Advertisements
Chapter 5 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 31

12K to 15K   out of 90.3K words

cika. Da asuba kowa ya tashi yin sallah,
seda ya Bari kowa ya fita massalaci, masu Yi a gida sun tayar, ya fito Dan shi ba
sallar yake ba se jefi jefi idan ya ga dama. Dakin Fatima ya wuce ya sameta tana
kan sallaya tana sallah, ya zauna Kan kujera har ta idar Dan ita Bata lura da
shigowar shi ba. Tana idar da sallar ya sakko ya nufo ta, da sauri ta juyo zatayi
ihu yace


" Junaidu ne!"


" Me kake min a daki? Fitar min daga daki nace"


Yayi dariya yace


" Ba wani Abu nazo nayi Miki ba, daki da kike cewa na fitar Miki daga shi, ai ni
Banga daki anan ba. Kinga sakamakon zagi da sharri da Kika min, ko Baki fahimci
nine nasa aka Miki sihirin da kikai kaikayin jiya, idan Baki fita harka ta ba Zan
saka an Miki wanda Zaki rasa rayuwar ki gaba daya, ko ki haukace, Kuma wallahi
zakiyi kyau da hauka.."


Yayi dariya ita Kuma tuni jikinta ya fara rawa, tsabar yadda ta tsorata da maganar
shi.


" Idan kinji shikenan kin tsira idan..."




Malam ya bude labulen dakin a zuciye ya Shigo, Fatima da Junaidu lokaci daya Suka
Mike, Fatima tayi saurin matsawa gefen Malam Neman kariya, yayinda Junaidu ya tsaya
sokoko Yana tunanin abinda zaiyi, Wani Mari Malam ya sauke Masa a saman kuncin sa,
yayi baya kamar zai fadi, ya cakumo wuyan shi ya tsayar dashi ya Kara Masa wani,
cikin tsananin bacin Rai yace


" Ni Dana zaije gurin bokan! Malamin tsubbu! A gidana"


Junaidu yayi shiru yana kallon Malam dake janshi har ya kawo shi tsakar gida, dake
fadan malam yasa duk sun firfito Dan ganin meke faruwa, duk suna tsakar gidan yasa
Sukai carko carko suna kallon Malam da Junaidu a hannu, ga Fatima a gefe se hawaye
ke bin fuskarta!




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria
send evidence to 09063467258.[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Junaidu ya runtse
idanun shi Yana tuno kalaman malam daya bayan daya, yasa hannun shi ya hargitsa
gashin da ya Tara a kanshi, looking like the bad guy he always is, ya sakko da
katon akwati ya fara life kayan shi a ciki


" Malam kada kayi haka, kada ka yanke hukunci lokacin da ranka ya baci, yawanci
idan akai haka a gaba zaayi Dana sani, Kai me fada ne, Kai me bawa Yara tarbiyya ne
kada kayi haka Malam!"


Hasiya ta fada tana jin kamar ta kurma ihu, Hajja dama tunda taji abinda ya furta
ta sulale a gurin ta zauna, saboda tasan matsawar ta cigaba da tsayuwa jirin da
take ji zai yadda ita ne a gurin, Kuma ba lallai ta Kara taka kafafunta ba. Malam
Bai ce ma Hasiya komai ba yaja hannun Fatima ya maida ita daki sannan ya dawo
tsakar gidan, Amarya ta dube shi tana kuka tace


" Malam ka sassauta zuciyar ka, ku kuke yiwa mutane waazi akan kada su Bari bacin
Rai yayi ruling din su se gashi Kai da bakin ka ka tsinewa Dan da ka Haifa ka Kuma
Kore shi daga gidan! Malam"


" Na fada Junaidu na fitar shi a cikin Yayana, kada ya Kara waiwayata sannan Kuma
kada ya Kara zuwa gidana"


Daga haka ya juya ya wuce dakin shi, Hajja ta fara kuka Hasiya na Taya ta, amarya
ce me Dan kwarin gwiwar Basu hakuri da lallashin su. Junaidu ya kammalla hada kayan
shi tas, ya fara kokarin Jan akwatin Sega Hasiya da Ummiey sun shigo, Ummiey kanwar
shi ce,


" Yanzun Junaidu baka bawa mahaifin ka hakuri ba, me yasa kake haka?"


