Advertisements
Chapter 23 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 50

66K to 69K   out of 147.7K words

salin-alin na yi al™awarin zan bi duk hanyar"

"da ya kamata gurin wanke ka a gaban Baffa da Innaye. Bazan taSa bari su ga laifinka ba, Wallahi da gaske nake yi..."""

"""Za ki koma gida, amma ba yanzu ba. Don haka gara ma ki rufe min tsattsamar bakinki tun kafin in"

"canza shawarar da na yanke. Fito muje."""

Ya sake ba ta umarnin da tsawa a muryarsa.

"Tana hawaye, ta fito daga cikin motar ta tsaya Wan nesa da shi. Shi ya buWe motar ya fito mata da jakar"

"kayanta, ya zage zip Win ya fito mata da takalminta ya bata umarnin ta sa a ™afafunta. Bayan ta saka ya"

"sake umartarta da ta gyara hijabinta da yake a baibai, har ta gama gyara hijabin hawayen idanunta basu"

daina sauka a guje kamar an buWe famfo ba.

Hannu yasa a aljihunsa ya zaro kuWi masu Wan dama za su kai dubu ashirin ´an Wari biyar-biyar ya dam™a

mata a hannunta.

"""Ki ri™e wannan, ko za ki bu™aci wani abun ba ni a kusa. Nan Win gida ne na mutanen kirki da karamci"

"ba na so ki ishe su da bani-bani. Kina ji na?"""

A raunane ta Waga mishi kai alamar ta ji.

"Hannunsa ya sake cusawa a aljihu ya zaro wata farar takarda da take a nannaWe, Wan shiru yayi yana"

kallon takardar. Sai kuma ya sake naWe takardar sosai ya mi™a mata

"""Ki Soye wannan a cikin kayanki, idan kin samu nutsuwa kin dawo cikin hankalinki sai ki karanta..."""

"""Takardar mece ce Yaya?"""

Ta tambaye shi tana Wan jujjuya takardar a hannunta.

"""Muhimman bayanai ne waWanda ba ni da lokacin da zan iya Satawa wajen karanto miki su da bakina."

"Allah yasa dai su Baffa basu yi asarar kuWin tara ba, domin da turanci na rubuta. Wuce muje."""

"Jikinta a sanyaye ta bi bayansa, ranta a Sace da ba™ar maganar da ya gwaSa mata da ya ce anyi asarar"

"kuWin tara. Ta sani tabbas asarar kuWin taran aka yi, domin baza ta iya karanta dogon rubutu da turanci"

ba. Sai a wannan lokacin Mashkura da al™awarin da tayi mata na koya mata karatun turanci ya faWo mata a zuciya.

"'Ba komai. In da rai, da rabo.'"

"Ta ayyana hakan a zuciyarta, sannan ta fara ™o™arin tsayar da hawayen da take yi ganin har sun isa ™ofar"

gidan ya fara ™wan™wasawa.

"""Waye?"""

Muryar namiji dattijo ya tambaya daga cikin gidan.

"""Baba ni ne. Hafiz ne."""

Ya amsa da girmamawa.

Cikin sauri aka buWe ™ofar daga ciki. Daga yadda dattijon yake gaisar da Hafiz da girmamawa sosai har

yana Wan du™awa ™asa yasa ta fahimci Mai gadin gidan ne.

"""Ina kwana."""

Ta gaisar da tsohon a mutunce da sha™a™™iyar murya bayan sun gama gaisawa da Hafiz. A daraje ya

"amsa mata, sannan ta bi bayan Hafiz da taga ya nufi cikin gidan kai tsaye."

Daga yadda yake kutsawa lungu da sa™o na gidan har suka isa Wan madaidaicin falon matar gidan yasa ta

"gane Yayanta ba ba™o bane a cikin gidan. Ita dai tana biye da shi a baya, da alamun gajiya ™arara a"

fuskarta.

