Author : Ayshatuuu Category : Complete Novels
ance na yanke shi a cikin shi har na taba internal organs dinsa,
Haka Kuma ba Kare kaina nakeyi ba. I was so confused har jiri nake ji Bayan sun
Gama magana da Kuma charges din da aka daura min. Gaba daya bani kadai ba hatta
uncle Babawo kawai kallon Kawu Sa'idu yake, irin dama you're this bad? Shi Kuma se
murmushi yake Yana kallon mu irin na cin nasara dinnan, Zama nayi saboda na kasa
tuna yadda akai akai murde wannan abin. Uncle Babawo ya fito shida rep din hisba da
Kuma Kawu Tijjani, sun Jima a waje kafin Uncle Babawo ya dawo ya samu dpo din yace
Masa shi Bai yarda da wannan report din ba, Dan Yana da tabbacin anyi tempering
dashi, sannan ya kamata aje can kazauren anyi investigating shi kan shi Junaidu,
station din da har zasu iya canja report da asibitin. DPO ya kalle shi yace Yana
shigar Masa aiki, ni I'm under arrest har se sun Gama bincike sun Kai court! Gaba
daya hankalin mu ya Kara tashi, uncle Babawo ya dubi Mummy yace
" Ki Kira baban Rooks yayiwa IG magana!"
Wani lokacin ka kalla mutum ka kyale shi ne, baka San shi waye ba, ko Kuma idan
Yana bacci kada ka tada shi saboda baka San idan ya tashi me zai iya Yi ba. Gaba
daya a tsorace nake idan na kalla cell dinnan se naji zuciyata kamar zata fito, ban
taba ganin irin wannan rashin adalcin ba, da zarar zanyi magana se ya hanani yace
ai report din says it all, hatta report din da aka kawo daga hisbah board Bai karba
ba, yace ai munyi tempering dashi. Har maghrib muna gurin, mummy da dukkan su se
waya suke Yi. Wajen bakwai se muka ji sirene, lokacin an kawo Mana abinci, se kuka
nake naki naci Suma dake ba a nutse suke ba babu Wanda ya takura min akan se naci.
Bansan waye yazo ba Amma Naga DPO din da sauran officers din suka sun fita waje sun
kame, Babu jimawa suka dawo da commissioner of police na jigawa state Baki daya.
seda yafi minti biyar a ciki sannan wani ya fito yace da mu mu Shiga, naji wani
sanyi ya ratsa ni, I just hope Allah ya tura min savior. Muna Shiga muka same shi
zaune kujerar da DPO yake dazun, yanzun Kam yana tsaye se muzurai yake, na kalleshi
Ina tuna abubuwan da ya fada some few hours ago akan ko waye zaizo we anyi
convicting dina, dama irinmu ne muke Hana society zaman lafiya, karama Dani har
nasan na yanki wani. CP ya kalli Uncle Babawo ya Mika Masa hannu sukai musabaha
Haka Suka da sauran kafin ya kalla rep din hisba ya fara Masa tambaya, ya Masa
bayanin hade report da aka harhada. Yayi going through sannan ya dubi DPO yace
" Me yasa wannan yake a hannun shi baka karba ba?"
Yayi saluting dinsa jiki na rawa yace
" Sir! It's contrary to karar da aka Aiko daga kazaure"
Ya gyada Kai yace
" Bani na kazauren"
Hannun shi na rawa ya Mika Masa ya karba, Nan ma yayi going through sannan ya
dubeni yace
" Amina right?"
Na gyada Kaina, na kwabe fuskata alamar kuka, se ya girgiza min kai yace
" Kar kiyi kuka fada min shekarar ki nawa?"
Ina hawaye tuni ya wanke min fuska ta, na fada Masa in the next few months zanyi
shekara Sha shida, se yace na bashi labarin parent Dina, wannan labarin da nake
bashi yasa muka Jima har na dai kuka, daga nan sequence of questions followed
kowacce Ina amsawa iya gaskiya ta, har seda aka zo zancen auren, nan ma na fada
Masa dukkan abinda ya faru har zuwa sarar shi da nayi. Ya jinjina Kai yace
" Idan na samu akasin hakan fa?"
Na Kara raurau da idanuna nace
" Allah it's nothing but the truth!"
