Advertisements
Chapter 36 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   36 / 50

105K to 108K   out of 147.7K words

ya zaunar da ita, cikin lallaSawa da tarairaya"

"kamar wata sarauniya. Jikinsa na rawa-rawa ya shige gurin ma'ajiyar kayan sawansa, ya buWe Sangaren da kayayyakin sakawarta ne sababbi sha™e da gurin. Kama daga laces, atamfa, shadda, har zuwa kayan barci da Inner wears."

Kayan barci masu kyau sosai ya Wauka mata ya fice daga gurin ya nufi inda take zaune. Daga irin yadda ta

"takure kanta ta naWe hannaye cikin ™irjinta kamar mai jin sanyi ya kusa saka shi dariya, amma sai ya"

daure baiyi dariyar ba.

"""Babe sanyi kike ji?"""

Ya tambayeta a tausashe.

"""A'a! Barci kawai nake ji."""

Ta amsa a kasalance.

"""Sorry. Ga kayan barci na Wauko miki. Yanzu dai ki shiga bayi kiyi wanka sai ki canja kayan jikinki zuwa"

"na barci ki kwanta."""

"Har ta buWe baki za ta ce mishi ta yi wanka tun a gida, sai kuma tayi shiru bayan ta tuna yadda Aunty"

"Balira ke ta jaddada mata banda yi ma miji musu. Kayan barcin hannunsa ta karSa, ta mi™e tsaye a hankali tana kallonshi ™asa-™asa."

"""Ina ne banWakin?"""

"Da yatsarsa manuniya ya nuna mata inda banWakin yake, ita kuma bata Sata lokaci ba ta nufi hanyar"

zuwa banWaki tana tafiya kalalau-kalalau kamar kazar da ™wai ya fashe ma a ciki.

"Duk yadda yake ta Woki da zakwaWin wannan dare don maimaita wainar da suka soya jiya, tsoro da"

fargabar da yake gani ™arara a cikin idanuwanta ya hana shi taSuka komai.

"Ta bakin Hajja ce, matarsa sabuwar shiga ce a komai, lallai ya kamata ya bita sannu a hankali, idan ba"

haka ba kuwa da sannu zai haifar da gagarumin tsoron gamuwa da shi a zuciyarta.

"Bayan ta yi wankan shi ma yayi, rungumeta da yayi tsantsan a ™irjinsa, bayan haka bai mata komai ba"

suka yi barci har ladanin masallacin unguwar ya kwaWa kiran sallar asubah.

********

"A kwanakin da suka biyo baya amarci suke zubawa tsantsa abinsu, soyayya zallah ake shimfidawa a"

"gidan, mai tsafta da burgewa, wanda ko kaWan babu algus a cikinta."

"Karima da ta je gidan a cikin satin, kasa rufe bakinta tayi. Cikin Wan kankanin lokaci har sun kara yin wani"

"fresh su biyun, fata ta kwanta luwai-luwai, saboda hutu da kwanciyar hankali, ga kuma lafiyayyun abinci da ake dafawa daga gidan Mommy ana kai musu."

"Ga Zulaikha gwana ce da ta kware wajen tarairaya da kulawa da Kamal, a Sangaren auratayya ne dai sai"

"a hankali take sabawa. Ta gama karantar mijinta ciki da bai, tasan duk wani abu da ke faranta mishi rai kuma ta kware akan shi."

"Karima Tana zaune tana kallonsu akan kujera 2 seater, kankana da abarba suke sha wanda Zulaikha ta"

"yanka musu bayan zuwanta. Yadda Kamal yake wani zuba ma Zuy shagwaba son ranshi kamar wani karamin yaro shi ne abin ke bata mamaki, ita kuwa ta dage tana ta tarairayarshi, sun hade kawuna suna ta kus-kus suna dariya ba tare da kunyar idanunta ba, sai ta kama ma suke sanyata cikin hirarsu."

"Ana nan kuma sai ya tashi wai zai shirya yaje ya gaida su Mommy, Zulai kuma ta tashi ta bi bayanshi"

bayan ta ba Karima uzurin za ta raka shi sama ya shirya.

Karima tana nan zaune shiru-shiru tana jira har aka fi minti ashirin babu duriyarsu. Abin ma ya kasa bata

"haushi ko dariya, sai kawai ta yayimi jakarta ta fita. A ranta tana fadin idan sun kara ganinta a gidan su mata abinda suka ga dama."

