Advertisements
Chapter 15 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 50

42K to 45K   out of 147.7K words

shiryawa yana rarrashin Bintu da take ta matsar walla, ta ci burin taron sunan nan ayi da shi, sai ga shi tafiyar ta bazata ta rusa musu bodjet."

"Taron suna ne suka shirya shi irinna an birni kuma yan gayu, domin ba ma a gidan za'a yi taro ba. Event"

"center suka kama mai matuar kyau da tsada, acan suka shirya za'ayi taron sunan. Duk Winke-Winken da tayi sunyi ne tare da Hafiz, taron suna ne da suka shirya gudanar da shi kamar gagarumin taron bikin aure. Sai ga shi tana ji tana gani tafiyarshi ya rusa kaso arba'in cikin dari na tsarin da suka yi ma bikin"

sunan.

"Ranta a bace ta raka shi har gurin mota yana kara rarrashinta da tausasan kalamai, bata koma cikin gida"

ba sai da taga direba ya fice da motar sun nufi Ofis inda za su haWu da sauran abokan tafiyar tasa.

"Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya tuna da su Aunty Balira, goshinsa ya dafe kadan alamun bai ji"

"dadin mantuwar ba, ya dauki wayarsa ya kira ta suka yi sallama bayan ya jaddada mata in sha Allah a ranar zai dawo."

"Tun da Hafiz ya bar gidan, sai ya zama kamar an shafe su Aunty Balira da manawarsu a zuciyar Bintu. Ta"

"manta gaba daya da babinsu balle ma har ta tuna da suna cikin gidan, ko kuma tayi kokarin sauke wani hakki na su da yake kanta a matsayinsu na dangin mijinta."

Harkokinta kawai take yi cikin yan'uwa da kawayenta. Da kuma matasan yara mata 'ya'yan Alh Lurwanu

"da suka je gidan tun da wuri, ta kuma karSe su hannu bibiyu kamar yadda ta saba, domin su ta ria a"

"matsayin dangin mijinta na gaske, ba waWancan gayyar auyawan da ta raina ma ajawali ba."

Hatta abin karyawa sai da aka doshi arfe goma da rabi na safe sannan Aunty Balira ta shiga can cikin

gidan tayi ma Bintu maganar abin karinsu.

"""Kin san mutanenmu basu saba Waukar lokaci mai tsawo basu karya kumallo ba. Kuma wasu a cikinmu"

"sun zo da ananun yara, idan manya sun jure yunwa kin ga yara baza su jure ba."""

Ba kunya ba tsoro ta kalli Aunty Balira cikin ido ta ce

"""Na ji ! Ki je, za'a kawo yanzu. Kin san yau ne taron ni har ga Allah na ma ma manta da ku. Kuma dai ya"

"kamata ko Wan yaya ne ku dinga yima mutum uzuri tunda kun san ranar sha'ani kai Waukar zafi yake yi."""

"Ta faWa da dukkan gaskiyarta, fuskarta babu walwala ko kaWan."

"Aunty Balira ta kalle ta da Sacin rai, kamar za tayi magana sai kuma tai shiru ta girgiza kai, ta fice daga"

Wakin ranta a Sace. Kafin ta isa can inda sauran suke ne tayi oarin sakin fuskarta don kar su fahimci da wata asa.

"Ko da taje tayi maganar abin karin, sai da aka Wauki fiye da mintuna ashirin kafin aka kai musu abinci,"

"shinkafa ce dafa duka da taji busasshen kifi a cikin wata atuwar kula sai alalen leda a kula daban, sai"

kuma ruwan sha na gora katan-katan da aka shigar musu da shi.

"Tun daga wannan abinci da aka basu, Bintu bata ara waiwayarsu ba. Ita ma Aunty Balira bata ara shiga"

"cikin gidan tayi mata maganar abinci ko wani abu da suke buata ba. arfe biyu na rana kuma suna daga can Sangarensu suka dinga jin tashin motoci na ficewa daga gidan, ko da suka lea da sauri, sai suka ga mata ne ake ta fita da su a mota sun sha kwalliya na gani a faWa."

Akan idanunsu Bintu da tasha wata ayatacciyar kwalliya kamar sarauniyar kyau ta saSo jaririnta tana

"tafiyar asaita awayenta na take mata baya, ko kallon Sangaren da suke tsaitsaye baki buWe suna"

kallonta bata yi ba ta shige cikin mota. awayenta ma suka shiga mota aka fice da su daga gidan.

