Advertisements
Chapter 26 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   26 / 50

75K to 78K   out of 147.7K words

bar gidan, Mummy za ta kira Zulaikha tayi mata umarnin shiga da kayayyakin kicin."

"""Tsarabar gida ne Yayanku ya kawo mana, ki rarraba komai ki adana inda baza su samu matsala ba kin"

"ji ´an matana?"""

"""To Mummy."""

"Da™yar take iya buWe baki ta gaisar da Hafiz sannan ta kwashi ledojin zuwa kicin, da yake an ce ba'a raba"

hanta da jini. Da ganin irin kayayyakin da ke cikin ledojin Zulaikha take gane takanas-ta kano wannan

"sa™on nata ne daga hannun Innaye. DaWi ne yake cika mata zuciya, sai tayi murmushi kawai ta cigaba da rarraba kayan zuwa inda suka fi dacewa."

Abubuwan ciye-ciye kuma tun kafin ta fice daga kicin Win za ta Wiba ta wanke na wankewa ta kai ma

Mummy da Hajja falo.

"A kwanakinta na farko-farko a gidan, idan Hafiz yaje har ya gama zamansa ya tafi bayan gaisuwa ba ta"

™ara yarda wata magana ta shiga tsakaninsu. Sai wata rana da Hajja tayi mata tatas ta umarci taje ta raka

"Wan'uwanta gurin mota, haka ta fice ta bi bayanshi tana zumSura baki."

"""Hmmm! Komai akai da jaki ai sai ya ci kara. Sai yanzu na ™ara yarda da aka ce ba™auye sai ya shekara"

"arba'in a birni kafin Wabi'a da al'adun mutanen ™auye ya bar jikinshi..."""

"""Jaka mai faWa irinna ´an daba tana can yanzu za'a tadda ta a gida, da tsinin bakinta irinna jaSa."

"˜auyanci kuwa naga duk za ni ce ta tadda muje mu, wanda yake gorin shi ma har yanzu Wabi'a da al'adun"

"™auyawan bai sake shi ba tunda ko shekara ashirin baiyi a cikin birnin ba."""

"Tana gama faWin haka ta wuce fuuuu, ta koma cikin gida ta barshi tsaye a gurin, baki da hanci buWe don"

tsabar mamakin irin ™warin gwuiwar da Zulai ta samu har ta iya mayar mishi da mummunan ba™ar

magana irin wannan.

"Bai ma san ta shige ba, sai da ya dawo hayyacinsa yaga ba ta a gurin. A fusace ya Waga ™afa zai bi ta ya ci"

"ubanta sai kuma ya tuna a gidan Mummy take fa, idan yayi wani mummunan action lallai zai zunguro sama da kara, ™arshenta Zulaikha ta tona mishi asiri, mutuncinsa na shekara da shekaru ya zube ™asa war-was a idanun Mummy."

"Mota ya shige a fusace, ya Wauki wayarsa ya lalubo tsohon lambar Aunty Balira da a yanzu ya zama"

"mallakin Zulaikha ya danna mata kira, yana fara ringing kuwa cikin sa'a ta Waga da siririyar sallama a bakinta."

"""Ke don ubanki ni kike faWa ma ba™ar magana? Ni sa'an ki ne...?"""

"""Wrong number"""

"Ta katse shi da faWin haka tun kafin ya aje numfashin maganarsa, kafin ya sake cewa komai ™it! ta katse"

wayar. Ko da ya sake kira fiye da sau bakwai na'ura na faWa masa wayar a kashe take.

"A fusace ya buWe motar ya fita ya ™walawa direbansa kira, wanda yake zaune acan gurin Maigadin gidan"

"suna hirar rayuwa. A wannan ranar, haka ya isa gida ranshi na ™una da raWaWi, duk yadda Bintu tayi"

"™o™arin shawo kanshi ta kasa, kuma ya ™i faWa mata takamaimai abinda ya Sata masa rai."

