Advertisements
Chapter 3 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 31

6K to 9K   out of 90.3K words

karbe
ta Babu Wanda yace zai karba, yanzun Kuma ita kadai nake gani na cigaba da rayuwa.
Kuyi hakuri Zan dai dinga kawo ta Dan ta Saba daku, Kuma se ku dinga zuwa yadda
zata gane ku"


" I knew bamu kyauta ba, a lokacin idan mu karbe ta gani muke it will break you
more, shiyasa muka bar maka ita, to yanzun ta fara girma she needs a mother ba
komai zaka iya Mata ba"


Ya girgiza Kai yace


" Afiyya needs only me, akanta tasan batada uwa ni ne ubanta ni ne uwarta, bana son
na dagula Mata lissafi Kuma. Beside Kun riga kun Yi missing chance din ku na rike
ta"


Duk yadda sukai Akan Abbu ya Basu ni yaki, they threatened him Amma dukda haka yaki
amincewa haka suka tafi ko abincin da aka hada musu Basu ci ba. Wannan shi ne
abinda ya fara hada gaba tsakanin dangin mamata da Abbu, su a ganin su duk lokacin
da suke so suna da right su karbe ni shi Kuma ya nuna musu akasin haka. Daga wannan
se suka shafe batuna cikin rayuwar su Suka manta cewar suna da ya a wani gurin.
Shima Abbu se ya tattara su ya kyale su kawai ya zuba musu idanu. Rayuwa ta cigaba
da tafiya har na Gama primary school dina. A wañnan hutun Abbu ya dakko Hajiya dani
da kawu Sa'idu da Nanny muka tafi saudiyya aikin hajji, acan muka samu Uncle Babawo
yazo daga Central Lancashire inda yake msc acan. Tunda yazo kullum zamu tafi harami
gurin shi nake zuwa ya rike ni, har Hajiya na cewa Uncle Babawo ya kwace wa Abbu na
ni, ni Kuma Kama take min sosae da Abbu, though bani kadai na fada ba, kamar su day
Abbu ta baci shiyasa nake son shi, Sabida I see my father in him. Da muka Gama
aikin hajji se ni da Abbu muka tafi Paris saboda yayi min alkawarin zai Kai no Naga
Eiffel tower. Harda Uncle Babawo muka tafi sauran Suka juya Nigeria. Kwana nan mu
uku muka koma Nigeria muma. Nigerian Turkish college nan na samu admission nayi
joining Js1 din, har lokacin tare muke da Amina tunda babanta ya tambayi Abbu se
yace Masa ai Turkish college zai kaini shima se ya nemawa Amina can muka tafi tare.
Baa boarding muke ba day mukeyi, so Abbu se yasa driver kawai yake daukar mu ya
kaimu, har gida muke zuwa daukanta mu maida ta, ita Kuma duk ranar Friday Mom dinta
zata zo ta dauke mu muje gidan su na wuni. A kwana a tashi kullum rayuwa tafiya
take, ni ina Kara girma kamannina suna Kara fitowa da mamana, idan ka ganni sak
uwata, komai nata irin nawa ne. Tamkar tayi kaki ta tofar haka nake da ita.
Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria. Send evidence through 09063467258




Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔


Seven (Free)


✍️ Ayshatuuu




Bayan Malam ya Gama sauraron duk bayanan zainab se ya sakata a gaba Suka tafi
police station Dan ita kadai ce zata saka ayi bailing Junaidu. Tunda dama it's din
ta hada husumar so seta Zama wadda zata warware ta. Lokacinda Suka Isa gaba daya
Junaidu ya canja kammanni saboda dukan da ya Sha, tunda Suka shiga DPO yace a
lallasa masa shi har se ya gane baa dukan mace. Ga Junaidu da bakar zuciya haka
yaki Basu hakuri se amsar dukan yake. Malam na Isa yayi ma officers din dake tsaye
a reception bayani, daya daga ciki yace Masa


" Malam kawai ka tafi Dan bansan ranar belin wannan gaggararren Dan naka ba"
Malam ya gyara tsayuwan shi yace


" Idan ba zaku damu ba Ina son magana da DPO din ku"


Daya daga ciki yace


" DPO baya gari yaje headquarter acan Dutse"


Malam ya gyada Kai yace


" Idan ba zaka damu ba ko Zan samu num..."
" Baya cikin aiki, kaga Malam Muna ganin girmanka a gurinnan, tunda munce ka wuce
kawai ka tafi"


Malam ya Kama hannun zainab Suka fita a station din, haihuwa kenan sanadin ta Babu
abinda bazai same ka ba walau sharri walau khairi, shi Bai taba zuwa police station
ba Amma dalilin Junaidu yau shi ake cewa ya fita duk girman shi da darajar shi.


