Advertisements
Chapter 40 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 50

117K to 120K   out of 147.7K words

tayi aure."

"""Yaya... Yanzu muka waya da Innaye ta ke cemin za ka je Fa™o yau. Don Allah idan baka yi nisa ba ga"

"sa™o ka tafi mata da shi. Nima da yau za mu je, sai kuma bagatatan tafiya ta kama Abban Imam. Allah"

"yasa dai baka yi nisa ba."""

"""Ban yi nisa ba Zulai. Na juyo ne, yanzu haka ma gani na kusa isa gidana..."""

Ya amsa mata da cusasshiyar murya mai bayyana damuwa ™arara.

"""Toh fa!! Lafiya? Me yake faruwa?? Ko ka fasa tafiyar ne???"""

"Ta tambaye shi cikin sanyin murya, zuciyarsa cike da tunanin me ke damunsa haka? Duk lalacewar"

"Wan'uwa Wan'uwa ne, lokaci Waya ita ma Zulaikha ta ji ta shiga cikin damuwa. Duk da bai faWa mata abinda ke damunsa ba."

"""A'a! Ba fasa tafiyar nayi ba..."""

"""To ko baka da lafiya ne?"""

Ta sake katse shi da tambayar tun kafin ya aje numfashin maganarsa.

Da yake zuciyarsa cunkushe take da damuwar da shi kanshi ya san tabbas yana bu™atar abokin tauna

"wannan damuwa. Kuma ™arin shawara daga wani Sangare na zuciyarsa da ta tunasar da shi mai shawara fa aikinsa ba ya Saci, sai dai ace yana da ™arancin sirri. WaWannan dalilan guda biyu suka ja mishi gora"

wajen zaiyane ma Zulai duk halin da yake ciki.

Da takaicin munanan halayen Bintu a muryar Zulaikha ta ce

"""Lallai ma Innaye. Ita Bintun wacece da har za'a ji tsoron ri™e Wan da ake da tabbacin ba nata ne ita"

"kaWai ba? Allah yasa dai baka yi gaggawar mayar mata da Aadil Win ba?"""

"""Ban mayar mata da shi ba. Amma ga ni a hanya zan mayar mata da shi. Ya zanyi Zulai? Dole in mayar"

mata da shi tunda dai ba ni da mai ri™e min shi... Ke dai kin san tunda Innaye ta ce baza ta ri™e shi ba cikin su Aunty Balira ma babu wacce za tayi gangancin ri™e shi. Balle ma yadda ba™in halin Bintu bai

"tsallake kowa ba..."""

"""Duk da haka dai Yaya... Ai hannun mutum bai taSa ruSewa ya yanke ya yar! Ni idan baza ka damu ba"

"ka kawo min shi in yaye."""

Saboda tsabar yadda maganarta ya dake shi bai san sa'adda ya taka burki da ™arfi ba. In da Allah ya

"taimake shi shi ne a lokacin ya shiga cikin layinsu, da a kan babban titi yake irin wannan burki da ya taka na ba zato babu abinda zai hana motar bayanshi ta buga mishi."

"Da saurin gaske ya gangara gefen hanya sannan ya kashe motar, bakinshi na rawa ya jefa mata tambayar"

"""Me kika ce Zulai?"""

Dariya tayi sannan ta sake maimaita mishi abinda ta ce.

"""Amma don Allah da gaske kike yi Zulai?"""

"Ya sake tambayarta da wani irin yanayi Soyayye, shi ba farin ciki ba shi kuma ba ba™in ciki ko fargaba ba."

"""Wallahi da gaske nake yi. Amma idan baka amince ba sai in ha™ura..."""

"""Na amince. Wallahi yanzu zan kawo miki shi Zulai. Na gode. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi"

"yayi miki albarka. Ga ni nan zuwa."""

Bai jira cewarta ba ya tayar da motar da sauri yayi revers ya mi™e hanya. Fuskarsa bayyane da

matsanancin fara'a zuciyarsa tumbatse da nutsuwa.