"A ™arshe sai kawai yayi mata ™aryar kanshi ke ciwo, da rawar jiki ta Wauko mishi paracetamol yasha,"

"sannan ta lallaSashi ya kwanta, ta daidaita mishi yanayin sanyin A.C ta bashi guri da cewar yayi barci."

"""Idan ka huta, in sha Allah ciwon kan zai tafi. Allah ya baka lafiya Sweetheart."""

"""Ameen."""

"Ya amsa da™yar yana cije laSSa, kamar da gaske ciwon kan yake yi. Nan kuwa tsabar Sacin ran kalaman"

Zulaikha ne da suke ta amsa kuwwa a ™wa™walwarshi kamar bitar karatu. Wannan shi ake cewa baki

"idan ya san abinda zai faWa, bai san amsar da za'a mayar mishi ba."

"Tun daga wannan ranar, bai ™ara gangancin ta™alarta da mummunar magana ba. Sai dai ya ™ara kamewa"

"daga gare ta, idan ya je gidan, ta gaishe shi a gaban mutane yana iyakar ™o™arinsa wajen amsawa da"

"sakin fuska. Amma idan zai tafi ta bi bayanshi da niyyar yi mishi rakiya ko kallonta ba ya yi, balle har ta saka ran zai amsa Allah ya tsare hanyar da take mishi."

***** *****

"Da gaske ne da ake cewa babu wani al'amari da ya gagari bawa ya koya, sai dai idan tun asali shi wannan"

"bawan bai saka a ranshi yana so ya koya ba. Zulaikha da ta saka ma ranta kuma ta ™wallafa zuciyarta tana so lallai ta koyi turanci, sai ga shi a cikin watanni biyu an shiga na uku sosai bakinta ya faWa da turanci."

Bayan ™o™arin koyarwa kuma a sau™a™e da makarantar online Win da Karima tayi mata register suke da

"shi. Mummy, Karima, Imam sun taimaka mata ™warai gurin faWawar bakinta a iya magana da turanci, domin gaba Waya suka daina yi mata magana da Hausa, sai turanci."

"Tun tana fahimta kaWan-kaWan, suna fassara mata manyan kalmomin da suke amfani da su a jimlolin"

maganganunsu. Wata kalmar kuma idan ta gani ko a kafar sadarwa a google take searching ta ga

ma'anarta da Hausa. Daga nan fa ta kafa ma kalmar ™ahon zu™a kenan har sai ta haddace a ™wa™walwarta.

Yanzu dai a gidan idan aka ji tana hira da hausa tana ™yal™yala dariya da Hajja ne kaWai. Sauran mazauna

"gidan idan tana so suyi dogon hira dole sai da turanci, tun tana kwaSo jagwalgwalo suna dariya, a haka har bakinta ya goge da iya turancin."

"Da gaske ne fa da aka ce da babu makoyi gwani ma da ya ji kunya. Zulaikha dai ta dage da koya, kuma"

Alhamdulillahi ta Wauko hanyar zama gwana.

"Ta inda rayuwarta yake burge mazauna gidan shi ne, ba ma turanci kaWai ba, abubuwa da yawa waWanda"

"bata iya ba a baya, yanzu ka'in da na'in ta dage da koyonsu. Rayuwarta ya Wauko hanyar canjawa gaba Waya, ta fara zama wata ´ar gayu kuma ™asaitacciyar mace ta musamman. Komai na ta ya canja, hatta yanayin yadda take magana yanzu a ™asaice kuma cike da yanga da nutsuwa take yi. Saboda kuskure"

"™alilan za tayi Karima ko Mummy su gyara mata, ita kuma da hanzari take karSar gyaran tayi godiya."

Yawan zuwan Hibbah gidan akai-akai. Da kuma yadda take Waukarta a mafiyawancin lokuta tana raka ta

"guraren sana'arta, ko babu Karima a gidan Mummy bata cika hana fitar ba, saboda ta yarda da nutsuwar Hibba da kamun kanta. Wannan yawan fitar, tana haWuwa da wayayyun ´anmata iri-daban-daban, shi"

ma ya ™ara taimakawa ™warai da gaske gurin gogewarta.