" Ai da ka sani ka tatse shi wallahi, malaman nan kudi be dasu, yaran Yan siyasa ne
fa"


Dayan yace


" A'a gwara dai a kyaleshi saboda wannan Yana da connection da manyan mutane kada
mu jawa aikin mu"


Yana zuwa gidan ya tarar da fada ya barke tsakanin Fatima da Hasiya, Hajja nata
kokarin raba su Amma sunki, sede suka hi sallamar shi sannan cacar bakin da suke ta
lafa, Bai ce musu komai ba ya nufi dakin shi, Amma kowacce Tasha jinin jikinta,
Hajja ta bi Bayan shi ta sameshi zaune ya kurawa guri daya idanu, he looks
disturbed. Zama tayi tana fadin


" Malam kayi hakuri kada ka Bari abin Junaidu ya dameka, adduar shiriya ita ce zata
rabamu dashi"


Ya gyada Kai Amma Bai ce komai ba hakan ya tabbatar Mata ba zaiyi magana ba, se ta
tashi ta fito dukda tana son taji yadda aka Kare a station din Amma Bata son damun
shi, Kuma alamu sun nuna baayi nasara ba, tunda ya shigo babu Junaidu. A tsakar
gida taji zainab na fadawa Hasiya yadda sukai a station da officers din, hankalinta
ya Kara tashi to Amma ya zatayi? Sai dai ta zubawa sarautar Allah idanu. Wasawasa
magana se ta Zama babba tun Malam yana zuwa wajen police din suna Masa yawo da
hankali har ya kyalle su, Fatima Kuma sunyi magana da DPO akan se Malam ya Bata
hakuri sannan zai sake Junaidu. Ko fahimtar abinda take nufi yayi se ya kyaleta Bai
ce da ita komai ba Amma se ya kaurace Mata, kwana biyu da tayi a dakin shi magana
ta fatar Baki Bata hada su ba, hankalin ta yayi mummunan tashi, washegari wajen
azahar se ga Junaidu an sako Shi, fuskar shi ta kumbura saboda duka, ga jikin shi
da duk shatin bulala a jiki. Hajja Huwaila ta daura ruwan zafi tasa yayi wanka, ta
gasa Masa jiki sannan ta shafa Masa man zafin da Hasiya ta kawo Mata. Yaci abinci
ya kwanta a ranshi Yana saka next abinda zaiyi!
Na karasa gaban gadon tareda jijjiga Abbu, Amma a hakan nan dai yake kwance
lifeless, Babu digon numfashi dake jikin shi, gaba daya jikin yayi sanyi, kwayar
idanun shi a rufe tamkar me bacci, hakan ya tabbatar min daga baccin aka zare Masa
Rai. Naja baya da sauri tareda rufe bakina da hannuna Ina jin ilahirin jikina Yana
rawa kamar ana kada min mazari. Hajiya na kuka ta fita yayinda ni banyi kukan ba
sede Ina tsaye a gaban shi Ina fatan Nanny ta buga min gefen gado na ta tashe ni
tace min na tashi zanje makaranta, Amma ba mafarki nake ba, idanuna biyu it's
happening in reality Abbu is no more. Nayi shiru ban masan me zuciyata ke sakawa
ba a wañnan lokacin, bazan iya Baku labarin yanayin da na shiga ba nasan dai I was
more than shattered. Babu wata kalma da Zan muku amfani da ita ta nuna bayyana muku
halin da na shiga, Wanda kadai ya rasa iyaye shi zai fahimci me nake nufi. Ina nan
a tsaye na fara jin koke koken mutane, Ina tsaye na tsira Masa idanu, Kawu Sa'idu
da wasu daga cikin Yayan sarki Suka shigo, duka Ina tsaye aka fara kokarin shiray
shi, nasan an ja hannuna an fita Dani, but bazan iya cewa waye ba, kowa kallon shi
kawai nake na Zama tamkar statue. Gidan kafin wani lokaci ya cika dam da mutane,
se kuka suke Amma gani nake duk yadda suke ji ba zai Kai yadda nakeji ba. Mummy
Maryam da Rooks Naga sun shigo, ta rike hannun Mummy dake wani irin kuka tamkar
ranta zai fita Amma Ina nikam nawa idanu ne. Seda aka fito dashi cikin makara
sannan na Mike tsaye, Kawu Tijjani yazo ya rike hannun na idanun shi se hawaye ke
fita yace