"Har ya yi nisa sosai a hanyarsa ta zuwa gidan Zulaikha, sai kuma ya tuna ai duk wannan budurin da suke"

yi shi da Zulai basu sako mijinta Kamal a ciki ba.

Kuma tsakani da Allah in dai shi matsayinsa na babba yana da lafiyayyen hankali ya kamata ya tuna

yanzu fa ba kamar da bane. Hatta Innaye da take kamar mahaifiya ga Zulai Kamal ya fi ta iko da Zulai.

"Jikinsa a sanyaye ya Wauki wayarsa ya buWo lambar Zulai ya danna mata kira. Yana shiga ta Wauka, abinda"

ta fara tambayarsa shi ne

"""Yaya ka ™araso ne?"""

"""A'a!"""

Ya amsa mata. Sai kuma ya Wanyi shiru kafin ya cigaba da cewa

"""Zulai kar inyi aikin marasa hankali. Kina ga Kamal zai amince a haWa Amaryarsa da raino alhalin ba"

"haihuwa tayi ba?"""

"Dariyar da Zulai ta ™yal™yale da shi yasa shi ma ya Wan saki dariyar, amma jikinsa a sanyaye."

"""Allah da gaske nake yi. Kin san fa Aadil har yanzu jariri ne. Shekararsa Waya ne kacal saboda tsabar"

"fitina irinta Bintu ta tsiro da zancen yaye shi."""

Ajiyar zuciya Zulaikha ta sauke bayan ta tsagaita da dariyar da take yi.

"""Kar ka damu Yaya! Ko ba ya tafiya za ta iya yaye shi a shekara Wayan balle kuma yana tafiyarsa ko ina."

"Batun Abban Imam kuma ka kwantar da hankalinka, sam ba shi da matsala. Ko rantsuwa nayi babu kaffara bazai taSa yun™urin hana ni duk wani abu da ya shafi ´an'uwana ba, saboda ya san muhimmancinsu a gare ni. Ta gwaSa mishi magana da gan-gar. Kuma yau Winnan yayi tafiya, zai Wauki tsawon sati shida acan. Anjima nima zan tattara ´an abubuwan bu™ata ne in koma gidan Mummy... ka"

"san ta kuma ba ta da damuwa."""

"""Haka ne! To ga ni nan zuwa."""

Ya amsa da sanyin jiki yana jinjina maganar da ta gwaSa mishi a zuciyarsa.

"Yana isa gidan Zulaikha, Aadil ya farka da wani irin gigitaccen kuka kamar wanda aka sa mishi wu™a a"

wuya. Da wannan dalilin yasa Hafiz yana shiga da motarsa harabar gidan ko gama daidaita fakin baiyi ba ya sungumi Wan hankalinsa a tashe ya nufi babban falon gidan.

Sau biyu ya ™wan™wasa bai jira an buWe masa daga ciki ba ya fara murza hannun ™ofar yana ™walla kiran

Zulai hankalinsa a tashe da irin kukan da yaron yake yi. Shi daman ba irin mutanen nan bane masu

"masifaffen son yara, duk yadda suke dariya da Aadil da zarar ya fara kuka zai mi™a ma Bintu shi."

"Daga can cikin falon, a gigice Zulai ta ™arasa sako hijabinta tazo ta buWe mishi ™ofa. Bai saurari kalaman"

barka da zuwa da take furta mishi ba ya fara mi™a mata Aadil da har wannan lokacin yake tsula kuka.

"""Šan tsaya mana Yaya."""

Tayi maganar a nutse.

A hankali tasa hannunta na dama ta Waga fuskar Aadil tasa idanunta a cikin na shi. Da™i™u goma bayan

"nan sai ta haske yaron da lallausan murmushi, sannan ta Waga hannuwanta biyu ta mi™a mishi alamar ya"

zo.

