Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
biyar ya hadu da wani Gaye Dan Niger, sunan shi Safiyyu ya hauro daga
Niger ya shigo Nigeria, inda ya samu mazauni anan Niger din. Halayen su iri daya ne
da Junaidu har gwara Junaidu ma ansan asalin shi Amma shi kuwa kana kallon shi ko a
accent dinsa zaka San cewar Dan Niger he's a foreigner. Shagon Dake gefen na
Junaidu nan ya kama haya, Babu Wanda kewa wani magana seda akafi wata biyu se yaga
kawai Safiyyu ya saya wannan shagunan gaba daya, shi ba aiki ma yakeyi ba hakan ba
karamin mamaki da Kuma daga Masa hanakli yayi ba, Amma saboda shi ba ma halin shi
bane yiwa mutane magana ba se Bai kula shi ba. Watarana ana zafi Safiyyu ya fito
Yana Shan iska shima Junaidu ya fito, suna zaune Babu me magana cikin su, se can
Safiyyu yaga Abu ya gilma, ya Mike tsaye ya dubi Junaidu dake faman danne danne a
waya yace
" Maciji na yawo anan gurin!"
Ai tuni ya Mike ya nade sallayya yayi baya Yana kokarin komawa shagon shi Amma ya
dakata, jin Safiyyu na fito Babu jimawa Sega macijin a gaban shi, ya tsugguna ya
dauka macijin sannan ya murde Masa Kai ya wullar Yana wata irin hatsabibiyar
dariya! Junaidu yayi shiru yana jin akwai Wanda ya fishi kenan? Safiyyu ya matso
cikin hausar shi ta Yan can yace
" Kana bukatar taimako ne?"
Junaidu yayi shiru deep in thought with so much hesitation Amma Kuma Yana bukatar
yayi kudi ya cika burin shi,
" Idan kana bukatar abu, kwankwasa min kawai zakayi!"
Ya fada sannan ya wuce ya bar Junaidu tsaye Yana tantanmar abinyi....
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment through 0906346725825
Kamar Wasa Sega shekara daya tazo ta wuce, se gashi har nazo Wai na gama secondary
school, abin har mamamki yake bani, ranar da na fito daga food and nuts wadda ita
ce last paper, nayi submitting sannan na fito na tsaya a gaban varender class dinmu
Ina kallon admin block kamar ranar aka kawo ni Amma gashi har shekaru uku sun wuce,
duniya zancen banza na ayyana a raina, Abbu ya fado min I remembered ranar Dana
Gama primary school dina, na dawo na samu baya gida nayi ta kuka saboda nasan ya
kamata ace Yana gida Yana Jirana, koma shi ne yaje ya dakko ni daga school. Nanny
dake zaune a parlor se kallona kawai take Amma Bata ma bani hakuri ba, hakan ya
Kara tunzura ni na tafi daki Amma Ina zuwa se Naga traveling bag dita a aje, na Isa
gurin Amma kafin na bude na hango wrapped box da ribbon a sama, nayi sauri na
karasa na yage, na kankame visa din zuwa Berlin Germany, se ticket dina Wanda take
reading time of flight baifi awa daya da rabi ya rage ba. Na sauri na cire kayan
jikina nayi wanka, Ina fitowa na samu Nanny ta fito da kayan da Zan saka , na saka
na janyo kayan na fito na samu Abbu a tsaye Yana tamin murmushi....Kaina na juyar
gefe Ina goge hawayen da ya gangaro min, ana mantawa da abubuwa da dama Amma bazan
taba mantawa da Abbu ba, memories din shi will forever be fresh cikin zuciyata. Na
sauka Ina tafiya a hankali Dan fita daga makarantar ba tareda na jira ko daya daga
cikin Yan ajin mu sun fito munyi sallama ba. Tunda dukkan su within Ringim vicinity
suke to watarana zamu hadu. Na cigaba da tafiya a hankali har na karasa gida,
zuciyata tayimin nauyi sosae, Ina karasawa kofar gida na samu Babu kowa a kofar
gidan, na saka kaina na Shiga na samu Ummaan su a zaune tana waya, hannun ta tasa
ta tsayar Dani na tsaya na jira har ta gama wayar tace min, me ya dawo dake? Na
kalleta da alamar rashin fahimta nace
" Na Gama exams din ai"
Ta tabe baki tace
" Se kizo ki daura abinci, kinsan Allah akan Ina Miki magana kina zare min idanu
zanci ubanki, ni Saar kice Zan na Miki magana kina amsa ni yadda kike so, Dan Kinga
kin girma ko?"