Ya kakkabe kanshi yace


" Ya Dade Bai hakura ba in har ni Zan bashi hakuri. Duniya da Fadi maye ba zaico
Kan shi shi kadai ba"


Ummiey ta rike hannun shi tace


" Dan Allah Junaidu karka tafi, Dan Allah kaje ka bashi hakuri, durkusawa wada ba
gajiyawa bane"


Ya doke hannunta yace


" Ni Zan durkusa na bashi hakuri, ni basamude ne Kinga yazan durkusawa wada kuwa?"


Ta share hawayenta tace


" Mahaifin ka ne fa, idan ka tafi Ina zakaje"


" Ke Wai Ina ruwanki, badai ya koreni ba yaje ai watarana zai neme ni, Baba Hasiya
ki kula min da Hajja nagode!"


Daga haka yaja kayan shi ya fita ko tsakar gidan Bai kalla ba balle yaje ya ma
Hajja sallama, Hasiya ta biyo shi ta rike rigar shi tace


" Tafiya zakai? Ba zaka bashi hakuri ba wai!"


" Ki Bari Dan Allah Baba Hasiya, kawai Zan wuce ne"


Daga haka Bai Kara waiwaye ba ya juya ya bar gidan, duk abin Junaidu da ya fita
daga gidan yaga Babu inda zau nufa, garin Babu mutane saboda safiya su Kuma ba Yan
uwa ke gare su ba se kawai yaji wani kunci da takaici ya lullube shi. Ya cigaba da
tafiya Yana cin buri da alwashi a cikin zuciyar shi, inda Suka Saba Zama yaje ya
zauna, shi daya sannan ya fito da bankin shi ya fasa, kudi sosae ya taru a ciki Dan
shi mutum ne Mai adani bawai komai ya samu yakai ciki ba. Kamar yasan irin wannan
ranar zata zo masa ya dinga Tara kudi, mikewa yayi ya siyo abinci yaci sannan ya
dakko wayar shi ya Kira huzaifa yace Masa ya sameshi a gurin su, sannan ya taho da
sauran.




Nanny kwana biyu ta kara, ranar asabar da safe ta gama Shirin ta zata tafi, tun
dare da Naga ta na saka min komai yadda ya kamata kayan data siyo min na fara kuka,
ko lallashin na Bata Kara Yi ba ta kyalleni. Na kalleta idanuna sunyi jawur nace


" Nanny tafiya zakiyi? Ki tafi Dani Dan Allah Nanny, it's horrible living here"


Ta rike hannuna tace


" Ni awa Zan tafi dake Afiyya? Zan cigaba da zuwa Ina ganinki inshallah, duk abinda
kike bukata kimin waya zansan yadda zanyi a kawo Miki. Karki manta you've to live
saboda iyayenki su samu masu musu addua, karki manta da maraicin ki, a kullum ki
tuna Allah shi ne gatanki Kuma komai ya faru dake kaddara ce. Naga hisnul Muslim
dinki a jaka, na Kara Miki wani kiyi ta addua komai zai zo da sauki ko ba yau ba,
akwai ranar da zakiji Dadi!"


Na saka kaina a hannunta na dinga kuka, zuciyata ciwo take min, a shekarun da nake
dasu kalilan na fuskanci abinda da yawa Basu San Yana wanzuwa ba.


" Idan naje maiduguri zanyi magana da dangin Maman ki muga ko zasu zo su dauke ki,
sannan zanyi magana da Alhaji karami naji ko akwai abinda zai iya Yi"


Nayi saurin girgiza Kai Ina jin bacin Rai Yana mamaye ni nace


" Nanny Dan Allah kada kiyiwa kowa magana, ki rabu dasu Dan Allah, a yanzun bana
bukatar su. Watarana Nima Zan fita daga halin da nake ciki"


Se tayi murmushi me ciwo tace


" AFIYYA kada kiyi fushi dasu, akwai abubuwan da a shekarun ki bazaki gane ba,nasan
nan gaba Zaki fahimci waye ainahin kawun ki Sa'idu. Kiyi addua sosae Allah zai kawo
Miki dauki"


Kasa rakata nayi, na tsaya kofar daki nayi ta kuka, Mino da Siyama na tsaye suna
kallona da tausayi musamman Mino, Ummaan su dama Bata fito ba, daki sukai sallama,
kawu ya leko yayi Mata godiya yace Yaya ya kaita Tasha, ya koma ciki. Har ta Kai
zaure se na nufe ta da gudu na rungume ta, na rike hannun ta Ina fadin


" Nanny kin yi min alkawarin Zaki dinga zuwa akai akai ko?"


