Advertisements
Chapter 28 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 31

81K to 84K   out of 90.3K words

Afiyya, Inshaaa Allah
burin mu na ganin rayuwar ki ta inganta ya a dab da cika"


Ta fada tana bude hannunta Babu musu na shiga ta rungume ni, se naji na Dan ji
sanyi a raina, Kuma Nima Ina hango idan baayi auren ba kamar na shiga hakkin shi da
yawa, all what matters to me shi ne naga Yana farin ciki.




" Nadia ya na ganki ke daya Babu Rukayya balle Afiyya"


Ummiey ta fada lokacin da Nads ta koma gida ita daya, ta cire veil dinta ta aje ta
dubi Shehu da ya fito rike da hula me glass, Yana sanye da wani yadi me laushi fari
tas hatta aikin da akai fari ne, hannun shi ya samu ado da kyakyawan silver agogo,
fuskar shi Banda annuri Babu abinda take fitarwa, ya karaso Yana jin Nads na fadin


" Rooks zatai bako ne, ita Kuma Afiy kinsan Yaya Shehu dai ya rabaki da yarki"


Shehu ya kalleta kamar yadda Ummiey ke kallonta


" Ban gane ba"


" Ba kace zaka aureta ba, tana can kunya takeji. That girl should be sent back to
18cents. She's too local"


Se Jin duka tayi a hannunta yace


" Afiy yayarki ce, you should know this"


Ummiey ta mike tana fadin


" Zo mu tafi, I need to see her"


Shehu yace


" Wai Ummiey Ina Zaki? Gurin Afiyya Wai?"


" To da Ina? Kasan yaushe rabon da na ganta?"
Ya Bata Rai sarki na ta dariya yace


" Ummiey Zaki Bata Masa shiri, ki Bari gobe se kije kawai"


Ta dauki mayafi tayi gaba tana fadin


" Sede shi ya fasa, Ina son azo a tukani"


Shehu ya kalli sarki yace


" Bro talk to your mother naaa"


Sarki ya kwashe da dariya yace


" Man just follow her kasan ba ji zatayi ba!"




. Afiyya is not free pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of
Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.60




Duk wannan fara'ar da murmushi duka suka dauke yayi kicinkicin da fuska shi a Dole
ta takura Masa, ita Kam Ummiey ko kallon shi batayi ba a ranta tana ayyanawa lalali
Shehu ya girma, she battled with him akan ma ya yadda yayi budurwa lokacin Kuma da
yayi budurwar se Kuma tazo a wadda Babu Wanda yake kallon ta dace ayi soyayya da
ita. Ta sauke ajiyar numfashi tana fadin yanzun Sarki ya rage dukda shima ya tsayar
Amma Kuma family yarinyar na ta Masa Wasa da hankali, Dan dai kawai Bata son shiga
irin wannan shirgin da zata ce kawai ya hakura ya nema wata.


Kallon shi tayi lokacin da yayi parking kofar gidan mu, ya dubeta fuskar shi a
sake, shi Haka yake Bai Faye fushi me tsaho ba yace
" Ummiey muje"


Ta fito sannan ya rufe motar Yana baya tana gaba, ni Kuma Ina daki na na Gama
shiryawa cikin wani Jan material me tsantsi, jikin shi anyi embroidery da green din
zare na kananan flowers. Dinkin riga da skirt. Inata kokarin daura dankwalin Amma
tsantsin shi ya Hana ni na daura. Se kawai na dakko veil na yafa tun daga kaina Dan
ya rufe bakin gashina. Body mist Dina na fesa sañnan Kuma na dauka wayata Dan
fitowa Jin kwalla min Kira da Mom keyi, na samu na fito kafata sanye da wani flat
shoe green Wanda aka Masa ado da clear Crystals a jiki. Ina fitowa mukai Karo da
ita alamar gurina zata zo, nayi saurin ja baya ta dubeni tare da maida ni daki tace


" Ina kallabin ki yake?"


Na nuna Mata nace


" Na kasa daurawa yayi tsantsi da yawa"


Ta girgiza Kai tace


" Come let me help you, ya kamata daga yau ya ganki cikin kyawun yanayi saboda yau
dinne akai officiating relationship din ku"


Ta fada tana daura min dankwalin in a turban wrap, na kalla kaina Naga yadda nayi
kyau na saki murmushi nace


" Amma an fada mishi cewar auren is close?"