Ya gyada Kai ya dubi uncle Babawo yace muje zuwa gobe zaa sake magana. A hankali
naji sanyi ya ziyar ci raina, na rike hannun Uncle Ina Kara sakin kuka Wanda kowa
yasan na relief ne. Seda CP ya wuce sannan muma muka wuce zuwa 3star hotel inda
mukai booking daki. Kusan wannan Daren raba shi nayi Ina kaiwa Allah kukan, duk
juyin da Mummy zatayi zata ganni akan sallayya hakan yasa ta sakko ta tada Rooks
sukai joining Dina Dan yin sallar Suma. Ana yin assalatu mummy tace nayi wanka Dan
idan nayi sallah na koma na danyi bacci, hakan nayi se 7am na tashi na saka Kaya
muka fita, ni cikin mota nayi breakfast. Muna zuwa Babu jimawa se gashi DPO din
Kazaure ya iso da Junaidu Wanda har lokacin Yana asibiti Basu sallame shi ba, hade
da report din da sukai compiling da Kuma asalin officer da yayi handling case din a
asibiti. Wannan shi ne dalilin da yasa idan akai assault ko accident ake cewa azo
da police officer saboda legal backing, a karshe baka San wakake dealing da ba,
yanzun da ace sunyi attending Haka Babu officer it will cost their work. Se takwas
da rabi CP yazo lokacin Kawu Sa'idu ya iso see hura hanci yake Dan duk tunanin shi
ko nace kamar yadda boka ya fada musu nasara tasu ce Amma idan sukai sake ta kubce
musu it will lead to their downfalls!
Dukkansu sun girgiza ganin CP da kanshi ke handling case din, ko sun manta waye
Uncle Babawo ne? Jikin Kawu Sa'idu yayi sanyi Haka ma Safiyyu Wanda su sukai
bypassing kazaure Suka shigo da sabuwar Kara Dutse, Akan Kazaure na kokarin rufe
maganar, Bayan Haka Suka dauki kudi me yawan gaske Suka bawa DPO akan kada ma ya
saurareni komai ya Zama a favor dinsu. To bayan mun bar Ringim mun tasar ma kazaure
se Anty Nafisa ta Kira Uncle Babawo akan police officers sunzo Kama ni daga Dutse,
wannan yasa muka juyo har mun wuce danbatta muka komo Dutse muka samu komai ya
canja. CP ya karba report ya duba Wanda shi ne asalin report din da akai compiling
lokacin da akai admitting Junaidu. Ran shi ya baci yasa aka Kai Junaidu asibiti Dan
a duba shi a kawo Masa report, iri daya ne dai yanka ne dai a hannun shi na hagu.
Anan aka Gama komai aka tura Kawu Sa'idu cikin cell shida Safiyyu, anan hisba tasa
seda ya rubuta min saki biyu sannan aka wanke ni daga zargin da ake min yayin da
shima aka tura shi rehabilitation home, Amma me Kuna ganin shikenan komai ya Kare?
Wani abun Yana gaba! Yanzun ma aka fara!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.42
Shikam officer din ko nace DPO stripping dinsa akai daga uniform din shi aka bashi
suspension, Amma dukda Haka se naji tausayin su nakeji, abin duka is simple Amma
sun Yi complicating din shi gashi nan dukka yazo musu Babu dadi. Muna gamawa da
division muka wuce asibiti, already Kawu Tijjani yayiwa wani resident Doctor abokin
shi dake aiki anan shekoni magana, akan zamuzo nayi running test, tun daga Kan
pregnancy test aka fara, aka min na HIV, hepatitis aka min scan da sauran abubuwan
da zanyi benefiting, but dukka amsa daya ne non reactive. Naji Dadi naji Kuma sanyi
a raina, naji duk duniya tamkar matsalolina sun Kare, Babu abinda ke fitowa daga
karkashin zuciyata irin hamdala ga ubangiji, I was so proud ni musulma ce, nayi
addua Allah Kuma ya amsa adduar tawa! Ya Kuma kawo min dauki. Se dare muka taho
daga dutse muka dawo Ringim wajen Tara na dare. Dukka a gidan Uncle Babawo muka
sauka, Ina Shiga Anty Nafisa ta rungume ni tana fadin
" Congratulations my dear! Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi"
Nayi murmushi Ina maida Mata martani nace Amin, Dan a raina fada nake ai hakan shi
ne alkhairi na San. Dukka tare muka zauna muka ci abinci, sannan uncle ya fita dasu
Rooks Dan komawa gidan su. Ya rage ni da Anty Nafisa da ta zauna tana fada min,
tsugunne Bata Kare ba, yanzun rayuwata ta fara, kada na sake nayi Wasa da addua,