"Ko da ya zauna akan kujera ita a ™asa ta zauna, ta nannaWe ™afafunta a cikin hijabi, hankalinta a tashe. Ta"

"rasa dalilin da yasa sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan ba™on muhallin da ya kawo ta, don dai"

kawai ba ta da yadda za tayi ne.

Sallamar da matar gidan tayi ta shigo cikin falon yasa ta Waga kai a hankali ta saci kallonta. Kyakkyawar

"dattijuwa, wacce gayu, gyara, cin abinci masu gina jiki suka taka muhimmiyar rawa gurin Soye"

"shekarunta. A haka idan aka bar Zulaikha za ta iya rantsewa da Allah Aunty Balira ta girmi matar, amma kuma a zahirin gaskiya ba haka bane."

"Tana waWannan tunane-tunanen har matar ta zauna, suka gaisa da Hafiz. Sai da Hafizu ya katse mata"

tunani ta hanyar kiran sunanta sannan ta iya gaisar da matar.

"""Lafiya ™alau. Ya kike?"""

"Matar ta amsa mata a mutunce, sannan ta ™ara da tambayarta lafiyarta, da fara'a sosai a fuskarta take"

"kallon Zulaikha, kamar dama can daWe da saninta."

"""Lafiya ™alau nake."""

"Ta amsa cikin sanyin murya, tana jin Wan nutsuwa kaWan a zuciyarta da ganin fara'ar da ke fuskar matar."

Bata yi kama da mugaye ba sam!

"""Kar dai ka ce min kaima yau baka je Ofis ba?"""

Matar da Hafiz ke kira Mummy ta tambaye shi bayan ta mayar da hankalinta kan shi.

"Šan sosa ™eya yayi, kafin ya amsa da"

"""A'a! Na je Mummy. Wani Wan rikici ne ya mayar da ni gida. Don Allah alfarma nazo nema idan bazan"

"takura miki b..."""

"""Dalla rufe min baki. Ashe Wa yana neman alfarma a gurin wacce take kamar mahaifiyarsa? Me kake"

"bu™ata Hafiz? Feel free and ask me anything, in sha Allah bazai gagara ba."""

"Duk da ya san babu abinda zai nema gurin Hajiya Balkisu ta gagara yi mishi, ™ara tabbatar mishi da hakan"

da tayi a yanzu ba ™aramin daWi da nutsuwa ya ™ara samu a zuciyarsa ba.

"""Na gode Mummy."""

A nutse ya cigaba da yi mata bayanin abinda ya kawo shi gidanta a daidai wannan lokacin

"""Wannan yarinyar da kike gani, ™anwata ce, Sunanta Zulaikha. Jiya da na tafi gida nazo da ita, aurenta"

nan da sati uku ne sai aka samu matsala daga can Sangaren mijin ya ce ya fasa.

"To kin san lamarin ™auye da ™ananun maganganu, wannan dalilin ne yasa Baffana ya ce in taho da ita"

"nan ko za ta samu nutsuwa. To kasancewar tun asali babu shiri tsakaninsu da Bintu, kwananta Waya"

"kawai har sun fara samun saSani, rikicin ne yasa har sai da na tsallake ayyukan Ofis na koma gida... Kawai don dai a samu maslaha, shi yasa na Waukota na kawo ta nan ta Wan kwana miki biyu."

"Baza ki samu matsala da ita ba in sha Allahu, duk wasu aikace-aikace za ta taya ki. Da farko na yi tunanin"

"in kai ta gidan Abba Lurwanu sai kuma naga kamar an gudu ne ba'a tsira ba, daga cikin gidan baza'a rasa wanda zai kira Baffa ya faWa mishi halin da ake ciki ba."""