Tayi dariya tana kallon fuskata tace




" Su Suka nema ai, dama Uncle din ki na kokarin yin hakan se Kuma Suka ce suna so"


Na gyada Kai nace


" School Dina fa?"


Ta mike tace


" Idan yazo feel free ki tambaye shi duk abinda kike so , ok?"


Na gyada Kia ta fita tana fadin na zauna idan yazo zata saka a Kira ni. Wayata na
dauka Ina karawa a kunne saboda Kiran da ya shigo, Yaya Hasher ne, mun Jima bamuyi
magana ba dama Kuma Ina son Kiran shi naji yaushe na Masa alkawarin aure kamar
yadda ya fada. A dakile yake magana kamar Wanda akai Masa Dole hakan yasa nima na
amsa kamar irin ya dameni dinnan.




" Afiyya yanzun ke Baki ji kunya ba a tambaye..."




" Sorry I've to go Ina da baki"


Na fada tare da sauke wayar daga kunnena na dubi Nanny dake tsaye nace


" Nanny nayi kyau kuwa?"


Bakinta dauke da murmushi tace


" Sosae ma kuwa. Afiyyata ta girma gashi har zatayi Aure. Allah ya albarkace ki"


Na karasa na rungume ta nace


" Amin Amin uwata ta kaina"


Se ta fara dariya tace


" Sakeni kije Hajiya Mariya na jiranki"


Na juyo da mamaki nace


" Ummiey Kuma? Me yasa tazo?"


Bata bani amsa ba Mom ta fara kwala min Kira, na bubbuga kafata nace


" Bata San kunyar ta nake ji ba ko?"


Na fita kaina a kasa , tana zaune kamar kullum cikin lace anyi Masa dinkin bubu,
she looks expensive like always, na kalleta kafin na Kara maida kaina kasa nayi
sallama sannan na tsugunna gefen ta tayi saurin dago ni ta zaunar gefen ta tace




" Haba Afiyya ta Yaya Zaki dawo Baki zo kin gaishe ni ba, I'm hurt Afiy"
Mom tana murmushi tace




" Ai me Borno ya shiga tsakanin ki da yarki fa"


Ta gimtse fuska tare da fadin


" Kowa Haka yake fada min Maman Afiyya, gaskiya ni bana son Haka. Afiyya I'm your
mother kinji? Ki saki jikin ki Dani"


Na gyada kaina na gaishe ta ta amsa sannan tace min


" Tashi kije gurin shi, I need to talk to your mom"


Na gyada Kai na sannan na silale na fice, Yana tsaye Yana kallon entrance din
alamar Yana Jirana, Ina zuwa ya saki murmushi Yana fadin


" Here comes the Queen!"


Na saki murmushi, Ina ganin watarana idan dariya da murmushi zasu Kare to tabbas
nawa zai Kare, hardly na hada idanu dashi banji Murmushi ya kubce min ba, he gave
me every reason to smile and laugh, kusan dukkan abinda nake so Yana kokarin ganin
yayi min, in fact we share and understand the same love language. Na karasa inda
yake nace


" Ni nayi fushi da Kai fa"


Ya shafa fuskar shi yace


" Tun dazun nace kiyi hakuri fa. Kinga yadda kikai kyau kuwa. You're putting the
stars to shame fa"


Na saki dariya Ina daga kaina na kalli kyawaawan taurarun da Suka kawata sama nace


" Am I that beautiful?"


Yayi murmushi ya dawo gabana ya tsaya yace


" You're beautiful, you're perfect Baby, I love everything about you"


Na rausayar da kaina Ina jin wani Abu Yana Kara shiga cikin zuciyata zuwa jinin
jikina, I found myself falling for him. Wannan lokacin bamuyi ma hirar da mom tace
ba se soyayya kawai da mukai, sede lokacin da muke Hira nake spotting wayar shi na
haske saboda ya aje ta a saman mota, sunan da akai saving ya fara da NU ya Kare da
BA. Banma nuna masa na gani ba saboda I'm really enjoying the moment. Seda Ummiey
ta fito sannan mukai sallama Suka tafi. Ina dawowa na wuce daki ko abinci ban nema
ba. Na cire kayan jikina Sega Mom ta shigo da waya a hannun ta Wai zamu zaba
furniture, na marairaice fuska nace


" Can we leave it zuwa safe Allah na gaji"


Se ta gayda kanta kawai ta yimin sallama, na dauki wayata na fara Kiran shi Bai
dauka ba ya katse ya kirani


" Har an fara kewata?"