kada Naga wannan abin anyi solving dinshi cikin sauki haka, to na dage sosae da
ibada. Na Mata godiya sannan na tafi daki nayi wanka na dauki takkadar sakin bayan
na saka kayan bacci na, a hankali na warware takaddar inda idanuna Suka sauka akan
watsatsan rubutu, yadda kuka San gajiyayyen Likita ne yayi rubutun, I remembered
lokacin da yake rubutawa sunana completely Bai sani ba, ya rubuta Afiyya, CP ya
karba ya yaga yace se ya rubuta complete sunana Wanda hakan ya gagara se fada Masa
akai ya rubuta, to Nima hakan take se a takkadar Naga Ashe sunan shi Junaidu
Ibrahim. Na kalla Naga saki daya, biyu yayi min. Na runtse idanuna a hankali Ina
Fadi cikin Raina
" Abbuna! Your little princess is a divorcee now! Allah ya jikan ku Kai da Mama,
Alhamdulillah da ba ku gan wannan bakin cikin ba. Allah nagode maka"
Se hawaye ya fara tickling akan kumatuna a hankali, na zauna na saka kaina tsakiyar
cinyoyina Ina sakin kukan da nasan na Kai limit bazai ruku ba Kuma, Dole se ya
fito. Na Jima Ina kukan kafin na goge idanuna, na ninke takaddar na aje dan nasan
ubana zau karba da safe, Ina Gama addua bacci me dadi ya daukeni, bacci Rahma ne
wani lokacin idan ka yishi tamkar ka mutu ne ka bar duniyar, Dan kuwa ka bar dukkan
wasu problems dinka behind Amma to some extent a wani baccin problems din will
still hunt you!
Washegari ban tashi da wuri ba, bama ni na tashi ba, hayaniyar da akeyi Wanda na
tabbatar cikin parlon mu ne ita ce ta tashe ni, na tashi na zauna tareda kallon
wayata da ta nuna min karfe Tara har da kusan rabi na safe, nayi mamaki irin wannan
baccin da nayi, Wanda na manta rabon da nayi irin shi, tabbas I'm born again!
Hayaniya sosae akeyi na sauka na shiga toilet na wanke fuskata da bakina sannan na
dawo na saka hijab har kasa na nufi kofar, Ina kokarin budewa naji
" Ai an fada min ance Kai kasa aka kulle shi! Idan ba Kai ba waye zai saka Dan uwan
shi ya shiga kurkuku! Me yayi muku Kun takura Masa Kun Hana shi rawar gaban
hantsi..."
Muryar Ummaan su Yaya ce, kaji fitsararru! Tazo kenan akan maganar kulle Kawu
Sa'idu da akai, na juya na cire hijabin na cire kayana Dan ita ce karshen matar da
nake son gani a yanzun. Wanka nayi na shirya zuwa lokacin shiru kake ji Babu
maganar tata. Na fito na samu Anty nata Kai kawo a parlor da kitchen da Kuma
bedroom din su. Da faraa ta na gaishe ta ta amsa tana cewa
" Yau kin Sha bacci! Darling yace Kar a tashe ki kiyi me isarki"
Nayi Murmushin jin Dadi nace
" Ai na tashi naji maman su Mino tazo se nayi wanka"
Ta gyada kanta ba tareda tace komai ba, Nima ganin hakan yasa na wuce kitchen na
taimaka Mata tana aikin. Mun Gama breakfast muna zaune muna kallo se naji sallamar
Rooks da Basman Kawu Tijjani, na Mike tsaye suka shigo bakinsu dauke da sallama da
murmushi ta karaso ciki, Basma ta rungume ni Dan min Jima bamu hadu ba, Rooks ta
zauna seda suka gaisa da Anty tace Mata
" Mummy tace Wai tana ta Kiran wayar ki, Kuma Anty Jidda tazo ke suke jira"
Anty Nafisa tayi saurin mikewa ta Shiga daki, Babu jimawa ta fito ta Mana sallama
akan sun wuce kazaure kwaso kayana. Kwanciya Basma tayi saboda kallon da ya dauke
Mata hankali, ni da Rooks muka fara Hira
" Kinsan duk abinda ya faru wallahi laifin su mummy ne, ni yanzun na daina ganin
laifin Kawu"
Nayi murmushi Dan Nima nasan hakane sakacin su ne ya kawo hakan nace
" Ai ya riga da ya wuce, Kuma gashi dukka mun koyi wani Abu a cikin rayuwa"
Ta gyada kanta. Daga nan muka cigaba da Hira take fada min sun kusa komawa NY Dan
Daddy ya Kira Mummy yace Mata daga can office sun fara complain akan hutun da ta
dauka yayi yawa. Har wajen laasar munata Hira se daga can Basma ta tashi akan Yunwa
takeji. Kitchen muka shiga muka daura abinci, munayi Muna hira har muka Gama. Na
juye cikin warmers tunda da yawa nayi nasan duka idan Suka dawo to nan zasu sauka.
