Advertisements
Chapter 9 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 50

24K to 27K   out of 147.7K words

™o™arin yin murmushi amma ya gagara saboda tsananin yadda ta jigata da ciwon dare Waya

kacal.

"Kafin yayi magana Bintu tayi sallama ta shiga cikin Wakin, idanunta kan agogon da ke Waure a tsintsiyar"

hannunta take cewa

"""My dear lokaci ya tafi sosai fa, sai kira na ake yi a Ofis. Ta gama break fast Win?"""

"""Eh! Ta gama."""

Ya amsa shi ma yana sauke idanunsa kan agogon bangon da ke cikin Wakin. ˜arfe takwas da mintuna

talatin da uku.

"Bintu idanunta ta mayar kan Innaye da fuskarta yayi zuru-zuru, idanunta suka zuz-zurma ciki sosai, ciwon"

"dare Waya kawai gaba Waya ya sa kamanninta ya canja, tsufanta ya bayyana ™arara. Haushi da tsanar"

Innaye da yayi kaka-gida a zuciyarta ya hana Wan guntun tausayin da ya taso mata yin tasiri.

"""Innaye ina kwana? Ya ™arfin jiki?"""

"""Lafiya ™alau. Da sau™i Alhamdulillah"""

Ta amsa da yanayin maganar da take yi ™asa-™asa tun da ta idar da sallah.

"""Allah ya ™ara sau™i."""

Tayi addu'ar a gaggauce. Muryar Hafiz kawai ta ji ya amsa mata. Cikin rashin damuwa ta Wauki ledar

"magungunan Innaye da ke ajiye a gefe guda ta fito da su ta fara harhaWa ruwan alluran, duk abinda take yi cikin sauri ne tana yi tana kallon agogo."

Babu wani tausasawa Innaye ta juya baya ita kuwa ta zurkuWa mata alluran biyu ba tare da tantance inda

"ya kamata tayi mata ba. Ta Salli magungunan kamar jiya shi kuma ya mi™a ma Innaye, ya tsiyayi ruwan gora a kofi ya mi™a mata ta haWiyi maganin."

"""Zulai sakko ki ga magungunan da za ki ba Innaye da rana."""

Bintu ta faWa idanunta kan Zulaikha da take zaune a gefen gado tun bayan shigarta cikin Wakin.

"Da farko ™in motsawa tayi, sai da Hafiz ya daka mata wani gigitaccen tsawa kafin ta taso da sauri ta"

tsuguna gaban Bintu tana zumSura baki.

"""Ki shiga taitayinki da ni na rantse da Allah. Idan ba haka ba kafin in fita Ofis na rantse sai na koya miki"

"hankali..."""

Hannun da Innaye ta Waga masa alamar dakatarwa yasa shi katse maganar ba tare da ya kai ™arshen

maganar ba.

Kala uku a cikin magungunan ta ware ta nuna ma Zulaikha da cewar su za ta ba Innaye tasha da rana.

"""Ki kiyaye fa, kar ki kuskura shirme da wawancinki yasa ki dawo min da treatment baya. Domin yadda"

"ta fara shan magani da allurannan kuskure kaWan za a samu na jinkirin shan maganin aiki ya dawo baya, ba fata nake yi ba amma irin ciwukan da za su taso mata sai sun fi waWanda tayi fama da su a baya."""

Ta yi maganganun cikin faWa-faWa tana aika ma Zulaikha mummunan kallo.

"Bata amsa ba, a madadin tayi magana ma Waga idanunta tayi a fili itama ta galla ma Bintu wata"

matsiyaciyar harara kafin ta mi™e ta koma gurin zamanta gefen gado.

"Baki buWe Bintu ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da mamaki. Ta buWe baki za tayi magana da sauri Hafiz"

"da yake ankare da komai ya Wan taSe ta, suna haWa idanu ya girgiza mata kai sannan ya nuna mata"

Innaye da ™wayoyin idanunsa.

