Advertisements
Chapter 43 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 50

126K to 129K   out of 147.7K words

™awa."""

"""Kar ki damu Bintu. Kin cancanci fiye da haka a gurina."""

"Da haka suka rabu, zuciyar Bintu cike da karsashi da ™warin gwuiwa, ita kuwa Raudha zuciyarta cike da"

"fargaba, da addu'ar Allah yasa Hafiz ba sakin Bintu yayi ba. Tunda da kunnenta ta ji maganar takarda, to wace takarda ce kuwa za ayi maganarta idan ba ta saki ba?"

"Bintu tana shiga layin gidansu da mota, ta hangi motar Hafiz na fitowa daga cikin layin. Lokaci Waya"

zuciyarta ta ™ara ™untata da Sacin rai.

'Kenan zancen Raudha ya tabbata?'

"""Uhmmm! Namiji kenan! ˜udan zuma ga za™i ga harbi. Na rantse da Allah ko me za kayi Hafiz kai da su"

"Umma baku isa ku hana ni ™watar ´ancina ba a matsayina na uwa."""

"Tayi maganar a fili cikin masifa, ko da suka zo gitta juna da™yar ta iya dannar zuciyarta bata buWe gilashi"

ta watsa mishi da™uwa ba.

"Ta ja motarta a guje ta wuce shi ma ya cigaba da tafiya, ko Wan horn Winnan babu wanda ya latsawa juna,"

kamar dai ba su ne masoyannan da suke bala'in ™aunar junansu ba.

"Ko da ta isa gida, da farko ta shiga ne da wani irin fitinannen izza da jiji da kai. Sai da taga ba a cikin falon"

"mahaifiyarta bane Aunty Sadiya da sauran yayyenta maza uku suke zaune. Suna cikin falon mahaifinta ne, kuma ™arin Waga hankali a gareta shi ne idanun magahaifiyarsu da Aunty Sadiya ya yi jajur, alamu ™arara da ke nuna sun ci kuka sun gode Allah."

"Tun daga nan jikinta ya fara sanyi. A Warare ta nemi kan kafet ta tsuguna, bayan ta yi sallama babu"

wanda ya amsa mata a cikinsu.

"""Daddy..."""

Wani gigitaccen tsawa da mahaifinta ya daka mata yasa bata san sadda ta zame daga tsuguno tayi

"zaman ´an bori a ™asa ba. Lokaci Waya idanunta suka kawo ruwa, lallai wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka."

"Bata daddara ba da tsawan da yayi mata ba, don ta sha alwashin baza ta taSa bari shirunta ya ja Hafiz ya"

"ci galaba a kanta ba, cikin rawar murya da saurin baki ta sake cewa"

"""Daddy don girman Allah ka bari inyi muku bayanin gaskiya..."""

"""Ba ma bu™atar wani bayani na gaskiya daga bakinki Bintu."""

"Ya sake katse ta a karo na biyu, da yanayin magana mai bayyana Sacin rai a fili."

Kafin ta amsa ko ™o™arin kare kanta ya cigaba da cewa

"""Mun ji gaskiyar zance daga bakin yayyen mijinki biyu da aka kira a waya aka saka su a handsfree."

Sannan Mun ji rekodin Win muryarki jiya da kika je tsakiyar Wakin sarkuwarki a can ™auyensu kika yi mata cin mutunci na ™arshe ita da ´a´anta. Sannan mun ji bayanin yadda kika je gidan ™anwar mijinki yau za kiyi mata duka. Daga nan Sangarenki kuma Yayarku ga ta nan ta kora mana bayanin duk irin rashin

mutuncin da taga kin yi ma dangin mijinki lokacin haihuwar Wanki. Wannan shi ya ™ara tabbatar mana da

"gaskiyar maganganun mijinki da ´an'uwansa. Don haka ki ri™e bayanin gaskiyarki, wata ™ila za tayi miki"

"amfani a gaba. A ™arshe dai ungo wannan."""