"Zulaikha dai kanta a ™asa, zuciyarta cike da ba™in ciki da takaicin yadda saboda tsananin ™iyayyar da Yaya"

"yake mata ba ya iya jingina mata matsayin matarsa. DaWin abin ba shi kaWai yae ™in auren ba, ita kanta ta tsani auren, kila ma fiye da yadda ya tsana. A yadda take ji gara ta ™are rayuwarta babu aure da dai ace ta tabbata matsayin matarsa ba ya son ta ba ya ™aunarta. Saurin kawar da tunanin tayi, lokacin da ta ji"

Mummy na cewa

"""Allah sarki. Babu komai in sha Allah Hafiz, ka san lamarinmu na mata sai ha™uri. Kuma na ji daWi sosai"

"da baka bari ka samu saSani da matarka akan ™anwarka ba, tunda dai ko wacce tana da Sangaren muhimmancinta da ha™™inta da yake wuyanka. Ka barta anan Win, kuma ba kwana biyu ba, iya tsawon satittika ko watannin da su Baffa suke so tayi ka barta tayi anan Win. Ba mu da damuwar hakan in sha"

"Allah."""

Da murmushi a fuskarta ta mayar da kallonta kan Zulaikha ta ce

"""Zulaikha? Za ki zauna nan tare da ni ko?"""

"""Eh Mummy."""

Ta amsa a hankali.

"""Yauwa! Kin ga nima ba ni kaWai bace a gidan, akwai mahaifiyata Hajja, da Yayanku Fadil, da ™anwarsa"

"Kareema, sai yaron Fadil mai suna Imam. Ko da na tafi Ofis i'm very sure zaman kaWaita bazai dame ki ba. Kin ji ko? Ki saki jikinki kamar kina gidanku. Kuma ina fatan daga Sangarenki baza ki kira su Baffa ki faWa"

"musu Yayanki ya canja miki muhalli ba?"""

"""Eh! In sha Allah bazan faWa musu ba."""

"""Yauwa! Madallah! Hafiz za ka iya tafiya."""

"Godiya mai yawa ya sake yi ma Mummy har sai da ta nuna mishi Sacin ranta kafin ya daina godiyar,"

sallama yayi mata. Ko kallon Zulaikha baiyi ba ya fice daga gidan.

"Mummy da kanta ta shiga kicin ta kawo ma Zulaikha lafiyayyiyar sakwara miyar agushi, wacce ta ji"

naman rago zu™u-zu™u a cikin miyar. Sannan ta kawo mata ruwa da lemu ta ajiye mata a gabanta.

"""Baby ki ci abinci, idan kin gama ga kicin can ki shiga da farantan ciki. Ga kuma Waki can na tsakiya daga"

"Sangaren dama, ki shiga ciki ki ajiye jakar kayanki, akwai banWaki a ciki sai kiyi alwala, daga yau nan ne"

"Wakinki, kin ji ko?"""

"""To Mummy, na gode! Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ™ara girma."""

"""Ameen. To ni bari in shiga ciki inyi sallah."""

"""To Mummy! A fito lafiya."""

"Idanunta na kan matar da a zuciyarta take jin nutsuwa da ita har ta Sace ma ganinta. Kafin ta ci abincin,"

"sai da ta shiga Wakin da aka nuna mata a matsayin nata ta ajiye jakar kayanta, ta shiga banWaki ta wanko hannuwanta duk biyu ta fito zuwa falo ta zauna a gaban abincin."

"""Uhmmm! In ba gayu irinna ´an birni ba ta ina sakwara zai ciwu da cokali?"""

"Ta tambayi kanta a fili tana Wan murmushi, bismillah tayi, ta gutsuri sakwarar ta Webi miya ta kai bakinta."

"""Uhmmm!"""

Ta faWa tana jin wani masifaffen daWi mai barazanar tsinke mata kunnuwa.

"""Allah na gode maka da ka rabo ni daga gidan Bintu. Ko babu komai daga irin tarbar da aka min anan"

"na san in Allah ya yarda bazan rasa abinda zan ci ba."""

"Ta faWa tana sake yanko ™aton lomar sakwarar da ya daku lu™wui kamar ba da hannu aka daka ta ba, ta"

haWa da miya mai yawa ta kai bakinta.