" Wacece NUSAIBA? Is she that same lady?"


Na tambaya Ina tsatsare shi da idanuna, ku kwace wallahi Yana gabana. Ya sassauta
murya yace


" Damsel ki tsaya kiji"


Nace


" A kwance nake Kuma shi ne dalilin da yasa na kiraka, I want to know who the hell
she's, wannan Karo na hudu Ina tare da Kai tana kiranka, fada min wacece ita"


Jin muryata ta fara sama na tashi na zauna shi dinma se ya fara lallabani


" Ai na Baki labarin ta, she's in the past Damsel..!"


Nayi dariya nace


" Ok yanzun ma daga past din take Kira kenan? See Honey gaskiya idan you over her
tell her karta Kara kiranka idan ba Haka ba ni Zan fada Mata"


Ko ta Ina zan iya? Waya ga cika baki a gurina, seda na tabbatar na hargitsa shi na
Kuma saka Masa a zuciyar shi ni ba wawiya bace and I'm not into such nonsense
sannan na kashe wayata gaba daya.




A wañnan yammacin Junaidu ya koma Kazaure, Yana zuwa ya Kira Safiyyu Wanda yace su
hadu can wani guri gaba da Shaiskawa, Haka ya Niki jiki ya tafi har zuwa can ya
sameshi a zaune shi daya. Bayan sun gaisa ya dinga Masa dariya Wai me yeya koma
wani kamili, shidai Junaidu ya dakatar dashi ya fada Masa ainahin abinda ke faruwa
Safiyyu yace a washegari zaije maradi ayi ta ta Kare. Junaidu ya tafi dukda Yana
jin Anya yayi hakan ko dai ya Bari yaga abinda Allah zaiyi Amma Ina yasan aikin
Safiyyu kamar yankan wuka take!




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria and send evidence of payment to 09063467258


Afiyya is not free pay 300 to A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send
evidence of payment to 09063467258[24/02, 13:22] +227 98 36 59 34: 61




Junaidu ya samu abun Hawa ya nufi gidan su Dan Hajja tun Yana Hanya take Kiran shi
akan ya Suka ji shiru Bai dawo ba, hakan yasa suna rabuwa da Safiyyu ya nufo gida,
Amma se yake Jin cikin zuciyar shi kamar abinda yake Shirin aikatawa ba daidai
bane. To Amma ya iya ya ayyana a zuciyar shi zai cigaba da Zama da kuncin zuciya
ne, Afiyya ita ce hasaken da ta shigo cikin rayuwar shi ta haskaka wannan duhun da
ya mamaye shi, uta din ce ta fitar dashi daga kangin wahalar da yake ciki, to Kuma
shi din me zaice tunda Afiyya ta nuna bashi take so ba bashida wani zabi sede ya
dauke ta daga abinda ya hanata ganin shi. Ya karasa gida ya samu su har gumin
tafiyar su ya tsane, ya rasa yaushe yarinyar nan Afiyya tayi bakin kallon shi,
yaushe ta daina tsoron shi da har zata kalla idanun shi tace Bata son shi wannan
Abu ba karamin mamaki ya bashi ba, yayi shiru tuni yadda ta Zama budurwa sosae tayi
kyau, duk yadda yake ganin kyanta da komai yanzun yaga ta kere da, ta Zama babbar
mace wadda maganarta ma is reformed .




" Yaro tunanin me kakeyi? Inata tambayar ka ya kukai da Aminatu din?"


Ya dawo daidai sannan ya dubi Hajja a marairaice yace


" Bata yarda ba ta Kuma ki yafe min".
Hajja ta gyada kanta cikin tausayin Junaidu tace


" Dama hakane, ka Bata lokaci har ta samu ta yafe maka, se Kuma ka fara nuna Mata
sonta da kakeyi da gaske. Abu na karshe mafi amfani ka cigaba da addua, idan ita
alkhairi ce Allah zai baka ita idan Kuma akasin hakanne to Allah zai saka maka
dangana a zuciyar ka"


A ranshi yace Ina wani dangana Hajja? Dan dai Baki San yadda zuciyata ke min bane
da Baki ce hakan ba.


