Advertisements
Chapter 23 Reading Afiyya by Ayshatuuu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Afiyya by Ayshatuuu

Author :  Ayshatuuu Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 31

66K to 69K   out of 90.3K words

gari.




I'm sorry, Dan Allah kuyi hakuri my exams is starting on Monday Inshaaa Allah,
shiaysa kuke jina shiru, I've lots of documents da ko budewa banyi ba. Amma
inshallah zanyi typing 50th page tomorrow se Kuma na Gama exams. Thank you for
understanding!




Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 50




Na Jima tsaye gaban wardrobe din nawa Ina tunanin abinda Zan saka, dama ta barni da
atamfar jikina Amma nasan idan tasan da atamfa na fita se nasha fada. Haka nan na
dakko black trouser da pink top na saka na taje gashina in a bun sannan na saka
bakar hula. Socks na saka na dakko sabon sneakers Dina pink da ya kawo min jiya na
saka, na fesa mist sannan na dakko katuwar jumper na saka na fito bayan na dauki
wayata da credit card din da nake amfani dashi. Yana zaune shi da Nanny suna Hira,
Ina rufe kofa dukkan hankalin su ya dawo kaina, Nanny nata murmushi ganin fitowa
ta, yayin da shi Kuma ya zuba min idanun shi Yana kallo na lokaci zuwa lokaci Kuma
se ya Dan lumshe idon shi, a hankali na tako inda suke na dube shi nace
" Yaya muje?"


Ya mike Yana sighing na dubi Nanny nace


" Nanny se mun dawo na siyo Miki ice cream?"


Ta harareni tare da fadin


" Tsofe tsofe Dani me zanyi dashi, Allah ya kiyaye. Me Borno kada kuyi dare"


Ya juyo Dan har yaje bakin kofar fita Yana murmushi yace


" Inshaaa Allah Nanny"


Daga nan ya fice Nanny ta dubeni tare da fadin


" Wuce Mana se yankare Baki kike"


Na turo bakina Ina juyawa na fice ba tareda na sake magana ba, Yana zaune a
mazaunin driver Yana kallon wayar shi, cikin nutsuwa na bude side din shi na shiga,
ya dago Kan shi daga Kan wayar yace


" You look beautiful Damsel"


Nayi murmushi Ina jin Dadi a raina Amma bance komai ba, ya tada engine sannan yayi
reverse muka hau titi sannan ya fara magana cikin nutsuwa


" Wanne course kike a school din?"


Nace


" Nursing nakeyi"


" Why? Nursing is stressing"


Na kalleshi Naga alamar zolaya a fuskar shi hakan yasa nace


" Law ma ai is stressing"
Yayi dariya wadda tasa na shagala kallon shi, ya Dan daki steer wheel din kadan
yace


" Kin Rama kenan? But can you do that tedious work?"


Na danyi Jim nace


" Zan iya"


Yace


" Ok! All the best then. Kinsan cewar I got your back ko? Komai Nene kike so Zan
tsaya Miki, I just want you happy"


Ina murmushi da ya fitarda hakorana na dube shi, I felt some gush of feelings cikin
jinina, nace


" Na sani and thank you"


Ya girgiza Kai Yana kara maida Kan shi Kan titi yace


" Meye na godiya, a husband should all this to his wife"


Idanuna a warwaje nace


" But you're not my husband ai"


Yayi dariya tareda Kai hannun shi ya lakuce min hanci na yace


" See you I'm trying to be, ai wannan Karan zaa bani chance ko?"


Na gyada Kai na Ina murmushi Wanda ke saka min nutsuwa cikin Raina, ya gyada Kai
tareda shafa kanshi yace


" That's my Damsel"


Daga Haka se mukai shiru, motar tayi shiru Nima na Dan lumshe idanuna tamkar me
yin bacci Amma bashi nake ba Ina tunanin rayuwa ne da yadda take canjawa, Ina
daukar rayuwa tamkar littafi Dake kunshe da chapters Wanda kowacce chapter baka San
menene a ciki ba, se idan ka bude, farin ciki da bakin ciki Basu dawwamma Dole
akwai canji Haka ma akai Mana alkawari, ba lalle rayuwa taxo maka yadda kake so ba
ko Kuma yadda ka tsarata ba Amma Kuma lokuta da dama canjin idan yazo zai Faye maka
alkhairi saboda Allah shi yasan menene kake bukata kaima kanka lalube kake a cikin
duhu. Na saki ajiyar zuciya tare da bude idanuna jin yayi parking, se Naga min iso
kofar wani katon mall ne, ya dubeni yace


" Let's go in! Ke ace ki nuna min gari Amma Naga alamar ba inda Kika sani"


Nayi murmushi nace


" Itama Mom tasan fa ba inda na sani se school Amma tace Wai na rakaka"


Yayi dariya tace


" She wants us together shiyasa"


Na Dan tabe baki nace


" Idan bana so fa?"


