Advertisements
Chapter 13 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   13 / 31

36K to 39K   out of 90.3K words

taba ji a rayuwata. A wannan Daren nayi kuka kamar Zan
cire idanuna, at some point na tuhumi rayuwa da yin walagigi da ni, nayi kuka na
rashin madafa, na rashin gata, na rashin abinyi!




Afiyya is not free pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria,
send evidence of payment through 0906346725827




Bana tunanin na taba ganin dare me tsawon wannan Daren, har so nake gari ya waye
tunda nasan bazan iya bacci ba. Kukan ma ya daina zuwa, there are times a cikin
rayuwar ka da kake jin komai baya tafiya daidai Kuma baka saka ran wani relief zai
taba zuwa, to Haka naji, naji zuciyata ta bushe, naji I was equal and ready to
whatsoever comes up, menene a rayuwa? Kin Dadi to ni nasan na Gama jin Dadi. Na
mike na duba tab dita da na dakko nake amfani da ita a boye Naga biyu da rabi na
dare se kawai na fita tsakar gida nayi alwala, na Jima a tsaye Ina jin iska me dadi
tana kadawa, a raina nayi wishing, Ina ma dai ace matsalolina zasu bi iskar nan su
tafi? Na dubi sama yadda tayi blue me kyau, ga taurari da Suka cika ta Suka kawata
saman. A lokaci daya na furta subhannallah! Se naji karfin gwiwar yin addua ya
kamani, na koma daki na tada sallah amma Dana idar zanyi addua se na gagara yi, na
fara kuka cikin zuciyata abubuwa tari ne barkatai a ciki, da tarin bukatu a ciki,
Amma bakina se yayi nauyin furta Haka, Abu daya ya kwantar min da hanakli nasan
Allah yafi kowa sanin bukata ta.


Kada na cika ku da wannan maganar,asuba nayi a kunnena na fito nayi sallah sannan
na gyara dakin, I wanted something to distract my mind away. Nayi shara nayi wanke
wanke sannan na kunna murhi nayi dumamen tuwo na dama koko. Ta lungun dakin ta anan
gawayi yake se na tafi dakkowa Dan na Kara na daura musu ruwan wanka, tun a kofar
dakinta nasan Kawu Sa'idu Bai fita ba saboda takalman sa na gurin. Na Gama dibar
gawayin naji tana fadin


" To ya zaka cewa Yan uwanka, kasan Dole zasu ki maganar auren"


Ya saki dariyar da naji tamkar ruwan zafi take cikin zuciyata yace


" Zance musu maza take bi, shiyasa"


" Ba zasu yarda ba, kaima ka sani! Shi mutmunin da kake fada zaka aura Mata yaushe
zai zo?"
" Tunda yau Zaki fita na fada Masa ya zo gobe"


Jikina ya fara rawa nayi saurin barin gurin, da gaske ban kawo zai iya yimin aure
ba, ban taba kawowa cewar Bayan wannan mummunar rayuwar da nayi ba Ashe akwai wata
dake jirana ba. Na karasa komai nayi wanka na koma daki abincin ma ban ci ba Dan
I'm not in the mood, bana ma jin yunwar. Ina zaune ta kwala min Kira tace min na
daura abincin Rana saura Kuma idan na ga dama na Kara fita, abin da aikai min jiya
ba komai ba me, sannan idan naga dama in Zama cikin shiri sati daya kawai ya rage a
daura min aure. Wannan maganar ta girgiza rayuwa ta, a hankali na koma daki na
zauna tareda runtse idanuna Ina tunanin aure zaayi min da gaske, nidai bana son
auren tabbas, fada ma Bata Baki ne Amma Kuma ya zanyi. Motsi naji a kofar dakin
Wanda yasa na juyo da sauri Amma ganin Yaya ne yasa na maida kaina kasa na bawa
banza ajiyar shi. Ya zauna Yana facing Dina, Amma se yayi shiru ya gagara yin
magana balle ni da ko kallon inda take ma banyi ba, na Mike Dan na fita na bar Masa
dakin, bazan iya cigaba da kallon shi ba, ganin shi kawai zuciyata zafi take min,
for some unknown reason se nake jin he doesn't worth me.


" They're planning to get you married, kin sani ko? Ya zamuyi ?"