"Tun Zulai tana ™arama, ba sau Waya ba sau biyu ba Hafiz ya sha ji Innaye tana yi ma Zulai kirari da mai"

"baiwar iya sarrafa ™ananun yara. Duk irin ™wuiyar yaro da fitinarsa sai dai idan Zulai bata so ™ulla har™alla da shi ba. In dai zuciyarta na son Wa, to fa ko ke uwar Wan sai dai kiyi ha™uri, domin idan za ta jera wata guda tana zuwa Waukar Wa ko ´a zuwa gidansu ana hana ta baza ta taSa gajiyawa ba. Idan kuwa har yaro"

ya saba da ita to fa uwa da kanta za ki ji tana aika ma da Zulai yaron ko bata je Waukarsa ba.

"A wancan lokacin, bai Wauka baiwar na ta ya kai yadda Innaye take kururutawa ba sai yanzu da yaga ikon"

"Allah. Aadil da kanshi ya mi™a ma Zulaikha hannu ta Wauke shi. ˜arin mamakin kuma yana zuwa jikinta ya kwantar da kanshi a kafaWarta, sannu a hankali yake rage ™arfin kukansa har zuwa sadda yayi Wif! Kamar anyi ruwa an Wauke."

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun kwanciyar hankali. Godiya ya fara yi mata haWe da

kyawawan addu'o'i.

"""Na gode ˜anwata. Ubangiji ya baki duk abinda kike nema duniya da lahira. Allah ya ji™an mahaifanki"

"da gafara."""

"""Amin thumma Amin."""

Ta amsa addu'ar da murmushi a fuskarta.

"""Ya yi break fast ne a gida?"""

Ta tambayeshi kafin ya ™ara cewa komai.

"""A'a! Tun misalin ™arfe uku na dare dai Mamanshi ta bashi nono, daga nan barci yake ta yi sai yanzu ya"

"farka."""

"""To ba damuwa. Yanzu dai shigo min da kayayyakinshi, ina zuwa."""

"Ko kafin ya gama shigo da kayayyakin, Zulai ta haWa tea mai kauri da zallar madarar peak ta 1,2,3 wanda"

"take ma Imam amfani da shi idan ya je gidan ta zuba milo ba tare da ta sa suger ko Wigo ba ta fara ba Aadil da Wan ™aramin cokali, yana sha tana mishi ´an wa™e-wa™e da wasanni."

Cikin ™an™anin lokaci sai ga yaron yana ™yal™yala dariya. Sai da ya ™oshi taf sannan ta surka ruwa tayi

"mishi wanka fes! Kafin Hafiz ya bar gidan, har Aadil yayi barci goye a bayan Zulai, abinda sam bai samu ba a gurin Mamanshi wai don tsoron kar tsayayyun nonuwanta su faWi."

"Ganin ™arfe goma sha Waya saura mintuna kaWan yasa Hafiz mi™ewa tsaye, sai da ya gama kai sa™onnin"

Zulaikha da zai tafi ma da Innaye cikin mota sannan ya koma a tsaitsaye ya bata abinda ke tsakaninshi da Kareema.

"Tsananin murna da mamakin lamarin yasa bakin Zulaikha ya ™i rufuwa, ta kasa cewa komai, har ya gama"

yi mata ™arin bayanin cewa

"""Wannan dalilin ne yasa komai rana in sha Allah zan tafi Fa™o ayau Winnan. Domin gobe da wuri nake"

"so su Baba Abubakar su shigo su samu Abba Lurwanu aje wajen iyayenta maza. Tunda dai Mummy ta bani dama gaskiya ba na son a Wauki wani lokaci mai tsawo ba tare da anyi komai an wuce gurin ba."""

"""Uhmmm! Ai ni na ma kasa magana Yaya. Allah ya tabbatar da alkhairi. Lallai ma Aunty Kareema, wato"

"shi ne ana ta kwasar love da Yayana ko a gista min..."""

"""A'a kar ki ga wani laifin ˜urratul-Ayni.. Ni ne nan na umarceta tayi shiru da bakinta har sai lamarin ya"

"fara nuna. Yanzu da ya kamata ki ji ba ga shi na faWa miki ba?"""

