Advertisements
Chapter 41 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   41 / 50

120K to 123K   out of 147.7K words

rawar murya.

"""Alfarmarki nake nema don Allah Raudha."""

Ta sake faWa muryarta na ™arasa karyewa sosai. Don tsabar fitina da bala'in da ta saka ma ranta duk

yadda nonuwanta ke ciwo suna tsikarinta saboda yaye ko jin su ba ta yi. Ba komai ke ™ara karya ma Bintu

"zuciya ba sai idan ta tuno ita tana nan a birni irin Abuja Aadil Wanta yana wula™antaccen ™auye irin na su Innaye, ™auyen da ko ita da girmanta bata taSa gigin yin kwana Waya a ciki ba."

Ta sani aminci ne mai ™arfi tsakaninta da Raudha. Babu wani alfarma da za ta nema gurin Raudha ta ™i yi

mata kamar yadda ita ma a Sangarenta za ta iya yin komai don kare martabar Raudha.

"""Kin sani kin wuce komai a gurina Bintu. FaWi duk abinda kike so kawai inyi miki ki ga aiki da cikawa."""

Cewar Raudha daga can Sangaren da muryar da ke nuna da dukkan gaskiyarta take magana.

"Nannauyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke, ta lalubi gefen gadonta ta zauna sannan ta cigaba da magana."

"""Ina wannan mutumin naki na filin jirgin ™asa wanda ke samar mana da ticket Win zuwa Kaduna a"

"sau™a™e?"""

"""Lurwanu? Yana nan. Me kike so yayi miki?"""

"""Ki tura masa sa™o a darennan ya tanadar mana da ticket biyu na jirgin gobe da safe. Bazan iya ba"

"Raudha, Wallahi tallahi bazan taSa iya barin Aadil ya kwana biyu a ™auyennan ba. Goben nan zan je in Wauko shi, duk abinda Hafiz zaiyi ya daWe baiyi ba..."""

"""To me ma ya isa ya yi? Ai shi kansa ya san ba shi da gaskiya... Duk inda za aje a dawo kin fi shi gaskiya"

"Bintu, kamar yadda kika fi shi girman ha™™i akan Aadil har a gurin Allah... Don haka kar ma ki wani Waga hankalinki. In banda ma tun safennan bamu yi tunanin zai iya barin Aadil acan ba ai da tun ayau za muje"

"mu Wauko shi. Ki kwantar da hankali ™awata..."""

"WaWannan maganganun na Raudha, su suka zaftare kaso arba'in cikin Wari na damuwar da ke dan™are a"

zuciyar Bintu. Da wannan dalilin yasa bayan sun gama waya da Raudha har ta iya samun ™warin gwuiwar

"zuwa kicin ta haWa tea mai kauri ta sha. Ta Salli paracetamol guda biyu ta haWiya, ta sake yin wanka sannan ta bi lafiyar gado."

Ko tunanin Hafiz bata yi ba balle tayi gigin zuwa Wakinshi su kwanta. Abinda bai taSa faruwa ba tsakanin

"su biyun raba makwanci tunda suka yi aure, in dai ba tafiya Hafiz yayi ba."

*********

"Washe gari tunda sassafe Hafiz ya ji ™arar tada motar Bintu, yana kwance a kan gadonshi. Tunda ya tashi"

"yayi sallar asubahi a makare saboda rashin barci da bai samu yi da wuri ba, ya kasa fita ya duba ta tashi ko bata tashi ba?"

Azkhar ma sama-sama ya yi ya sake bin lafiyar gado da nufin yin ramuwar barci. Ya kwanta kenan ya ji

"tashin motar Bintu, mamaki ne ya kama shi har ya tambayi kanshi."

'Ina Bintu take niyyar zuwa ba tare da ta faWa mishi ba?'