Bata san tana jin yunwa sosai ba sai da taga cikin ™an™anin lokaci ta cinye manyan ™ullin sakwara guda

"biyu, duk yawan namomin da ke cikin miyan haka ta cinye tas, ta shanye ragowar miyan ta suWe kwanon tas kafin ta kwashe su zuwa kicin."

"Wanke-wanke kaWan ta gani a cikin sink, tattare hijabinta tayi ta haWa da nata farantan ta wanke su tas"

ta kife a cikin kwandon da ta gani a gurin. Goge ruwan da ya Wan zuba tayi da mopper kafin ta fice daga cikin kicin Win ta nufi Wakinta don sauke farali.

"[1/30, 5:32 PM] Fareeda Abdallah: ***** *****"

"""Haba don Allah! Ta ina aka taSa irin wannan rayuwa? Ace mace gandamemiyar budurwa baza ta iya"

"tu™e tuwon dawa lu™wui ta haWa shi da lafiyayyiyar miyar kuka wacce ta ji daudawa ba? Ni kam ba haka nake ba, sunana Karimatu aka saka miki amma sam ba haka halina yake ba. Yanzu saboda Allah da"

"Annabi idan Allah ya haWa ki aure da dattijo maciyin tuwo fa? Ya za kiyi...?"""

Wacce ake yiwa sababin ™ara zumSuro baki gaba tayi ranta a Sace ta ce

"""Allah ma baya sa haka ba Hajja. Ni kam in Allah ya yarda bazan taSa auren tsoho ba balle kuma ya"

"kasance mai masifar son tuwo, tuwon ma ya wuce na shinkafa, ya tsallake tuwon semo, ya shallake tuwon garin surfaffen masara har sai an gangara tuwon dawa. Kuma da kike ta wannan mitar kina min sababi ca nake sadda za ki fita na tambayeki abinda kike son ci zaSi biyu kika bani? Ke fa kika ce ko inyi miki sakwara ko tuwon dawa, da naga bazan iya tuwon dawan ba shi ne na miki sakwara. Kuma ki tambayi Mummy ki ji tun bayan fitarki da safe ban zauna ba sai da na gama haWa miki lafiyayyiyar sakwara miyan agushi, amma da yake ke ba'a miki gwaninta duk gidannan ba wanda bai ci abincin ya jinjina min ba sai ke, kuma saboda tsabar sabo da yi tun kafin ki WanWana za ki sauke min kwandon"

"sababin da kika taho da shi daga gidan Aminiyarki Hajiya Talatuwa mai tuwo-tuwo?"""

"A fusace Hajja ta buWe baki za ta mayar mata da martani, sai ga Zulaikha ta shigo cikin falon bakinta"

"Wauke da siririyar sallama. Ta yi wankanta tsaf! Ta yi kwalliya cikin Waya daga dogayen rigunan da Mashkura ta bata. Duk da fuskarta fayau yake babu wani Wige-Wige ko jagira sai powder kaWai, ba ™aramin kyau tayi a cikin doguwar rigar ba, kasancewarta farar fata, rigar kuma ba™a ce. Abu Waya da ya Wan Sata kwalliyar tata shi ne, bayan Wankwalin rigar da ta yafa a kanta, sai ta kawo wani hijabi kuma ta"

yafo ta bayanta don ya rufe tudun mazaunanta.

"""Sannunku da hutawa! Ina yininku?"""

"Ta gaishe su da sanyin murya, da Wan murmushi a fuskarta. Amma kallo Waya za ayi mata a fahimci tsoro"

"a fuskarta, domin hayaniyarsu ne ya fito da ita. Da kamar ma baza ta fito ba, sai kuma ta tuna tana wanka ta ji motsin an buWe ™ofar Wakinta an shiga, daga bisani kuma aka fita. Wannan shi ne dalilin da"

"yasa ta fito falon, a tunaninta ko Mummy ke son ganinta."

