Advertisements
Chapter 22 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 50

63K to 66K   out of 147.7K words

ji a shirin In da Ranka... wannan ba komai bane."

"Da saurin gaske ta lalubo lambar Hafizu mai alamar mota ta danna mishi kira. Yana Wauka, bata tsaya jan"

wani dogon zance ba ta fara kora mishi ™wa™™waran kashaidi

"""Hafizu, kabar duk abinda kake yi yanzunnan ka tafi gidanka ka duba min halin da Auta take ciki. Domin"

"na kira Bintu na faWa mata Zulai matarka ce, na ji ta ™wallah ihu, to ina rantse maka da Allah idan"

"mahaukacin kishi yasa Bintu illata min Auta bazan taSa yafe muku ba har duniya ta naWe..."""

Šif! Cajin wayarta ta Wauke ba tare da ta gama kora ma Hafizu kashaidi ba.

"Duk yadda take ta kunna wayar a ™o™arinta na sake kiransa, wayar da ta kawo sai ta Wauke. A zuciye tayi"

"cilli da wayar akan gado ta mi™e tsaye tana safa da marwa, bakinta Wauke da duk wata addu'a da ta zo zuciyarta."

A Sangaren Hafiz ma ko da ya gwada kiran lambar Innaye ya ji swich off! Ya kira lambar Bintu ita ma a

"kashe, ya kira lambar Aunty Balira da yake hannun Zulai ita ma ya ji a kashe. Hankalinsa a tashe ya tsallake tarin ayyukan da ke gabansa ya fito daga cikin Ofishinsa ya nufi gida."

***** *****

"Ba ita ta farka ba sai ™arfe tara da minti biyu na safiya, ganin yadda garin ya waye sosai yasa ta yin"

mamakin irin barcin da tayi akan dadduma. Da sauri ta faWa banWaki ta yi wanka ko jikinta ya ™ara

warwarewa daga gajiyan da yake tare da ita.

Bayan ta fito ne ta lura da wata ba™uwar fallen takarda da aka nannaWe ajiye a gaban madubi. A hankali

ta ™arasa ta Wauka.

"""Mashkura"""

Shi ne sunan da ta gani rubuce da manyan ba™i a farkon sa™on. Šan murmushi ne ya suSuce mata kafin

ta fara karanta ta™aitaccen rubutacciyar sa™on da ya kasance da hausa ne.

"_""˜awata, Na shigo mu gaisa sai na ga kina barci. Sanin jiya baki wani samu isasshen barci ba shi yasa"

"na kasa samun ™warin gwuiwar tashinki. Ki huta lafiya ˜awata, ni na wuce makaranta. Idan na dawo in"

"sha Allah yau za mu fara Waukar darussanmu kamar yadda muka tsara. Bye._"""

A hankali ta nannaWe takardar har lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba.

"""Allah sarki Mashku. Ubangiji Allah ya dawo min da ke lafiya. Na gode ™warai da karamcinki a gare ni."""

"Tayi maganganun a fili. Gefen gado ta ™arasa ta Wauki wayarta, sai a lokacin taga wayar a kashe. Ko da ta"

"kunna sai taga ashe cajin wayar ce ta ™are, kuma Aunty Balira bata ba ta cajar wayar ba."

"Šan Sata fuska tayi alamun bata ji daWin haka, wayar da wasi™ar da Mashkura tayi mata ta cusa a aljihun"

jakar kayanta sannan ta ciro manshafawarta ta zauna a gaban madubi ta fara shafawa. Zuciyarta cike da tunanin Innaye.

Ta so ™warai ta kira Innaye yau da safennan su daWe suna hira. Abinda yasa ta kasa kiran Innaye jiya shi

"ne ba ta so ta ™ara Waga mata hankali, shi yasa duk yadda take son jin muryarta ta danni zuciyarta har zuwa safiyar yau. Sai kuma ga shi wayar nasara ta yi mata tsiya."

Ta gama shiryawa kenan a fisge ta ji kamar an yanka ihu daga can waje. Tsam! Ta tsaida hankalinta guri

"Waya ta ™ara saurarawa, sai kuma bata sake jin ihun ba. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, ta Wauki hijabinta ta zura ta kama hanyar ficewa daga Wakin a niyyarta na zuwa kicin don sama ma kanta abinda za ta karya da shi."

"Hankalinta yayi nisa sosai a tunanin da take yi, kuma baza ta ce ga takamaimai abinda take tunani ba."

Sam bata lura da tahowar Bintu a haukace ba sai ji tayi anyi mata wani wawan angiza da yasa lokaci Waya tayi taga-taga ta zube a ™asa.