Na ji muryar shi me cikeda rauni ta daki kunnena, na juyo na kalleshi he looks so
pitiful, kallon shi kawai seda ya raunana zuciyata, na dauke Kai nace


" And so? Meye naka na auren da zaayi min? Ni kaina Ina mamakin dalilin da yasa na
fara sonka, bansan har me na gani a tattare da Kai da yasa na soka ba..."


" AFIYYA!..."


Ya Kira da karfi tare da mikewa tsaye, Nima na katse shi da fadin


" Kar ka min ihu! Bari na Gaya maka you don't worth aurena, nayi tunanin duk inda
zaaje ba zakaji tsoron ka fito kayi defending Dina Amma jiya se Naga akasin hakan,
se ka kasa cewa gurin ka nake zuwa, akanka na jure abubuwa da dama Amma Kai ka kasa
Kare ni a wajen iyayenka, Kai kuwa me zaka iya yimin idan na aureka"


" Afeey please kizo mu gudu, I can't imagine you with another guy..."


Ya ciji leben shi idanun shi sunyi jawur yace


" Zan Kira uncle Babawo right away na fada Masa halin da ake ciki"


Ya fada Yana Ciro wayar shi daga pocket din pants din dake jikin shi na
tracksuit, na karbe wayar nace


" Don't blow up the matter so quickly Dude! Beside ni bana tunanin tunda iyayen ka
Suka dage se sunyi min aure akwai Wanda ya Isa ya hanasu. Na mafi so su cigaba da
daukar alhakina yadda Ina kallo zasu Shiga jahannama.."
Hannun shi ya daga a zafafe zai mareni na tsaya cak nace


" Mari? Mare ni Yaya,ai abinda ka koya kenan, sannan Dan Allah zo ka fita kafin
mahaifiyar ka ta dawo tace na maka fyade!"


Ya kalleni idanun shi kamar zasu fito Dan mamakin maganganu na sannan ga bacin ran
halin da muke ciki. Yana fita na saki kuka a hankali Ina rike kirjina dake
barazanar konewa saboda zafin da nake ji, na Jima Ina kuka sannan na Mike na Ciro
tab dita nayi connecting na Kira Rooks, kamar tana jira tayi picking fuskar ta
dauke da murmushi tace


" Afeey darling!"


Na Dan saki faint murmushi nace


" Rooks darling! Ina Mummy da Abbah?"


" Wait me ya sameki, Afeey marinki akai? Me ya sameki?"


Na saki kuka da nake ta rikewa na fara fada Mata dukkan abinda ya faru, tayi shiru
har na gama sannan tace


" Afeey bazan iya rike wannan secret din ba, I've to inform Mummy. Ta Yaya Zaki
cigaba da rayuwa a Haka? Afeey Mari ? Ciki? Shege shi Kuma yayan dama I never like
your relationship wallahi! Kinsan ko kin aure shi kina tareda su Kawu Sa'idu, kinyi
aure Amma zaa cigaba da rayuwar da akeyi, Allah ya hada kowa da rabon shi, don't
feel bad Dan Kun rabu better days are coming"




Cikin kuka nace




" Se yaushe? Yaushe ne better days din? Yau ko gobe? Na gaji Rooks Ina jin kamar
kaddarar ta yimin nauyi"




Se ta fara kuka tana fada min nayi hakuri Allah Yana sane Dani, a karshe tace Dole
zata fadawa Mummyb, Ta fada tana share hawayen dake bin fuskarta, na girgiza Kai
nace


" Baki gane ba Rooks, da Mummy dasu Kawu Tijjani suna da maganin yimin da tuni wani
zancen ake ba wannan ba, tunda kiga Ina Shan wahala to tabbas Haka Allah ya tsara
min, idan kin fada musu tada musu da hanakali kawai zakiyi, Dan hakan Dan Allah
kiyi shiru, kema na fada Miki ne Dan naji sanyi a cikin raina. To Baki sani ba
Rooks, Kawu sure zai min, karki fadawa kowa"




" Da wa?"


Na girgiza Kai alamun ban sani ba tace




" Auren Dole AFIYYA? you mean Kawu zai maki aure da wanda Baki sani ba? Baki taba
haduwa dashi ba? come on AFIYYA this is freaking 21st cent not lokacin da, rayuwa
ta canja Afeey!"