Ya Wauki laifin komai ya jibga ma kansa don kawai ba ya so a ™ullaci rabin ransa.

Ita dai Zuly ta kasa daina dariya... Abubuwa da yawa ne suka haWe a zuciyarta.

"""Amma kuwa Bintu ta sani Yaya?"""

Ta tambaye shi tana hasashen irin tashin hankali da haukar da Bintu za tayi idan ta ji irin gagarumin

tashin hankalin da ke tunkaro ta.

"""Bata sani ba. Amma zan faWa mata idan na dawo."""

Ya amsa a lokacin da ya kama hanyar fita daga falon.

"Sallama suka sake yi, tayi mishi addu'ar Allah ya tsare ya kiyaye hanya sannan ya fice daga cikin falon."

Tana tsaye jikin window tana hangenshi har maigadi ya buWe mishi ™ofa ya fice daga gidan.

"Labulen windon ta saki, ta koma tsakiyar falon sannan ta saki wata ™a™™arfar dariya da yasa Aadil da ke"

"bayanta motsawa kamar zai tashi, da sauri ta toshe bakinta don rage ™arfin dariyar tana haWawa da Wan jijjiga shi."

"""Bintu ruwa ya ™are ma Wan kada bai gama wanka ba, daWina da gobe saurin zuwa..."""

Ta sake ™yal™yalewa da dariya a hankali don kar ta tashi Aadil. Zuciyarta cike da wani irin farin ciki mara

misaltuwa.

******

"˜arfe biyu da ´an mintuna na tsakar rana ya isa Fa™o. Kamar ko wane lokaci, haka ´an'uwa da abokan"

arziki suka tarbe shi da matsananciyar murna. Shi kuma ya buWe bakin aljihu kamar yadda ya saba yayi musu yayyafin alkhairi.

"Da™yar ya samu ya ™waci kansa suka keSe da mahaifansa, bayan sun sabunta gaisuwa ne yake sanar da"

su muhimmin abinda yake tafe da shi a wannan rana. Wani abu da ya lura da shi shi ne daga Innaye har

"Baffa farin ciki ya gaza Soyuwa a fuskokinsu daga jin wannan labarin, wannan shi ya ™ara tabbatar mishi lallai ba™in ciki da takaicin munanan halayen Bintu ya daWe yana damun iyayensa."

Tambaya Waya da Baffa yayi mishi shi ne

"""Ka faWa ma Alhaji Lurwanu?"""

"""Ban riga da na faWa mishi ba Baffa. Amma ina komawa gida in sha Allah ayau zanyi ™o™arin sanar da"

"shi."""

Ya amsa kanshi yana ™asa.

"""Lallai ya kamata ka sanar da shi da gaggawa, saboda kar su Abubakar su je ya zama ya ji labari daga"

"bakinsu, ka ga idan aka yi hakan ba'a kyauta ba."""

"""In sha Allah zan faWa masa ayau Baffa."""

Bayan sun gama magana da su Innaye ya fita da nufin zuwa gidan Anty Balira ya gaishe ta. Wani arashi

da ya tarar shi ne acan ya tarar da Aunty Rakiya da Aunty Ladidi sun je gaishe da Aunty Balira da tayi zazzaSi kwanaki biyu da suka wuce.

"Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokinsu, sa'ilin da suka gama gaisawa yake faWa musu zai auri Kareema"

"™anwar mijin Zulai. Addu'o'i kyawawa da fatan alkhairi suka yi mishi, sannan Aunty Balira ta tashi ta zagaya banWaki."

"Kuma kun san irin banWakunan da ake yi a ™auye, can nesa da Wakunan gida ake yi saboda masai ne ake"

yi na gargajiya.

"""Haba! Ko kai fa Hafizu? Amma me ake da mace mai mugun ba™in hali da kafirin munafunci da kissa"

"irin Bintu?"""

