Advertisements
Chapter 24 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 50

69K to 72K   out of 147.7K words

ita da kanta tayi ma kanta karatun ta nutsu,"

"addu'a mai tsawo tayi kan Allah ya tabbatar mata da duk abinda yafi zama mafificin alkhairi a rayuwarta. Damuwa, ™unci, tunani da ba™in cikin Hafiz ta sama musu matsuguni can ™arshen sa™on zuciyarta tayi musu mummunan Soyo. Ta sa a ranta lallai za ta fuskanci gaba, ga gaban kuma da alamun za ta zo mata"

da alkhairai masu yawa da farin ciki.

"Nan falo suka bararraje suna hira da dariya, Zulaikha da ba ta da ba™unta sai labarin ™auye take basu"

"suna dariya. Ita ma Hajja da yake ™uruciyar ™auye ce kafin aurenta da marigayi Modibo ya tsallako da su cikin birni har suka hayayyafa sai labarin ™auye take ba su, irinna zamaninsu da can."

"Ko da lokacin Wora tuwon da za ta yima Hajja yayi, ita da Karima suka shige kicin Win, sai dariyar maganar"

Hajja suke yi da take ta jaddada ma Zulaikha kar ta kuskura ta bar ma Karima tu™a tuwonta.

"""Bata iya komai ba, duk sadda tayi tuwo haka za ki ji shi duk gudaji. Sai ki rasa shin ido rufe take tu™a"

"tuwon ko kuwa ya take yi, kamar dai ba mace ba."""

"Mamaki ne ya kama Karima ganin yadda Zulaikha ke aikin tuwon cike da ™warewa da gwanancewa,"

"kamar wacce tayi zaman birni, kayan miya da daddawa da kayan ™amshi sai da ta soya su sama-sama"

"sannan ta tsayar da sanwan ruwan miyan. Ta kasa ha™uri, har sai da ta tambayeta shekarunta nawa?"

Duk da Zulan tana da girman jiki fuskarta kawai za'a kalla a ga zallar ™uruciya.

"""Shekaruna goma sha takwas Aunty Karima."""

Ta amsa tana dariya.

"""Ikon Allah! Amma gaskiya kin burge ni, yanzu kina nufin duk su dambu, fate, burabusko, Wanwake, da"

"sauran girke-girken gargajiya masu wahalar nan duk kin iya?"""

"""Eh! Kin ga duk da Yaya Hafiz yana ™o™arin kai mana kayan abincin birni Innaye da Baffa sun fi sabawa"

"da kalolin abincin gargajiya. Shi yasa na fi ™warewa a dafe-dafen irin su."""

Ta sake amsawa har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba.

"""To gaskiya dole za mu koyar da juna, amfanin zaman tare cuWe ni ne in cuWe ka. Kar ki wani ji kunya ko"

"nauyi na kin ji? Duk abinda kike son koya daga tsarin rayuwar birni ki faWa min, ni kuma zan koyar da ke daidai gwargwado. Duk da dai lokacina na zaman gida ragagge ne, domin ni ma'aikaciyar jinya ce a asibiti. Amma ya zama dole in mayar da hankali in koyi girki a gurinki. Kema kuma in sha Allah zan koyar da ke"

"ire-iren girkin birni da na iya, da sauran duk abubuwan da kike bu™ata, in sha Allah"""

"""Allahu yasha Aunty Karima, ai kam na gode. Na ji daWi ™warai."""

"Cikin ™an™anin lokaci sabo mai girma ya shiga tsakaninsu, kamar dama can sun daWe da sanin juna. Ko da"

"aka gama tuwon, duk yadda Karima ta tsani tuwo musamman na dawa wannan kam sai da ta ci mai Wan dama. Saboda yadda miyan take ta ™amshi, ga kuma kyawu da tayi sosai a idanunta. Ta sha mamaki"

"™warai yadda ta ji tuwon ya tu™u sumul babu gudaji, kamar ba a gabanta aka tu™a ba."

Albarka kam Zulaikha ta sha shi a bakin Hajja da Mummy babu iyaka. Tun tana amsawa da baki har sai da

ta koma sakin murmushi kawai.

"A gurin Karima ta samu aron cajar da ta jona wayarta, jikinta na rawa, wayar tana yin 10% ta cire ta"

lalubo lambar Innaye ta danna mata kira.

"""Auta? Auta ke ce? Auta kina ji na? Ina fatan dai kina nan lafiya babu abinda ya same ki? Duk da Hafizu"

ya rantse haWe da tabbatar min lafiyarki ™alau rashin jin ki ta wayar tarho ya saka ni cikin wasu-wasi. Ina

"fatan babu abinda Fatima tayi miki ko kuma tayi yun™urin aikata miki?"""