******

"""Bintu? Sai naji kamar jiya Hafiz yana faWa ma Abbansu an'uwansa za su zo suna daga can gida. Ya"

"banga ko mace Waya a cikinsu ba?"""

Hajiya Balaraba uwargidan Alh Lurwanu ta tambayi Bintu da mamaki a fuskarta. Ganin tun da aka fara

shagalin taron sunan ko ire-iren dangin Hafiz bata gani a gurin ba.

"Dariyar yae ta Wanyi, ta Wan sosa gefen Waurin Wankwalinta da mai kwalliya ta Sata fiye da minti talatin"

tana Waura mata. Sai kuma tayi saurin wayancewa ta ce

"""Wallahi Mama kin san abinki da mutanen karkara. Babu yadda banyi da su ba su shirya a taho da su"

"gurin taron nan suka ce baza su zo ba, a cewarsu sun fi so su zauna a gida. Da naji haka sai kawai na bar"

"musu komai da za su buata a wadace mu kuma muka taho."""

"""Habawa! Ko da na ji. To don Allah kafin su wuce dai a saka direba ya kawo su mu gaisa, akwai saon"

"da nake so in basu su tafi ma da Innaye."""

"""To shi kenan Mama. In sha Allah za a kawo su, gobe da wuri zan saka direba ya kawo su."""

Da haka suka rabu da Mama ta cigaba da warwasawa cikin awayenta.

angaren Hafiz acan Lagos duk irin hotuna da Vidion taron da Bintu take ta tura mishi kanshi ya Wau

"zafin da bai samu buWe ko guda Waya ba. Meeting suke ta shiga da manyan Oganninsu, daga wannan sai wannan. Duk yadda ya so su juya Abuja a ranar ma hakan bai samu ba, saboda basu gama komai da komai ba sai bayan magrib."

"Daman akwai ayataccen masaukin da aka kama musu na kwana Waya, su ne dai kawai suka yi tunanin"

za su gama komai a ranar su juya Abuja cikin iyalansu.

"Sai da daddare, bayan ya gama duk wasu al'adunsa na kwanciya ya bi lafiyar gado sannan ya samu"

nutsuwar buWe data ya hau online.

"Ko a waya da yaga taron ya ayatar kamar yadda suka so, shi kaWai yake ta sakin murmushi yana sake"

"buWe hotunan, yana kallon Yadda Bintu da jaririnsa suka yi wani fitinannen kyau kamar a sace su a gudu."

"Yana daga cikin dalilin da yasa a kullum soyayyar Bintu ke ara sabuntuwa a zuciyarsa, kyakkyawa ce ta"

"arshen arshe. Shi kuma a rayuwarsa haka Allah yayi shi da bala'in son mace mai kyau na Waukar hankali, kallon dirarriyar mace kuma kyakkyawa kamar Bintu a matsayin matarsa kaWai yakan saka shi jin"

alfahari.

"Mace ce ta nunawa tsara, duk girman taro da ayatuwarsa babu inda zai kasa shiga da Bintu a matsayin"

matarsa.

Sai da ya gama kallon hotuna da vidiyin tsaf! Ya kira ta suka Wauki fiye da awa Waya suna hirar yadda

"taron ya kasance, a gefe guda kuma suna ara ba ma fulawarsu ta soyayya ruwa. Dayar suka yi sallama"

bayan kiran Ogansu ya shigo wayarsa.

Bayan ya gama waya da Oga sun tattauna kan yadda meeting Win da suka yi ya kasance hotunan ya sake

"buWewa, yana kallo zuciyarsa na ara tunbatsa da farin ciki. Nan take ya ware waWanda suka yi kyau sosai da zai sa a wanke manyan hotunansu. Sannan ya tsara a zuciyarsa idan ya koma gida lallai dole ya sake shirya wani Wan warya-waryan taron tsakaninshi da iyalinshi suyi hotuna, domin ya sake ware"

waWanda za a bugo manyan kati su maala a falonsu na tarihi.

"arfe goma da rabi na dare, Aunty Balira da sauran an'uwansa suka faWo mishi a zuciya. Da saurin gaske"

"ya lalubo lambarta ya danna mata kira, a zuciyarsa yake jin lallai bai kyauta ba na yadda duk yinin ranar bai samu ya tsuke lokacinsa ya kira ta yaji yadda suka yini da yadda taron sunan ya kasance a Sangarensu ba. Sai kuma a lokacin ya sake tunawa da ai duk yawan hotuna da Vidion da Bintu ta tura"

mishi ko mutum Waya bai gani daga cikin an'uwansa ba.