Bance Mata komai ba na juya na shiga daki, na cire uniform dina na saka wata bakar
soft morning gown da ta kode saboda kullum ita nake sakawa idan zanyi aiki, Zan
fito Naga wani karamin wrapped parcel a gefen kayana, na karasa na yage parcel din
se ya greeting card ya bayyana da kwalin turare, na aje jin Kirana da Ummaan su
keyi, na wuce Bayan na zura kayan cikin na fito na nufi mangal da aka samu Yaya ya
siyo min danyi moving to gawayi min bar itace. Na hada na hura hayakin ya dake ni,
nayi saurin mikewa na dakko tukunya na daura sannan na koma na Kama jajjage, Ina
nan Ina aikin se naji sallamar Hafsa ta shigo, a gabana ta tsaya tare da rungume ni
tace
" Congratulations Afiyya, Allah ya sanya alkhairi!"
Se naji dadi cikin Raina tunda na dawo ba Wanda yamin makamancin abinda ta yimin,
nayi murmushi nace
" Nagode Hafsisi. Kije ki cire uniform din "
Ta amsa ni sannan ta shige ciki, Babu jimawa na kammalla abinci na koma daki
lokacin Hafsa ta koma dakin Babar su, na ciro kayan na bude greeting card din,
idanuna Suka sauka akan short note da aka rubuta jikin card din da bakin pen, Babu
tantama Yaya ne dan shi ne me using black pen. Ma saki sirirn murmushi na fara
karantawa, idanuna Suka Kara haske saboda yadda zuciyata ke wani tsallen murna, he
confessed Yana Sona, na kankame card din a kirjina Ina jin wani sanyin Dadi Yana
bin dukkan gabban jikina, hawaye ya sakko min daga idanuna, tabbas soyayyar shi
itace abar da ta dinga bani karfin gwiwa cigaba da Zama dasu, na sani zuciyata shi
take so sede takan tuna min lokaci zuwa lokaci akan nayi a hankali kada se na zarma
yazo bama Sona yake ba ko Kuma iyayen shi Suki amincewa . Amma duk da Haka kullum
Rana Kara son shi nake har wancan watan Nanny da tazo seda ta fahimci hakan, muna
Hira da yamma Ina taje kaina tace
" Soyayya kuke keda Yaya ne?"
Na Dan kalleta da sauri se Kuma na rasa abinda zance Mata tunda ni ban iya karya
ba, ko nayi karya ma se an gane karya nake, tace
" Hakane kenan ko?"
Na gyada Mata kaina, tayi shiru Wanda yasa gaba daya naji na takura, se nayi saurin
daure kaina na fita tsakar gida Dan awkwardness din baya min dadi, se dare min
kwanta tace min
" Yaya mutumin arziki ne, yaro ne na gari Dan albarka, shi mutum ne da nake da
tabbacin ba zai cuceki ba, Kuma da auren ku zai kasance da zanfi kowa murna Kuma
hankalina zai kwanta nasan kina hannu nagari, sede Afiyya Ina tsoron abinda zaije
ya dawo, Ina tsoron idan iyayen shi zasu amince ko Kuma kawunnan ki zasu amince
dashi"
Na Dan gyara kwanciyata Ina jin words dinta suna sinking cikin kaina nace
" To kiyi min addua Amma ni Ina son shi gaskiya"
Se batace min komai ba a Haka mukai shiru bacci ya daukeni daga nan.
Jin motsi yasa na rufe card din na aje na samu turaren na fesa kamshin so sweet,
nayi murmushi Ina jin duk wata kewa da nake ta ragu. Da yamma Ina zaune gaban Miya
da maburgi a hannuna naji sallama, Ummaan su ta dubi Hafsa dake gefen ta tace ta
duba waye, kafin ma ta Kai ga fita, Sega masu sallamar sun shigo, Yan Mata ne guda
biyu sun Sha kyau abinsu, Ummaan ta fara musu barka da zuwa, su Kuma se kalle kalle
suke suna yatsina fuska kamar sunga kashi, but ba se an fada maka ba kana kallon su
kaga yayan masu kudi, ta kalleni tace
" Se nace a kawo tabarma?"