Tambayoyin da Innaye ta dinga jera mata kenan da bayyanannen tashin hankali a muryarta.

"Idanunta ciccike da hawaye ta nemi guri ta zauna a gefen gadon Wakin da aka sauke ta, sannan ta amsa"

"Innaye da lafiyarta ™alau. Kamar za ta ba Innaye labarin abinda ya faru, sai kuma ta tuna al™awarin da ta Waukar ma Mummy cewa baza ta sanar ma su Baffa Yaya Hafiz ya Wauke ta daga gidanshi ba."

Kuma ko ba haka ba ma a yadda ta fara jin daWin zaman gidan Mummy baza ta so a raba ta da shi cikin

"Wan lokaci haka ba. Ta sani ko da ta koma ™auye tabbas tsugune ne bata ™are ba, to da wannan dalilin"

gara kawai ta bi tsarin Hafiz har zuwa sadda za ta ga iya gudun ruwansa.

"Hira sosai suka sha da Innaye, duk yadda Innayen take ta bugun ruwan cikinta don ta ji ko da wata"

damuwa daga Sangaren Hafiz ko Bintu sam Zulaikha ta ™i faWa mata komai.

"""Kin san halina fa Innaye. Idan mutum ba shiga harkata yayi ba nima bana shiga tasa. Kuma batun"

"abinci Yaya shi da kanshi ya jaddada ma Baba Rabi lallai kar ta barni da yunwa, to har yanzu dai gaskiya ban ga wata matsala da za ta takurani ba. Kin san idan da matsala ma da kaina zan kira in faWa miki."""

Ire-iren kalaman da tayi amfani da su kenan ta kwantar ma da Innaye hankali.

"Har sai da kuWin cikin wayar ya ™are, Innaye ta kira ita ma nata kuWin suka ™are, sannan suka ha™ura da"

"magana, ta mayar da wayar a caji tana jin yadda zuciyarta ya ™ara cika da matsanancin farin ciki."

"[1/31, 5:39 PM] Fareeda Abdallah: Washe gari, da yake Karima aikin dare take da shi. Haka kawai ta"

"™ir™iri fita ita da Zulaikha, ba don komai ba sai don kawai ta zagaya da ita taga cikin garin Abuja."

"Imam, yaro Wan shekara shida da tun jiya ya dawo daga makaranta daf da magriba ya tarar da Zulaikha a"

"gidan ya ma™ale mata. Duk da ba wata shahararriyar hira ke gudana a tsakaninsu ba, saboda shi turanci"

"ya fi kama bakinsa fiye da hausa, ita kuwa Zulaikha ba turanci. Kasancewarta wacce bata iya Soye-Soye"

"ba, idan ya takura mata da dogon turanci ba wani kunya a tare da ita ko a gaban su Mummy ne ba ta jin"

kunyar ce mishi

"""Hey Boy! No English."""

"Da yake su Mummy wayayyu ne sai suyi kamar basu ji me ta ce ba, shi kuma da yake yana da son ba™i"

"haka zai kwaSo hausar a jagwalgwale, ita kuma ta daddage ta bashi amsa yadda ta fahimta ba tare da nuna gundurarwa ba, domin Allah ya yi ta da son yara."

"A haka dai duk inda Zulaikha ta saka ™afa nan yake mayar da tasa, duk inda ta zauna a jikinta zai raSu ya"

"zauna. Aikin gida da aka bashi daga makaranta ma takardun ya kwaso gaba Waya ya zube a gabanta, yana yi tana kallo duk da ba ta fahimtar abinda yake rubutawa. Ba ita ta samu hutu ba, sai da yayi barci aka"

kai shi Wakinsa.

"Da sassafen ranar ya ma ™i yarda Karima tayi mishi shirin makaranta, sai tarewa sukai su biyun a Wakinshi,"

"Zulaikha tana shirya shi Karima tana harhaWa mishi abubuwan da yake tafiya da su makaranta. ˜arfe takwas saura minti ashirin motar makarantarsu tazo har ™ofar gida ta Wauke shi, kamar zaiyi kuka haka"

"yake ta jaddada ma Zulaikha lallai ta jira shi ya dawo, kar ta tafi, ya yi al™awarin zai kawo mata tsaraba."

"Da dariya a fuskarta take jaddada mishi baza ta tafi ba, za ta jira shi ya dawo. Kuma za tayi ta zama a"

gidansu har sai ya gaji da ganinta.