"˜asa-™asa tayi ™wafa kafin ta mi™e tsaye, fatan ™ara samun sau™i tayi ma Innaye sannan ta kama hanyar"

ficewa daga Wakin.

"""My Dear ni kam na wuce. Sai munyi waya."""

Bata jira amsawarshi ba ta fice daga Wakin.

"Aka ce albarkacin kaza ™adangare ke shan ruwan kasko. Albarkacin Innaye, yasa duk yadda Zulaikha ta"

Sata ma Hafiz rai bai ce mata komai ba har ya gama tarairayar Innaye ya fice daga Wakin bayan yayi musu sallama zai wuce Ofis.

Da harara Zulaikha ta raka shi har ya Sace ma ganinta.

"Innaye dai jingina tayi da jikin bango ta lumshe idanunta. A yanzu babu zazzaSi a jikinta, amma fa ba ta"

"jin ™arfi ko mis™ala zarratin, sakayau take jin ta kamar an kwashe duk wani ™warin jiki da Allah ya huwace"

mata. Tana a haka har barci ya fara Waukarta.

"""Innaye ko za ki dawo kan gado ki kwanta sai in gyara tsakar Wakin?."""

Maganar da Zulaikha tayi shi ya farkar da ita daga barcin da ya fara Waukarta.

"Bata ce komai ba, sai yun™urin mi™ewa da ta fara yi, da sauri Zulaikha tazo ta kamata ta mi™ar da ita,"

tana tallabe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gadon ta rufa mata bargo a rabin jikinta.

Kafin ta gyara Wakin sai da ta zauna ta take cikinta tayi nak! Tana cin alalen dankalin turawan tana

korawa da daddaWan kunun gyaWar a zuciyarta take zabga Allah ya isa ga Bintu da a dabarance ta daina basu dafaffen abinci lokacin karyawa sai dai su sha shayi.

Ita kam da yake rainon ™auye ne abu mai suger da safe bai cika damunta ba. Ko a gida idan akwai

"Wumamen tuwo ko sauran abincin da aka dafa da daddare sam ba ta kallon kokon da ake damawa a rarraba ma yaran gida a cikin kofuna ™ananu. Šumamen Tuwo take sakawa ta zambaWa yaji ta cika cikinta tayi nak, sai ta kai ™arfe Wayan rana da ™oshinta ko da an samu jinkirin gama abinci sanadiyyar"

Wanyen itace ko gawayi.

"Bayan ta gama karyawa tattare kuloli da farantai da kofuna tayi gefe Waya ta gyara tsakar Wakin ™al, har"

mopping Win kan tiles Win tayi ya fita fes! Sannan ta maida hijabin jikinta ta bi lafiyar gado ta kwanta gefen Innaye domin ta rama barcin da bata samu yin isasshe jiya ba.

******

Darare uku masu kama da darare dubu saboda masifar tsawonsu a gurin Zulaikha Innaye ta kwashe tana

fama da bala´a´´en zazzaSi mai zafin gaske kamar baza ta wayi gari ba.

Wani ikon Allah kuma da asubahi tayi sai zazzaSin ya sauka. Haka za ta yini cikin rashin ™arfin jiki da

"kasala, ba ciwon jiki kaWai ba, hatta tafin ™afafun Innaye jin su take kamar an kwashe ™asusuwan da suke taimaka mata gurin yin tafiya an bar zallar tsoka kaWai. Dai dai da zuwa banWaki sai Zulaikha ta ri™e ta sannan take iyawa, sallah kuwa tun ranar farko da ta fara yi a zaune har yau bata ™ara samun ™warin"

gwuiwar yi a tsaye ba.

Innaye ta rame ta zabge ta tsuke kamar ba ita ba. Tsufa da galabaita sun bayyana ™arara a jikinta. Ba

"Innaye da take fama da ciwon cikin dare ba, hatta Zulaikha da take jinya duk ™ibar nan ta fara zazzagewa."

