasu dalilai min Bari ki zauna anan ki karasa makaranta,
Kinga na Miki alkawari da kin Gama secondary Zan tafi dake. Kinji?"


Nayi Dan murmushi da zai karfafa Mata gwiwa nace


" Allah ya kaimu Mummy nagode!"


Ina Gama fadar hakan na sauka na fita daga dakin nayi bayan gidan na tsaya, na
tsugunna na Kara tashi wani irin abu nake ji cikin zuciyata, Banda tafasa Babu
abinda takeyi, na lumshe idanuna da na tabbatar sun kada sunyi ja, jinsu nake har
zafi suke min saboda bacin Rai, na Kara tsugunna wa nasa kaina tsakanin cinyoyi na
na fara kuka a hankali, na Jima inayi seda naji zuciyata ta Dan rage radadin da
take min sannan na wanke fuska na koma daki, Rooks na samu idanunta sunyi jawur
tana hada Kaya, na zauna nace


" Me ya samu fuskar ki?"


Tana jin abinda nace se ta fara kuka, na tsaya Ina kallonta Ina ayyana me yasa
zatayi kuka da uwarta, da ubanta, cikin gata da kwanciyar hankali kukan me zatayi
ita kuwa?


" Wai anan Zaki zauna, Wai ba zamu tafi dake ba"


Naja tsaki nace


" Shi ne kike kuka? Allah ya kyauta"


Ina fadar hakan na wuce toilet saboda wata kwalla ke son zubo min daga idanuna.
Wani Abu da Suka manta Babu Wanda yayi tunanin ya gudu Dani, na kanyi tunanin me
yasa Suka dinga bin Kan Kawu Sa'idu Basu daukeni min tafi ba. Duk lokacin da wannan
tunanin yazo min se zuciyata tace saboda haka Allah ya tsara. Kwana biyu da suka zo
gaba daya bana cikin dadin Rai, gani nan gani nan dai, ana uku mukaje Mummy ta duba
kayana, ta samu duk an kwashe haka ta loda min wasu, komai seda ta siya min sabo
hatta panties, ta bani kudi me yawa tace na boye, tana tsaye na boye sannan ta siya
min sabuwar katifa da tafi tawa girma. Washegari ta dawo dani Akan a Daren zasu
tafi Kano zasu bi jirgi zuwa Abuja zuwa NY, a wañnan Daren nayi kuka kamar Zan cire
idanuna, bana tunanin bacci kodan bacci barawo ne nasan ya dauke ni na farka. Da
safe Dana tashi na kalli tsakar gidan hawaye ya kara gangaro min, na dauke su day
hannuna nayi alwala nayi sallah sannan na fito ko komawa banyi ba na fara aikin
Dana saba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. A wañnan kwanakin shakuwa me karfi ta
Kara Shiga tsakanina da Yaya, se na manta da abinda Yaya Shehu yace min Wanda tunda
akai abin kullum kwakwalwa ta na tariyo min abin, idanuna na hasko min idanun shi,
duk lokacin Dana tuna hakan se nayi gasping kadan, wani irin nishadi nake tsintar
kaina a ciki. Haka kunnuwa na Basu gazawa wajen echoing wannan L word din daya
furta. Amma influence din Yaya seda yasa gaba daya abin ya daina tasiri cikin Raina
da zuciyata, saboda shi se na daina jin wahalar zaman gidan su,

9 / 31