Ya ™ar™are maganar haWe da Waukar wata farar nannaWaWWiyar fallen takardar da tun shigarta cikin falon

"bata lura da ita ajiye kusa da shi ba, sai yanzu da ya Wauka ya mi™a mata."

"Da farko ™in karSa tayi, sai da Yayanta Faru™ da yafi sauran zafi ya ™unduma mata ashariya haWe da"

"yun™urawa zai mare ta sannan ta karSi takardar a tsorace. Lokaci Waya Jikinta ya Wauki rawa, kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi lokacin hunturu."

Duk da bata buWe takardar ta ga ko ta mece ce ba haka kawai jikinta ke bata babu alkhairi ko kaWan

tattare da wannan takarda.

Yayanta Abubakar ne ya fara magana shi ma da nashi salon Sacin ran.

"""Kin bani kunya Bintu. Na rantse da Allah ban taSa tsammanin irin wannan munanan halayen daga"

"gareki ba. Haba!! Sai kace wacce bata yi ilimin boko da Arabi ba? Ta ina kika taSa ji mata ta fi uwa da ´an'uwa? To bari in sake tuna miki, ana canja mata, amma ba a taSa canja uwa da ´an'uwa. Don haka kin ga yanzu ga sakamakon ™o™arin raba miji da danginsa nan kin karSa, zai canja ki, amma bazai taSa"

"canja ´an'uwansa ba. Dubi nan"""

Wayarsa ya buWe ya lalubo hoton Invitation card Win Auren Hafiz da Karima ya matsa har kusa da inda

take zaune tana rawar Wari ya aje mata a cinyarta.

"Duk yadda ta so ta runtse idanu don kar ta karanta hoton I.V Win kasawa tayi, raWau idanunta suka sauka"

"akan hoton, cikin ™an™anin lokaci ta haWa ba™a™en ta karanta sunayen da ke manne a jikin hoton."

"Wata wawuyar bugawa zuciyarta ya yi, cikin ™an™anin lokaci ta fara jan numfarfashi da™yar, kuma sama-"

sama kamar mai cutar athma. Hannunta shi ya jagoranci umarnin zuciyarta gurin warware fallen

takardar da ke dam™e a hannunta don ganin me ta ™unsa.

"_"".... Hafiz Aminu Fa™o na saki matata Fatima Bintu saki Waya...""_"

"Kalaman da suka manne a cikin idanun zuciyarta kenan, kuma kalaman da suka ™ara assasa hauhawar"

bugawar zuciyarta fiye da misali.

"A haukace, cikin Wimuwa, gigita, ficewar hayyaci Bintu ta mi™e tsaye a zabure. Tayi taku Waya, biyu, uku,"

sai kuma ta zauna daSas! Ta Waga idanu a gwalale ta kalli Ummansu da Aunty Sadiya. Sai kuma kamar tsikarin basir ta ™walla wani gigitaccen ihu! Sai kuma ta Wauke Šif! Kamar an saka seletef an Waure mata baki.

"Da saurin gaske ta sake mi™ewa tsaye, ta tattare siket Win jikinta za ta yanka da gudu Yayanta Aliyu da"

"yake mata kallon wacce gigita yasa ta haukace yayi gaugawar dam™o kafaWunta, da ™arfin gaske ya"

girgiza kafaWunta haWe da ™walla kiran sunanta da ™arfi.

"""Yaya... Hafiz... Ya sake ni... Na mutu..."""

Daga faWin haka sai ta tafi luuuu ta kife a kafaWunsa a sume.

********

Tabbas da gaske ne... A yayinda saki ya shiga tsakanin ma'aurata biyu wanda ya kasance bai da gaskiya

shi zai fi jigatuwa. Irin haka ne ya kasance a Sangaren Bintu. Shi kuwa Hafiz kwanakin da suka biyo baya harkokinsa yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

"Shirin aurensa yake yi a nutse, rashin Bintu a gidanma sai ya bashi damar cin karensa babu babbaka."