Ita kanta kallo Waya za'a yi mata a fahimci rashin nutsuwa da rashin kuzari a tattare da ita.

Shi kuwa Hafiz duk yadda ciwon Innaye yake Waga mishi hankali har lokacin bai ji a jikinsa ya kamata

Bintu ta canja ma Innaye magunguna da allurai ba. Maganar da ta faWa mishi tun ranar farko ita ya ri™e

daram a zuciyarsa

'Jikin Innaye bai taSa karSar magunguna masu kyau da ™arfin waWannan ba shi yasa a yanzu dole za ta

galabaita na kwana biyu. A bayan waWannan cututtukan lafiya wadatacciya ce za ta biyo baya fiye ma da wanda suke nema.'

Da waWannan kalaman yake ta dannar zuciyarsa da irin damuwa da tashin hankalin da yake ciki.

Abu Waya dai da ya iya yi shi ne kullum bayan ya dawo sallar asubahi zai umarci Bintu ta haWa ma Innaye

"lafiyayyen abin kari, idan ta gama ya kwasa ya fice musu da shi."

A rana ta uku har yayi ma Innaye sallama zai tafi Ofis bayan Bintu tayi mata allurai ta bata magunguna ta

fice gurin nata aikin Innaye ta ri™o gefen rigarsa.

"""Innaye? Sannu. Akwai abinda kike so inyi miki kafin in tafi Ofis ne?"""

Ya tambayeta a tausashe bayan ya dawo ya zauna a kusa da ita.

"""Hafizu, gida nake so ka mayar da ni yau. Ko da mutuwa za ta Wauke ni na fi so ta Wauke ni a cikin"

"iyalaina."""

"Tayi maganar da™yar, shi kanshi bai ji abinda ta ce ba sai da ya kai kunnensa daidai bakinta."

Hankalinsa ne ya ™ara Wugunzuma fiye da wanda yake ciki. A yadda ya Wauko Innaye da ™arfi-™arfinta ko

kusa bazai so ya mayar da ita can ™auyensu yadda ta fara kwararraSewa haka ba.

Saboda ba ya son Waga ma ´an'uwa da mahaifinshi hankali ne yasa shi tun fara zazzaSin daren Innaye

"kullum sai ya gargaWi Zulaikha kar ta kuskura idan Waya daga cikin Yayye, mahaifinsu, ´an'uwa suka kira"

Innaye don jin yanayin jikinta tayi suSul da bakan sanar da su irin ciwon da ya taso ma Innaye gadan- gadan.

Daga bisani ma karSe wayar Innaye da ke hannun Zulaikha yayi ya kashe. Ya zama sai lambarshi kaWai

"ake kira aji ya jikinta, shi kuwa duk wanda ya kira shi ya san abinda yake faWa musu. Ko sun nemi yin"

magana da ita kai tsaye yake kawo wani ™a™™arfan uzuri ya basu.

Hankalinsa a tashe ya gyara zama zai fara kalallame Innaye da daWin bakin tayi ha™uri ga mamakinsa da

tsoro kawai sai ta fashe mishi da kuka. Wani abu da bai raSa faruwa tsakaninshi da ita ba.

Wannan kuka da Innaye take yi hai™an ba ji ba gani sam ta ™i tsayawa ta saurare shi shi ne abinda ya ™ara

"Waga hankalinsa zuwa ™ololuwa. Afujajan ya mi™e tsaye ya fice daga cikin Wakin, can jikin famfon da ke tsakar gurin ya hangi Zulaikha zaune ta tasa kayan wankinsu a gaba tana zaune dirshan a ™asa tana matsar ™wallah."

"Kaman zararre, ya ™arasa gurinta da sauri."

"""Kukan me kike yi?"""

Ya tambayeta cikin tsawa.