Abun daWin shi ne har yanzu bata yarda ta zubar da kyawawan halayenta na koyi da addininmu ba. Duk

"wani abu da za tayi addini shi ne gaba, kafin aikata komai."

***** ******

"""Daddy pls kar ka yanke wayar, ga Aunty Zulai ta shigo ku gaisa."""

Imam bai jira amincewar uban ba ya ruga a guje ya kamo hannun Zulaikha da shigowarta cikin falon

"kenan da waya ma™ale a kunnenta, tana magana tana sakin wani lallausan murmushi."

"Ita da Mashkura ce a wayar, wacce da farko kamar zumuncin nasu zai yanke bayan barin Zulaikha gidan,"

saboda tsoron abinda zai je ya zo kasancewarta ™anwar Bintu.

"Shi yasa Zulaikha ta so yanke duk wata ala™a ta kusa ko ta nesa da ita. Amma saboda naci irinna Mashku,"

"duk yadda Zulaikha take ™in Waga wayarta ita kuma ba ta taSa gajiya da kira ko nuna Sacin ranta ba har dai ta gaji ta sakar mata. Suna gaisawa da zumunci ta waya sosai da sosai, tunda har yanzu da take cikin"

wata na uku a Abuja ta ™i yarda Mashkura ta san gidan da take zaune.

"""Oyoyo Aunty Zulai."""

Imam ya faWa cikin karaWin murna sannan ya rungumeta kamar sun daWe basu haWu ba.

Ri™e shi tayi ita ma tana dariya fuskarta na nuna jin daWin ganinshi ™arara. Da harshen turanci take

tambayarsa yaushe ya dawo gidan? Ina tsarabar makaranta da ya kawo mata?

"""Tsarabarki na nan ta musamman Aunty Zulai. Ga Daddyna can ya kira Vidio call a wayar Granny, zo"

"muje ku gaisa. Pls yau ma kar ki ce a'a! Pls... pls... pls Aunty Zulai... ba don shi ba don ni kaWai."""

"Ya ™arasa mata magiyar a marairaice, lokaci guda kuma yana Wan jan hannunta zuwa inda wayar take"

ajiye akan kujera.

"Kamaluddeen, babban Wan Mummy Saudah kuma baban Imam, wanda ziyarar aiki na tsawon watanni"

"shida ya kai shi ™asar Gambia. Watanninshi biyu acan ™asar Zulaikha ta zo gidan, har izuwa yanzu da yake wata na biyar acan ™asar ko sau Waya bai taSa gaisawa da Zulaikha a waya ba."

Sai dai yana ganin hotunanta jefi-jefi a status Win ™anwarsa Karima. Sannan labarin Aunty Zulai a bakin

"Imam Wan shi sai dai idan bai kira a waya an haWa shi da yaron ba. Tun yana kore hirarta daga bakin Wan har ya ha™ura, domin matu™ar yana so hirar shi da yaron yayi tsawo to kashi biyu cikin uku na hirar"

labarin Aunty Zulai da irin yadda take kula da yaron ne.

"Idan ya zauna shi kaWai har mamaki yake yi, na yadda a cikin ™an™anin lokaci sha™uwa mai girma ya shiga"

tsakanin Imam da Aunty Zulai amma bai shiga tsakanin yaron da Safina da ta kasance ™anwa a gurin

marigayiya Aisha mahaifiyar Imam ba.

"Yau dai haka kawai, shi da kanshi ya ji a ransa lallai ya kamata ya ga Aunty Zulan nan ya gaisa da ita."

"Sannan yayi mata godiyar irin kulawar da take ba yaronsa, ko a Sangaren Haddar karatun Al™ur'ani mai girma na yaron da a baya yake tafiyar wahainiya, amma a yanzu ba ™aramin nisa yayi ba, abin mamaki"

har ya kusa haWa izufi goma cif a kansa.

