Advertisements
Chapter 50 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   50 / 50

147K to 147.7K   out of 147.7K words

da ta rasa gane ta inda yake SuSSugowa. Bakinta na rawa ta ce"

"""Zuly... Tsoro nake ji Wallahi. Ki ga yadda Aunty Bintu ta ™ara komawa wata mace mai aji ta"

"musamman fa... Dama ya ya lafiyar giwa bare ta yi hauka? Na shiga uku! Shi yasa auren mijin wata bai ba. Idan Nurul-™alb ya ce zai mayar da ita ban san inda..."""

Make bakinta da Zulai tayi yasa ta yi shiru tana hawaye.

"""Wani lokacin dai ke banza ce Aunty Karima. Ni Wallahi kin ma ba ni haushi. Yanzu ke har akwai wata"

"mace mai Waura Wankwali da kike fargabar za ta iya ™wace mijinki a hannunki? Ba'a aure ita aka aure ta? Kar ki sake faWa min zancen banza wai wani mijin wata. Bayan haka ma, ke kina ganin a irin matsanancin Son da yaya yake miki har akwai wata ´a mace da za ta sha gabanki a zuciyarsa? Bintun da dai ita ce a yanzu, babu wani abu na musamman da ta canja. Sannan kuma Miji naki ne, a hannunki yake, ki daina ma wani banzan tunanin wai Yaya zai mayar da Bintu Wakinta, da zai mayar da ita da tuni an wuce gurin."

"Ki saki zuciyarki kiyi walwala a cikin mutane..."""

˜wan™wasa ™ofar Wakin da aka fara yi ta waje yasa Zulai ta katse maganar da take yi.

Da muryarta ™asa-™asa ta cigaba da cewa.

"""Saura kuma ki fito in ga kin cigaba da tsangwamar kan ki, ki shiga bayin Abban Imam ki wanke fuska."

"Zan turo Hibba ta sake miki kwalliya."""

Tana gama maganar ta fice daga Wakin ba tare da ta saurari cewar Kareema ba.

"Wasu ™awayen Mummy ne suka shiga gurin mai jego duba ta da baby, ashe shi ne kiran da aka yi mata."

"Da ladabi sosai Zulaikha da gaishe su, suka ™ara yi mata barka suka bata kayan barka, sannan suka fice"

daga Wakin.

Ba a Wauki tsawon lokaci ba Kareema ta dawo cikin ™awayensu da su Mashkura suka cigaba da

"warwasawa. Bintu na can cikinsu Aunty Balira suna hira, tun da tazo ko idanun Aadil bata gani ba, yana can tare da Imam da sauran yara suna wasa."

"Kareema ta zo fita daga falon Zuly zuwa cikin gida karaf maganar Aunty Balira ya sauka a kunnenta,"

"maganar da yasa ta rage saurin tafiyar da take yi, don kawai ta ji amsar da zai fito daga bakin wacce aka jefa ma tambayar."

"""Bintu? Na ce wai ya maganar aure ne? Kar dai ki ce na yi miki shisshigi, amma tsakani da Allah zaman"

"hutun dai isa haka. Aure shi ne daraja da cikar mutuntakar ko wace ´a mace, in dai Allah ya kawo miki"

"miji, ki daure kiyi aurenki. Idan kuma kun daidaita da Hafiz ne..."""

"""Babu maganar daidaitawa Aunty Balira. Zama ya ™are tsakanina da Daddyn Aadil. Domin a yanzu haka"

"saura wata Waya ne da ´an kwanaki a Waura min aure."""

"A hankali Kareema ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, sai kuma ta ™ara sauri har ta fice daga falon."

Wani kwanciyar hankali na musamman na sauka a duk sassan jikinta.

"""Too ma sha Allah! Allah ya sanya alkhairi, yasa ayi da mu."""

Rakiya da Ladidi suka faWi haka da fara'a a fuskarsu. Dama can su ba sa wani ™aunar dawowar Bintu

"cikinsu, duk da dai ta shiryu, taje can ta ™arata da shiryuwarta."

Ita kuwa Aunty Balira a sanyaye tayi fatan alkhairi. Allah ya sani duk da Kareema bata rage su da komai

"ba, ta so ace Hafiz ya yi ha™uri sun daidaita da Bintu. Ko don Aadil, amma inaa... Sam-sam Hafiz ya tsani ma a dinga tayar mishi da maganar wata tsohuwar matarshi wai ita Bintu."

Sai gaf da Magriba Bintu da Tawagarta suka bar gidan sunan. Sun rabu suna raha a tsakaninsu. DaWai

wani abu na muni ko rashin fahimta bai taSa shiga tsakaninsu ba.

"Anyi taron suna lafiya, an tashi lafiya. Mai jego da Jaririnta sun tashi da rikitiSar arziki mai yawan gaske."

Sai fatan ayi wanka lafiya a gama lafiya Zulaikha ta Abban Imam.

*_Alhamdulillah. Komai yayi farko zai yi ™arshe. Anan na kawo ™arshen labarin RANAR NAKA SAI NAKA

"DAŠIN ZAMA SAI BARE. Kuskuren da ke ciki ina ro™on Allah ya yafe min. Alkhairan da ke ciki Allah yasa mu amfana gaba Waya ya haWa mu a cikin ladan. Ina godiya gare ku ´an'uwana masu karatun wannan littafi tun daga farko har ™arshe. Sunayenku da yawa, bazan iya ambatanku Waya bayan Waya"

"ba Na gode, na gode. Allah ya bar ™auna da zumunci. Sai mun haWu a Cigaban labarin"

"˜ASAITACCIYAR MACE... In sha Allah Fareeda Abdallah ce, domin magana da ni kai tsaye a tuntuSeni ta wannan lambar 07039080978_*"

50 / 50