"Soyayya mai lasisi kuma irin ta bugawa a jarida suke sha shi da Karima, a gefe guda kuma Zulaikha tana"

™ara ™arfafa masa gwuiwa akan duk wasu shirye-shirye nasa.

Sai a yanzu ne ya fahimci ma'anar karin maganar da Aunty Balira take yawan faWa masa na *RANAR

"NAKA SAI NAKA...*, In banda Zulai ta kasance nasa ta ina ™aramar yarinya kamar Zulai da ko haihuwa"

bata yi ba za ta karSi yayen Aadil?

Sai ga Hafiz duk yadda yake yawan faWi a baya cewa Zulai ba ta da hankali yanzu ba shi da abokiyar

"shawarar da ya wuce Zulai. Tsarin yadda za'a fasalta gidansa a canja masa tsari, da yadda za'a fitar da"

gurin saukar ba™i ´an'uwansa duk da ita yayi shawara.

"Haka Sangaren haWa kayan akwati, ba tare da jin zafin kuWi ba haka ya dinga antaya mata manyan"

kuWaWe tana shiga kasuwa ita da Hibba da Karima suna haWo kayan akwati. Ba tare da ™yashi ba kuwa

"Zulai ta dinga zaSo komai mai bala'in tsada, cikin ™an™anin lokaci ta haWa mishi akwatuna guda goma sha biyu cif!"

Sai daga baya ne ma da Mummy ta ga kayan tayi faWa kamar za ta ari baki. Ta rage kaya masu yawa har

akwati biyu ta dam™a ma Zulaikha da cewar lallai ta aika ma Innaye da su Aunty Balira su samu na cin

buki.

"Ko da Hafiz yaje gidan, Zulaikha ta faWa mishi yadda aka yi kuma ta nuna mishi kayan ba ™aramin kimar"

Mummy ne ya ™aru a idanu da zuciyarsa ba. A ransa yake ji lallai yanzu ne fa zaiyi aure.

Idan ya kalli Aadil kuwa farin ciki da nishaWinsa ™ara ninkuwa yake yi. Duk yadda Bintu take ji tana

"gatanta yaron sai dai kawai ace ita ta haife shi, amma ko rantsuwa yayi babu kaffara an fi gatanta shi a gidan Mummy fiye da gurinta."

"Kuma wani abun burgewa shi ne yaron sam yanzu ba ya ™wuiya, ga wani wayau da ™iba, kyau na"

"musamman da yaron ya ™ara. Ba shi gurin Mummy, ba shi gurin Karima, ba shi gurin Hajja, balle kuma"

Zulaikha da take riritasu shi da Imam kamar su kaWai ne ´a´aye a duniya.

********

Tsawon sati biyu kenan da faruwar al'amarin amma Bintu ta kasa komawa dai-dai. Tun iyayenta suna

"hantarar ta, suna share al'amarinta, suna watsi da damuwarta, har sun zo sun fara tausaya mata. Amma a Soye, saboda dukkansu sun san irin matsanancin soyayyar da take ma Hafiz."

"Duk wanda yasan Bintu a baya, idan ya ganta yanzu abu na farko da za'a fara tambaya shi ne"

"""Ta yi rashin lafiya ne?"""

"˜ara auren Hafiz, da sakin da yayi mata na bagatatan, wasu abubuwa ne da ko ana ya™in duniya na uku a"

zamantakewar aurensu bata taSa tsammanin za su gitta a tsakaninsu ba.

Ta daWe da gama sakankancewa Hafiz na ta ne ita kaWai. Don ita kaWai aka halicce shi kamar yadda aka

halittota don shi kaWai.

Duk da tun kafin faruwar wannan al'amarin zamantakewar na su ya Wan fara tangal-tangal sanadiyyar

sakaci da kasa danne zuciyarta ita bata taSa tsammanin zai iya kallon wata ´a mace da idanun so balle

har ya nemi sama mata sarari a filin zuciyarshi ba.

Saki kuwa... Idan ta tuno wannan kalmar wasu sababbin hawaye ne ke sake Salle mata kamar an buWe

famfo.