Se Naga ya tsaya da unbuckling seat belt dinsa yace


" What? Me Kika ce?"


Na juyar da kaina dayan bangaren Ina kallon yadda mutane ke zirga zirga a ciki da
wajen mall din, ya saka hannun shi ya juyo da fuskata Dan na kalleshi, hakan yazo
min a bazata na ture hannun shi, shima se ya sauke Amma still fuskar shi a Babu
annuri but he looks Charming, exactly Ina kallon shi naji tamkar charm nayi saurin
cewa


" Nifa ba Haka nake nufi ba! Ni fa bana son kaga ko Zan soka Dan wani relationship
we have, no I want to love you for who you are"




Wannan Murmushin da yayi Yana kallona tamkar wani karamin yaro da ake Mika Masa
alawa, he was so happy as I can see, nayi saurin bude kofar motar na fita Ina gyara
moppler dake wuyana a zagaye, kaina a kasa Ina tuhumar kaina da sakin bakina har na
fada Masa abinda na boye tuntuni nake tunanin Kuma yaushe Zan bayyana shi, but
wannan Charming looks din nasa yasa na furta abinda banyi niyya ba. Nayi shiru har
ya karaso ya kalleni Yana Murmushin da Bai bar fuskar shi ba yace


" Muje Damsel!"


Na gyada Kai har lokacin kaina a kasa yake, yayi dariya da tasa na kalle shi ya
dage min girar shi, munyi yawo cikin mall din sosae na ware duk abinda na gani Ina
so se na dauka takama ta na taho da credit card Dina, shima idan yaga girly Abu zai
dauka nayi tunanin Nads yake Siyama seda muka je biya na Mika nawa credit card
shima ya Mika nashi, na dubi cashier Dake kallon mu nace


" Use mine please!"


Hannun shi yasa ya karba nawan sannan Kuma ya bada nashi aka Mana packaging muka
saka a mota, ya daukeni zuwa Bayan mall din Wanda yake kamar garden ga swings dasu
wheels a gurin, kasancewar weekends ne couples da yawa da Kuma Yara sunzo gurin. Na
hau Kan swing na kasa swinging seda yazo ta bayana ya tura ni sanann na fara Yi
with full force, ya dawo gabana Yana min video,inata dariya tun karfina, har cikin
zuciayta nake jin tsananin farin cikin da nake ciki. Se bayan laasar sannan muka
fara kokarin komawa gida, Amma Kuma Ina Shiga mota Sega Kiran Aisha kawata, course
mate Dita ce, na dauka muka gaisa tace min na zo school akwai tutorials da zaa fara
in 10 minutes, na kalleshi dukkan hankalin shi na kaina, na girgiza Kai saboda na
gaji ruwa kawai nake son naji a jikina dukda sanyin da ake ciki, na


" Ba lallaii nazo ba gaskiya, kiyi min jotting down seki turon ko ta telegram ne
please"


Daga Haka mukai sallama, ya dubeni yace


" Whatsup Damsel?"


Cikin ko in kula na mashi bayani ya girgiza Kai yace


" No you're going, muje na kaiki will wait for you har ki Gama kinji?"


Ba yadda zanyi na gyada kaina muka dauki hanya, Babu jimawa muka Isa, tare dashi
muka Shiga har venue din ya samu guri ya zauna, yayin da Aysha ke cemin


" Kince da ba Zaki zo ba Kuma?"