A tsorace ta Waga idanu tana kallon Bintu da tayi amfani da wannan damar na faWin da Zulaikha tayi ta

"haye ruwan cikinta tayi mata wani mugun sha™a, ko da ta kalli cikin idanun Bintu, matsanancin tsoro da firgici ne suka ™ara lulluSeta ganin yadda idanunta suka kaWa suka yi jajur."

"""Munafuka, algunguma, matsiyaciya, tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba. Da gaske ne an"

"Waura miki aure da Mijina Hafiz ko kuwa wancan tsohuwar banzan ™arya take min?"""

Ta ™arasa da tambayar tana zazzaro ma Zulaikha idanu kamar wacce ta hau aljanu.

"[1/28, 7:23 PM] Fareeda Abdallah: Sai a lokacin Zulaikha ta fahimci dalilin haukar Bintu, idanu ta Wan"

runtse jin yadda Bintu take ta ™ara tattare hijabinta da wuyanta tana ™ara sha™o ta da hannayenta duk

biyu. Lokaci Waya kuma tana ™ara maimaita mata tambayar cikin tsawa da Waga murya

"""Za ki amsa min tambayar da nake miki ko sai na illata ki? Da gaske ne ™iyayyar da matsiyata kuma"

™auyawan iyayenku suke min ya kai matsayin da yasa suka aura ma mijina ke ko ™arya tsohuwar banzan

"nan take min?"""

Da Sacin ran yadda Bintu take ta furta kalaman tozarci ga iyayensu saboda mahaukacin kishi da ya rufe

mata idanu yasa ta amsa mata tambayar ita ma cikin tsawa da Waga murya.

"""Eh! Da gaske ne. Shekaran jiya an Waura aure na da Yaya Hafiz. Idan kina da abinda za kiyi ko kuma kin"

"isa kiyi wani abu sai kiyi."""

"Tana gama faWin haka da ™arfi tasa hannuwanta biyu ta SamSare hannayen Bintu daga wuyanta, tayi"

kukan kura ta wancakalar da Bintu daga ruwan cikinta ta mi™e tsaye a zafafe.

"""Ke jaka kuma dabbar ina ce da za ki dinga zagin tsofaffin da suka zama silar zuwan mijin da kike"

"ta™ama da shi duniya? Ko kina tunanin tsoronki suke ji da za su zuba ido kiyi ta wula™anta su a gidan Wan da suka haifa da cikinsu? Wannan auren ba kowa ne ya janyo shi ba face ke da kanki, ba™in halinki da mugun halinki na dabbobi yasa suka nema ma kansu mafita ta hanyar Waura ma Wansu aure da ni. Domin sun san duk tsiya ni bazan taSa wula™anta su ba, ranar naka sai naka... ko sun fi haka ™auyanci da jahilcin"

"da kike kira bazan taSa tozarta su ko in banbanta su da nawa iyayen ba..."""

"A haukace, Bintu ta sake ™wallah wani gigitaccen ihu a karo na biyu. Kalaman Zulaikha kamar zuban"

tafasasshiyar dalma haka suke sauka a kunnuwanta zuwa ™wa™walwarta.

"""Ni za ku ciwa amana??? Ni kike faWa ma irin waWannan banzayen maganganun? To na rantse da Allah"

"yau ko ni ko ke a gidannan. Zan kashe ki har lahira, in ga uban da ya isa ya tsaya miki duk faWin tsinannen"

"™auyen naku da jahilan iyayen naku da kike ta™ama da su."""

"Bintu tana gama faWin haka, da mugun gudu ta nufi cikin babban kicin Win ta da yake falon. Šaya daga"

"cikin sababbin wu™a™enta manya masu masifaffen kaifi waWanda bata taSa amfani da su ba ta Wauka, ta sake ficewa da gudun gaske."

"Zulaikha da take tsaye hannuwa ri™e da ™u™umi tana huci duk ga tsammaninta Bintu taSarya za ta Wauko,"

shi yasa ta tsaya domin ta gwada mata idan hauka da Wanyen kai take ji ta dame ta ta shanye.

"Hango wu™ar da ke ™yalli a hannun Bintu yasa ta zare ido, bata tsaya raba Wayan biyu ba ta juya da gudu"

"zuwa Wakin da aka yi mata masauki, tana shiga ta danno ™ofar Bintu ta isa gurin. Da™yar ta samu nasarar murza makullin ™ofar daga can ciki ta kulle tana numfarfarshi."