Ta gyada min Kai ta share min hawayen dake zarya a kumatuna tace
" Kiyi shiru kinji, karki Kara kuka komai zai wuce"


Ta dubi Yaya dake a hargitse, idanun shi sunyi ja tace


" Me sunan waziri amanar kanwar ka, ka kula da ita Dan Allah"


Daga haka ta fita, na Dade a zauren Ina kuka, Babu Wanda yazo ya lallashe ni seda
nayi me isata sannan na dawo ciki nayi shara na hada wuta. Nayi wanka na saka Kaya,
Yan kayan Dana cire naje na wanke su dukda ba iyawa nayi ba Amma wannan rayuwar da
nake ciki ni ce uwata ni ce ubana, Babu me cemin nayi wanki ko akasin haka, ita dai
indai nayi Mata aikin ta to idan naga dama ma kada nayi wanka. Inata sakin ajiyar
zuciya naji an kwalla min Kira,na fito Amma na kasa magana ta dubeni tace


" Bakin ki ciwo yake Miki da Zan kiraki ki ki amsawa?"


Nayi Mata shiru kawai, daka min duka tayi a cinya ta tareda dangwarar min da shayi
tace


" Shegiyar yarinya kawai"


Bance komai ba na juya na bar tea din a gurin, ba abinda nake son Sha kenan ba, in
fact abinci a wañnan lokacin shi ne Abu na karshe a wanted list Dina, kawai space
nake bukata. Na koma daki nayi jugum se jin kawu Sa'idu nayi Yana kwalla min kira,
na fito a hankali shima ban amsa ba, Ina tsayawa kawia naji saukar Mari a kuncina,
bana tunanin an taba Mari na, idanuna a warwaje na rike gurin na dago na fara
kallon shi, kallon da nake Masa na mamaki, tsoro, tsana da Kuma warning, hakan yasa
ya daka min tsawa yace


" Saukar da idon ki kasa shegiya kawai!"


Have you ever felt pain radiating daga zuciya zuwa kowanne sashe na jiki kuwa?
Wannan kalma ta shegiya na tsane ta, tafi Marin ciwo a gurina. Naki dauke idanuna
yau taurin Kan ya motsa , sede ya motsa inda bazan ci nasara ba. Waya ya dakko ya
min duka da ita, na dinga kuka Ina ihu Amma se zagina yake Wai taimko na yake na
Isa nama matar sa rashin kunya. Sede yayi min lilis, Mino na gefe da Siyama na
kuka. Ya kalleta yace idan na Kara Mata Abu ya Bata go ahead ta dakeni! Anan ko
tashi banyi ba na dinga kuka Banda tukuki Babu abinda zuciyata keyi, se jikina da
nake jin ya fashe saboda dukan da nasha da cord wire. Ba Wanda ya kulani Dan
yaranta tuni ta daka musu tsawa Suka baje, shi Kuma har lokacin Yaya Bai dawo ba.
Ina wannan kukan tace naje nayi wanke wanke idan na ga dama na kashe kaina damuwata
ce. Haka na tashi naje inayi suka zo suka fice gaba daya sunyi kwalliya Hafsa
kayana ne ma a jikinta, shima Babu jimawa ya fita ya rage ni kadai. Ina gamawa na
fara maida kayan kitchen, har lokacin hawaye Bai daina sauka ba, mafita kawai nake
nemawa kaina. Na shiga kitchen wukar Dana wanke ta silale ta fado seda na aje
kwandon sannan na dauki wukar, I began to think ko dai na kashe kaina kawai kowa ya
huta, na rike wuakr Ina lumshe idanuna, na saita ta daidai cikina se Kuma na maida
ta inda aka cemin major arteries da veins na jiki na gurin wato wuyana, na saka a
hankali na furta
" Astagfurillah, Abbu Mama I failed you!"