Sanin ko daga can asibitinsu ne aka yi mata kiran gaggawa tana faWa mishi kafin ta fita yasa shi yin

"mamakin fitar tata a yanzu. A hankali ya ya ye bargon da yake lulluSe da shi ya sauka daga kan gadon, ko kafin ya fita daga Wakin ma har mai gadi ya buWe mata get ta fice daga gidan."

"Don haka bai Sata lokacin duba Wakinta ba ya san ita ce ta fita, tunda direbansu ba ya nan. Idan ba ita ba"

wa zai Wauki motarta ya fita da ita da sassafen nan.

"Ko da ya koma cikin Wakinsa, har ya kwanta, sai kuma yayi tunanin bai kamata ya ri™e Bintu har ya"

banzatar da al'amarinta haka ba. Tunda su kansu iyayenshi sun ro™e shi alfarmar kar ya kuskura ya

hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.

"Wayarsa ya Wauko, ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sannan ya kara wayar a kunnensa yana jiran"

ta Wauka ya ji me yasa ta fitan sassafe haka? Don a saninsa yau ba ta da aiki in dai ba wani muhimmin abu bane ya taso mata.

"A can Sangaren Bintu, tana ganin kiran ta jaa wani dogon tsaki ranta a Sace."

"""Aikin Sur in ji tusa! Ai kuma sai ka yi. Na rantse da Allah idan za ka kira sau dubu bazan Wauka ba. Kai"

ma ka WanWana ka ji idan a kira mutum ya ™i Wauka da daWi. Don ma dai ni da hannuna bazan iya blocking

"Win ka bane kamar yadda ka yi min."""

Ita kaWai a cikin mota tana tu™i tana masifa har ta isa gidan Raudha. Ko da ta shiga ciki basu wani Sata

"lokaci ba suka fito, domin a shirye ta tarar da Raudha. Motar ta suka sake shiga mai gadi ya buWe musu"

™ofa ta figi motar a guje suka bar gidan.

"Kamar yadda suka tsara, komai ya tafi musu daidai yadda Bintu ta so. ˜arfe goma sha Waya da minti"

hamsin na safiya mai taxi Win da suka Wauki shata tun daga Kaduna yayi fakin a ™ofar gidansu Innaye.

Tana gyara zaman ™wamemen ba™in gilashi no respect da ta siya a Kaduna ta saka a idanunta take cewa

da direba.

"""Malam ka Wan jira mu kaWan, kamar yadda na ce maka ba daWewa za muyi a ciki ba. Yaro kawai zan"

"Wauko ka juya da mu inda ka Wauko mu."""

"""Babu damuwa Hajiya. A fito lafiya."""

Ya amsa a ladabce.

"Har sun nufi zauren gidan Raudha ta dakatar da ita, zip Win jakarta ta zage, ta cusa hannu a ciki ta Webo"

cingam guda huWu ta mi™a ma Bintu biyu itama ta Sare biyu ta watsa a baki ba tare da kunyar idanun mutane da ke kallonsu ba.

"""Saka wannan a baki ki tauna cikin ™warewa ™awata. Kin san sheggun ™auyen nan in bi ki nuna musu ke"

"ma ´ar iskar kanki bane baza su baki Aadil a sau™a™e ba. Kuma ko da wasa idan muka shiga kar ki kuskura kunyar ´ar iskar tsohuwar nan ya hana ki yayyaSa mata ba™a™en maganganu..."""

"""Kin san wannan ai dole ne Raudha. Yadda raina ya Saci Wallahi dole nata ya ninka nawa Saci. Mu je."

"Shegu yaran ™auye dubi yadda suke kallonmu kamar mayu... kurwanmu kur!!!"""

Ta ™arasa maganar da Wan ™arfi tana kallon wani yaro Wan tsamurarre da tulelen ciki wanda tun Wazu

yake tsaye gefe ya ™ura musu idanu.

Bayan ta Sare cingam Win ta watsa a baki sai ta nufi cikin gidan tana sake tamke fuska. Raudha na biye da

ita a baya itama da nata fuskar a haWe babu sassauci ko kaWan.