Basu Suka dawo ba se Bayan sallar ishai, Muna daki min shiga YouTube muna kallon
latest videos. Ni na fara fitowa, idanuna ya sauka akan Nanny dake tsaye, na wullar
da wayar hannuna Kan kujerar Dake gefena, na ruga inda nake tsaye na fada jikinta
tareda kankame ta
" Nanny!"
" AFIYYA!!"
Na Kara rungume ta Ina sakin murmushi me kayatarwa tundaga karkashin zuciyata, na
nuna tsananin farin cikin da nake ciki. Mummy ta shigo da sauran Suka zauna suna
kallon mu, na saketa sannan na rike hannun ta Ina fadin
" Nanny yaushe kika zo? Amma ba Zaki tafi ba ko?"
Ta gyada kanta, Uncle yace na kyaleta ta huta idan yaso idan munje kwanciya se
muyi duk hirar da zamui. Mu ukun muka kawo abinci muka musu serving, cikin jin
Dadi muka fara ci, se na tuna lokacin da dukka zamu hadu gidan Hajiya ayi ta Hira
Muna Yara, lokacin Basma na Baby, se Anty jidda ta goya Mana ita, ni da Rooks mu ta
fada wani lokacin Hajiya ta karbe ta tukun. Allah sarki rayuwa kenan, gashi har ya
wuce se tashin labari. Bayan Tara gidan ya watse se mu hudu, Uncle ya kirani yace
jibi zamu wuce Abuja zaayi min visa, passport Dina yayi expire zaayi renewing sabo
sannan zamu wuce London Dan tuni ya fara nema min admission. Ya nuna min ya dawo
min da Nanny Dan na Kara samun nutsuwa, yace na manta duk wani Abu da ya faru na
fuskanci sabuwar rayuwar Dake jirana. Naji Dadi Dan Haka washegari duk ta tafi a
parking da muke, dan kayana na Kazaure da kayan sawa kawai Suka dawo se trolleys
Dina Amma furniture din dama sun tafi da masu siya, ana jirgewa aka siyar dasu aka
saka kudin cikin account Dina. Da daddare kowa na daki, naji sallama a parlor na
dubi Nanny da ta fara guangyadi nace
" Nanny ki kwanta, ana sallama zanje na duba"
Ta gyada kanta cikeda gamsuwa tace
" To"
Na dauki hijab Dina na fita parlon, daidai Anty ma ta leko tana cemin
" Bakiyi bacci ba?"
Na kalla agogon parlon nace
" Takwas ne fa Anty, sallama naji shi ne na fito na duba"
Ta gyada kanta na nufi kofar parlon inda na tarar da Yaya a tsaye shi da Hafsa,
muna hada idanu da ita ta rungume ni tana fadin
" Afiyya Ashe kin dawo?"
Na gyada Mata kaina na Basu hanya su shigo, Yana ta kallona ko kiftawa bayayi nace
" Yaya ka shigo Mana!"
Ya saki ajiyar zuciya yace
" Tohm!"