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence through 09063467258.
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Dake yan class din sun fara lesson a month ago se
ya zamana sunyi nisa a physics din, motion shi ne topic din da ya rubuta a jikin
board, Amma kafin ya fara bayani Kan motion din seda ya tambayi Yan class Wanda zai
iya recapping abinda aka koyar. Sauda dake kusa Dani ta daga hannu, hakan yasa
malamin yayi pointing din ta ta tashi ta fara bashi amsa, ta Jima tana bayani kafin
Kuma yace ta zauna bayan yasa an tafa Mata. Na kalleta Bayan ta zauna nayi Mata
murmushi itama tayimin. Babu dadewa ya shiga bayani Alan motion, nayi shiru Ina
assimilating abinda yake fada, haka Ina jotting points where necessary. Seda ya
Gama sannan ya mikawa class rep note din yace ta rubuta Mana a board ya fita gaba
daya. Na sauke ajiyar zuciya na kalla Sauda nace


" Sauda Dan Allah naga note book dinki"


Tayi murmushi ta Miko min tace


" Amina kinada kyau!"


Nayi murmushi kawai Amma ko godiyar compliment din banyi ba, na bude na fara kwafar
note dinta, dake inada sauri Kuma Yan class din sun tsaya Wasa ko fara rubuta sabon
note din baayi ba yasa na Gama kafin wata period din ta shiga. Nutsuwa nayi inata
going through Dan na samu na iya abinda aka koyar. Ina cikin Yi se ga wani malamin
ya shigo me maths, wani young guy haka, muka gaishe shi yayi abinda zaiyi ya fita,
har lokacin Babu Wanda yayi noticing Dina a ajin, a ranar da aka tashi Sauda ta Ara
min books dinta Dan naje na kwafa. Ana tashi na hada books Dina na saka cikin jaka
na dubi Sauda na Mata sallama, se sauran dake kusa damu da bansan sunan su ba na
musu sallama na fito Ina kallon yadda kowanne dalibi ke kokarin tafiya gidansu, se
na tuna tawa rayuwar a NTIC. Na girgiza Kai kawai na fara tafiya a hankali, ga Rana
ga zafi ga Yunwa, Amma haka na nufi gida bakina ya bushe saboda kishin ruwa. Tun
daga kofar gida na hango Yaya a tsaye Yana magana a waya, cikin sauri na karasa Ina
hango murmushi kwance saman fuskar shi, na karasa kafin yayi min magana ko ni nayi
ya Miko min wayar shi, na karba na Kara a kunne ba tareda na duba me Kiran ba.




" Hello Afeey darling!"


Kadan ne Bata kashe min dodon kunne na ba saboda ihun da tayi, na saki dariya a
hankali Ina kallon Yaya da ya lumshe idanun shi Yana kallona nace


" Rooks! I missed you"
Tace min she missed me too sannan tace


" So fada min ya makaranta? Yau ranar ki ta farko how do you find it"


Tambaya dai a gurin Rooks ba daga nan ba, na zauna kan bencin da Yaya ya janyo min
na fara fada Mata komai akan makarantar, a karshe nace Mata


" Nafi son waccan ta Abuja, saboda idan na dawo gida Ina tarar da Abbu da Nanny a
gida!"


Seda na fada naji idanuna sun ciko da kwalla, itama a yanayin yadda tayi min magana
nasan jikinta yayi sanyi, na danyi murmushi me ciwo nace


" I've to live Rooks ko Dan nayi ma Abbu da Mama addua, I've a reason to live"




" Yawwa Afeey, kiyi addua komai zai zo da sauki. Yanzun kin fini class!"


Nayi dariya na gama tsokanar ta, cewa ya kamata ta fara Kirana senior, I'm not
match for her Dan kuwa na fita aji yanzun. Haka muaki sallama Raina fari Kal, duk
gajiyar Dana kwaso se naji ta Dan tafi. Na Mika masa wayar Ina murmushi nace


" Thank you Yaya!"


Yayi murmushi Yana kallona so intense yace


" Ya makarantar?"


Na amsa da alhamdulillah sannan nace Masa Zan shiga gida bayan na kara Masa godiya,
I felt his eyes trailing on me har na shige gidan. Ina shiga na tarar dukka sun
dawo, da sallama na shiga, Mino ta amsa min tana fadin


" Ina Kika tsaya?"