" Hajja aure fa zasuyi Mata"


" To ya zakai, se kayi hakuri ka duba wata ka aura, dama Allah baiyi dogon Zama a
tare daku ba"


Duk yadda ta dinga lallashin shi da nasihu iri iri se yaji Kuma zuciyar shi tayi
taushi, mussamman da yaje yin sallar ishai Bayan ya idar malam ya daura Masa
karatu, a ciki ya nuna Masa dukkan abinda ya samu bawa to da sanin ubangijin shi,
Kuma cikar musulmi shi ne ya yadda da wannan kaddarar me kyau ko akasin hakan. Se
yaji Anya bazai bar Afiyya ba, shi din ta Yaya akai ya cancanta ya aureta? Ya manta
dukkan abubuwan da yayi Mata, ya dubi hannun shi ya tuna abubuwan da yayi Mata da
wannan hannun nashi me Kama da katako, ya tuna Mari, duka , zagi, kulle da Kuma
rashin Bata abinci dukda gara da aka kawo Masa daga gidan su Amma se ya siyar ya
Kara jarin drugs dinsa da yake safara. Ya dafe Kan shi ya rasa abinda yake damun
shi, ya riga ya Bata komai baya tunanin wani me hankali me Kuma zuciya zai ma
sparing Wanda ya Masa Haka second glance. Ko shi dinne tabbas ba zai yafewa ko waye
ya Masa Haka ba. Dan Haka ya kamata ya kyalle Afiyya Bai cancanci Zama da ita ba
kamar yadda Yaya jamilu ya fada Masa da Kuma kawunta da take hannun shi, ya fada
Masa ko Afiyya ta rasa miji ba zai taba aura Masa ita ba, Kuma Koda Afiyya na son
shi. Dan Haka ya lalubo wayar shi ya fara neman layin Safiyyu Dan dakatar dashi
daga aikin, Amma Kuma se wayar taki Shiga, ya Kara Kira Amma still wayar Bata ma
magana sede kawai ta dauke. Ya saki nannauyar ajiyar zuciya ya koma ya kwanta Amma
a wañnan Daren Bai runtsa ba.




A bangaren mu shirye shirye sun kankama wanda har mamaki abin yake bani, saboda ku
zaku ce dama can sun hada bikin ne, ba zaka ce irin short notice wedding bane. Kowa
bangaren shi kokarin shiryawa yakeyi. Da farko bayan munyi wannan fadan Akan that
Nusaiba se Naga meye Kuma na Bata lokacina akan ta, tunda ni ya zaba ni yake so se
na kyale shi. Dan Haka kafin ma ya Kira ni da safe na kirashi, ni na tashe shi a
bacci, muka Yi Hira sannan ya tambaye ni


" Kina son Lancaster ko Istanbul?"




Na danyi shiru na dakiku kafin nace
" Saboda school na zauna a Lancaster din ko?"


Yace


" Duk yadda kike so, Amma inaga sede jibi na koma gurin aiki Naga idan zasu iya min
transfer zuwa firm dinsu dake can"


Nace


" To hakan yayi, Amma me Ummiey tace?"




" Ummiey doesn't have business with this, rayuwar mu ce mu n zamu tsara yadda
zamuyi ko?"


Na gayda kaina sannan mukai hira se Kuma mukai sallama yace na fadawa Mom zai
fadawa Daddy da Ummiey da Kuma Dad dina. Ina fitowa na fadawa Mom tace maganar da
suka Gama Yi kenan da Mummy hakan yafi sauki akan ace ni Zan bishi. Kafin dare an
Gama deciding Dan Haka washegari ya tafi abuja, the next day ya wuce turkey. Anan
aka fara shiri sosae da sosae kowa nashi bangaren. Akwai wata Anty na kanwar Mama,
ita ta taho daga maid tazo gyara min jiki, sunanta Anty Falmata, Kama muke Sosae da
ita. Ranar da ta karaso Ringim a gidan Ummiey ta sauka seda tayi wanka ta shirya
sannan Harith ya rako ta gidan mu, an Gama Mata komai na Shirin tarba, Ina kwance
ka kujera a parlor Ina kallo ta shigo, na Mike na zauna shi ne karon farko Dana
fara ganin ta, wancan time din Bata zo ba mijinta ba lafiya, daga nan baa fi wata
biyu ba se ya rasu, Bata taba haihuwa ba dashi, a lokacin Ummiey tasa na kirata na
Mata gaisuwa, shi kenan muke gaisawa, she's one of my best aunties da ko kwana biyu
taji ni shiru she will check on me.