Na aje maburgin hannuna na nufi daki Dan dakkowa naji daya daga ciki tana fadin
" No need kawai! Sako aka Aiko Wai a bawa Afiyya!"
Na juyo na kallesu da kyau lokacin na fahimci ai nasan daya daga ciki, she's called
Shahida na Dan taba ganin ta gidan su Rooks sau daya. Umman su najin Haka ta Bata
fuska tace
" Se ku Bata ai gata nan!"
Na dube su nace
" Sako from where?"
Dayar da ba Shahida din ba tace
" Istanbul"
Suka Mika min katuwar Leda, na karba na musu godiya suka juya Suka tafi, Nima na
nufi daki Dan ajewa tace min na dawo na kawo ledar, ko musawa banyi ba na aje Mata
ledar na juya na koma aikin burge miyar, ko Kara kallon gurin banyi ba, idan da
sabo ai na Saba, shekara uku da wani abun ba kwanaki uku bace ba. Ina jin yadda
Hafsa ke exclamation na kyan only God knows what! Na sauke miyar na juye gawayin a
gaban rijiya na kashe sannan na tattara na aje inda nake adanawa, na dawo Zan wuce
naji sallamar Yaya,cikin sauri na juya fuskata dauke da murmushi nace
" Yaya!"
Ya kalleni Yana min wink tareda sakar min tattausan murmushi Amma Bai amsa ni ba,
se ya nufi wajen Babar shi, ta riga ta hade kayan kafin ya karaso ta kalleni tace
" Zo ki dauke tsiyar ki!"
Na karasa na dauki ledar na nufi daki Ina jin kaifin idanun Yaya da ya bini dasu,
na zauna na fara Ciro kayan dake ciki, waya ce me kyau kirar infinix sabuwa dal
cikin kwalin ta, se turarrruka masu kyau Wanda kwalin kawai abin kallo ne. Se abaya
da takalmi a ciki. A kasan kayan Naga small paper
It's your graduation today, you know that u always in my thoughts for a second I
never forget you. I hope you will like the gift. Please give me a call after! Shehu
Matawalle!
Nayi murmushi Ina Kara kallon kayan, shi Bai manta Dani ba na ayyana cikin raina,
gashi ni tsakani da Allah na manta dashi gaba daya. Ture kayan nayi daga gabana na
aje paper, Hafsa ta shigo ta zauna gefena tace
" Saurayin ki ne ya Aiko Miki?"
Nayi dariya nace
" Wai ke ba gidan Siyama naji ance zakije ba"
Ta mike tana zumbura Baki tace
" Na tafi!"
Na Bata sakon ta gaida Siyama wadda daga baya tayi aure tana zaune acan sabon gari.
Bayan sallar maghrib na samu na sulale na fita kamar yadda nakeyi, daga can gefe
Yana tsaye Yana kallon kofar gida na Isa inda yake tsaye nace
" Yayana!"
Ya juyo Yana kallona fuskar shi dauke da murmushi me kwantar min da hankali yace
"Afeey ta! Congratulations know that wannan shi ne starting point, Inshaaa Allah
Zan tsaya Miki Naga kinyi karatu"
Nayi murmushi nace
" Zanyi farin ciki kuwa, saboda Ina son cika burin Abbuna, I've received your gift
I'm grateful"
Yayi min murmushi yace
" Inshallah! Kayan meye Ummaan mu ta baki dazun Dana shigo?"
Na gyara tsayuwa ta na fada Masa daga gurin Yaya Shehu ne, ya Bata fuska yace
" Ai nace Zan siya Miki waya ko ba Haka ba?"
Na Dan rausayar da kaina nace
" To ai bani nace ya kawo min ba, he felt like ya aiko se kayi godiya Mana"
Ya Kara tamke fuska yce
" Kinsan I don't like you with that guy ko?..."
Nayi saurin katse shi nace
" Because?"
" Saboda yadda yake kallon ki Yana nuna sonki yake, Kuma I'm sure kin fahimci hakan
kawai pretense ne."
Yanayina ya Dan canja nace
" To ai shikenan!"
" And what's that? Kenan kinsan Yana son naki ko?"