" So ki Masa addua"


Haka na bi bayan shi na zauna gaban gawar, my Father,my love, Abbuna, abokina,
uwata da ubana? Shi ne a cikin makara ya tafi, ya mutu Kuma bazai dawo ba. Se na
kankame shi na saki wani kuka me daci Ina fadin


" Abbu why will you leave me? Bansan kowa ba, you're my everything Abbu ya zanyi
rayuwa yanzun..."




Na kasa karasawa saboda gaba daya na shide, ban Kara farkawa ba se Bayan awoyi goma
da wasu abubuwa sannan na farka a firgice Ina Kiran sunan Abbu, Nanny dake gefena
tayi saurin rungume ni a jikinta tana kuka, tana rungume ni nasan ita ce Dan haka
na saki jikina na fara kuka bance komai ba Amma radadin da nakeji a cikin zuciyata
ya wuce gaban na rubuta muku. Allah sarki Abbu ya tafi ya barni se nake jin inama
Nima na mutu na huta, Babu abinda ke tsoratar Dani shi ne na tuna Wai Dole Zan rayu
Kuma Babu Abbu.




A cikin gida an kaishi makabarta a wañnan yammacin, itama Hajiya tunda aka dawo da
abinda aka lullube shi ta mike se kuwa ta yanke jiki ta Fadi, Babu shiri aka dauke
ta se Kano asibiti, kafin suje ta rasu itama, Dan hakan mutuwar se ta hade Mana, ga
ta Abbu ga ta Hajiya, kowa ka kalla kasan ba karamin blow sakon ya bashi ba, a
lokaci guda Allah ya nufi tafiyar su! Rayuwa kenan. Kwana uku gida ya watse Nima
aka sallamoni a asibiti , na dawo gidan kowa ya kalleni yadda na rame na lalalce
lokaci daya se hawaye ya fita a idanun shi, fada min rasuwar Hajiya ta Kara daga
min hankali Amma ban nuna ba Dan ko magana banayi, bana kuka se idan Babu kowa na
zauna nayi kuka na share hawayena, a Rana ta biyar Yan maiduguri suka zo, suka Mana
gaisuwa, Mummy da Nanny ke kaina wajen tabbatar da naci abinci Kuma Ina nan, wani
lokacin ji nake kamar na gudu na fada ruwa Nima ace na mutu da wannan kuncin da
nakeji a cikin Raina. Da zasu tafi sukace suna so su tafi Dani nan Mummy ta nuna
musu ita zata tafi dani Dan hakan se suka Mana sallama suka tafi, wani lokacin Ina
jin inama na bisu may be da duk haka Bai faru ba, to Amma idan na kara wani tunanin
se Naga duk abinda ya faru Dani dama is already written in my book, Dole ne ya faru
Dani. Ranar sadakar bakwai aka watse ranar nayi kuka Dan Ina zaune kowa ya dinga
bajewa sede su shafa kaina su ce min nayi hakuri, nayi kuka na rashin gata, na
rashin madafa na rashin sanin yadda rayuwa zata zo min. Abinda kadai ya rage min
shi ne Nanny da Rooks. Nanny ta zauna gefena tace


" Ki ci abinci kinji, ko so kike kiyi rashin lafiya?"


Ina kuka nace


" Meye amfanin naci abincin, Abbuna ne ya mutu fa Nanny, banida kowa Nanny"


Ta rungumeni tana shafa min baya hawaye itama na bin fuskarta, tausayi na na
dawainiya da ita, shigowar Mummy da Uncle Babawo yasa na Mike na nufe shi, ya rike
hannuna Yana lallashina, se akai saa nayi shiru har Nasha tea. Fita sukai Shi da
Mummy tace


" Ina ganin Zan tafi da ita kawai, kallonta is breaking my heart"


Ya shafa kanshi Yace


" Ita ce abin tausayi Kam, da nayi aure ni Zan dauke ta Amma Zan bar Miki kawai"


Washegari Suka zauan meeting akan fate Dina, Mummy ta dubi kawu Sa'idu da mamaki
tace