"Tun kafin ta fito, duk su biyun Mummy ta riga ta yi musu bayanin wacece ita. ˜osawa da Wokin yin tozali"

da abokiyar hira da Karima take tunanin ta samu yasa ta gaza ha™uri har sai da ta le™a Wakin da aka sauki Zulaikha. Da ta fahimci tana wanka ne yasa ta fita ta shige Wakinta.

"Dama Wakuna uku da suke jere a Sangaren Waya na Imam ne, Waya na Karima, Wayan kuma shi ne aka"

sauki Zulaikha a ciki.

Ita ma sababin Hajja ne bayan ta buWe kular abincinta ta ga sakwara saSanin Tuwon dawa da tayi

tsammani shi yasa ta fitowa.

"Duk su biyun, a tare suka mayar ma da Zulaikha martanin murmushinta. Karima ta buWe baki za tayi"

magana Hajja ta riga ta cewa

"""Zulaihatu ko? Amma fa sai dai kiyi ha™uri, ni kam gaskiya Zulai zan dinga ce miki. Zulaihatu yayi min"

"tsawo da yawa..."""

"""Hajja ba fa sunanta Zulaihatu ba, Zulaikha, haka Mummy ta ce. Don Allah kar ki wani Sata mata suna"

"da wani Zulai kamar wata tsohuwa."""

˜an™ance idanu Hajja tayi cikin sababi ta ce

"""To ina ruwanki ´ar'iya? Sunanki ko na ta? ³anmata akwai wani damuwa ne idan na kira ki da Zulai?"""

"""A'a! Babu wata damuwa Hajja. A gidanmu ma haka wasu suke kira na."""

"Ta amsa tana Wan dariya, don izuwa yanzu diramar jika da kakar ya fara daina ba ta tsoro sai dariya."

"""To kin dai ji, aka ce miki kowa irinki ne, ga cikakken sunanki na musulunci Karimatu amma kika yanke"

"shi wai ke nan gayu kika mayar da shi Karima. Ita Zulai ba haka take ba, da ganinta ´ar duma-duma yarinyar kirki ce. Zo nan ki zauna kusa da ni kin ji Zulai? Ina miki maraba da shigowa cikin ahalin Marigayi Modibo, alkhairin da ke tare da junanmu Allah ya sada mu da shi, sharrin da ke tattare da junanmu Allah"

"ya kare mu ya yaye mana."""

"""Ameen ya Allah"""

Zulaikha da Karima suka amsa addu'ar gaba Waya.

"""Na gode Hajja."""

"Zulaikha ta ™ara da faWin haka, fuskarta cike taf da murmushi. Kusa da ™afafun Hajja ta ™arasa ta zauna"

"akan kafet kamar yadda ta umarce ta, lokaci guda kuma tana satar kallon Karima, wacce take zaune can gefe Waya tana murmushi."

"""Ke fa Zulaikha da alamun kin samu shiga a gurin Hajja. Ai kam ina tausaya miki, domin samun shiga a"

"gurin Hajja daidai yake da tsayuwar..."""

"""Uwar tawa kike yiwa sharri Mamana?"""

Mummy da take fitowa daga cikin Waki ta katse maganar da Karima take yi.

"""A'a toh! Ai gara ki ji da kunnuwanki kuma ki gani da idanuwanki Saudatu. Yau fa tunda na kushe"

"wannan gantalallen sakwarar da take ta tutiyar ta daWe tana aikinsa ai ni kam na shiga uku. Gaskiya ce kuma sai na faWa, sakwara ce dai ba ita na so ayi min ba, tuwon dawa na so miyar kuka ke kuma baki iya"

"ba."""

"Zulaikha da karambani, kamar an saka ta, a hankali ta buWe kulolin abincin Hajja da suke ajiye akan Wan"

"™aramin teburin cin abinci a gabanta. Šaurin sakwarar guda Waya ta saka mata, ta zuba miya da namomin a gefe Waya, ta mi™a mata farantin, har lokacin murmushin fuskarta bai Sace ba."