A tsorace ta Waga idanu ta kalle shi. Maimakon ta amsa tambayar da yayi mata kuma kamar haWin baki

itama sai ta fashe mishi da ™a™™arfan kuka.

"""Gida kike son tafiya?"""

Ya sake jefa mata tambayar hankalinsa a tashe.

"Da saurin gaske ta dinga gyaWa mishi kai alamar eh kamar ™aramar yarinya, ta kasa buWe baki ta amsa"

mishi saboda kuka.

"""Ki haWa kayayyakinku bari inje in dawo mu tafi yanzu."""

Ya sake faWa hankalinsa a dagule.

Yana kallonta ta kwashi kayan wankin nasu da ko ji™awa bata yi ba ta wuce cikin Wakin da sassarfa jikinta

na rawa.

Jikinsa a sanyaye yaja ™afafunsa da yake ji kamar baza su iya Waukarsa ba ya wuce zuwa Sangarensu.

"A yadda ya tsara da farko, ™arasa shiryawa zaiyi yaje gurin aiki ya Wan rage wasu ayyukan kafin yazo su"

"tafi. Amma da zaran ya tuna irin kukan da ya bar Innaye tana yi, sai hankalinsa ya ™ara Wugunzuma."

"Ya rasa abinda ke mishi dad'i, a kasalance ya k'arasa shiryawa ya fice daga falon ya nufi can tsakar gidan"

ya sanar da direba ya canja motar da za su fita da ita. Ba Ofis za su ba can ™auye za su je.

"""˜auye a yanzu Oga? Allah yasa dai lafiya?"""

Direba ya jefa mishi tambayar fuskarshi na bayyana damuwa.

"""Lafiya ™alau. Innaye ce ta matsa lallai a mayar da ita gida yau."""

"Ya amsa mishi yana cigaba da tafiya zuwa Sangaren Innaye, wayarsa na hannunsa yana daddanawa don"

kiran Bintu ya sanar da ita abinda yake faruwa.

Kamar ta mi™e ta taka rawa take ji don tsananin farin cikin da ya sauka a zuciyarta lokaci Waya daga jin

bayanin da yake mata. Amma da yake ta ™ware a nuna yanayin da ba haka bane a zuciyarta sai ta

"kwantar da muryarta sosai, cikin yanayin damuwa da jimami ta ce mishi"

"""Sweetheart ™auye kuma? To ya bayanin sauran alluranta da suka rage na kwana biyu? Kuma ka san"

"halin mutanen naka dai da rashin kulawa, idan suka tafi da magungunan nan ba lallai su kiyaye ba ta akan lokaci ba. Kar ciwon ya dawo baya fa..."""

"""To ya zanyi mata Bintu?"""

Ya katse ta da kalar tasa damuwar da yake ji kamar ya Wora hannu aka yaita rusa ihu.

"""Duk irin kalaman da ya kamata in yi amfani da su gurin yi mata bayani sam ta ma ™i saurarata. Ni"

"babban damuwata ma Wallahi ba ragowar allurai da magungunan bane, ki tuna yadda na Wauko Innaye daga gida."

Ko da dai ba ta da lafiya amma ke kin san yanayin jin jikinta ko kaWan bai kai yanzu ba. Ki duba yadda ta

"rame ta lalace, raunin tsufa ya bayyana ™arara a jikinta. Ko tafiya ba ta iya yi ita kaWai fa sai an ri™e ta,"

"saboda Allah idan na mayar da ita a irin wannan halin da take ciki me mutanen gida za su ce a kaina?"""