'Ita Bintu Hafiz ya saka? Ita? Ita Bintu fa?'

Zuciyarta na cika da tantamar anya kuwa Hafiz ne da kanshi ya iya sakinta? Ko dai wani mai ba™in ciki da

aurensu ne ya shiga rigar Hafiz ya tafka wannan ™atoton kuskuren? Sai ta yi kamar baza ta yarda da sakin ba kuma sai ta tuna ai ranar da abin ya faru ta ga ficewar Hafiz daga layinsu. Kuma wanda ya bata takardar sakin wani mai mutum ne mai muhimmanci a rayuwarta da bazai taSa yi mata ™arya don ya

kassara ta ba.

"A cikin waWannan kwanakin ™unci da raWaWin, ta yi Allah ya isa ga Innaye da ´a´anta mata ya fi baki"

dubu!! Domin ita a ganinta duk su ne ummul-aba'isin faruwar waWannan munanan al'amura a gareta.

"A karo na barkatai, ta yi juyi akan gadon, zuciyarta cike da ™unci da matsanancin damuwa. Sannu a"

"hankali ta fara jan shesshe™ar kuka kamar yadda ta saba, tana yi tana taushe bakinta don kar Mashku ta"

ji kukan da take yi.

"A karo na farko, tun bayan faruwar al'amarin da tsawon dararen da ta kwashe tana raba biyu bisa uku da"

kuka Mashkura ™anwarta da suke kwana Waki Waya tayi mata magana a tausashe.

"""Aunty Bintu a ganina kukan nan da kike kwashe tsawon lokaci kina yi ko wane dare, ke baki yi barci ba,"

ni baki barni na yi nutsattsen barci ba bazai taSa miki magani ba. Why not baza ki Sata lokacin kukan

"akan dadduma kina kaima mahaliccin sammai da ™assai kukanki ba...?"""

"""Mashku... Don Allah ki faWa min. Aduk cikin wannan al'amarin ina abin saki? Me nayi ma Hafiz da zai"

"sake ni? Me nayi masa?"""

Ta katse Mashkura da jerin tambayoyin muryarta na fita da matsanancin kuka.

Abu Waya da Mashkura ta fahimta a maganganun Bintu shi ne har yanzu ita bata yi da na sanin abinda

"tayi ba. Kamar ma laifin Wungurungum ta kwashe ta Wora kan Hafiz ne da danginsa, bayan kuma ita ke da laifi kaso casa'in da biyar bisa Wari."

"Kafin ta amsa Waya daga cikin tambayoyin Bintu, lalubawa tayi a kusa da filonta ta Wauko wayarta ta"

"duba lokaci, ™arfe uku da minti arba'in na dare. Barci ne sosai a idanunta, don haka ta katse dogon"

maganar da Bintu ke neman jan ta da shi ta hanyar cewa

"""Uhmmm! Ba ni da amsar Waya daga cikin tambayoyinki Aunty Bintu. Ni dai shawara kawai na ba ki, da"

"ki dinga Sata tsawon lokaci kina rusa kukan da bazai miki magani ba, gara ki dinga Waukan lokacin kacokan kina kai ma Allah kukanki. Ko babu komai za ki samu sanyin zuciya da nutsuwa. Allah ya tashe"

"mu lafiya."""

Daga haka bata sake ce mata komai ba ta juya mata baya.

"Da yake Bintu ba ta daga cikin irin matannan da ibada ya dame su, duk da wannan shawarar da ™anwarta"

"ta ba ta bata yi amfani da shi ba. SharSen Kukanta ta cigaba da yi, tana haWa da jan ajiyar zuciya tana saukewa, ta Wauki tsawon lokaci a haka har zuwa sadda gwanin iya sata da taimakon shaiWan yayi awon"

"gaba da ita, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallah a wasu masallatai."

"Washe gari, kamar yadda Raudha ta saba zuwa gidan duba jikin Bintu duk bayan kwana biyu, misalin"

™arfe huWu na yamma tayi ma gidan dirar mikiya.