"Gaf da za ta fita sai ga Zuly ta biyo bayanta a sukwane, ta hau sunne kai tana bata hakuri cikin dadin"

"murya, da kyar ta samu ta lallasheta suka koma cikin gida. Shi kuma ya musu sallama ya tafi."

"Sai lokacin suka samu lokacin zama su yi hira sosai. Kwarai Karima ta yabawa yanayin da ta gansu a ciki,"

har cikin ranta tayi murna da fatan Allah Ya dorar da su akan wannan rayuwa da soyayya har abada. Itama kuma tana yiwa kanta fata da dacewa da samun rayuwar aure irin wannan.

Sai can bayan isha'i sannan ta bar gidan lokacin da Kamal din ya koma.

Sai da Zulaikha ta cinye sati uku cif ana kai musu abinci daga gidan su Mommy kafin ta fara cancada

musu kalolin girke-girken da ta kware akai na gargajiya da na bature.

"Rigima kuma sai ta koma akan a dawo mata da Imamu gidan. Shi kuwa gogan tsoron akai shi can yake,"

"kulawar da ake bashi tayi kasa, a raba musu ita biyu. Shi ne yake ta mata kauce-kauce da bada excuses iri-iri."

"Ita kuwa da ta ga haka sai ta dangana shi ga Mommy, ita ta dage tsakaninta da Allah a bar mata Imamu,"

shi kuma yace ai Imamu ya riga ya zama dan gidan Mommy. Ta hakura kawai ta lalubi junior Imamu. Sai gata tana kuka riri har abin ya so basu dariya. Har cikin ranta tana kaunar zama da yaron.

Ga zaman kadaici da take tunanin shiga ciki idan Baban Imam din ya koma bakin aikinshi ka'in da na'in.

"Daga karshe dai Mommy ta kashe rigimar ta hanyar raba musu gardama, tace Imam zai dinga zuwa yana"

"yi musu weekend duk karshen sati, sannan a ranakun karatu watarana zai dinga zuwa da yamma yana kai dare daga can makaranta. Duk da ba haka taso ba, a haka dai aka tashi."

Suna komawa gida ya hau kalallameta da dadin baki da ban hakuri don ya kula dai hukuncin da Mommy

"ta yanke ba haka taso ba. Daga karshe dai ya samu ya shawo kanta da kyar. Don kuwa shi yasan yar kayanshi, ya kuma san ta yadda yake shawo kan abinshi."

******

"Watansu biyu da aure, rayuwarsu na tafiya cikin tsari da ban sha'awa. Rayuwace suke shimfidawa mai"

kyau da tsafta wacce babu boye-boye da cutarwa a cikinta.

"Kamal yana girmama matarshi da Waukaka duk wani sha'ani nata, haka itama tana kaffa-kaffa da"

"al'amuranshi, kuma tana iyaka kokarinta wajen ganin ta kyautata mishi yadda yakamata."

A cikin satin ne kuma kwatsam ba zato ba tsammani Bintu da Hafizu suka kai musu ziyara. Bayan sun

buga rikici mai yawa har Hafiz yayi mata rantsuwar idan bata shirya sun tafi gidan tilon ™anwarsa ™wallin ™wal da take aure a garin Abuja ba za ta haWu da mummunan Sacin rai daga gare shi.

"Haka ta shirya ranta a Sace, bakinta a gaba, ta ja tsaki ™asa-™asa ya fi sau hamsin kafin su isa gidan. Tun"

"daga bakin gate ta fara buWe idanu tana kalle-kalle. Lokaci Waya zuciyarta ta ™ara jagulewa, komai ya ™ara"

kwance mata.

"Tun sadda aka yi bikin, taji labarin irin gidan da aka kai Zulai a bakin Mashku, amma ko da wasa bata yi"

tsammanin irin wannan tsararre kuma haWaWWen gidan aka kai Zulai ´ar ™auyen ™ayau ba. Da gaskiyar

bahaushe da yace gani ya kori ji.

Ashe haka gidan yake da masifar kyau tun daga bakin gate sai kace a kasar turawa? Aka ce ido wa ka

raina? Ya ce wanda ya saba gani kullum! Duk ™ayatuwar gidansu da irin kwalliyar da ke ciki sai taji ta

raina kyawunshi saboda gani yau da gobe.

"Kai tsaye falon gidan aka yi musu masauki, ta zauna akan kujera tana yatsine-yatsine na rainin ajawali."

"Ita da kanta ta sani ko hasidin Iza hasadin idan ya gani sai ya yaba, amma don tsananin tsanar da take ma"

Zulai yasa ta™i ba zuciyarta damar bayyana irin kyawun da gidan yayi mata akan fuskarta.