******

"A cikin gidansu Innaye, misalin ™arfe goma sha Waya da kwata na safiyar ranar, Aunty Balira, Rakiya,"

Ladidi suka yi ma gidan dirar mikiya.

"Bayan barinsu gidan Aunty Balira jiya, da daddare ta kira su kan cewa su tambayi mazajensu su haWu su"

"ukun su je suyi ma Innaye Allah sanya alkhairin aure da Hafiz zaiyi. Wannan shi ne abinda ya kawo su, ashe rabon suyi kiciSus da Hajiya Bintu ne."

"Suna zaune a tsakar Wakin Innaye kan tabarma suna shan Fate da Mama Laraba tayi, hira suke da"

"dararraku a tsakaninsu ukun, Innaye tana zaune a kan kujera tana saka musu baki jefi-jefi."

"Suna cikin wannan halin ne suka ga an yaye labulen Wakin, kwatsam! Sai ga Bintu ta bayyana da Raudha"

"tsaye a bayanta, sai taunar cingam suke yi ™aras-™aras cike da tsantsar raini da fitsara."

Da farko duk ™amewa suka yi ana kallon-kallo a tsakaninsu. Sai Aunty Rakiya ta karya shirun da cewa

"""A'uzubillahi minasshaiWanirrajeem."""

Da matsanancin Sacin rai a muryar Bintu ta ce

"""Kan'uba!! Amma lallai Rakiya kin ci uwar rainin wayau. Ni za ki kalla kiyi wa a'uziyya? To Me kike"

"nufi?"""

"""Me kuwa nake nufi in banda korar shaiWan da nayi? Idan banyi a'uziyya ba me kike so inyi? In ba"

"shaiWaniya a cikin siffar mutane ba wacece za ta shigo Waki mai daraja irinna sarkuwarta babu sallama...?"""

"""Rakiya!"""

Innaye ta kira sunanta da Wan tsawa-tsawa a muryarta.

"""Ya isa haka nan."""

Ta sake faWa tana ™o™arin sassauta muryarta.

A karo na biyu ta mayar da idanunta kan Bintu ™irjinta na bugawa kaWan-kaWan. Ta daWe da sanin Bintu

"ba ta da mutunci, amma tsantsagwaron rashin mutunci irin wanda take ™o™arin shimfiWa musu yau bata taSa ganin ta yi ba. Tunaninta Waya ne, Bintu ta ji Hafiz zai auri ™anwar mijin Zulai shi ne ta zo ta sauke"

musu rashin mutunci don a tsammaninta da haWin bakinsu ake shirin ™ulla auren.

"""Fatima lafiya? Me yake tafe da ke?"""

Ta tambayeta bayan ta tuna zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya.

"Yatsarta manuniya tasa ta ja gilashinta ™asa kaWan, ya zama tana kallonsu Waya bayan Waya ta saman"

"gilashi. Cingam Win da ke bakinta ta tauna yayi ™as, ta huro shi yayi ™aton balo-balo ta fasa sannan ta fara"

magana tana yamutsa fuska kamar tana sha™ar warin kashi.

"""Innaye... Kin ga ina ganin mutuncinki, kuma da gaske ina ganin girmanki. Bana tunanin tunda na auri"

"Hafiz wani sa'insa ya taSa shiga tsakanina da ke, don haka kar ki bari mu fara ayau. Salin-alin ki bani Wana in tafi da shi..."""

"""Saurara Bintu! Wani Wan kike magana akai?"""

Aunty Balira ta katse mata numfashi da wannan tambayar.

"""Šana Aadil, jinina. Wanda na haifa a cikina..."""

"""Uhmmm! A sanina dai ™arfe Waya ba ya amo... idan kuma Wan naki ne ke kaWai ai sai mu ji. In dai har"

"Babanmu Wan da Hafizu yayi miki cikinshi kika haifa ne, a tunanina yana da ikon yin yanda yaga dama da"

"Wanshi?"""