"A waWancan kwanakin, duk zuwan da take yi bata taSa samun damar yin nutsattsen hira da Bintu ba."

"Cikin kuka ta faWa mata Hafiz ya sake ta, sannan kuma zai ™ara aure. Daga haka har ta bar gidan ba ta"

"™ara samun kan Bintu balle har suyi wata doguwar magana, sai dai ta gama zamanta da maWaukakin"

damuwa a fuskarta daga bisani tayi ma Umma sallama ta tafi.

"A yau, ko da ta isa gidan ta yi mamakin samun Bintu cikin ´ar nutsuwa kaWan. Ta yi wankanta tsaf, duk"

"da dai babu ko Wigon kwalliya a fuskarta. Wayarta ne ma a hannunta tana dannawa, fuskar nan a Waure tamau."

"""Raudha... Ashe don tsabar wula™anci tun ranar da muka je Fa™o misalin ™arfe biyar da rabi na yamma"

"Hafiz ya turo min sa™on saki ta text message..."""

"""Da gaske kike yi?"""

Raudha ta jefa mata tambayar da mamaki a murya da fuskarta.

"Bata iya amsawa ba, sai wayar ta mi™a mata tana nuna mata sa™on."

"""Uhmmm! Allah ya kyauta... Sai ha™uri kawai."""

"Raudha ta faWa jikinta a sanyaye, bayan ta gama karanta sa™on."

"""Ni yanzu kin san menene damuwata?"""

"""A'a! Sai kin faWa!"""

Raudha ta amsa mata.

"""Wace ´ar iskar matsiyaciya tsinanniya annamimiyar yarinyar ce za tayi gangancin aura min miji uban"

"´a´ana? Duk tunanina ya ™u™e, na rasa gane wace Karimatu ce? Ko dai wata ba™auyiyar ce matsiyatan danginsa da basa ™aunar Allah da Ma'aiki SAW suka sake haWa shi da ita..."""

"""Uhmmm! Za kiyi mamaki idan na ce miki Nurse Karima ce, ´ar gidan Hajiya Saudah da kike kira"

"Mummy sama Mummy ™asa..."""

"""Mmmmm me kika ce Raudha? Dddddddda gaske kikkkkkkkeeee yi?"""

Bintu ta tambayeta da wata fitinanniyar in'ina a muryarta saboda tsananin tashin hankali.

"""Wallahi da gaske nake yi. Lamarin maza ba sai dai a barsu ba Bintu? Abinda ya kawo ni gidanki kenan"

"ranar sai na tarar da ke cikin tashin hankalin Wauke Aadil da Hafiz yayi."""

"Gyara zama Raudha tayi, ta kora ma Bintu labarin duk abinda ya faru wancan ranar a asibitinsu gaban"

idanunta.

"""Karima dai Raudha? Karima? Yanzu sakayyar da Mummy za tayi min kenan? Ni ce fa na shiga na fita"

"har na sama mata aiki a asibitinmu, ashe sakayyar da za suyi min kenan?"""

Ta jera ma Raudha tambayoyin cikin rawar murya da tashin hankali.

Kafin Raudha ta amsa ta cigaba da cewa

"""Saboda Allah me Karima take da shi wanda ni bani da shi da har za ta Wauki hankalin Hafiz..."""

"""Uhmmm! Bintu kenan! Sau nawa ina faWa miki Namiji Wan kunama ne ga za™i ga harbi kina saka"

"auduga ki toshe kunnenki? Ko da yake yanzu da layi ya biyo ta kanki ai za ki ™aras a gaba."""

Raudha ta katse mata sambatun da take yi hankalinta a tashe kamar wacce ™wa™walwarta ya fara

taSuwa.

"""Bar tuna min Raudha! Don girman Allah ki bar tuna min."""