Kalaman da suka fara fita daga bakin Aunty Rakiya kenan bayan ta tabbatar Aunty Balira ba ta jin me

take cewa.

Nan fa kamar an matsi bakunansu su biyun suka buWe baki suka dinga kora ma Hafiz labarin irin cin

kashin da Bintu tayi ta musu ba sau Waya ba ba sau biyu ba. Amma saboda tsabar munafunci idan yana gurin sai ta dinga musu haba-haba kamar za ta haWiye.

Suman zaune kawai Hafiz yayi yana jin waWannan ba™a™en labarai masu barazanar fasa mishi zuciya.

"Tabbas idanunshi sun buWe, kuma ya fahimci kissa da munafuncin Bintu, amma bai taSa tsammanin ta daWe tana wasan kwaikwayo da fahimtarshi har na tsawon lokaci haka ba."

Bai ™ara shiga cikin tashin hankali ba sai da Aunty Ladidi ta ce

"""Ni fa duk waWannan munanan halayen nata abu Waya da idan na tuna har yanzu yake min ciwo a"

"zuciya shi ne yadda da gangar ta so kashe Innaye... Yo ta so kashe ta mana. Tunda ai likitan nan na asibitin Nasin Ham (Nursing home) Ya faWa ma Aunty Balira cutar da ke damun Innaye daban magunguna da alluran da aka yi ta zurkuWa mata daban, har ya ™ara da cewa lallai duk likitan da ta ba"

"Innaye waWannan magungunan ta so kawai ta illata ta ne..."""

"""WaWanne irin zantukan banza ne kuke faWa ma Hafizu haka Rahina?"""

Aunty Balira ta katse ta cikin tsawa da Sacin rai.

"Firgigit suka yi duk su biyun, sai a lokacin suka dawo hayyacinsu suka lura da wasu zafafan hawaye da ke"

"kwaranya a idanun Hafiz. Duk da sun san gaskiya suke faWa, sai kuma jikinsu yayi sanyi ™alau da ganin irin"

hawayen da ke gudu akan fuskarsa.

"FaWa Aunty Balira ta rufe su da shi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, a ™arshe ta ce su Sace mata"

da gani tunda su ba su da hankali suna so su shiga tsakanin mata da miji.

"Sum-sum suka saka hijabansu suka fice daga Wakin, jikinsu sanyi ™alau, kamar an she™a musu ruwan"

sanyi.

Kusa da Hafiz Aunty Balira ta zauna ta fara rarrashinshi da tausasan kalamai. Duk da ta nuna Sacin ran

abinda su Rakiya suka yi amma ko kaWan bai ji ta ™aryata maganganun da suka faWa mishi ba.

Sai da ta daWe tana rarrashinshi sannan da™yar ya tsagaita sharSen hawayen da yake yi. Ya Waga kanshi

yana kallonta da idanunsa jajaye ya ce cikin rawar murya

"""Amma... Amma... me yasa baku taSa ankarar da ni ko ku fito ™arara ku faWa min irin abubuwan da ke"

"faruwa ba...?"""

"""Ta ina za mu samu ™warin gwuiwar faWa maka Hafizu bayan duk mun fahimci irin son da kake mata,"

"sannan mun ga yadda idanunka suka rufe ruf a kanta. Ca nake don a sama maka sau™i ne Baffa ya Wauki Zulai sukutun da guda ya aura maka amma ka watsa masa ™asa a ido?"""

"A karo na biyu du™ar da kanshi yayi ya cigaba da sharSen hawaye, a zuciyarsa yake tuna yadda ya"

™e™ashe ™asa ya biye ma Bintu ya kasa yi ma iyayensa biyayya. Ya daWe a haka kafin ya iya tsayar da

"hawayen da™yar! Ya laluba aljihunsa ya Wauko damin kuWi yayi mata alkhairi kamar yadda ya saba, ya"

"bata na Ladidi da Rakiya, sannan ya bata wanda za ta raba ma ´an'uwansa mata da suke uba Waya."