Aunty Ladidi ta katse ta da faWin haka ranta a Sace da maganganun da Bintu ta faWa.

Habawa!!! WaWannan maganganu da Ladidi ta faWa ina wuta Bintu da Raudha su jefata a ciki wai tana

"neman sheganta Aadil. Haka suka shigo har tsakiyar Wakin Innaye suna zuba rashin daraja ko takalmansu basu samu sararin cirewa ba. Suna yi, Rakiya da Ladidi suna basu amsa, nan da nan guri ya fara rikicewa kamar za'a ba hammata iska. Kishiyoyin Innaye da tashin muryarsu Bintu ne ya shigo da su babu abinda"

"suke yi sai aukin bada ha™uri, tunda sun taki babbar sa'a Baffa ba ya nan."

"Su Baba Abubakar da kusan yini suke yi a ™ofar gidan kuma su ma basa nan, tun sassafe suka hau motar"

da Hafiz ya Wauka musu shata suka kama hanyar Abuja don a tsayar da maganar aure tsakanin Hafiz da Kareema.

Wannan shi ne dalilin da yasa su Bintu suke cin karensu babu babbaka cikin rufewar idanu.

"Innaye dai tana zaune ™i™am kamar mutum-mutumi. Kanta a ™asa, a idanunta kuwa babu abinda ke fita"

sai zazzaafan hawaye. Zuciyarta cike da tunanin yadda Šan kuka ke ja ma uwarsa jifa. Wai yanzu fa

"wannan matsayin matar Wanta take. Saboda tsabar rashin kirki ta shiga har tsakiyar Wakinta da takalmi, kuma take zuba musu rashin mutunci yadda take so."

A Sangaren Aunty Balira da take zaune itama ba™in ciki da takaicin Bintu na neman kai ta kushewa

"wayarta ta zura hannu a lalita ta ciro. Lambar Hafiz ta lalubo ta danna mishi kira, a niyyarta na tambayarsa wai shin shi ne ya turo Bintu tazo ta zubar musu da mutunci ta Waga hankalin mahaifiyarsu? Ko kuwa zuwan na gaban kanta tayi?"

"Acan Sangaren Hafiz, yana ganin kiran ya Waga, da Wan ta™aitaccen murmushi a fuskarsa. Ya buWe baki"

zaiyi sallama kenan sai ya jiyo hayaniya na tashi sosai ta cikin wayar kamar ana faWa.

˜irjinshi ne ya buga daram! Don haka ya saurara sosai don jin hayaniyar me ake yi haka a gidan Aunty

Balira.?

Muryar Baba Laraba da ya fara jiyowa tana magana yasa shi fahimtar hayaniyar a gidansu Innaye ne ba

gidan Aunty Balira ba.

RaWau ya cigaba da saurarar muryar Baba Laraba tana magana cikin magiya da ro™o

"""Hajiya Bintu... kinga Hajiya Bintu ina gama ki da girman Allah da ma'aiki kiyi ha™uri... Tunda dai baki ga"

"alamar wani Wa naki anan ba ki koma..."""

Muryar Bintu da ya ji cikin masifa tana mayar da martani yasa shi wuntsilawa daga kan gadon hankalinsa

"a tashe. Bai ™ara shiga tashin hankali ba sai da ya ji irin munanan maganganun da ke fita a bakinta. Tana mayar ma da Baba Laraba martani, amma kamar tana yi da ™anwarta."

Lokaci Waya jikinsa ya fara rawa kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a tsakiyar Wakin Innaye bayan ya ji

kalaman Bintu.

"""Ke tsohuwa saurara. Na rantse da Allah tunda na sa ™afa na shigo wannan tsinannen ™auyen babu"

"inda zan je sai wannan tsohuwar da munafukan ´a´anta sun fito min da Wana..."""