Ya shige cikin mota yana Waga mata hannu tana Waga masa har sai da motar ya Sace ma ganinta sannan

ta shiga gida.

"˜arfe goma sha Waya da rabi na safe suka gama shiryawa ita da Karima, ta kwashe su a mota suka fice"

kasuwa yin siyayyan abubuwan gida da basu da shi.

"Gurin shirin Zulaikha ne dai haka aka sha dirama da ita gwanin ban dariya, da™yar ta iya ajiye babban"

hijabinta ta karSi Wan madaidaicin gyalen da Karima take mi™a mata ta saka. Shi ma kafin ta saka sai da Hajja ta ishe ta da gorin ko ita da take tsohuwa baza ta zumbula wannan ™aton hijabin ba idan za ta fita.

"""Kin ga Zulai ki kwantar da hankalinki, nan fa binni ne ba ™auye ba. Idan kika ji inda ake rayuwa babu"

ruwan wani da wani to binni kenan. A ™auye ne suke da masifaffen sa'ido da abu kaWan ko ba na saSon Allah bane sun dinga yamaWiWi da ke kenan. Bayan wannan zumbuleliyar riga da kika sa saboda Allah menene amfanin sake zumbula hijabi kuma? Ai wannan mayafin da takwara ta baki shi ne daidai da

"kwalliyarki Zulai. Ko ba kya so Allah yayi miki gyaWar dogo ki samo mana wani sabon miji ne Wan binni?"""

"Ta tambayeta da dukkan gaskiyarta, saboda yadda Hafiz ya faWa ma Mummy saura sati uku auren"

Zulaikha mijin ya ce ya fasa haka ta faWa ma Hajja.

"Bata iya cewa komai ba, sai Wan dariya kawai tayi, ta karSi mayafin ta yafa tana ta jero istigfari a"

zuciyarta. Domin ba ta jin za ta iya kware ma Wan'uwanta baya ta hanyar tona asirin auren da yake tsakaninta da shi. A idanun su Mummy da ta lura sun yarda da shi Wari bisa Wari.

Ko da ganin yadda take ta jan gyalen tana ™ara tale shi don ya ™ara sauka mata za'a san bata saba

sakawa ba. Ita kuwa Karima me za tayi mata in ba dariya ba

"""Kin san Allah? Za ma ki ware ne, sai yanzu na ™ara tabbatar da ina da babban aiki a gaba na. Har na ji"

"na fara addu'ar Allah yasa ko wata biyu ne kacal kiyi a gidanmu, in sha Allah zan mayar da ke ´ar gayu fiye da yadda ba'a zato. Shi fa tsoron Allah a zuciya yake, in dai ba tsiraici mace za ta bayyana ba, babu wani laifi ki saka yalwataccen suturarki sannan ki yafa Wan siririn gyale. Don Allah ki saki jikinki kin ji"

"™anwata?"""

"""Toh Aunty."""

"Ta faWa cikin sanyin murya, sai dai har suka isa kasuwar ta kasa sakin jikinta yadda ya kamata."

"Abu Waya da yayi ma Zulaikha daWi shi ne ganin kasuwar ma a birnance ne, ba irin kasuwarsu bane na"

"™auye da za aga mutane cunkus ana yamutsi tsakanin maza da mata. A ta™aice ma, duk siyayyar da suka yi a cikin manyan kantuna ne, nan taga yadda aka san daraja da kimar kayan miya. A babban kanti anyi packaging Win tumaturi irin manyan nan a leda anyi sealing Win shi, su tattasai ma da tarugu da albasa ma"

"duk sun samu mu™ami na musamman, ba kamar yadda take ganinsu a wula™ance a ™auyensu ba."

"Basu bar cikin kasuwa ba sai ™arfe Waya da rabi na rana. Kuma maimakon su nufi gida, juya akalar motar"

Karima tayi suka nufi gidan Aminiyarta. Sunanta Hibbah uwar gayu. Bayan sun gaisa da mahaifiyar

"Hibbah wacce ´a´anta ke kira da Mama, kai tsaye Wakin Hibbah suka shige, kan gadonta suka bararraje"

suna hira irinta aminan da akwai sha™uwa mai girma a tsakaninsu.

"Ita kuwa Zulaikha banWaki ta tambaya aka nuna mata, ta ajiye mayafin jikinta ta shige da sauri saboda"

fitsarin da ya matse ta. Hibbah ta bi ta da kallo ™asa-™asa. Sai da ta shige ta rufe ™ofa sannan Hibba ta

"mayar da idanunta kan Karima, da salon tsegumi ta ce"

"""Ina kika samo kyakkyawar yarinya haka mai ™ira irinta Hadiza gabon? Ke kin ga wasu manyan kaya da"

"take Wauke da su a bayanta kuwa?"""