Nayi shiru Ina tunanin me zance ma Rooks dake bambami cikin wayar, abinda take
bazai canja fact that aure kawu zai min ba, banida Wanda zai taimaka min. Da gaske
na fahimci a wañnan lokacin zumunci ya Kare, lokacin da Abbu keda Rai ban taba
kawowa watarana Zan tsinci kaina cikin wannan halin ba, ban taba kawowa ni wadda
nake da gata Zan Kare a Haka ba, tabbas rayuwa zancen banza ce.




" Come on Rooks, maganar nan ta tsaya tsakanin mu, bana son kowa ya sani, saboda
Kawu Sa'idu yace zai fadawa kowa ni nake son mijin. do this for me sister please"


Tayi shiru se can tace


" Afeey are you ok? Are you sure Zaki iya hakan?"


Na gyada Mata Kai inajin yadda zuciyata ke tarwatse wa tana bajewa and I was left
shattered Amma dukda Haka Ina da yakinin Allah zai kawo min dauki!




"But know that I'll always be there for you?"


nayi murmushi daya fitar da dimples Dina Wanda ko magana nake lotsawa suke, I
remembered Ummaan su na yawan cewa Yunwa CE tasa nake da dimple ba kyau ba.


Auren ma nayi tunanin zaa hadani da Wanda Zan kalla naji dadi Amma da aka tashi se
aka Nemo Wanda ko a lahira bana zata Masa Shiga aljanna, Kar kuga laifina Manzon
Allah SAW yace Wanda yabi iyayenshi kamar ya bini ne, idan ka Saba musu ni ka
sabawa! Shi yayi fatali da wannan maganar.
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.28




Komai se nake ganin shi tamkar almara, cikin kankanin lokaci Kawu yayi blowing
magana zuwa sauran Yan uwan shi uku. I was so naive then, I was so young then ko
addua ba sosae nake ba gaba daya banyi understanding concept of kaddara ba, saboda
Gani nake kawai duk abinda ya faru da Kai kawai kaddara ce and nothing, absolutely
nothing will change kaddarar. Haka nan na Hana Rooks t fadawa kowa saboda Ina ganin
Dole na karba dukkan abinda yazo cikin rayuwata. Yammacin jumaa Ina kwance se naji
sallamar Kawu Sa'idu, bama sallama zance ba kwala min Kira kawai yake Yi, nayi
saurin mikewa na dauki hijabi na na fito Yana tsaye a kofar dakin har na kusan yin
Karo dashi, na Dan ja baya nace


" Kawu Ina wuni?'


Ya dalla min harara yace


" Ki canja Kaya kizo mijinki yazo"


Idanuna a warwaje nace


" Miji Kuma?"


Nayi saurin janyewa baya saboda dukan da ya kawo min, komawa nayi ciki Ina tausar
zuciyata, Dan na riga na sawa zuciyata I'm accepting aurennan, da dai in cigaba da
Zama gidannan to gwara na aura ko waye, bansan fadar hakan kuskure bane babba.
Skirt da riga na saka, na kalla kaina Anty Nafisa matar uncle Babawo ita ta dinka
min zuwanta na karshe Nigeria, ita kadai tazo wani biki shi ne tazo taga yadda
nake. Yayi min cif cif, na fara budewa ta kasa, dukda shekaru na basuda yawa Amma
Kuma Babu laifi jikina me kyau ne. Mayafin kayan na dakko na yafa na fito, Ummaan
su na zaune ta kalleni ta kyabe Baki, bance komai ba na nufi waje wata kyakyawar
307 sabuwa dal se sheki take da daukar idanu baka wuluk. Yaya na tsaye ya hade Rai,
na kalleshi shima tunda na fito idanun shi akai na yake, fuskar shi tana kunshe da
tashin hankalin da kana kallon shi za ka iya karantawa, se Naga yayi rama a rabuwar
da mukai shekaran jiya, tun da muka Gama wannan maganar ban Kara ganin Shiba. shida
Baba da Kawu Sa'idu suna tsaye se wasu Baki Wanda nake tunanin daya daga cikin su
shi Zan aura Yana tsaye , na karasa na gaishe su, dukkan su idanun su a kaina Kawu
yace


" Tsayuwar me kike ba Zaki karaso ba"


Na tako a hankali har nazo dab dasu idanuna a kasa, ya dube ni yace
" JUNAIDU se kayi hakuri, Haka take kamar Yar kauye, gata nan!"