Na danyi murmushi nace


" I changed my mind ne"


Tace ai gwara da Kika zo, gurin shi naje nace


Bari mu fara, ya min murmushi tare da dunkule hannun shi na bani courage na koma na
zauna, duk inda na kalle shi se Naga ko dai Yana kallon wayar shi ko Kuma Yana
kallona a Haka muka Gama sannan muka fito, Yana gaba Ina biye dashi se few of my
friends da muka fito tare dasu. Aysha ta dubeni tace


" That guy a Bayan class kamar ba Dan class dinmu ba ko?"
Na gyada Kai nace


" Tare muke dashi"


Ta zaro idanun ta tace


" OMG! Amina he's so cu.."


Da sauri nayi cutting dinta Dan Kar ta Fadi abinda zanji haushin ta ko Kuma nan
gaba taji kunya nace


" He's my fiance, shi Zan aura idan mun Gama level 2. Muje ku gaisa"


I can see kunyata a idanun ta, Naja hannun ta har sauran ma, Yana tsaye Bai shiga
motar ba, nace


" Honey! My friends"


Ya dube su da fuskar shi wadda ke dauke da Murmushin kullum yace


" Is nice meeting you! How's studies?"


Duka suka amsa, ya dubeni inata murmushi Nima yace


" I'm taking my Damsel away hope you don't mind?"


Janet tayi dariya wadda kusan dukkan su dariyar suke tace ba karamin matching mukai
ba, we look beautiful together, idan bazai damu ba zata Mana hoto. Na Dan matsa
kusa dashi dukka hakoran mu a waje akai Mana, ta min waving wayar akan zata turon,
mukai sallama sannan na shiga shima ya zagaya ya shiga ciki ya tada motar, a
hankali yake tafiya tamkar a kafa muke tafiya yace


" Da gaske after level 2 zamui aure?"


Na dube shi da sauri nace


" Ya akai kaji?"


Ya nuna min kunnen shi Yana dariya, na dauke kaina yace


" It will be coming soon kenan, na kusa Nima nayi owning abinda tunda na fara ganin
shi ya hargitsa min lissafi, how will it be having you as my wife Damsel?"
" It will be lovely ko?"


Na fada Ina dariya ya girgiza Kai yace


" Abu ne da ni kaina bansan yazan kwatanta shi ba, Ina fata komai yazo cikin sauki
ko?"


Na gyada Kai. Munata Hira har muka Isa gida, ya kashe motar ya fitar min da kayan
sannan ya bani key din akan zaije yayi wanka ya dawo dinner, Ina tsaye har ya kule
kafin na shigo ciki da Kaya Niki Niki, dakin Mom na Kai Dan har lokacin Basu dawo
ba, kitchen najee na samu tana burabusko, na zauna bayan mun gaisa na hada coffee
na Sha sannan na barta Dan hutawa kafin dare ya karasa Yi.




_There goes my heart beating_
_Cuz you're the reason_
_I'm losing my sleeping_
_Please come back now_
_There goes my mind racing_
_And you're the reason_
_That I'm still breathing_




_I climbed every mountain_
_Swim every ocean,_
_Just to be with you_
_Fix what I've broken oh_
_Cuz I need you to see that you're the reason!_




Banbi ta Kan wayata ba seda nazo kwanciya, Ina Hawa WhatsApp Naga dukkan cousins
Dina sun updating story dinsu, na Nads na fara dubawa tun kafin na bude Naga
caption din " Love birds...let the feelings speak". Se ga hoton mu a garden ni
dashi, na tsura ma fuskokin mu Idanu da suke fitar da annuri, you don't have to ask
kinsan ba karamin so mukewa juna ba, na cigaba da dubawa har da aunties Dina ma sun
daddaura, na fara kokarin duba nashi se na tuna ai banida contact din shi ma gaba
daya. Na duba Rooks wadda tayi dogon sharhi akan picture din, yawanci tana nuna how
much I meant to her, da Kuma adduar Allah yasa wannan shi ne farin cikin da kowa
kemin adduar samu. Na kasa replying se kawai na koma chat Dina nan Naga messages,
na Yaya Hasher Dake da yawa na fara dubawa, he sent me the picture da Kuma wani
video lokacin munje wani guri da suke culture show, an bani Abu Ina kadawa Ina
dariya yayi min video, a raina nace how on Earth abinnan ya fita Haka? Nasan shi ya
daura kowa ya samu ya dauka ya daura, I'll be the hottest topic of gist kenan,
tunda ba kowa yasan aurena ya mutu bama. Na sauke ajiyar zuciya na fara karanta
messages dinsa