" Yaya Sa'idu ni Zan tafi da Afiyya tunda kaga dama ta Saba da Rooks"


Ya dago idanu ya kalleta yace


" A'a ba zata je gidan wani ta zauna ba watarana ayi Mata Gori ni Zan rike ta"


Kawu Tijjani yace


" Eh da wannan dukda nasan Daddyn Rooks bazai taba haka ba, dama mafi Dadi ace mu
mazan muka riketa. Sede Yaya ka Bari na tafi da ita kawai"
Ya Kara Bata fuska yace


" Ni Zan rike ta anan Ringim, magana ta kare"


Mummy ta hade Rai tace


" Yaya Sa'idu in har bazan dauki Afiyya ba to kaima ba zaka dauketa ba, Allah ya
gani sede Tijjani ya tafi da ita, ya zaayi yarinya ta tashi a Abuja a dawo da ita
Ringim"


" Ke wawiya ce Maryam, ke baa Ringim din aka haife ki ba? Mutuwa kikai da Kika
girma anan. Kunji maganar banza"


Haka dai sukai ta musu aka tashi Babu dadi, Mummy tace musu Dole suyi fighting din
Kawu Sa'idu ita Bata yadda dashi ba, washegari da suka je aka raba gadon Abbu,
sannan aka raba na Hajiya nan ma yace se de a bashi nawa anan ne Uncle Babawo ya
fito da will din Abbu kan dukiya ta ya damka ta a hannun Uncle Babawo haka kawu
Sa'idu ya hakura. Bansan me ya faru ba kawai se dawowa sukai sukace Wai a gidan
Kawu Sa'idu Zan zauna, Nanny ta bi Mummy dake ta kuka ganin Ina kuka Dan taji me
yasa bazan zauna hannun daya daga cikin su ba, Mummy tace itama ba yadda zatayi she
can't fight him. Ina ji Ina gani aka tattara kayana duka aka maidani gidan Kawu
Sa'idu Kuma yace Nanny ta tafi maiduguri!




Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, A'isha Hassan kwalam first Bank of
Nigeria, send evidence through 09063467258




Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔


Eight (Free)


✍️ Ayshatuuu
Cikin kiftawar idanu na rasa koma, mahaifina, gatan da nake dashi da komai na tashi
banida kowa da Zan kalla na Kira a matsayin Wanda zanyi kuka a kafadar shi. Ina
zaune Nanny ta Gama hada kayanta taxo ta zauna gefena ta rike hannuna cikin
barbarcin da take koya min Kuma na dauka sosae Dan duk maganar da zakai Ina ji,
Kuma Ina mayarwa sede ba can sosae ba.


" Kiyi hakuri nasan komai zai canja, Amma kiyi hakuri kiyi addua, n samu kawun ki
Tijjani jiya na tambaye shi tunda Anty Maryam Bata bani amsa ba, yace Yallabai yace
su amince da duk hukuncin da kawun ki Sa'idu zai yanke, shiyasa suke Masa biyayya.
Ki sani zamanki a gidan shi kamar biyayya kike ga Yallabai, kiyi musu addua Zan
dinga zuwa duk lokacin da na samu dama. Ki rike maraicin ki kiyi amfani da illimin
ki, kiyi hakuri Allah Yana tare dake..."


Nayi ta kuka da hannunta cikin nawa Amma ko sau daya ban manta abinda Nanny tace
ba, haka Ina kallo ta tafi ko waiwaye babu, dukda ta hada min kayana tsaf tace da
Mummy ita ba zata iya ganina na koma wannan gidan ba. Mummy da yamma ta Gama hada
kayan su da Rooks Dan washegari zasu tafi NY, Muna daki na idar da sallar laasar,
Rooks ta zauna gefena mukai shiru se can tace


" I'm going to miss you Afeey"


Na Dan Mata murmushi Amma bance komai ba, ta Kara gyara Zama tace


" Promise me duk halin da kike ciki Zaki fada min?"