JUNAIDU na nanata cikin zuciyata, na daga idanuna na kalle su dukkan su shekarun su
baya wuce talatin ba, sun Sha bugaggun shaddodin su, daya ruwan sararin samaniya
dayan Kuma ruwan toka, dukkan si babu me hula a Kan shi and I wonder yadda banji
Kawu yayi korafi ba, na tuna zuwan mijin Siyama na farko Bai zo da hula ba aka ta
ciccira maganar se gashi wannan ma yazo a hakan. Tarkata yaran shi yayi Suka shige
ciki ya barni tsaye Ina Wasa da hannuna cikin mayafi,


" To Bari na Shiga mota se kuyi magana"


Dayan ya fada Wanda ya tabbatar min da bashi bane Junaidun, ya wuce cikin motar, na
dago na kalle shi he's handsome wannan shi ne abinda na fara fahimta Bayan kallon
fuskar shi, he looks decent daga fuskar shi zaka fahimci baya da magana, he looks
innocent and good. Wannan shi ake cewa illusion, what the eyes sees is not always
real! To wannan shi ne abinda nayi idan ka kalle shi ba zaka taba tunanin he's thug
ba, shi da halayen da yake exhibiting sunyi hannun riga, he appears a good man.
Ganin yayi shiru Bai ce komai ba yasa na gaishe shi a karo na biyu, ya kalleni ya
ce


" Lafiya!"


Ban Kara magana ba naji Raina na kokarin baci, a Haka nayi ta tsaye wajen minti
talatin Dan hakan na Kara duban shi nace


" Allah ya kiyaye hanya nagode!"


Ban jira amsar shi ba na wuce cikin gida, Ina jin kaina ya cunkushe da tambayoyi
iri iri sede Babu Wanda Zan iya amsawa a ciki Dan ni na bansan amsar ba, Babu Wanda
na samu tsakar gida Dan haka na wuce daki na kwanta na lumshe idanuna Ina adduar
Allah ya zaba mafi alkhairi. Bayan ishai Suka fita Ummaan su day Kawu se ya rage no
kadai Dan Hafsa anyi hutu ta tafi Kano, Ina nan a kwance naji sallamar Yaya, da
sauri na Mike Ian bin shi da kallo har ya samu guri ya zauna, na tsare shi da idanu
Ina jin yadda ake min tickling a cikina, gaba daya naji farin ciki ya lullubeni,
hakan ya Bata min rai kenan har yanzun Ina son shi.


" Seems kamar kin yadda da wannan auren da zaayi Miki ko?"


Nace


" Eh!"


Da mamaki ya kalleni yace


" Bakya Sona kenan? Kin manta munyi alkawarin zamuyi Aire"
Na mishi banza saboda gaba daya nema yake ya fitar min da nutsuwar da na fara samu,
ganin nayi mishi shiru se ya Mike ya fita. A hankali na Kai hannuna na rike kirjina
dake min zafi,nidai ban cancanci wannan rayuwar ba!




" Me yasa kaki Mata magana?"


Safiyyu ya tambaye shi lokacin da suka dauki hanya, Junaidu yace


" Me zance Mata, nifa kaina mamakin yadda akai na yadda Zan aureta nake"


Safiyyu yayi dariya yace


" Nasan Mata basa gabanka Amma yarinyar nan karama ce Bata San komai ba , Dan Allah
ka rike ta da kyau"




Junaidu ya kalleshi Yana sakin dariya yace


"Kai da bakin ka kake hadani da Allah?"


Ya Kara kwashewa dariya yace


" Kai kanka kasan badan an bani saa da aurenta ba Banga dalilin da zaisa na aureta
ba, Kuma bayan Haka nafi son ta shigo da Shirin cewar uwarta zataci ba Dadi zata ji
ba"


Safiyyu yace


" Tayi kankanta yarinyar, baka ganin kamar shima Sa'idun Yana da wani dalili na
aura maka ita"


" Eh mana dama ban Gaya maka ba? Yarinyar nada dukiya wadda take hannun kannenshi,
yasan idan ya bar yarinyar tayi karatu watarana zata karbi dukiyar ta shiyasa ya
hanata karatu, sannan ya aura min ita, to shi Malam na Dan Issa ya fada Masa idan
ya aura min ita Babu jimawa dukiyar zata dawo hannun shi, ni Kuma idan na aureta
zata zame min kariya daga dukkan sharri, sannan gidan mu da nake son ya tarwatse to
zai tarwatse"