*Dama shi ne dalilin da yasa Kika ki kulani yau kenan? You opened Chats Dina Amma
Baki bani amsa ba, Wait tukunna meye tsakanin ki dashi? Do you want to rush again,
yaushe auren ki ya mutu ko shekara bakiyi ba fa.*


Na dafe kaina Ina jin kaina ya fara sarawa, Amma dukda Haka na cigaba da karanta na
kusa dashi


*Kinsan Ina son ki, kinsan da gaske nake son ki Amma ta Yaya Zaki ma soyayya ta
Haka ta hanyar nunawa duniya Baki ma lura ba...*


Ban karasa ba na aje wayar so confused...




AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of
Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 51




Na dafe kaina Ina tunanin a yaushe ya nuna cewar Yana Sona da har zaice na nunawa
duniya bani bukatar shi, na matsara da wayar gefe tare da furzar da iska daga
bakina, yeah I actually know Yaya Hasher ya kula dani lokacin da nake cikin
tsananin damuwa da matsala, lokacin da na ke bukatar Wanda zai kula Dani, Wanda Zan
saka kaina Kan kafadar shi nayi kuka akai shi din ya zame min hakan,sede ko kadan
ban kawo cewar Wai Yana Sona bane. Shiru nayi ba tareda nayi replying ba Dan ban ma
San me zance Masa ba, a cikin zuciyata babu wani namiji da ke da matsayi irin na
Yaya Shehu a raina, bazan taba manta abubuwan da yayi min ba, he was there for me
when no one was there, he lend a helping hand, yaso kubutar Dani a lokacin da Wanda
nake Kira iyayena Suka kasa min komai, Suka hakura suka made hannun su I remembered
Bai hakura ba har seda yaga Babu yadda zaiyi sannan ya hakura, he kept telling me
zai gudu Dani, ya Kuma nuna min na gani, bawai Ina returning favor din da yayi min
ba, a'a zuciyata tayi naam da shi ta Kuma karbe shi hannu bibbiyu saboda shi din ya
cancanci na soshi. Na numfasa na kashe data tareda kwantar da kaina Kan pillow a
hankali Ina jin jikina Yana min Dadi Dan kowacce gaba ciwo take min, wayar na janyo
jin alamar Kira Yana shigowa, na Dan tsirawa numbers din idanu kafin Kuma nayi
sliding tareda karawa a kunnena, kafin nayi magana yace


" Damsel"


Take na fahimci shi ne, na saki murmushi jin nutsuwa tana Shiga ta, I felt kamar
I'm safe a tare dashi,


" Bakai bacci ba?"


" Se kace ke wadda am sure yanzun kina Kan gado zakiyi bacci ko?"


Na saki murmushi nace
" How do you know? "


Yayi dariya wadda naji ta har kaina, yace


" Saboda Ina son ki! I can guess abinda kikeyi ta muryar ki. I can tell Koda
numfashin ki ya canja, I can sense that!"


Na gyada Kai kamar Yana gabana ina ayyana ok wannan shi ne ake Kira soul connection
kenan. Tabbas souls dinmu are connected, mun Dan taba Hira inata Hamma yace


" Awwww! Se yawning kike kamar Zaki hade ni. Oya sleep kinji?"


Ba lumshe idanuna nace


" To se yaushe zaka kwanta Kai Kuma?'


" Immediately after na Gama tura mail dinnan kinji?"


Na gyada Kai nace


" Zakazo breakfast gobe?"


" Noo Damsel zanje office da wuri am not sure idan Zan shigo"


Se naji banji dadi ba, na Dan pouting lips dina nace


" Ok then Good night"


Yayi murmushi yace


" I'm sorry, Zan so school da zarar na samu time. Sleep well Damsel"


Daga Haka ya kashe wayar na kwanta Babu jimawa bacci ya daukeni ba tareda na kara
tunawa da maganganun da Yaya Hasher yayi ba. Washegari da wurwuri na tashi Dan kuwa
inada lecture da karfe takwas na safiya. Kitchen na shiga na daura tea sannan na
fara hada noodles da prawns. Na Gama se zuwa lokacin Mom ta fito sanye da sleeping
wears se katon veil data daura a sama, ta dubeni Ina zaune Ina kurban tea da wayata
hannu Ina duba pharmacodynamics da pharmacokinetics saboda suna Dan rikita ni
suke, Zama tayi na gaishe ta tace


" Ya gajiya jiya Kun Sha yawo, I've seen pictures masu kyau har da videos"
Nayi kasa da kaina, Ina sakin murmushi nace


" Kai Mom"


Ta danyi dariya tace


" Feel free ni din nance fa, your friend. Kina son shi?"