Na Mika Mata hannuna nace Mata na Mata alkawari, shigowar Mummy tasa mukai shiru,
ta zauna ya nade kafafun ta sannan tace Rooks ta fita zamuyi magana, haka ta mike
ta bamu guri. Mummy ta Jima ta na yimin nasiha wadda na rike ta tsaf sannan tace
duk abinda nake so na Kira su zasu bani. Nace Mata to , Bayan maghrib muka shirya
se gidan Kawu Sa'idu, na taka zauren da kafata Ina jin kuncin a cikin zuciyata, tun
a lokacin na fahimci duniya zancen banza ce, Babu wani Abu da zai daure. Suna zaune
an kunna wasu kwayaye Yan kanana an sakale sun haska tsakar gidan, suna zaune akan
tabarma Hafsa nata kuka, yayinda Mino ke wanki se Ummaah su na raba abinci,
akwatina na da aka kawo tun Rana suna aje a gefe yadda aka barsu, mazan Basu nan. A
hankali kamar kwai ya fashe min a ciki na tako na zauna gefen Siyama inda Rooks da
mummy Suka zauna, ni na fara gaida Ummaah ta amsa tana cewa Mummy Bari ta karaso. A
cikin su Babu Wanda yayi min magana Nima haka, seda ta gama sannan ta dakko kujera
ta dawo gefen Mummy ta zauna, nayi jugum Ina bin gidan da kallo, Ina ayyana wacce
rayuwa zanyi Kuma a gidan, gidan Kato ne sosae, sede anyi rashin basira a ginin, an
bar katon tsakar gida Amma Kuma anyi dakuna biyu kawai se kitchen Wanda bama amfani
take dashi ba se bayi guda daya, ta can gefe wajen zauren gidan shi ne dakin dasu
Yaya suke ciki, gidan mu na Abuja ya fado min, my spacious bedroom, parlon mu,
garden da komai na jin dadin rayuwa. Ina wannan tunanin har bansan sun Gama magana
ba se da naji ta taba ni sannan na kalleta ta min alamar na tashi , na kuwa Mike
na bi bayanta, Mino ta raka mu dakin, Babu komai se katuwar katifa an gyara ta da
bedsheet, daga nan Babu komai, Mummy ta gyara min zaman akwatina na, ta nuna min
komai inda yake sannan ta dakko kudi tace min na boye inda ga amfani dashi kadan
kadan idan ya Kare zata Aiko min da wani. Ta Kara min nasiha sannan ta tafi ta
barni a tsaye a tsakiyar dakin nayi shiru Ina tuna Abbu. Bansan iyakar lokacin da
na dauka a tsaye ba seda naji muryar Mino tace min nazo Ummaan su na Kirana, na
fito a sanyaye naje na tsaya nace


" Gani!"


" Dallah samu guri ki zauna"


Na koma na zauna aka Miko min Yar karamar silver da tuwo a ciki, na kalla tuwon ban
ma gane miyar dake ciki ba saboda abinda aka haska gidan dashi ya fara disashewa,
na wanko hannu na saka hannu na tasting miyar first se naji kuka ce, na Dan saki
jiki naci Amma se half way naji cikina ya koshi, Dan hakan na tsame hannuna Amma
tsoron cewa nake na koshi, se na ta juya hannuna a ciki, se can naji Hafsa da
Siyama dake bayana sun fara fada, hankalina haya kansu Amma Ina jin fadan sede ba
zance ga dalilin fadan ba, Ina zaune naji Mino tazo kaina tace


" Ummaah Bata cinye ba"


" Karba ki bawa Hafsa, ni abinda ya rage anan na babanku ne dasu Baba"


Nayi saurin cire hannuna tace min


" Kin koshi?"


" Kar ta koshi Mana, tun karfe nawa na zuba Mata abincin, Wasa ake?"


Haka Suka karba abincin Suka bawa Hafsa, na mike na wanke hannuna ina share
hawayena na tuna yadda Abbu zai ta lallaba ni har se naci abinci, na wanke fuskata
nayi alwala nazo nayi sallah, Ina cikin sallahn naji sallamar Yaya, daga yanayin
yadda yake fadin


" Ina Afiyya?"


Nasan Yana cikin farin ciki, Amma response din Ummaan su ya Sagar Masa da gwiwa


" To uban shishiggi, daga shigowar ka ko ni baka tambaya ba se kanwar uwarka
Afiyya, gaba daya ku tsaya ki jini man, Afiyya tazo ta zauna bance kowa ya zurfafa
muamula da ita ba, bana son kawance ko shishigge mata, ba wata bace, itama ya ce
kamar kowa. Ka dauki abinci kaci"


Yayi shiru duka suna sauraron ta, Yaya yace


" Kai Ummaah, Afiyya abar tausayi ce fa, ya zaai ba zamu jata a jiki ba"
" Mhmm kanwar uwarka ba, Dole Ina fada kana mayar min"


Baice Mata komai

3 / 31