Safiyyu ya jinjina Kai yace
" Akwai samu kenan! Amma dukda Haka banso a saka yarinyar a ciki ba"




Kamar yadda nayi tunani, washegari Sega Mummy da yamma itada Rooks, Kawu Tijjani ma
ya iso. Ina daki na zubawa kayana Dana wanke idanu Amma ko daya na kasa ninkewa
naji sallamar Mummy, nayi saurin sakin hular hannuna na mike, fuskarta dauke da
murmushi ta rungume ni, Nima na rungume ta inajin sanyi cikin raina, ta sakeni ta
zauna Nima na zauna se Kuma na dauki hijabi na fita Ina kallon Rooks da taki
kallona, nayi murmushi na je wani shop kusa damu na siyo ruwa na dawo, Ina Zama
Rooks ta matso nace Mata


" Ni nayi fushi!".




Mummy tana Mana dariya har muka fara Hira, na dubi Mummy nace




" Yanzun na bayar a siyo awara abincin ya Kare"


Tayi min murmushi yace


" To daughter, kawun ki yace min kin fitar da miji ko?"


Na danyi Murmushin yake na tuna kashedin da yayi min yau da safe akan kowa yazo
nace ni nake son Junaidu ni na zabe shi, anan yake fada min shi din Dan kazaure ne.
Na gyada Kai Ina sunkuyar da kaina , tayi murmushi tace


" Amma jikina na bani you were forced. Tell me Afiyya gaskiyar magana"


Na dago na kalla Rooks da ta ke Wasa da zoben hannunta Wanda take nuna nervousness
dinta, nace


" Mummy da gaske!"


Se tayi murmushi again tace


" Amma shi ne baki fada Mana ba, se saura sati biyu yake fada Mana. Allah ya Sanya
alkhairi Amma naso ace ba aure Kika zaba ba karatu Kika zaba, dukda auren ma is in
line, But tunda Haka ne ki sani Ina tare da
Ke duk abinda kike so ki fadamin"


Na Share hawayen idanuna nace
" Mummy nagode!"


Aka kawo awara tana ta min nasiha da guda min yadda zamantakewar aure take, se
yamma Suka tafi Kawu yace na bisu saboda Shirin biki. Kwana biyu duk yadda nake son
aiki ta hananin se hutawa kawai da nake tace nayi Rama da yawa kullum girki take
koya min tana bani nutritious food Ina ci, ban Kara ji daga gurin angon ba, tunda
ba waya ce Dani ba Dan ta gurin Yaya Shehu Kawu ya karba tun kafin na hada ta.
Mummy ta Kira Nanny se gata ta taho ta fara guarani, nayi yar kiba nayi kyau. Da
daddare tana mulka min wani yellow abu me azabar kamshi a jikina Rooks na zaune
tana mitar se an shafa Mata tace


" Ku fada min gaskiya meye zancen aurennan?"


Nayi kirikiri nace


" Ai na fada Miki ni na fito dashi"


Tayi dariya kawai tace




" Yara kenan!"




Shirye shirye sosae Mummy keyi,saura sati daya Ina zaune a daki na hada kaina da
gwiwa nayi shiru Kuma ni ba kuka nake ba Rooks ta zauna gefena tace




" Afeey yanzun auren zakiyi? Wanda Baki taba sani ba shi Zaki zauna dashi, Afeey
Ina jin kamar I'm a bad person da nake kallo kina Shan wahala Amma na kasa fadawa
kowa"


Na riko hannunta nace


" Watarana zanji Dadi karki damu"




A wañnan Daren Ummiey ta iso da family dinta, Haka Uncle Babawo Wanda min ringa
munyi waya a wayar Mummy. Ummiey na yin wankan ta taho gidan Mummy ta same ni a
parlor ana turara ni, Mummy nata duba kayan kitchen din da tayi order. Ummiey ta
zauna Suka gaisa, Suka gaisa da Nanny


" Yanzun Maryam yarinyar nan tayi kankanta da aure shekara Sha biyar fa!"
Mummy ta sauke ajiyar zuciya tana kallona tace




" To ya zanyi? Ita ke son shi, da farko nayi tunanin Yaya Sa'idu ke fada kawai Amma
ta tabbatar min da bakinta Haka ne"


Ta girgiza Kai tace


"

13 / 31