"Daga wannan maganar, bai sake jin wata ba sai ™arar saukar marin da daga ji ba Waya bane, marin da ya"

rasa wa aka yiwa? Bintu aka mara ko ita ce ta mari Waya daga cikin yayyinsa? Ko kuma ha™urin Innaye ne yakai ™arshe ta mari Bintu? Kuma sanadiyyar marin ne yasa duk hayaniyar da ake yi ya Wauke Wif! Kamar Waukewar ruwan sama.

"Sai da aka Wauki mintuna biyu kafin ya ji muryar Aunty Balira tana magana cikin kuka, saboda hawayen"

da sai a lokacin ta lura Innaye tana yi ya Waga mata hankali.

"""Tir da mace irinki Bintu!!! Tir da ke da munanan halayenki Bintu!! Sai yau na ™ara tabbatarda lallai"

"Hafizu yayi asara baiyi sa'ar mata ba. To saurara ki ji, ke kinyi kaWan ki ce za ki zo ki saka mahaifiyarmu kuka sannan mu zuba miki ido. Idan shi wanda ya auro ki ba ya kishin mahaifiyarsa mu muna yi. Ki je can ki nemi inda Hafizu ya kai miki Wa, mu kam saboda sanin mugun halinki da ba™in halinki babu wacce tayi gigin karSar mummunan tsatso irin naki. Zo ki fice mana daga Wakin uwa, za ki fice ne salin alin ko sai na"

"nakaWa miki tsinannen duka in barki kwance?"""

"Ta ™arasa maganar cikin tsawa da hargagi, jikinta sai rawa yake yi saboda yadda kukan Innaye ya ke"

bugun zuciyarta.

"Bintu da tunda Aunty Balira ta sauke mata tagwayen maruka ita da Raudha suka ™ame ™am kamar statue,"

sai a lokacin ta iya buWe baki da rawar murya idanunta ciccike da hawaye ta ce

"""Nnnnnn ni kika mara Balira...?"""

"Ai ko kafin ta rufe baki, Aunty Rakiya da Aunty Ladidi da tun Wazu hannuwansu ke ™ai™ayi suka sake"

gaura mata wasu ™arfafan maruka a kuncinta na dama da hagu.

"""An mare ki Win! Don abu kaza-kazanki idan kin isa ki sake cewa uffan anan gurin idan bamu yi ™asa-"

"™asa da ke ba."""

Suka haWa baki gurin faWin haka a zafafe.

Aunty Rakiya da ta daWe tana jiran irin wannan ranar da za ta jibgi Bintu a haukace ta cire Wankwalin

"kanta ta ci Wamara da shi. Ta tsaya gaban Bintu tana jijjiga, babu abinda take jira sai Bintu ta ce kule ta rufe ta da mahaukacin duka."

"Raudha da tun da aka yi marukan farko hankalinta yakai ™ololuwa gurin tashi, a Wan tsorace ta ™are ma"

"Rakiya kallo, ta ganta irin sangama-sangaman matannan ne ga tsawo ga ™iba. Ko dambe aka ce suyi su"

biyu ita da Bintu su taru ma Rakiya ko rantsuwa tayi babu kaffara tun a mintuna biyun farko Rakiya za

tayi ™asa-™asa da su.

"Domin daga ita har Bintu ba su da ™iba ko kaWan, kuma Mal bahaushe ya ce alamun ™arfi yana ga mai"

™iba. Da sauri ta ri™o hannun Bintu ta fara janta da nufin su fice daga Wakin.

"""Zo mu je ™awata. Idan muka tsaya taron dangi za suyi mana. Idan sun ™i ba mu Aadil ta lalama ai"

"akwai hukuma. Kuma na rantse da Allah waWannan marukan da suka yi miki basu ci bulus ba, tabbas za su biya bashi amma a gaduron Win sojoji. Zo mu je mu sake sabon shiri."""