"Bintu ta katse ta da sauri, da murya mai bayyana matsanancin takaicin da zuciyarta ke ciki. Babbar"

"yatsarta ta sanya ta Wauke wasu zafafan hawaye da suka sake taruwa a kwarmin idanunta. Da asubahin ranar tasha alwashin in Allah ya yarda za ta danne zuciyarta baza ta sake yi ma wannan mummunan al'amarin kuka ba, amma duk yadda ta so tsayar da fitar hawayen ta kasa, shi yasa take saurin share"

hawayen tun kafin su gangaro zuwa kumatunta su saka ta azumin kaffara.

"Nannauyar ajiyar zuciya ta ja ta sauke, a hankali ta cigaba da cewa"

"""Abinda ya wuce mu barshi a matsayin wanda ya wuce Raudha. Ilimi Waya da na ™aru da shi a cikin"

"kwanakinnan shi ne, duk mazajen duniya halayensu Waya, kuma a kullum sauyawa suke yi kamar wahainiya. Lallai da gaske ne duk matar da ta Wauki namiji uba za ta mutu marainiya... Yanzu dai mafita nake nema da gaggawa... Ya zanyi Raudha? Ya zanyi? Wallahi zuciyata zafi da tafarfasa take min kamar"

"za ta babbake... Don Allah ki taimaka min"""

"""Kul! Kul!! Kul Bintu!! Kar ki kuskura ki bari zuciyarki ta buga akan namijin da idan kika mutu yau, ya yi"

"tsananin daWewa ne yayi wata shida zai manta da shafinki ya buWo na wata kamar yadda yake shirin faruwa da ke a yanzu."""

"Ta yi shiru tana mayar da numfashi, sannan ta cigaba da magana a hankali, tana yi tana waige-waige,"

alamun duk abinda za ta faWa ba ta so kowa ya ji

"""Akwai mafita... Amma sai kin nutsu sosai kin saurare ni da kunnen basira..."""

Jikinta a sanyaye ta tari numfashin Raudha da cewa

"""Allah yasa dai mafitar ba na bin hanyar da Hajiya Rabi ta faWa min rannan bane."""

Sai da Raudha tayi dariya sannan ta amsa da

"""Wannan old version kenan ai. Ita ma don tsohuwar yayi ce shi yasa har yanzu take ganin idan ba ta"

hanyar malamai da bokaye da ´an tsibbu ba babu hanyar da za ta bi wajen ladabtar da ŠA NAMIJI har

"yayi laushin da zai rusuna mata..."""

"Fitowar Mashkura daga banWaki, wacce shaf Bintu ta manta da shigarta daf da Raudha za ta shigo cikin"

"Wakin, shi ya katse Raudha daga maganganun da take yi masu Wauke da zallar cika baki."

"A tsorace suka kalli Mashkura, itama ta Waga idanu tayi musu wani kallo mai bayyana ™as™anci ™arara."

Sannan ta Wauki hijabin sallarta ta zura a jikinta ta fice daga Wakin.

Da damuwa sosai a fuskar Raudha ta ce

"""Na shiga uku ! Amma dai Bintu baki kyauta min ba. Me yasa tun Wazu baki faWa min Mashkura tana"

"bayi ba kika barni ina ta zuba zance? Allah dai yasa bata ji maganganun da nake yi ba..."""

"""In Allah ya yarda ma bata ji ba. Wallahi sam na manta ta shiga wanka sadda kika shigo, kuma kin santa"

"da bala'in daWewa gurin wanka kamar wacce za ta canja halitta. Yanzu dai ina ga ki tashi kawai ki tafi, ma"

"™arasa zancen da muka fara yi a waya..."""

Numfashin maganarta ne ya Wauke Wif lokacin da Ummansu ta shiga cikin Wakin da wata iriyar

"murtukakkiyar fuska, kamar bata taSa dariya ba."

A Warare duk su biyun suka kallete da yanayin rashin gaskiya. Da saurin gaske Raudha ta yayimi jakarta

da mayafi ta mi™e tsaye.

"""Bintu bari in wuce, sai na sake le™owa..."""

"""Ki le™o ina Raudha?"""

Ummansu ta tambayeta cikin tsawa.

"""Munafuka algunguma, dama ke ce kike hure mata

43 / 50