"Bintu a haukace ta kai ma ™ofar wani wawan suka da wu™ar hannunta, amma da yake dakakkiyar ™ofa ce"

mai tsada Wan karcewa kaWan jikin ™ofar tayi.

"""Ashe ke ™aramar mara kunya ce? Jaka, kucakar ™auye dabba, na rantse da Allah yau sai na ga bayanki"

"a gidannan. Zan nuna miki mijina nawa ne ni kaWai, ko da macen birni ´ar gayu bata isa inyi sharing Win shi da ita balle ke da nake miki kallon ™azantacciya a cikin dabbobi. Na rantse da Allah yau sai na bar ma waWancan munafukan tsofaffin mummunar tabon da bazai taSa gogewa a zukatansu ba. Zan kashe ki, in"

"kashe banza a banza, duk faWin ™auyenku sai in ga idan da shegen da ya isa yayi shari'a da ni..."""

"A haukace ta sake kaima ™ofar wani wawan tokari da ™afafunta, ihu ta ™wallah saboda azaban zafi da"

"raWaWin da ya ratsa ™afar nata lokaci Waya, sai kuma ta zube ™asa ta fashe da wani ™a™™arfan kuka gwanin ban tausayi, hannayenta duk biyu Wore a kanta. Ga kuma wu™ar da take ri™e da shi tsirara har lokacin bata yar da wu™ar ba."

A haka Hafiz ya shiga cikin falon a sukwane Raudha na biye a bayanshi. Ya matsa zai ™arasa kusa da ita da

saurin gaske ta nuno shi tsinin wu™ar hannunta.

"""Munafuki! algungumi!! maci Amana!! Wanda bai san darajar Al™awari ba!!!"""

Ta jefa mishi munanan kalaman cikin matsanancin kuka na tashin hankali.

"""Na rantse da Allah idan ka ™araso kusa da ni sai na caka maka wu™ar nan sannan in cakawa kaina."

"Gara duk muyi mutuwar kasko in san babu wata tsinanniya da za ta sake rayuwa da kai a matsayin mijin aurenta."""

Ta cigaba da magana cikin kuka.

"Hankalinsa a tashe, ya fara mata magana da taushin murya don ya kwantar mata da hankali."

"""Bintu, Bintu, kin ga, don girman Allah kiyi ha™uri ki ajiye wu™ar, ki saurare ni..."""

"""Me zan saurara?"""

Ta katse shi cikin tsawa tana wani zaro mishi idanu kamar ba ita ba.

"""˜arya? Ko kuwa kalamanka na yaudara da daWin baki da ka saba cika kunnuwana da su? Ayau na"

"tabbatar babu soyayya tsakanina da kai Hafiz, kuma na rantse da Allah sai dai idan Munafukar Allah ta'alan nan baza ta fito daga Wakinnan ba, sai na kashe ta har lahira, sai dai duk abinda zai faru ya faru."""

Bai san muhimmancin tahowa da Raudha da yay ya kai ™ololuwa ba sai da yaga cikin hikima ta ™arasa

"kusa da Bintu ta rungumota jikinta, sannan a dabarance ta zare wu™ar da ke ri™e a hannunta tayi hurgi"

da shi gefe Waya.

Cikin kuka da magagin kishi take yi ma Raudha bayanin abinda Hafiz yayi mata.

"""Ki ™yale ni Raudha... Hafiz ya ci amanata... ku kuke faWa min namiji ba Wan goyo bane ni kuma ina"

muku tutiyar nawa Wan goyo ne har da majanyi... Ashe duk mazan mamugunta ne halayensu Waya? Ashe da gaske ne da Hajiya Binta take yawan faWin Namiji ™anin ajali? Wai Raudha kamar ni Hafiz zai yaudara? Ni zai ciwa amana ya karya min al™awari? ˜auyensu ya tafi aka Waura masa aure da tsinanniyar ™anwarsa amma saboda ya raina ni shi ne yake faWa min ya taho da ita ne don ta taya ni aikin gida? To na rantse da

"Allah sai na kash..."""

"Da saurin gaske Raudha tasa hannu ta rufe mata baki. A tausashe ta fara ma Bintu magana, fuskarta na"

"bayyana yanayin Sacin rai da jimami, alamun itama tana jin ciwon abinda Hafiz Win yayi ma Aminiyarta."

"""Tabbas! Hafiz bai kyauta ba Bintu. Amma kar ki manta, idan hankali ya Sata hankali ke nemo shi."

"Yanzu abinda nake so da ke kiyi ha™uri, ki kwantar da hankalinki. Ki sama ma kanki nutsuwa ko Wan kaWan ne don mu samu mafita cikin ™an™anin lokaci. Tashi mu tafi zuwa Wakin ki, Hafiz Win me? Ina ™udan yake balle romonsa? Ai shi ma ya san yayi kaWan, ba irinmu ake yiwa wannan cin amanar a zauna lafiya"

"ba."""