Ko da uban ya tambayeshi ya akai haddarshi take sauri yanzu? Kai tsaye yaron ya faWa mishi Aunty Zulai

"ce take ™ara mishi, kuma tayi ta maimaita mishi cikin nutsuwa da lalama har sai ya haddace."

Duk diramar da yake gudana tsakaninta da Imam na yadda yake ™o™arin janyo ta zuwa gurin wayar ita

"kuma tana tirjewa, tana ba shi wasu ™ananun uzurirrika marasa muhimmanci yana jin su. Amma ba ya"

"hangen fuskarta sosai sai gefen kafaWunta. Shi kaWai ta cikin wayar, babu abinda yake yi sai murmushi."

"""Haba Aunty Zulan Imamu. Kiyi ha™uri mana don Allah, yau dai Waya ki gaisa da Baban Imamu shi ma"

"yaga wacece Auntyn Imam."""

Mummy da take zaune acan kan dining ta saka baki don kawo ™arshen ta™addamar da ke tsakanin Imam

da Zulaikha.

"""To Mummy."""

"Zulaikha ta amsa a kunyace, don bata san Mummy na zaune a falon ba. A kunyacen dai ta bi bayan Imam"

da har lokacin ya ™i sakin hannunta har suka ™arasa kusa da wayar.

"Da™yar ta iya Waga kai ta saci kallon fuskarsa, wani kwarjini da haiba sosai da yayi mata a idanunta yasa"

babu shiri ta zube a ™asa ta fara gaishe shi a daburce.

"""Ina yini...? Au! Ina kwana...? Lah! Yi ha™uri... Good evening."""

Ta ™arasa maganar a tsorace da tunanin kila ma ba ya jin hausa.

"Da wani irin tattausan murya mai tafe da zallar kwarjini da mazantaka ya fara magana, har lokacin"

murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba.

"""Aunty Zulan Imam! Barka da yamma. Ai ni ya kamata in gaishe ki, saboda ™o™arin da kike yi wajen jure"

"surutun Imam. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi."""

"""Amin. Nima na gode."""

Ta amsa a kunyace sannan ta tashi da Wan gudu-gudu har tana harWewa ta wuce Wakinta. Mummy da

Kamal suka bi ta da kallo fuskokinsu cike da murmushi. Shi kuwa Imam me zaiyi in ba ™yal™yala dariya ba.

"Tun daga wannan ranar, bata sake yarda gaisuwa ta waya ko ta Vid call ya shiga tsakaninta da Baban"

"Imam ba. Don a yadda take ji a zuciyarta kamar ma tsoronshi take ji, shi yasa sawunta a likkafa da ta ga an fara gaisawa da shi za ta zame ta gudu zuwa Wakinta."

***** ******

"[2/3, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: ""Sweetheart?"""

Ya kira ta a tausashe.

"Siririyar hamma ta sake, cikin saiSi da mutuwar jiki ta sake gyara kwanciyar kanta a ™irjinshi."

"""Na'am...My Dear."""

Ta amsa aWan shagwaSe.

"Lallausan gashin kanta ya cigaba da shafawa, yana mata waiwayi sannu a hankali. Kamar bazai yi magana"

"ba, can kuma sai ya ce"

"""Jibi idan Allah ya kaimu, ki shirya da wuri. Tare za mu tafi Fa™o..."""

"Da saurin gaske ta Wago kanta tana kallonshi cikin ido, sai kuma tayi la™was! Ganin shi ma kallonta yake"

"yi, yana karantar yanayinta. Saukar da ™wayoyin idanunta ™asa tayi a hankali, sai kuma ta mayar da kanta ™irjinsa ta kwantar, duk a ™o™arinta na danne maWaukakin tashin hankalin da yake taso mata."

"""Aadil just 4 month yake da a duniya. Ba ka tsoron muyi doguwar tafiya da shi ya kwashi iskar hanya?"