Na hade hannayena alamar gajiya da maganar nace
" Please Yaya! Kai kasan Kai nake so, Kai kadai nake kulawa, so kana ganin zaka
hana wani yace Yana Sona ne? It will not be, Abu me muhimmancin shi ne Kai nake so
ba wani ba!"
Ina Gama fadar hakan na juya na wuce gida, Ina jin shi Yana Kirana na Masa banza,
matsalata dashi kenan Babu dama wani yayi min magana ranar Haka zai wuni Yana
fushi, yayi ta mita kenan. Ina zuwa tsakiyar gidan aka kawo wuta, gaba daya tsakar
gidan ya dauki haske gani Kuma a tsakiyar gida sanye da hijabi, Ummaan su na zaune
kofar dakin ta, ta zuba min idanu tana kallona!!!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 First bank of Nigeria A'isha Hassan
kwalam, send evidence of payment to 09063467258.26
Ban taba jin tsoro ba kamar yadda naji a wannan lokacin ba, idanuna a warwaje na
zuba Mata idanu Ina jiran abinda zata ce, nasan na kade Tau har ganyena. Ta mike
tana kallona har ta karaso inda na tsaya na kasa motsawa, kafin na ankare ta dauke
ni da Mari Wanda saukar shi seda tasa na matsa daga gurin saboda it landed
unexpected
" Dama so nake na Kama ki da kaina, ai nasan kina fita. Gidan uban wa kike zuwa?"
Nayi shiru Ina rike da kuncina, Ina zance Mata naje? Ko Ina Wasa da wuta bazan ce
gurin Yaya nake zuwa ba, balle ko na fada ma nasan bazata yadda ba. Jin nayi shiru
ta Kai min wani dukan, na tsugunna a gurin na saki kuka, tasa kafarta ta hanbare ni
" Shiru shiru dake kamar ba Zaki aikata ba, dama nasan wannan nunkunfurcin da kike
bana Allah bane, Zakici ubanki a cikin gidannan!"
Jan takalmin da naji yasa na Kara sakin kuka Dan nasan na Gama yawo Kawu Sa'idu ne,
ba zai taba daga kafa yayi tafiya yadda ake Yi ba, sede ya dinga Jan takalmin
sharaf sharaf, nayi saurin mikewa tasa kafarta ta maida ni , saboda yadda ta taka
kafar tawa yasa naji zafi ya ratsa jikina har na saki karamar Kara.
" Gata nan! Dama na fada maka fita take Yi kaki yarda, gata yanzun dai ka ganta da
hijabi, to shigowar ta kenan daga yawon ta zubar!"
Banma San meye yawon ta zubar din ba Amma nasan tabbas ba Abu ne decent ba,
tsugunnawa yayi Yana fuskanta ta yace
" Ina Kika je?"
Na girgiza kaina sede bazan iya cewa komai ba, yasa hannun shi ya kwada min Mari
Wanda da farko nayi tunanin fuskata ta fashe, na saki Kara Ina jin wani dum! A
kunnena, ya Kara matsowa ni Kuma nayi saurin Jan jikina bayana yace
" Ina Kika je? Iskanci Kika fara? To baa gidana ba muna tausayin maraicin ki Ashe
ke Baki tausayin kanki, to aure zanyi Miki tun kafin ki dakko min abun kunya"
Yadda kalmar aure zai min ta dake ni na Kuma ji zafin saukar ta bana tunanin naji
zafin Marin da Suka min, na fara kuka sosae Ina fadin
" Wallahi Kawu ba abinda kuke tunani bane! Allah kofar gida kawai naje. Allah Kawu
ka yarda Dani"
Ni kaina kukan da nake was breaking me, zuciyata ji nake kamar an watsa min ruwan
zafi, tun farkon da nake sneaking nake fita to meet Yaya nasan I was making a lot
big mistake Amma saboda yadda nake son shi ban mayi kokarin danne zuciyata ba, shi
yace min Yana son abun ya Zama a little secret between us saboda yasan iyayen shi
zaiyi wuya su amince da maganar auren mu, plus yana ganin idan maganar ta fito zasu
ga ai har na Kai shekarun da zanyi soyayya, kenan na Isa aure!