Haka kawai irjinsa ya Wan buga daram! A daidai lokacin kuma kiran da yayi ma Aunty Balira ya tsinke

"bata Wauka ba, bai gaji ba, ya sake danna kiranta a karo na biyu, nan ma dai har ya tsinke bata Waga ba. A"

"taaice sai da ya kira ta sau huWu bata Wauka ba, kawai sai ya danna kiran lambar Bintu, ita ma dai har ya kira ta sau uku bata Wauka ba."

Ya kuma rasa dalilin da yasa haka kawai irjinsa ke cigaba da bugawa akai-akai.

"""Uhmmm! Allah yasa dai lafiya."""

Ya faWa a fili bayan ya haWiyi wani kakkauran miyau da ya taru a bakinsa.

"A can gidan Hafiz kuwa, a daidai wannan lokacin da yake kiran Aunty Balira tana can cikin gidan ita da"

an'uwanta biyu suna yi ma Bintu wankin babban bargo akan wulaancin da tayi musu a wannan rana.

Kun san abinku da mai hauri bai iya fushi ba. Sannan Bintun ta daWe tana shiga musu hanci da

"udundune, su Aunty Ladidi da Aunty Rakiya sun daWe da burin son su fyato ta Aunty Balira da Innaye suke dannarsu."

"[1/6, 10:15 PM] Fareeda Abdallah: Yau kam da suka samu dama basu tsaya sanya ba, Aunty Rakiya da"

duk ta fi su zafin zuciya saboda Sacin ran yadda Bintu take mayar musu da magana cikin tsantsar raini da

gadara sau uku tana yunurin janyota don rufeta da duka Aunty Balira da an'uwan Bintu da suka rage a

gidan suna shiga tsakani.

Cikin fushi da Sacin rai sosai Aunty Ladidi ta cigaba da magana cikin faWa tana nuna Bintu da yatsarta

manuniya

"""Ke har kin isa ki ce za ki raba mu da Wan'uwanmu? Na rantse da Allah baki isa ba. Kinyi kaWan, kuma"

"kinyi tsururu. Duk take-takenki mun daWe da gano abinda kike nufi, kar muke kallonki. Hafiz ne tunda kina son shi dole ki rungumi iyaye da an'uwansa da suka kasance auyawa. Gidannan kuma ko kina so ko ba kya so baza mu taSa daina zuwa ba, idan kin isa kuma kin kai isasshiya, ki saka Hafiz ya kore mu..."""

"""Ai kuwa ko yanzu na nuna muku na isa har nayi yawa."""

Bintu ta katse ta da sauri kuma cikin raini da gatsali. Da hannu biyu ta rie ugunta tana karkaWawa tana

fari da idanu sannan ta cigaba da cewa.

"""Gidannan dai gidan mijina ne, ni da nake matar gidan ni nake da girman ikon sakawa da hanawa ko"

"kuna so ko bakwa so. Na riga na zame muku Wuwawu, dole ku zauna da ni, tunda Wan'uwanku ya ce ya ji ya gani ni yake so matsayin abokiyar rayuwa dole duk yadda na dama haka za ku sha..."""

A zafafe Aunty Rakiya ta katse ta da cewa

"""Wallahi arya kike yi Bintu. Babu dole a zama da ke, bari in tunatar da ke abu Waya idan haukar"

"wawalwarki yasa kin manta... Hafizu namiji yake, ana canza mata, amma ba'a taSa canja an'uwa. Sannan ana canja mata amma ba'a taSa canja uwa da uba. In banda ke jaka ce mare hankali wulaancinki har ya iya tsallake kan dangin miji ya haura kan iyayenshi? Duk mugunta da ulla-ullar da"

"kikai ta yi ma Innaye sadda tazo gidannan jinya babu wanda bamu sani ba..."""

"Da saurin gaske Aunty Balira tayi saurin katse Rakiya, a ganinta yanzu ba muhallin yin wancan maganar"

bane. Kuma baya ga haka tun a wancan lokacin sun yi ma Baffa alawarin baza su taSa canja ma Bintu kan abinda ya faru da Innaye ba.

"""Dakata Rakiya dakata! Idan kika sake magana anan gurin ba tare da na gama faWin abinda zan faWa ba"

"sai na tsinka miki mari."""