"Ka san mura a jikin jarirai fa, yanzunnan sai ta zame musu Nemonia..."""

"""Babu abinda zai faru in sha Allah! Za mu tafi tare da shi, kuma mu dawo lafiya. Ki tuna fa yaushe"

"rabonki da Fa™o? Tun bayan haihuwar Aunty Balira, to ga Babyn nata nan har yayi 2years. Duk irin jinyar"

da Innaye baki samu kin je gaisheta ba saboda laulayin ciki. An haifi Aadil har yau Innaye bata taSa

"Waukar gudan jinina ba balle ta saka mishi albarka. Jibi tare za mu tafi tabbas, ku shirya da wuri."""

"""To shi kenan! Allah ya kaimu."""

"Ta amsa da sanyin jiki, duk zuciyarta a ™untace. Amma ba ta da yadda za tayi ta nuna mishi, saboda ko"

kaWan ba ta ™aunar abinda zai sake janyo wani saSani ko mis™ala zarratin a tsakaninsu.

"Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin mabanbantan tunanin da yake yi a zuciyarsa. A haka barci ya"

kwashe su.

"Washe gari da yamma, bayan sun dawo guraren aikinsu, suna zaune a falo suna hira. Tana zaune a"

"gefensa, Aadil na ri™e a hannunsa yana mishi wasa, yaron kuma sai dariya yake yi, da alamun ya fara"

gane fuskar Babansa.

A tausashe ya kalleta ya ce

"""Gobe idan muka je gida, duk irin magana ko tambayar da za'a yi miki game da Zulai ki amsa musu da"

"to kawai, ki kuma tabbatar musu muna zaune lafiya ™alau. Kin gane?"""

"""Eh!"""

"Ta amsa, ba don ta gane Win ba."

"""Good. Duk da tun bayan faruwar al'amarin har yau bamu zauna ni da ke na warware miki yadda"

"al'amuran suka faru ba, domin a ganina sam hakan ba shi da wani amfani, tunda dai matsalar na riga na maganceta. Amma na san a wancan lokacin Raudha ta yi miki bayani kamar yadda nayi mata, ko ba haka"

"ba?"""

"""Haka ne."""

"Ta amsa, a zuciyarta take sake tunano cikakken bayanin da Raudha tayi mata wancan lokacin, wanda har"

"yayi sanadiyyar zubda makaman kishinta, hankalinta ya kwanta luf kamar tsumma a randa."

"""Madallah! To ko bayan da na magance matsalar har yanzu su Innaye basu san takamaimai halin da"

"ake ciki ba. Akwai lokacin da na tsara zan musu cikakken bayanin komai, yadda ransu bazai Saci da ni ko ke ba, amma ba yanzu ba. Don haka gobe idan mun je ki kama bakinki, kar ki kuskura ki bada wata kafar da zai sa su gane akwai matsala tsakaninmu da Zulai. Kin gane ko?"""

"""Eh"""

Ta amsa a sanyaye.

Shiru yayi yana cigaba da yi ma Wanshi wasa. Can bayan wasu da™i™u ta matsa kusa da shi ta rungume shi

ta gefen kafaWarsa.

"""Na gode My dear... Na gode. Ina ro™on Allah yabar ™auna da tabbatacciyar soyayya a tsakaninmu. Da"

"ace a wancan lokacin baka Wauki matakin da ya dace ba, na tabbata da yanzu na daWe a kushewata..."""

"""Shshshshhhhhhh! Kar ki sake faWan irin wannan maganar."""

"Ya katse ta da sauri, jin tana zancen mutuwa."

"""Na daina Daddyn Aadil. Allah ya huci zuciyarka."""

"Bai amsa ba, sai lallausan murmushi da ya sakar mata, kafin ya mayar da hankali kan Aadil yana cigaba"

da yi mishi wasa.