Duk tambaya daya se ya mareni, saboda mugunta se ta rike min hannayena ta baya
yadda bazan iya karewa ba, tun Ina kokarin kwatar kaina har na daina se hawaye da
ya dinga bin kuncina, naji fuskata ko Ina radadi kawai yakeyi kamar an zuba min
borkono. Se daya ji marin ya ishe shi sannan yace ta sakeni, ta sakeni na kallesu
tsabar su ta Kara nunkuwa cikin zuciyata, yanayin fuskar Ummaan su kawai na kalla
nasan farin ciki take.
" Ba Zaki tashi ki bace min anan ba?"
Nayi saurin mikewa Zan nufi daki naji Ummaan tace
" taje Ina Kuma? Ai asibiti zaa kaita amata gwajin ciki, ta Yaya na fada maka
wannan ba shi ne Karo na farko da take fita ba, na kyalleta ne Naga gudun ruwanta!"
Se Naga Kawu ya kalleni fuskar shi da wasi wasi Amma Dan ya faranta ran matar shi
Haka ya Jani ya tasa keyata muka tafi wani Rahma clinic dake nan kusa damu, Banda
kukan fili Dana zuci Babu abinda nakeyi, Muna zuwa Babu mutane Dan haka na shiga
dakin scan din, likitan na zaune da wayar shi a hannu alamu sun nuna ya Jima Babu
patient. Kawu ya samu guri ya zauna tareda fadin
" Likita zargi muke tana da ciki saboda yawon banza da take..."
Babu shiri doctor ya dubeni sannan ya dubi kawu da yayi dare dare a kujera, hawaye
Suka Kara gudu akan fuskata, baa taba cimin mutunci irin wannan ba. Doctor y dubi
Kawu Sa'idu yace ya bamu guri, bayan ya fita yace na hau gadon Babu musu na hau ya
zuba min gel cikin bare cikina Wanda seda taikar jikina ta tashi saboda sanyin shi,
ya dauki pointer ya dinga gogagwa akan gel din da ya bawa light rays din damar
penetrating cikin cikina, seda ya Gama ya Mika min tissue na goge cikina naja
rigata sannan yace
" Amina! Waye wancan mutumin? Me ye hadin ki dashi"
Nayi mishi shiru se kawia kallon shi da nake a raina Ina saka meye amfanin fada
Masa? Maganin me zai min? Yayi yayi nayi magana naki, se kuka da nakeyi Wanda Ina
jin azabar ciwo da kaina keyi, zugin da fuskata takeyi da Kuma dum da kunne na
yayi, har na mutu bazan manta da wannan ranar ba. Ganin ba zanyi magana ba ya fita
ya bawa Kawu Sa'idu sakamakon sannan yace Masa ai alada ma nakeyi, ya Kuma San Babu
yadda zaayi me ciki tayi period. Daga Haka muka juya zuwa gida, a hanya yace min
" Ba dai abin kunya Zaki jawo min ba, to aure zanyi Miki! Aure Zan Miki se kije ki
dandana abinda kowa yakeji"
Bance Masa komai ba Dan banida bakin maganar, plus ban masan me zance Masa ba, roko
na riga na roke shi na Kuma fada musu iyakar gaskiya ta, kuskure nasan nayi Amma I
don't deserve abinda akai min. Muna zuwa gida na tarar da Yaya, Baba da Hafsa da
umman su sunyi cirko cirko kamar zakaru. Muna hada idanu dashi na Kara sakin kuka,
Kawu yayi tsaki ya fada Mata sakamakon scan din da nayi, ta tabe baki tace
" Ni fa bazan taba yarda fitar da yarinyar nan take ba shagon wani namijin take
zuwa ba! Yadda kace kawai kayi Mata aure shi ne maslaha!"
Na dubi Yaya da gaba daya fuskar shi tayi turning pale saboda tsabar tashin
hankali, idanuna na saka cikin nashi Ina rokon shi ya fada musu gurin shi nake
zuwa, amma se ya kaudar da kanshi gefe, karshe ma daki ya tafi abin shi ya barni
nan tsaye. Na bi Bayan shi da kallo cikeda madaukakin mamaki, how do you want me to
believe cewar Yaya ya juya bayan shi a kaina, ya kasa fitowa yace dashi muke haduwa
, in fact shi ya kawo shawarar Ina fita Dan mu hadu. Zuciyata naji tana bugawa da
karfin gaske tamkar zata balla kirjina ta fito, hawayen dake ta suntiri a fuskata
na neme su na rasa, what's the worst feeling better than been betrayed? Ina ganin
shi ne worst feeling Dana