"A tare duk su biyun suka kwashe da dariya. Kafin Karima tayi magana aka yi sallama a ™ofar Wakin, bayan"

sun amsa mai aikin gidan ta shigo da babban faranti a hannunta Wauke da kulolin abinci da abin sha. Gefe Waya ta ajiye tayi musu sallama ta fice daga Wakin.

"˜ofar banWakin da Zulaikha ke ciki Karima ta kalla, sannan ta mayar da hankalinta kan Hibbah ta ce"

"""Kin shiga uku da sa'ido ˜awata. ³ar danginmu ce tazo daga ™auye, kuma za ta Wan kwana biyu a"

"gidanmu. Kin san me yasa na zo da ita gurinki?"""

"Girgiza kai Hibba tayi, a zuciyarta take mamakin yadda kyakkyawar yarinya haka mai sanyin kyau za'a ce"

daga ™auye take. Irin wannan da a birni take kuma ta san kanta ai ba ™aramin gwarama za ta haWa na

"samari ba. Shi yasa fa wasu mazan ke cewa tsantsar kyawun mace na gurin ´ar ™auye, matan birni mafiyawancinsu gayu ne kawai da ™yale-™yale."

"˜ara rage murya Karima tayi, sannan ta cigaba da cewa"

"""So nake ki wayar min da ita a cikin kwanaki ™alilan, ki koya mata salo-salo na gayu don Allah. Kin ga"

"waWannan mazaunan da kika hango a bayanta? Baki ga komai ba Wlh, sai yau da na shiga Wakinta da sassafe, na ganta sanye da doguwar rigar barci da ya Wan kama ta. Uhmmm! Ke dai abin ba'a cewa komai, ™iran jiki ne da ita mai kyau Wlh! Ga wani shape da take Wauke da shi abun sha'awa, ta bakinki"

"dai kamar Hadiza gabon. Duk wannan ™ibar na ta sam ba ta da tumbi..."""

Fitowar Zulaikha daga banWaki yasa suka bar maganarta da suke yi suka shiga wata hirar.

Tana Wan goge ruwan da ke kwance a fuskarta da gefen Wankwali tace ma Karima

"""Aunty ni fa nayi alwala ne, a taimaka min da Hijabi inyi sallah."""

"""Ba kya jin yunwa Zulaikha? Ai da kin bar sallar mu fara cin abinci, idan mun gama sai muyi sallah a"

"tsanake."""

"Sai da Karima tayi maganar, sannan Zulaikha ta lura da kulolin abinci da aka ajiye a tsakar Wakin. Ga"

"kuma Jug Win tangaran nan sha™e da zoSo, jikin jug Win sai raSa yake fitarwa alamun sanyi ™arara."

"""Ku fara ci Aunty, tunda na yi alwalar bari in fara yin sallar, idan na idar sai in ci abincin in huta gaba"

"Waya."""

"""To shi kenan! Yi sallar, ni kam dai sai na ci abinci zan sauke farali."""

"Hijabi da sallayar da Hibba take mi™a mata ta karSa, ta tambayi gabas aka nuna mata, ta shimfiWa ta"

tayar da sallah.

"Ko da ta idar da sallah tayi ´an addu'o'inta, bata Sata lokaci ba ta cire hijabin ta ninke, sannan ta ™arasa"

kusa da abincin ta Wiba a Waya daga cikin farantai uku da aka ajiye musu. Duk yadda Hibba take ta mata

"nacin ta tashi ta zauna a gefen gado kamar yadda suke zaune ™iyawa tayi, nan ™asa ta zauna ta fara cin abincin, lokaci bayan lokaci take amsa musu hirar da ™arfi da yaji suke ta tsoma ta a ciki."

"""Fuskarki za tayi kyau da sassau™ar kwalliya Zulaikha, gama cin abincin in gwada kwalliya a fuskarki mu"

"gani ko za ta zauna miki yadda nake hasashe. Kin san ni fa sana'ata kenan, kwalliya, Waurin Wankwali, lalle, da duk wata harka ta gyaran jiki ba wanda ba na taSawa. Mamana da kika ganta a waje ´ar maiduguri ce, kin san kuwa mu ne sirrin ™amshi da gyaran jiki. Da wannan dalilin yasa wasu daga cikin"

"™awayena ke ce min Uwar gayu."""

Ta ™arasa maganar tana kaWa idanu tana wani yarfe hannaye don tsabar yanga da firirita.