*****

Washe gari da sassafe suka kama hanyar tafiya Fa™o kamar yadda suka tsara. Saboda a ranar yake so

"suje su dawo. Bayan motarshi sha™e yake dam da tsaraba, saboda a wannan karon ba tsarabarsa bace"

"kaWai, har da zannuwan da Bintu ta lodo da sunan za tayi tsaraba wa su Innaye."

Wani irin shirin jibga-jibgan kayan sanyi da Bintu tayi ma Aadil shi kaWai ya isa abin dariya. Amma a

"zahirin gaskiya kayan ta saka mishi ba don iskar hanya bane, ta saka mishi ne duk a ™o™arinta na kiyaye"

yaron daga kwasar cututtuka saboda Waukar da take tunanin zai sha a hannun mutanen gidansu Hafiz.

"Da yake gudu sukai ba na wasa ba, ™arfe goma sha Waya da rabi ta yi musu ne a ™ofar gidansu Hafiz na"

"™auyen Fa™o. Wani sau™i da Hafiz yake ganin sun samu shi ne taron sunan Balki, ´ar Wakin Umma laraba da ake yi anan gidan Baffan."

"Haihuwar fari ce, kuma ta zo mata da gardama. Shi yasa tun daga can asibiti kai tsaye gidan iyayenta aka"

"dawo da ita domin ta samu ingantaccen kulawa. Yau ta kama suna, don haka sun tarar da gidan Baffan ne dam™am da ´an'uwa da abokan arziki, wanda hakan ko kusa baiyi ma Bintu daWi ba, domin ta san jagwalgwalon da Aadil zai sha a hannun mata ´an ™auye sai ya ninka wanda tayi tsammanin zai sha da"

farko.

"Motar na fakawa, kafin ma tayi yun™urin saka yaron a Wan abin Waukarsa mai kama da kwandon Waukar"

jarirai ta kulle shi har Hafiz ya Wauki yaron daga cinyarta.

Ya buWe mota ya fice waje sannan ya saSa Wan a kafaWarsa

"""Fito muje. Kin ga na manta yau ake sunan Balkin Umma Laraba. Kin ga shi kenan ma mun samu sau™i,"

"ba sai munyi ta jelar zuwa gidajen ´an'uwa a gaisa ba. Na san duk za mu tarar da su a nan gida."""

"""Haka ne."""

Ta amsa da™yar! Tana jin yadda bakinta ke wani irin Waci kamar ta tauna flagyl.

"Tun kafin su shiga cikin gidan, har labarin isowarsu ya riga isa cikin gidan. Ko kafin Bintu ta fito daga cikin"

mota har wasu daga cikin ´an'uwansu sun lulluSe jikin motar suna yi musu barka da zuwa.

"""Yauwa... Sannunku. Labaran, Inusa, ina su Kadiri? Ku zo a buWe muku boot ku kwashi kaya ku shiga da"

"su cikin gida."""

"Ya faWa da fara'a sosai a fuskarsa, idanunsa na kan ™annensa maza da yayi ma umarnin kwasar kaya."

"""Hafizu? Ina Zulai? Baku taho da ita ba?"""

"Indo ta tambaye shi bayan ta ga Bintu ce kaWai ta fito daga cikin motar, kuma ta rufe ™ofar ba tare da ta"

ga fitowar Zulai ba.

"Kafin ya amsa ma Indo ™anwarsa Halima ta mi™a hannu da nufin karSan Aadil, nan take kuwa ya sakar"

mata shi ba tare da wani damuwa ba.

"""Oyoyo Babanmu! Tubarkallah ma sha Allah! Kai ne haka kayi kukkuSeSe barakallah? Hajiya Bintu"

"sannunku da zuwa."""

Bata jira amsawar Bintu ta take ta ™o™arin haWiye wani gululun takaici da ya tsaya mata a wuya ba ta

wuce da yaron cikin gida.

"""Zulai tana gida Indo, ban zo da ita ba. Ai ita da zuwa gida sai ta yi wata shidda cif a Wakin aurenta. Idan"

"ba na manta ba haka Baffa ya saka doka

26 / 50