"Saboda tsananin biyayya da girmama na gaba da aka hore su da shi, Rakiyar bata ara cewa komai ba,"

"sai baya da ta matsa tana sauke zafafan numfarfashi, tana huci kamar kububuwa."

Ita ma Ladidi da ba'a mata umarnin yin shiru ba kusa da Rakiya ta matsa ta tsaya tana d'an karkaWa

kafafunta. Ita ma nata fuskar babu walwala ko kad'an.

"""Bintu na dawo gare ki."""

Aunty Balira ta fada bayan ta mayar da hankalinta kan Bintu da take tsaye har lokacin tana wani karkad'a

kafaWu babu alamun nadama ko rusunawa ko kaWan tattare da ita.

"""FaWi duk abinda za ki faWa dai-dai nake da ku dukkanku. Kunne ke ji, baki ne zai faWa kuma baki ne zai"

"bada amsa."""

Ta faWi hakan cikin gatsali tana wani harare-hararen gefe.

"Kasancewar hasken wuta ne tar ta ko wane Sangare a cikin falon kamar rana, shi yasa duk abinda take yi"

suna kallonta rayukansu na ara Saci.

Nannauyar ajiyar zuciya Aunty Balira ta sauke ta cigaba da cewa

"""Ki kalle ni da kyau Bintu. Shekaruna a duniya arba'in da biyu. Ina da shekara goma sha uku Baffa yayi"

"min aure. Da ace Allah ya bani haihuwa tun sa'adda nayi aure da yanzu na haifi kamar ki, ko wacce ta girme miki. Sannan baya ga darajar shekaru da ya kamata ace na ci a gurinki, duk mu ukun nan yayyen mijinki ne. A lalace ko Ladidi da take arama a cikinmu shekara biyar ke tsakaninta da Hafizu."

"WaWancan gayyar auyawan matan da kike cewa mun kwaso su mun cika miki gida, daga Gwaggwannin"

"Hafizu sai Innoninsa, sai kuma Aminan Innaye da sa'annin haihuwar Hafizu da annensa da suke uba Waya."

Yanzu duk waWannan dalilan saboda Allah ke a gurinki basu kai matsayin da za ki girmama mu ki karrama

"mu don su ba...?"""

"""Don Allah tsaya Aunty Balira?"""

Bintu ta katse ta cikin fushi.

"""Wai da kuke ta wannan fuffukar tun da kuka zo gidannan menene nayi muku na wulaanci? in dai ba"

"rashin godiyar Allah da son maala min laifi ba? Gurin taron suna ne tun kafin ku zo an riga an ayyade iya yawan mutanen da ake so su halarci gurin, kawai saboda ni ce ar daWi dangin miji sai in kwashe ku"

"yuuuu zuwa gurin? bayan kuma ba'a tsara gudanar da taron da ku ba?"""

Ta katse Aunty Balira da tambayoyin cikin hayayyaa tana yi tana Waga hannuwa sama kamar za ta mare

ta.

"A bazata, idanun Aunty Balira suka kawo ruwa, da sauri tayi oarin haWiyewa. aya bayan Waya ta kalli"

"an'uwan Bintu su huWu da suke tsaye a gurin suna bayar da hauri lokaci bayan lokaci, sai ta tsayar da"

"idanunta akan wacce take ganin alamun ta Wan fi sauran shekaru, da sanyin murya ta ce"

"""Baiwar Allah don Allah ki mana alalanci. Ni duk Sacin raina ba akan in zuwa da mu gurin taron suna"

"bane. Ita kanta Bintun ta sani, tabarmar kunya ce kawai take neman naWewa da hauka yasa take waWannan surutan. Yanzu saboda Allah ya kyautu ace tun abincin karin safe da aka bamu a gidannan ba'a sake waiwayarmu da waran abinci ba har yanzu da arfe goman dare ta wuce? Manyan mata da kananun yara mu ashirin da bakwai muka zo gidannan, duk da direbobinmu uku mu talatin. Saboda Allah idan Bintu bata ba mu abinci a gidannan ba ina take so mu sa kanmu? Ko don ta ga Wan'uwanmu ba ya"

"nan shi ne take wulaanta mu?"""

Ta arasa tambayar wasu sabbin hawaye suna sake cicciko idanunta.

"""Bintu?"""

Babbar yayar Bintu wacce Aunty Balira ta gama yi ma orafi mai suna Sadiya ta kira sunan Bintu da

yanayin mamaki a fuskarta. Domin ita sai yanzu da Balira tayi bayani a nutse sannan ta fahimci inda aka dosa da inda matsalar take. Kafin Bintu ta amsa ta sake cewa

"""Da gaske ne abinda wannan baiwar Allahn ta faWa?"""