Mahaifin su Mama nada Mata hudu. Maman Mama bama Yar Nigeria bace ance she's
Ethiopian, Kuma Mama kadai ta Haifa ta koma can Ethiopia Amma ance da ciki a
jikinta ta tafi, maman su Ummiey yaran ta bakwai, hudu maza uku Mata, Ummiey ce ta
uku se Anty Falmata ta auta. Se wadda Bata taba haihuwa ba se kuma me Yaya shida
ita ce wadda ta rike Mama a gurin ta. Ita ce mahaifiyar Anty Bintu maman Yaya
Hasher. Dukkan su bazan iya tuna su ba Dan rabo na dasu tun Abbu da ya kaini, Haka
Kuma dama kowa yasan ba nemana sukai ba se yanzun ne nake sabawa dasu. Ko wancen
auren kadan Suka zo saboda Ummiey tace da Mummy Bata son suzo su ganni a wañnan
halin, Amma wannan auren ni kaina nasan it's going to be grand.


Na taro ta, Harith na ta min tsiua Nanny tana shigar min, na gaida Anty tace


" Dama Babana (Shehu) yace Baki Kama da Anty Halima Dani kike Kama. I'm really
sorry Afiy for dumping you. Bansan me ya hau kanmu ba"


Nayi murmushi nace


" Kai Anty!"
Ni na Kira Mom wadda ta kule a daki se order takeyi, Suka gaisa tace a dakinta zata
zauna Nima na kwaso kayana na koma can, Haka mukai a ranar aka fara shafe shafe da
turare. Ana gamawa kafin yamma kuraje sun fito min akan fuskata Wanda response ne
na rashin sabo. Yaya Sarki ta Kira Yana specializing akan dermatology ya min
prescription.


Gaba daya bayan an Gama komai aka tsaida date din bikin da koami wata daya. A cikin
wannan watan se naji ko fitsari nayi Kamar kamshi yake, mura kullum nakeyi saboda
turarruka. Amma Kuma nayi kyau na canja tamkar wata sabuwar halitta, jikina santsi
da glowing kawai yakeyi. Se ana saura sati biyu sannan ya dawo. Anty Falmata na
bacci nayi wanka na shirya cikin wani lace me kyau, na bude powder Zan shafa naji
muryar ta tace


" Don't break the rules!"


Nayi saurin ajewa na fara dariya ta taso tace


" Ya dawo kenan! Nayi Masa farin ciki da zai aureki, you've a golden heart Afiyya
Wanda duk Wanda ya zauna dake se soki. Haka Ya Halima take, Haka Kuma Abbun ki
yake. Continue been good ok?"


Na gyada Kai sannan ta sallame ni na fito, Yana zaune ya Dan fada saboda he has
been busy seda yayi reporting Lancaster sannan ya samo gida da taimakon Baban su
Sheriffa da Dad daya koma can attending ma business.


Na karaso inda yake zaune na zauna se naji kunyar shi nake ji, na Dan sunkuyar da
kaina yace


" What! Kunyata Kuma? No please karkiyi Haka"


Nayi murmushi muka gaisa sannan muka fara Hira ya fara fada min yadda aikin da
komai ya kasance dukda na sani tunda kullum se munyi waya ya bani labari, gidan ma
seda muka zauna muka planning irin Wanda muke so kafin Kuma muka zaba.




AFIYYA is not free pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria
and send evidence of payment to 09063467258
[24/02, 13:22] +227 98 36 59 34: 62




Ana saura sati biyu biki da daddare na fito daga toilet nayi alwala Dan yin sallar
ishai, wayata Dake aje Kan dressing mirror ta fara haske Dan a silent take. Na
karasa na dauki wayar Naga Honey ne. Na dauka tareda karawa a kunne na, muka gaisa
sannan ya sanar min idan sun idar da sallah zasu shigo shi da Daddy. Jin da Daddy
ne yasa nace


" Lafiya?"


Yayi dariya kadan yace


" I dunno. Inaga Yana son yaga yarinyar da zata dauke Masa Dan sa ne"


Ya fada sounding playful, na Bata fuska nace


" Kai ko? Ni sallah zanyi"


Na kashe

28 / 31