Tare muka shigo parlon inda Anty ke tsaye suna gaisawa da Siyama, ganin harda Yaya
tace Bari ta Kira Uncle, se Yaya ya girgiza Kai yace
" Gurin Afiyya nazo"
Anty ta gyada kanta Bayan ta min kallon da ni kadai na gane me take nufi sannan ta
koma daki. Zama nayi nace
" Me yasa Baku zo tun dazun ba"
Ya shafa Kan shi yace
" Ai Uncle Babawo yace Kuna parking zaku wuce gobe"
Nayi murmushi nace
" Eh inshallah"
Se ya gyara Zama yace
" Ina Miki farin ciki da cikin kankanin lokaci komai ya warware a cikin rayuwar ki,
yanzun hankalina zai kwanta Dan nasan zakiyi rayuwa cikin aminci da alkhairi. Kiyi
hakuri! Nasan an zalunce ki a gidan mu, Bai ma dace nazo gabanki Ina Baki hakuri
ba, Amma nasan ke me hakuri ce Zaki yafe musu, sannan Zaki bamu wani chance mu Kara
zame Miki cousins, Dan Allah Kar kiga kamar I'm selfish ko Zaki yiwa Uncle Babawo
magana a fito Mana da Baban mu? Ummaah Bata bacci tana cikin tashin hankali, can
you please do me that favor?"
Na kalleshi Ina murmushi Wanda karkashin zuciyata tafasa kawai take, a raina
ayyanawa nake har shi ya Isa ma yazo gabana Yana fada min Haka? Ya manta irin
abinda iyayen shi su kayi min? Ya manta duka zagi, yunwa da suka saka ni a ciki?
Duk wata se an bada kudin abincina Amma a Rana a naci abinci da yawa sau biyu ne a
Rana, me yafi wannan? Duk shekara se an bada kudin makaranta tata Seda yayi amfani
da kudin wajen biyan bokan Shi, ko ya manta ranar da nayi sneaking naje wajen sa na
dawo iyayen shi su kace cikin shege nayi, yazo a gaban shi ake dukana aka kaini
scan Amma ya kasa fitowa ya Kare ni! To me yayi saura Kuma? Me zaice min yanzun?
Ina ganin bamu da wani abun fada a tsakanin mu.
" Afiyya I'm so so...."
" Don't be! Abinda bakai da ba yanzun ma idan kayi bashi da amfani. Ka sani
iyayenka bazan taba yafe musu ba, ko na yafe musu Allah se ya Kama su da cin amanar
maraya, Nabiyyu SAW yace ka shafa Kan maraya saboda zuciyar ka zatai taushi, Amma
shi se ya sakani cikin tsananin kunci da masifa, to me zance kuma? Zaman shi a
prison dokar kasa ya taka ba tawa ba, ni sakayya ta Baku fara ganin komai ba, I'm
not that naive girl anymore, Kun nuna min cewar ya kamata na canja"
Duk maganar nan da nake Hafsa ko a jikinta cake din da na kawo musu take munching
abinta, taci ta dauka exotic din Dana kawo ta kurba abinta hankali kwance.
" Afiyya baban mu kawun ki ne, a yanzun matsayin mahaifi yake a gurin ki..."
" Amma..."
Se nayi shiru kawai ban karasa abinda nayi niyyar fada ba, ganin hakan yace
" Hannunka baya rubewa ka yanke ka zubar!"
Nayi dariya nace
" Haba?! Da alama baka taba zuwa asibiti ba, ka kalla yadda mutane suke zuwa
willingly ake cire musu hannun su Dan su huta da azaba, balle ku da Babu wnai Abu
Dan nayi cutting dinku down"
Ina Gama fadar hakan na shafa fuskan Hafsa dake kallona, innocently, nace
" Hafsisi Bari na dakko Miki Abu kinji?"
Ta gyada kanta na koma ciki na dakko kayan da na riga na hada Dan ita sede Ina
dawowa parlor na tarar sun tafi, na daga kafada ta na kulle parlon na koma dakina
na samu Nanny ta Jima da bacci. Maimaikon bacci se kawai na dakko kur'ani nayi
tilawa sannan na kwanta Ina tabbatar da nayi blocking dukkan channels din tunani
na, ya kamata wannan abin su tsaya a Haka, Dole nayi bacci me dadi!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam to First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
Please can I have your prayers?43
Daga emirate council din Ringim suka kaimu Kano, tun sassafe muka kammalla
breakfast da sauran abinda ba zaa rasa ba. Na kalla kaina jikin fuskar wayata
idanuna da sukai can ciki duka sun fito, wannan unexplained ramar da nayi a fuska
ta cike se abinda bazaa rasa ba, jikina ne dai nasan wannan se a hankali dukda
shima ya fara karbar canjin. Na saki ajiyar zuciya Ina Kara nanata kalmar
alhamdulillah, na sani