"Da ire-iren waWannan kalaman tayi amfani har ta samu nasarar mi™ar da Bintu tsaye, tana ri™e da ita a"

jikinta suka taka a hankali tana sake faWa kalaman kwantar da hankali har suka haura sama zuwa Wakinta.

"Suna Sace ma ganinsa, hankalinsa a Wugunzume ya ™arasa zuwa ™ofar Wakin. Ya daWe da sanin Bintu tana"

"da masifaffen kishi, amma bai taSa tsammanin kishi zai iya rufe mata idanu har tayi yun™urin kisan kai ba. Yau in da ace kafin dawowarsa gidan ta samu nasarar caka ma Zulai wu™ar nan fa?"

"""A'uzu billahi minasshaiWanirrajim"""

Yayi ta'awizi da sauri yana ™o™arin kawar da mummunan tunanin daga zuciyarsa.

"Wu™ar da Raudha ta cillar zuwa gefe Waya ya fara Wauka ya kai kicin ya Soye, ba ma ita wannan wu™ar ba,"

"duk wasu wu™a™e manya da ™ananu da suke kicin Win kwashe su yayi gaba Waya zuwa cikin wata durowa ya kulle, ya zare makullin ya jefa a aljihu."

"˜ofar Wakin da Bintu take ciki ya koma ya fara ™wan™wasawa. Bintu da take ciki hankalinta a tashe, izuwa"

wannan lokacin ta shiga bayi sau biyar don tsananin firgita da tashin hankali. Cikin ™an™anin lokaci ta

zabge gaba Waya kamar wacce ta kwana ta yini tana amai da gudawa.

Duk irin maganganun da Bintu take yi tana jin ta. Ta kunna wayarta ya fi sau talatin don kiran can ™auye

"ta bada wasiyyar halin da take ciki, amma da yake matsiyaciyar waya ce da ta kawo sai ta Wauke. A ™arshe ma wayar sai ta daina kawowa. Tsananin tashin hankali yasa ta zube a ™ofar bayi tana sharSan hawaye, hannayenta duk biyu dafe da bakinta, don kar sautin kukanta ya fita balle har ta ™ara janyo ma"

kanta wani tashin hankalin daga Bintu.

"Tana cikin wannan halin ne taji an fara ™wan™wasa ™ofar Wakin da Wan ™arfi. Idanu ta zazzaro a tsorace,"

"ta cire hannuwanta daga baki ta Wora a kai hankalinta a tashe. Ko da ta ji ™wan™wasar ya ™i tsagaitawa sai ta yanke ma kanta shawarar gara ta fara ™wallah ihu, wata™ila idan aka ji ihunta ya karaWe gidan wasu"

daga cikin ma'aikata suyi ™o™arin kawo mata Wauki.

Ta buWe baki za ta yanka ihu kenan sai ta ji muryar Hafiz a fusace yana cewa

"""Zulai don ubanki baza ki zo ki buWe ™ofa in fitar da ke daga gidannan ba? Na rantse da Allah idan kika"

"yi wasa zan ficewata in ™yale ki da Bintu, in yaso ba caka miki wu™a ba, idan taga dama ma ta ™ona ki ™urmus! Ko babu komai an rage mugun iri a doron ™asa..."""

Tsulum! Ya ganta a gabansa ba tare da ya ji sadda ta buWe ™ofar ba. Kallo Waya yayi mata ya gane a

"bala'in firgice kuma a tsorace take, Zulai da ba ta ™aunar zama ba hijabi sai ga ta tsaye a gabansa ™i™am"

"babu hijabi babu Wankwali. Rigar ma duk ta tattare, har yana hangen wani sashe daga farin fatar cikinta. Ko da ya kalli idanunta duk sun zurma ciki sun canja kala."

Da bala'in haushi da takaicinta da ke cike da zuciyarsa ya galla mata harara.

"""Ina hijabinki?"""

"Da saurin gaske ta koma cikin Wakin jikinta na rawa ta fito ri™e da hijabin a hannunta, ta ma kasa"

"sanyawa, sai da ya daka mata tsawa da umarnin ta saka hijabin mana, sannan ta saka a baibai tana ta zare idanu tana waige-waige don kar Bintu ta shammaceta ta caka mata wu™a."