"Jikinsa a sanyaye ya mi™e yayi mata sallama zai wuce, har zaure ta raka shi tana sake haWa shi da girman"

Allah kar ya kuskura ya ce zai hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.

"""Ka gode ma Allah da yasa idanunka suka washe akan halinta. Ka ga yanzu sai ka sake sabon lale akan"

"zamantakewar da za kayi da ita. Mu dai Allah ya sani bamu ri™e ta arai ba."""

Da haka suka rabu.

"Ko da ya koma gida gurin Innaye, duk yadda ya so su sake tauna zancen ta ™i bashi damar haka. Da"

"murmushi a fuskarta take ™ara tabbatar mishi ita bata ri™e Bintu arai ba, kuma bata yafe mishi ba idan ya"

hukunta Bintu da laifukan da suka gabata.

"A karo na barkatai ya du™a har ™asa ya sake neman yafiyarta, ta ™ara jaddada mishi ta yafe sannan ya fita"

gurin Baffa.

"A can Win ma dai zancen suka sake taunawa, a matsayin Baffa namiji, ya sake bashi shawarwari masu"

"kyau na yadda zai zauna da Bintu, a yanzu, da kuma bayan ya ™ara aure. Kamar haWin baki shi ma dai sake jaddada mishi yayi kar ya kuskura ya ce zai Wauki wani mataki akan Bintu. Abinda ya wuce a barshi a wanda ya wuce."

"Yamma li™is ya bar Fa™o, bakunan iyaye da ´an'uwanshi cike da addu'ar Allah ya maida shi Abuja lafiya."

Da yake tun yana hanya ya kira Abba Lurwanu ya sanar da shi akwai muhimmiyar maganar da yake so

"suyi, amma yanzu yana hanyar komawa Abuja, idan Allah ya sa ya koma lafiya kuma dare baiyi sosai ba zai tsaya a gidanshi suyi maganar."

Wannan dalilin yasa ko da ya shiga Abuja ™arfe goma na dare ya wuce gidan Abba Lurwanu. Acan ya ci

"abincin dare, bayan sun gama tauna maganar neman aurenshi da Kareema sannan ya kama hanyar komawa gida."

Da wannan gajiya da Sacin ran ne bayan isarsa Bintu ta so ta kunno ma kanta bala'i shi kuma ya karta

"mata kashaidi, haWe da rantsuwar ba don rayukan mutane uku mafiya muhimmanci a gare shi ba (Baffa, Innaye, Aunty Balira) Da yanzu wani zancen ake yi tsakaninsu ba wannan ba."

************

"Ta Wauki tsawon mintuna ashirin a tsaye inda ya barta, jikinta sanyi ™alau. Zuciyarta a cunkushe, ta ma"

rasa wani irin takamaimai tunani ya kamata tayi.

A ™arshe dai da taga tsayuwar bazai fissheta ba sai taja ™afafunta a sanyaye ta koma cikin falon. Har ta

"Wofana mazaunanta akan kujera, sai kuma ta mi™e tsaye tsulum kamar an tsunguleta."

"Wayarta da ke ajiye can gefe Waya ta Wauka ta fara tafiya zuwa Wakinta. A hannunta tana lallatsa wayarta,"

lambar Raudha ta lalubo ta danna mata kira ba tare da duba tsalawar da dare yayi ba.

Wayar tana daf da tsinkewa Raudha ta Wauka da magagin barci sosai a muryarta.

"""Bintu? Lafiya kike kuwa? Me ya faru?"""

Ta jera mata tambayoyin a rarrabe.

"""Yi ha™uri Raudha na tashe ki kina barci... Daman zan faWa miki abinda ya faru bayan dawowar Hafiz"

"ne..."""

"""Toh! Toh!! Ina jinki!!! Amma Ina fatan dai ya dawo miki da Aadil?"""

Ta tambayeta da murya mai cike da Woki da sakankancewa.

"""A'a! Bai dawo da shi ba."""

Ta amsa da

40 / 50