Na danyi shiru Ina tunanin abinda zanyi cooking, se nace


" Mhmm! A hankali na dinga tahowa"


Ta gyada kanta na shiga ciki na cire kayana sannan na fito nayi wanka, tunda naji
gidan shiru nasan Ummaan su Bata nan, Nima ban tambaye ta ba Dan idan Bata nan
gidan yafi Dadi. Abinci muka ci sannan nayi shara na dawo na fara kwafar note,
sallamar Ummaan su naji, na daga labule na Mata sannu da zuwa, ta amsa sannan tace
na aje littafin nan nazo na Mata wanke wanke, na bude baki da niyyar ce Mata ai
nayi tawa sharar tunda dama shi ne aikina, Amma se nayi sealing bakina kawai na
tattara littatafan na aje na fito, dogon hannun rigar dake jikina na nannade na
hada kayan wanke wanken guri daya na zauna, na fara a hanakli kamar me wanke Raina,
nayi nisa ta leko daga daki ta kwalla min Kira, bafa Afiyya take cemin ba sede tace
min


" Ke!"


Shikenan Kuma Dole na amsa, hannuna na dauraye, kafin na karasa dakin naji sallamar
Yaya Yana kwalla min Kira, na tsaya tareda juyowa kawai se Naga Nanny a Bayan shi,
na cire slippers din kafata na ruga a guje na fada jikinta, na kankame ta kamar Zan
koma cikin ta, ta rungume ni itama, na saki dariya wadda take so genuine and
sincere nace


" Nanny!"


Ta Kara rungumeni, bana tunanin Zan manta farin cikin da naji a wannan ranar, da na
sake ta Kuma se na fara Kuka me ciwo, na tuna gida na tuna beautiful moments din da
mukai tare, na tuna Abbuna. Na rike hannun ta na dinga kuka Ina jin tamkar Ina
shading dukkan bakin ciki, da gajiyar Dana kwasa a wannan kwanakin. Ummaan su ta
fito dasu Mino dake daki, ta hade Rai tana hararata da ni bama lura nayi ba.
Lallashina ta shiga Yi sannan na dakko Mata kujera nace ta zauna, se lokacin ta
lura da Ummaan su Suka gaisa ni Kuma na koma kan wanke wanken da nake, Ina wanke
wanken Ina Mata tambayoyi tana amsa ni, su kansu nasan Basu taba sanin inada surutu
har haka ba. Na Gama wanke wanken tana ta Bina da kallo har na Kai kwanukan kitchen
tana zaune, fuskarta na nuna tausayi da Kuma mamakin wata daya yadda na koma wata
daban, tana zaune na hura wuta kafin ta Gama kamawa na leka nace da Ummaan su me
zaa dafa, tace na Kira Mata Mino na tafi gurin Nanny. Ina Shiga daki da Nanny Sega
Yaya, ya shigo hannun shi da Leda ya bani, ruwa ne me sanyi da carbonated drink,
nayi murmushi na Masa godiya, na bude Mata na Bata Amma se kallona take, na riko
hannunta nace


" Nanny naji dadi da Kika zo, kullum se nayi addua ko ke ko Uncle Babawo wani yazo,
Allah ya amsa addua ta"


Se Naga hawaye suna sauka daga fuskarta, nace


" Me yasa kike kuka Nanny, kin tuna Abbuna ko? Ina Masa addua kullum bana mantawa"


Ta riko hannuna tace


" Me yasa Kika rame? Baki cin abinci ne? Ko aiki kike da yafi karfin ki?"


Yarinta ce tsagoro a tare dani, ga wautar Yan fari, ga gabuntar autanci na zauna na
fada Mata duk halin da nake ciki, na Kara cewa


" Nanny Babu dadi anan, komai Babu dadi, rayuwar gaba daya Babu dadi, dama haka
kowa yake komawa idan baban shi ya rasu ko Kuma ni ce Kawu Sa'idu baya so?"
Ta girgiza Kai Amma ta kasa magana, se ta rungume ni a jikin ta, mukai sallah, a
Jakarta ta fito min da foiled kaza, na kalleta na Kara rungume ta, na zauna naci
nayi nak, Dan haka da aka bani jollof din taliya nace na koshi. Guntun lemon da
tayi na shanye, wa yaga komai se da dalili Kuma an Dade Baa hadu ba. Ranar bacci
nayi me dadin gaske, dukda katifar ta matse mu Amma ban damu ba. Da sassafe kamar
kullum na tashi na fita shara na hura wuta sannan na gama nayi wanka na dawo na
tarar ta bude akwatina na, ta dubeni tace


" Ya akai duk kayan datti a ciki?'


Nace


" To Nanny bazan iya wankewa ba"


Ta gyada kanta kawai, ta fito dasu, wankakkun kadan kawai

5 / 31