"Lura da yayi Zulaikha fa ba ta a cikin nutsuwarta, harara ya sake galla mata sannan yasa hannu ya finciki"

"hannunta Waya ya matsar da ita daga ™ofar Wakin ya shige ciki. Šankwalinta da ya gani yashe a ™asa,"

wayarta da ke ajiye a ™ofar bayi da takalmanta da suke ajiye a bakin ™ofa ya Wauka ya cusa mata a cikin

jakar kayanta.

Duk abinda yake yi shi ma a gurguje yake yi da tsoron kar Bintu ta fito ta tarar da Zulai a falon. Bai tsaya

ba ta umarnin su je ba kawai ya finciki hannunta da sauri tana biye da shi tana harharWewa har suka fice daga cikin falon.

"Bai saki hannunta ba, sai da ya buWe ™ofar baya na motar ya zaunar da ita a ciki, ya aje jakar kayanta a"

kusa da ita sannan ya mayar da ™ofar ya rufe.

Mal Musa har ya taso a zatonshi tare za su fita amma sai Hafiz ya dakatar da shi.

"""Yanzu zan je in dawo Mal Musa, ba nisa zanyi ba. Idan na dawo sai mu koma Ofis."""

Makullin motar ya amsa ya shiga mazaunin direba ya figeta a guje suka bar gidan.

"Hankalin Zulaikha bai fara kwanciya ba sai da taga sun bar unguwar gaba Waya, sun harba kan babban titi"

suna ta Sanana gudu. A fili taja wani nannauyan ajiyar zuciya da yasa Hafiz Wan kallonta ta cikin madubi.

"Harara ya sake gallah mata, ya ™ara da jan wata doguwar tsaki, ya saki wata ™a™™arfan ™wafa."

"Duk abinda yake yi tana jin shi, amma ko kallo bai ishe ta ba. Sai ™ara gyara zamanta tayi akan kujera a"

"fili ta fara godiya ga Allah, addu'a lokaci Waya tana haWawa da sambatu."

"""Allah na gode maka da ka kuSutar da ni. Allah kasa ko mutuwata ce tazo bazan mutu a wula™ance"

"hannun wacce ba ta so na, ba ta ™aunata, kuma bata san darajar rayuwata ba. Na yi dambe iri-iri zamanin yarintata, na ga dambe-dambe kala-kala a rayuwata. Amma irin wannan ta'addancin damben da ake amfani da wu™a mai shegen tsini da kaifi ban taSa yi ba, kuma ban taSa gani ba. Sai yau a gurin matar birni da take tutiya da wayewa amma ta bari linzamin kishi ya ja ta zuwa hauka, har take yun™urin"

"aikata abinda ni ´ar ™auye bazan taSa aikatawa ba..."""

"""˜iiiiiii..."""

Ya taka wani wawan burki da yasa ta katse surutan da take yi a tsorace. Ta Waga kanta a firgice tana

"kallonsa. Sai taga ashe har ya gangara gefen titi bata sani ba, hankalinta a tashe take kallon yadda ya buWe ™ofarsa a fusace ya fita daga cikin motar."

"Tana kallonshi, har ya gangara gurin wani mai kanti da yake can gefen hanya. Baza ta iya cewa ga"

"takamaimai abinda ya aikata a gurin ba, tunda hangen bayansa kaWai take yi daga cikin mota. Yana hanyar dawowa dai ta hango shi yana saka wani abu a cikin aljihun rigarsa."

": Duk da bata taSa yin doguwar tafiya a motar haya ba, amma ta gama sakankancewa tashar mota zai kai"

ta ya saka ta a motar zuwa Fa™o. Bata ankara duk doguwar tafiyar da suke yi ba tasha suka nufa ba sai da taga ya faka motarsa a ™ofar wani gida madaidaici amma kuma mai kyau tun daga waje.

"""Fito muje."""

"Ya umarceta bayan ya fita waje, fuskarsa a Waure tamau. Babu walwala ko mis™ala zarrah."

"A tsorace ta kalle shi, ta sake kallon ™ofar gidan da suke tsaye a gabansa. A marairaice ta ce"

"""Yaya ina ne nan Win ka kawo ni? Dan girman Allah kayi ha™uri ka saka ni a motar zuwa gida. Wallahi"

"gaba Waya a firgice nake da Habujan nan, ka taimaka ka mayar da ni gurin Innaye inda na fi wayau."""

Sai ga hawaye sun zubo mata shar... Da rawar murya ta cigaba da cewa

"""Ni Wallahi daman auren nan yadda kake jin tsanarsa a ranka na ma fi ka jin tsananin tsanarsa a"

"zuciyata. Ka kwantar da hankalinka, idan ka mayar da ni gida

22 / 50