Irin yadda yake jan numfashi yana saukewa a zafafe cikin damuwa shi ne abinda ya Wan so Waga mata

"hankali. Alal ha™i™a a yanzu kam shi ya bata tausayi ba halin da Innaye ke ciki ba. Don haka tayi shiru tana tunanin da zai samar mishi da mafita, duk da dai ba ta ™aunar cigaba da zaman su Innaye a gidanta saboda damuwarsa kaWai yasa ta cewa"

"""To ko dai za ka mata dabara ne kai tafiyarka Ofis ne ka ™yale su a gida? Idan bata ganka ba ai dole ta"

"ha™ura da zancen tafiya gida ayau Win. In yaso idan zan dawo gida sai in taho mata da wasu magungunan saSanin wanda take sha, duk da dai ba haka na so ba."""

"Da yake wayar da yake yi a ™ofar shiga Sangaren da Innaye take ne, ya buWe baki zai ba Bintu amsa"

"kawai sai ganin Zulaikha yayi ta fito tana ri™e da Innaye, sun shirya tsaf! Da alamun gajiya sukai da jiransa"

suka fito.

"Ransa a Sace ya galla ma Auta harara kafin yayi ma Bintu sallama a gaggauce, ba tare da ya bata amsa"

kan shawarar da ta bashi ba.

"""Me yasa kika fito da ita ba tare da nayi miki umarni ba? Ko an faWa miki na gama shirye-shiryen tafiya"

"ne...?"""

"""Yaya ba fa laifi na bane. Tun Wazu ita ta matsa min in fito da ita, da nace mata baka shirya ba sai cewa"

tayi mu fito ko a motan haya ne mu tafi. Ta rantse ta sake rantsewa da Allah ita kam ba ta ™ara kwana a

"gidannan."""

Sau uku yana buWe baki da nufin yin magana amma ya rasa ta cewa. Sai kawai ya juya zuwa tsakar gidan

"suka bi bayanshi, shi kaWai yake ta ™wafa yana jan tsaki saboda tsananin damuwa da ™uncin zuciya."

Direba yana kan wanke motar da za suyi tafiya a cikinta ganin fitowar su Innaye a dole ya dakata. Yadda

aka tarairayota yasa da saurin gaske ya kai hannu zai buWe ™ofar baya sai Hafiz ya riga shi buWewa.

Da sassarfa ya ™arasa ya karSe ta a hannun Zulaikha ya ™arasa da ita cikin mota ya zaunar da ita.

Idanunshi akan Zulaikha har lokacin bai saki fuskarsa ba ya ce

"""Shiga kusa da ita ki zauna, idan ta gaji da zama ki kwantar da ita a jikinki."""

"""To Yaya. Amma ban fito da kayanmu ba, bari in je in kwaso..."""

Da tsawa sosai a muryarsa ya katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"""Dallah shiga cikin mota zan je in kwaso muku. Kuma ina fatan kin haWa har da sauran magungunanta"

"da alluran da suka rage?"""

"""Eh."""

Ta amsa da sanyin murya. A zuciyarta kuma cewa tayi

"'Bala´a´´e, ka ci kanka kasha ba™in ruwa. Gidanka ne dai ko kana so ko ba ka so yau za mu bar shi.'"

Da sauri ta shige cikin mota ganin har lokacin bai daina aika mata da wani fusataccen kallo ba.

Kayansu gaba Waya a ghana most go Waya ne. Don tabbatar da bata manta da magunguna da alluran

Innaye ba sai da ya buWe jakar ya gansu sannan ya maida jakar ya rufe ya Wauka zuwa mota.

"Saboda irin jan ™afar da yai tayi za su tafi baza su tafi ba, ya shiga cikin Sangarensu ya ™i fitowa akan"

"lokaci kuma shi ba wani takamaimai abu yake yi ba basu bar gidan ba sai ™arfe goma da rabi na safe. Tun da Hafiz yayi aure, zuwanshi ™auye ya kwana Waya bai fi sau bakwai ba."

"Duk sa'adda za su tafi asubanci suke bugawa yadda za su isa da wuri, ya gama duk abinda zaiyi zuwa"

"la'asar su Wauko hanyar komawa Abuja, komai dare a gida yake kwana."