"Tana jan hannun Bintu, Bintun tana turjewa hawayen ba™in cikin mari huWu da aka mata na zuba a"

"idanunta amma bata iya rama ko Waya ba, kuma ta kasa cewa uhummm Win saboda tsoron kar su dake ta"

"abinda ta san za su aikata tunda shegun ™auye ne, a haka har suka fice daga gidan gaba Waya tana sharSen hawaye."

****** ******

"Misalin ™arfe bakwai na daren ranar, Bintu tana kwance akan gadon Wakin Raudha. Ta ci kuka har ta"

"gode Allah, hawayen da tunda suka Salle mata a can Fa™o har yanzu sun gagara tsayawa. Duk kuwa da"

yadda Raudha ta yini tana rarrashinta sam ta kasa daina kuka.

"A yanzu abubuwa ne suka haWe mata goma da ashirin. Ga damuwar rashin sanin inda Hafiz ya kai Aadil,"

ga damuwar irin wannan mummunan cin mutunci da tozarci da dangin Hafiz suka yi mata.

"""Yanzu shi kenan? An sha ta misilla-banza? Hafiz da ™auyawan ´an'uwansa sun ci galaba a kanta? Sun"

"raba ta da Wanta lokacin da bata yi tsammani ba sannan sunyi sukuwar sallah akan kima da martabarta?"""

Tunanin hakan kaWai tayi sababbin hawaye ne ke sake Salle mata.

"Ko bayan da suka koma Abuja a yammacin, kafin su isa gidan Raudha sai da ta kira Hajiya Maama matar"

Abba Lurwanu ta tambayeta cikin hikima ko Hafiz ya kai mata Aadil?

"""Bai kawo shi ba Bintu. Hafiz Win bai dawo bane ko kin kasa samun shi a waya ne? Kin san Aadil da"

"™wuiya na tabbata duk inda yake yana tare da mahaifinsa. Kiyi ha™uri, zai dawo miki da Wanki."""

Amsar da Hajiya Mama ta ba ta kenan.

"Gidan Zulai shi ne guri na ™arshe da tayi tunanin Hafiz zai iya kai Aadil. Har sun kusa isa gidan Raudha,"

haka ta sake neman alfarmar Raudha ta juya da kan motar da a yanzu Raudha ke tu™awa suka nufi gidan

Zulai.

Suna hanya kamar mahaukaciya haka take ta kuka tana rantse-rantse da shan alwashin duk waWannan

marukan da su Balira suka yi mata akan Zulai za ta rama.

Sai dai wani rashin sa'a da suka buga shi ne suna isa mai gadi ya tabbatar musu Zulaikha ba ta nan. Ta

tafi can babban gida saboda Oga yayi tafiya.

"Da fari ta so suje gidan Mummy Saudha tun a daren, amma sai Raudha ta taushi zuciyarta da shawarar"

"tayi ha™uri su bari zuwa gobe da safe. Lokacin Mummy ta tafi aiki sai su je, yadda za su samu damar cin ™aniyar Zulai ba tare da anyi yun™urin hana su ba."

"Amincewa da shawarar tayi, don haka ta jingina da kujerar mota ta lumshe idanu ta cigaba da hawaye"

zuciyarta na ™una da tafarfasa. Har suka isa gidan Raudha bata sani ba sai da ta taSa ta cewa ta tashi su shiga ciki.

Tunda ta shiga kuwa tayi kwance-kwance tana kuka akan gadon Raudha. Ko ramakon sallolin da suke

"kanta ta kasa yi, tun Raudha tana rarrashinta har dai ta gaji ta zura ma sarautar Allah ido. Daga ™arshe ma ficewa tayi zuwa kicin, ta samu abinci ta ci tayi nak, sannan ta koma Wakin bayan ta yi nakwa-nakwa da fuska, sak yanayin taya Bintu ba™in ciki da jimami."

Agogo yana buga ™arfe tara daidai ta Waga jajayen idanunta da suka kumbura

41 / 50