"Nan ma dai Bintu ta kasa amsawa, sai zumSura baki da tayi gaba tana ara anance idanu."

"""Daman su Win shaian mijinki ne amma kika ce mana gayyar soWin karabitin an'uwan Hafiz ne daga"

"auye? Kuma ca nake a gabana kika faWa ma Hajiya Balaraba kin sallame su da duk abinda za su buata?"""

"Nan ma dai shiru tayi, sai sunkuyar da kanta asa da tayi tana mui-mui da baki alamun gunguni take yi a"

zuci.

Da matsanancin faWa Aunty Sadiya ta fara zazzaga mata masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

"""Baki kyauta ba Bintu, gaskiya baki kyauta ba. Kin Sata wayon ki, sannan kin bani mamaki. Ban taba"

"tsammanin za'a sami irin wannan halin daga gare ki ba. Wannan mummunan banzan halin na wulaanta Wan'Adam don kawai sun kasance an auye ban san inda kika kwaso shi ba. Kuma na rantse da Allah idan baki gyara ba sai na haWa ki da Daddy, kin dai san halinshi sarai, ba ya Waukar irin wannan iskancin"

"da wulaancin, ko da kike ganin kin yi aure kin haihu ke kin san baki fi arfin hukuncin Daddy ba."""

"Ta mayar da idanunta kan Aunty Balira, sannan tayi oarin sassauta murya da yanayin da ke nuna"

nadama arara ta cigaba da cewa

"""Baiwar Allah don girman Allah kuyi hauri. Ba'a kyauta muku ba tabbas! Amma don Allah kuyi hauri,"

"a matsayina na Yayar Bintu na ari bakinta na ci mata albasa, kuyi hauri don Allah ba don mummunan halin da ta nuna muku ba. Ke Bintu maza basu hauri kafin in saSa miki!"""

Ta arasa da yi ma Bintu umarnin cikin tsawa.

Ta cika tayi dam! Amma sanin halin Aunty Sadiyar na rashin Waukar raini yasa ta cewa

"""Allah ya baku hauri. Bazan sake ba."""

Bakinta a zumSure kamar zai taSa bango.

Aunty Sadiya ta cigaba da cewa

"""Aunty yanzu dai ku koma can gurinku, yanzunnan za mu shiga kicin mu sama muku abinda za ku ci a"

"daren nan in sha Allahu. Kuyi hauri don girman Allah, kuma ina fatan baza ku faWa Hafiz abinda aka yi muku ba. Don Allah ku yafe mata, ba don halinta ba."""

"Ko da ace da kissa Aunty Sadiya ta ba Bintu laifi a gabansu, abinda tayin ya taka muhimmiyar rawa gurin"

rage girman Sacin ransu. Hatta su Aunty Rakiya da suke ta cika suna batsewa abinda Aunty Sadiyar tayi

ya tsaya musu arai. Ga dai maganganun da suke burin sake gargasa ma Bintu da arara ya nuna ta basu

"hauri don babu yadda za tayi ne, amma kwarjinin Aunty Sadiya yasa dole suka haWiye komai a ransu."

Godiya kawai Aunty Balira tayi ma Aunty Sadiya ba tare da ta amsa roonta na su yafe ma Bintu sannan

kar su faWa ma Hafiz abinda ya faru ba. Ficewa tayi daga falon annenta suka rufa mata baya.

Suna hanyar komawa Sangaren da aka sauke su babu abinda Aunty Balira take yi sai sharar hawaye.

"Daman tun farko abinda ta guda kenan, sanin halin Bintu na wulakanci da daukarsu da take yi a banzan- banza yasa sam bata so zuwa sunan ba balle har wasu su ce za su biyo su."

"Daman ta sani, in dai Bintu ne dole sai ta aikata mummunan abinda zai haska ma sauran dangi yadda ta"

Wauke su gaba Waya a marasa daraja. Yanzu zuwan na su me ya haifar kenan? Duk da sauran an'uwan

basu yi magana ba ta sani dole sun dasa ma zukatansu ayar tambaya.

Abincin karin da aka kai musu da safe ragowar ne aka ba yara zuwa arfe Waya da rabi na rana. Zuwa

"arfe biyu da rabi, uku manyan gaba Waya idanunsu ya fara raina fata. Da kunnenta

15 / 50