Ko a yanzu direba ya zaci irin waWancan tafiyoyin da suka saba yi ne na yini Waya. Don haka ya ™ure

manejin mota yana ta zabga gudu kamar masu shirin barin ™asar.

"Ko da suka isa Kaduna baiyi niyyar tsayawa ba sai da Hafiz ya ce mishi ya tsaya ya sai ma su Innaye abinci,"

a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar azahar a wasu masallatai.

"Da yake ko bayan an isa Kaduna tafiya ce mi™a™™iya zuwa ™auyen Fa™o, ga kuma tsiya irinta ™arfen"

nasara da ba ta da tabbas. Bayan tsayawa gyara da suka yi a garin Kujama basu isa Fa™o ba sai La'asar.

Sun isa ™ofar gidansu Innaye daidai lokacin da aka fito sallar la'asar a babban masallacin da yake ™ofar

gidan.

'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un'

Hafiz ya faWa a zuciyarsa hankalinsa a tashe.

Ko kafin ya waiga yayi ma Zulaikha umarnin ta dakata da buWe ™ofar sai mazan da suke fitowa daga

"masallaci sun ragu har ta riga ta buWe ™ofar Sangarenta, ta zura ™afafunta zuwa waje, fuskarta cike da matsanancin farin ciki na ganinta a ™ofar gidansu."

Kafin ma ya kira sunanta har ta fita waje. Bai ™ara tabbatar da rashin hankali da wautar Zulai ba sai da

yaji ta buWe murya tana ™wala ma mahaifinsu da yake tsaye suna magana da Ladan kira.

"""Baffah... Mun dawo."""

Hakan bai ishe ta ba sai da ta ™ara da

"""Zo ka ga Innaye ba ta da lafiya sosai."""

Wannan maganar da ta faWa shi ya dawo da hankalin gaba Waya mazan da suke tsaye a gurin zuwa kan

"motar Hafiz. Kun san mutanen ™auye da kara, Wuuuuu kusan gaba Waya suka yo gurin motar."

Babu abinda ke fita a bakunansu sai

"""Assha! Subhanallahi! Hajiya Rahina jikin ya motsa kenan."""

Tsananin damuwa da Sacin ran abinda Zulaikha ta aikata yasa idanun Hafiz suka cicciko da hawaye. Ba

"shi da yadda ya iya, haka nan ya buWe ™ofar Sangarensa ya fita waje ya tarbi mahaifinsa da sauran mutanen gurin da suka rufu a kanshi suna mishi jajen ya mai jiki? Haka nan yake ta amsa musu cikin"

rashin nutsuwa da kwanciyar hankali.

"Bai san Yaya aka yi ba yana cikin mazan nan sai ganin matan gidansu abokan zaman Innaye yayi sun fito,"

"suna sanye da zumbula zumbulan hijabai, biye a bayansu Zulai ce tana musu jagora zuwa gurin motar"

Sangaren da Innaye ke kwance.

"Kafin ya ce wani abu har Zulai ta buWe musu ™ofar, su kuma suka tarairayo Innaye da gajiyar zaman mota"

da rashin ™arfin jikin da take fama da shi ya ™ara ramar da ita. Suna ri™e da ita sannu a hankali suke amsa

gaisuwar mazan da suke mata ya jiki har suka shigar da ita cikin gidan.

"Kamar wutar daji, haka zancen gaggarumin rashin lafiyar da Innaye ta dawo da shi ya fantsama a ™auyen"

Fako cikin kankanin lokaci.

"Suna tsaye a ™ofar gida, bayan watsewar maza masu jajantawa yana yi ma mahaifinsu da yan'uwansa"

biyu ™arin bayanin ciwon Innaye bazai iya ™ididdige yawan matan da suka shiga cikin gidan duba jikin

Innaye ba.

Kun san ™auye da kara da mayar da al'amarin wani nasu. Balle kuma Innaye da ta kasance mace ta

"mutane, kowa

9 / 50