"""Ki daure ki ci sakwarar Hajja. Ta yi daWi sosai Wlh, kuma ta daku lu™wui, miyar ma ta yi daWi kamar za"

"ta tsinke kunne. Anjima da yamma idan akwai garin dawar ni sai inyi miki tuwon, in dai za ki iya cin girkin"

"´an ™auye ni kuwa zan tu™a miki tuwon da duk kalar miyar yau™in da kike so."""

"Da idanuwan burgewa suke kallonta gaba Waya su ukun. Hajja bata tankwaSe ™o™arinta ba, farantin da ta"

"zuba mata sakwarar ta karSa, bayan ta yi bismillah ta yanki loma guda ta kai bakinta. A lokaci guda kuma tana tauna sakwarar tana cewa"

"""Na gode Zulai. Ni ko me zai hana ni cin girkin ´an ™auye? Nima fa daga can nake. Ba ma haka ba, duk"

wani Wan birni da za kiga yana bo™ara idan kika binciki tarihinshi tun tale-tale kakanninshi ™auyawa ne na

"asali."""

Ita kuwa Mummy cewa tayi

"""Da gaske kike yi Zulaikha? Kin iya tu™a tuwon dawa da ko wace kalar miya ta yau™i?"""

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannayenta.

"""Eh Mummy. Kin san mu mutanen ™auye ba kasafai muka cika yin kalolin abinci na ´an birni ba, ko da"

"yaushe an fi gane ma tuwo, sai kuma shinkafa ita ma jefi-jefi. Duk ranar girkin Innaye kashi tamanin cikin"

"Wari na aikin ni nake yi, in dai Sangaren abincin gargajiya ne na iya su gwargwadon hali..."""

"""Tubarakallahu ma sha Allah! Ke kuwa Zulai kin huta, Allah ya saka ma Innaye da alkhairi. Babu"

"ruwanta da fargaban aurar da ke ga ko wane irin miji. Takwara don Allah a sauke gwalli da iyayi a koyi kalolin girke-girken gargajiya don gudun gorin miji a gaba."""

Hajja ta ™arasa maganar idanunta na kan Karima.

"""Ni dai kam yau na bani da ke Hajja. Tunda dai na ™i miki tuwo kushe ni kawai kike yi, kiyi ha™uri mana"

"tunda ga ™anwata Zulaikha za tayi miki anjima. To ya kika ji sakwarar? Ta yi daWi sosai ko?"""

Sai da ta gyatsine fuska kamar wata ™aramar yarinya kafin ta amsa da

"""Ba laifi dai. Ta Wan yi. Zulai ™aro min rabin malmala in ™arasa da miyar nan kar ta min fatalwa na ™i cin"

"sakwara da yawa."""

"A tare Karima da Zulaikha suka tuntsure da dariya. Ita kuwa Mummy Wan murmushi kawai tayi, zuciyarta"

cike da farin cikin ganin yadda aWan ™an™anin lokaci sabo ya shiga tsakanin Zulaikha da iyalanta. Tabbas

"kamar yadda Hafiz ya ce, da alamun baza'a samu matsala da yarinyar ba."

"˜an™ance idanu Hajja tayi tana harararsu duk su biyun, a Wan fusace ta ce"

"""To miye kuma abin dariya? Ko don kawai an ga na daure tashin zuciya ina cuccusawa? To tunda haka"

"ne ma ke Zulai bar shi kawai na fasa ™arin..."""

"""Allah ya baki ha™uri Hajja. Ba da ke muke dariya ba fa."""

"Zulaikha ta faWa tana danne dariyar da ke sake tu™o ta. Ta rasa dalilin da yasa, bayan dariyar diramar"

Hajja haka kawai take jin zuciyarta yalwace da farin ciki. Duk wani ™unci da damuwar Hafiz da

mahaukaciyar matarsa ta aje su gefe Waya can ™arshen zuciyarta.

"Bayan farkawarta aWan gajeren barcin da ya kwashe ta Wazu,

23 / 50