Na Dan dago Ina kallon ta ta gyada min Kai hakan yasa nace


" Mhmm! Amma tsoro nakeji'


Ta Dan kalleni da alamar tambaya tace


" Tsoron me? Kada abinda ya faru ya maimaita Kan shi? My dear Inshaaa Allah Kim
Gama kunci a duniya, ai Junaidu da Shehu mutane ne mabanbanta, hallayr su, dabiun
su, wayewar su, sanin Allahn su. Da bakin ki Kika ce baya sallah, Wanda Bai Kare
hakkin Allah ba ta Yaya zai Kare hakkin mutum? Shikam dai kinsan Shehu kinsan waye
shi, tun ranar da na fara ganin ku tare naji how I wish shi din mijin ki ne to Amma
akwai yadda Allah ya tsara komai, follow your heart and pray!"


Na fahimci dukkan abinda take nufi Kuma Nima Ina jin hakan, na Dan langwabar da Kai
nace


" To Mom Yaya Hasher fa?"


Kafin ta bani amsa muka ji fitowar Dad, ya karaso inda muke zaune ya tsaya daidai
kanta Yana fadin


" Me ake cewa Babu ni?"


Mom ta dube shi ni Kuma na Mike Ina gaishe shi, ya amsa Yana murmushi yace


" Princess Ina zakije? Kije ku karasa maganar ki"


Na girgiza Kai nace


" I'll be late to school"


Daki na wuce bayan na leka kitchen na gaida Nanny sannan na wuce dakina na shirya
na fito da backpack sabe a bayana, Dad na cin breakfast, Mom na zaune ta tattara
dukkan hankalinta akan shi, da alamu magana suke me muhimmanci, na tsaya nace


" Zan tafi"


Mum ta dubeni tace


" Wanne irin Zaki tafi, breakfast din fa?"


Na yatsina fuska nace


" I've took tea, se na dawo"


Dad ya bani kudi sannan na juya na nufi kofar naji muryar Dad yace


"Princess kinsan me yasa Yayanki Bai shigo ba?"


Na juyo nace


" Mhm! Dama zai je office ne shiyasa"


Ya gyada Kai yace,


" You call him for lunch ok? Kinsan saboda ke yazo garinnan ko?"


Na gyada Kai Ina saka hannuna a baki kamar wata doluwa, Anty Nafisa tana murmushi
tana Kara juya Masa tea din gaban shi


" Treat him kindly he's your guest!"


Nace


" To Dad!"


" Good girl!"


Na juya Ina murmushi, a raina nace idan naki Yaya Shehu I'm sure yadda mutanen nan
ke son shi akwai damuwa. Ba jimawa na Isa makaranta, mukai test akan pharmacology
sannan na fito na kunna data ta ready to face Yaya Hasher. Aikuwa dai da sakon shi
na fara cin Karo, hakan yasa na bude kafin na karanta Kiran shi ya shigo ta
WhatsApp, na sauke ajiyar zuciya na dauka, muryar shi so down na gaishe shi ya amsa
yace
" Kin Gama guje gujen kenan?"


Na Dan Bata Rai nace


" Nifa ba gudu nake ba"


" To me kikeyi? Tun yaushe na Miki magana Babu reply"


" I was busy ne fa"


Na fada straight away, yayi shiru har seda nayi tunanin bazai Kara cewa komai ba
yace


" Been busy Bai hanaki fita da Wanda kike so ba ko?"


Na danyi tsaki siriri nace


" Yaya Hasher let's stop this please, Yaya Shehu came all the way daga Istanbul to
Lancaster, just for him to see me, kaga Dole Zan kashe komai nawa na bashi lokaci"


" Saboda ni ban zo ba kenan. Amma kinsan Ina son ki ko?"


Na girgiza Kai kamar Yana gabana nace


" Bansani ba

23 / 31