"Zulaikha dai sai kallonta take yi, kamar tayi dariyar irin yadda take ta fari da idanu tana wani watsa"

"hannaye kamar za ta tada aljanu, amma sai ta matse dariyar bata yi ba. Ko da ta gama cin abincin, bata"

™i tayin kwalliya da Hibbah tayi mata ba.

Haka take ta bin komai da kallon mamaki ganin wani ™aton akwati da Hibba ta Wauko wai duk kayan

"kwalliya ne a ciki. Kamar da wasa, ta zauna a kujerar gaban madubi Hibba ta fara yi mata kwalliya kala daban-daban a fuskarta."

"Kuma da yake Hibbar ta san aikinta, kwalliya kala huWu da aka gwada ma Zulaikha ba ™aramin hawa da"

kyakkyawar fuskarta suka yi ba. Su kaWai a Waki sai tuntsura dariya suke yi suna shewa kamar ´an matan

"Amarya. Duk kalar kwalliyar da aka yi sai an yi mata Waurin Wankwalin da zai hau da ita, Karima kuwa sai aukin Waukarta hotuna take yi tana Wora ta a status Win whatsapp."

"""My luvly ˜anwa Zuly. Allura cikin ruwa... mai tsananin rabo ka Wauka."""

Ire-iren kirarin da tayi ta bin hotunan da shi kenan.

"""Gaskiya ni dai wannan kwalliya da Waurin Wankwali sun burgeni matu™a Wallahi. Ashe lokacin auren"

Wiyan mai garinmu da aka Wauko mai mata kwalliya tun daga Kasuwan magani zuwa ™auyenmu ta

"cancaWa mata mukai ta yabo muna zuzutawa ashe Sata mata fuska kawai ta yi?"""

"Zulaikha tayi maganar fuskarta cike da farin ciki, tana sake ™ure kanta da kallo a gaban madubi ganin"

"yadda ta canja gaba Waya. Kamar ba Zulai ´ar Innaye da Baffah ba, ta yi wani irin kyau na musamman da"

bata ma san zai iya kwatanta shi ba.

"Kamar wacce ta tuna da wani abu, da sauri ta matsa kusa da Hibba ta ri™e hannayenta, fuskarta a"

marairaice ta ce

"""Aunty Hibbah, don girman Allah ki koya min kwalliya da Waurin Wankwalin. Ba kuma wai don in dinga"

"sana'ar da kike yi in kashe miki kasuwa ba, don fuskata kaWai, na rantse da Allah fuskata kawai zan dinga yiwa kwalliya ina ma matan ™auyenmu burga. Daman kullum idan suka tashi gwaSa min magana suna cewa don na ga ina da Yaya a Habuja shi yasa nake musu Wagawa, haka ma Mudan ya ce min kafin ya ce"

"bazai aure ni ba, kuma fa Wallahi ba haka bane."""

Ta ™arasa maganar idanunta ciccike da ´an ™ananun ™wallah.

"""Kar ki damu Zuly, ai tunda Karima ta kawo ki gurina babu abinda bazan iya miki ba."""

Ta mayar da idanunta kan Karima ta ce

"""Besty kiyi adding Win ta a group Win da nake koyar da kwalliya da Waurin Wankwali na whatsapp..."""

Da murna sosai a fuskar Karima ta katse Hibbah tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"""Lallai ke kam Zulaikha kina da sa'a. Besty Allah ya saka da alkhairi, kin gama mana komai. Na san ko iya"

"haka aka tsaya cikin ™an™anin lokaci Zuly za ta faso gari, ta zama babbar yarinya."""

A tare duk su ukun suka sake kwashewa da dariya.

"A haka suka ™ara cinye fiye da awoyi uku a gidan, har sai da Mummy ta kira Karima a waya tana faWan"

"daWewar da suka yi, ga shi a lokacin Hibbah ta kwaSa lallen zamani ta fara yi ma Zulaikha a bayan"

hannunta da saman ™afafunta. Tunda dai tafin ™afa da tafin hannu akwai lallen aure da Aunty Rakiya tayi

mata a gida.

Ha™uri Karima tayi ta ba Mummy tana ba ta uzurin lalle ake yi ma Zulaikha har dai aka zirara mata lallen

"ba mai yawa sosai ba, haka suka fice daga gidan da Wanyen lalle ko bushewa baiyi ba. Mama sai dariya"

"take musu, bayan ta ba su ´an ™ananun ledoji Wauke da turarukan jiki na shafawa irin nasu na ´an mata."

"[2/1, 5:15 PM] Fareeda Abdallah: ******"

"A marairaice ta kalli

24 / 50