"Falon a gyare yake ™al, ga wani daddaWan ™amshi kuma tattausa na turaren wuta da yake fitarwa."

"Kasancewar ranar Assabar ce, Kamal yana gida, bayan zaman mintuna biyar da suka yi suna jiran masu gidan suka fito shi da ita a lokaci guda."

"Daga ganin yadda Zulai ta ™ara yin Sul-Sul, farar fatarta da ya dusashe saboda zaman ™auye ya goge ya"

"tsatso kamar a taSa ta jini ya Sullo, daga kallon fatar za a fahimci jikinta sumul-sumul yake sai shekin hutu da jindadi yake fitarwa."

Daga cikin matsakaicin hijabin da ke jikinta suke hangen kananun kayan da take sanye da shi. Shi kuwa

gogan nata gaba-daya ya kasa dauke idanunshi a kanta sa'ilin da take zirga-zirgar Wauko musu Wan abin taSawa da ji™a ma™oshi.

"Ta tare su da fara'arta, sosai fuskarta ya bayyana jin daWin ganinsu. Har kasa tasa gwiwoyinta ta gaishe"

da Hafiz. Shi kanshi Hafiz Win bakinshi ya ki rufuwa ganin irin kyau da tayi da girma da nutsuwar da ya bayyana a tattare da ita. Babu wannan yarinta da gigin da ya saba gani a jikin Zulan Innaye.

"Bintu kuwa ba™in ciki kamar zai kashe ta, ita kaWai take ™ara kumbura tana han™oro kamar za ta fashe."

Jindadi da farincikin da ta gani a tattare da Zulai ya bala'in ™ona mata rai. Wani rashin wayau da ta yi

kuma shi ne kasa boye hakan da tayi.

Hassada da bakinciki da kishi suka bayyana a fuskarta ™arara. Ita duk a tunaninta wai me wannan banzar

"Zulai Win take da shi ne da zata kasance a cikin irin wannan daular? Yarinyar da ko karatun sakandare bata fita da sakamako mai kyau ba? Yarinyar da tayi rayuwar kauyen kayau? Wacce ta rayu a cikin duhun jahilci da rashin wayewa? Amma ace yau ita ce a cikin babban birnin tarayya, a cikin unguwar da sai"

wane da wance suke zama a cikinta?

Shi daman Kamal irin matasan nan ne masu kwarjini da nutsuwar da in ba sabo kukayi sosai a tsakaninku

"ba basa iya sakin fuska da jiki suyi hira. Ita kuwa Zulai ko da taga take-taken Bintun sai tayi banza da ita, ta share ta, ta mayar da hankali kan Wan'uwanta suna hirar yaushe gamo. Aadeel da ke hannun Bintu ma da taga tana ta wani kara rirrike shi da kankameshi don kar ma ta amshe shi sai tayi kamar ma bata"

ganshi ba.

Tana zaune kusa da mijinta tana sunne kai cikin kunya sa'adda Hafiz ya fara tsokanarta kan irin ™iban da

"ta ™ara, a nutse Kamal Win ke tare mata suna dariya su ukun, kamar sun ma manta da Bintu a cikin falon."

"Izuwa sa'adda suka yi mintuna talatin a cikin gidan, Bintu ta kai ma™ura wajen takura, so take yi su tafi,"

amma ko kallonta Hafiz baya yi balle tayi mishi alamar su tafi.

"Daga ™arshe dai da taga hirar tasu ta ™i ™arewa sai ta fara saka hannu tana tsikarinsa. Ta yi na Waya, ta yi"

"na biyu bai kalleta ko ya tanka ta ba, tana tsikarinsa na ukun kuwa ya daka mata wani gigitaccen tsawa ranshi a Sace."

"""Wai ke miye matsalarki ne?"""

"A tsorace kuma a kunyace ta saukar da ™wayoyin idanunta ™asa, ta kasa ce mishi komai saboda kunyar"

wannan tsawar mai cike da tozarci da yayi mata a gaban Zulai da take gani babban ma™iyiyarta.

"˜asa-™asa yaja tsaki, sai da ™yar ya iya mayar da hankalinshi kan Kamal suka cigaba da tattaunawa kan"

halin da ™asarmu ta tsinci kanta a ciki. Zuciyarsa cike da tunanin murWaWWen hali irin na Bintu.

"'Tun a mota ya faWa mata zai barta a gidan Zulai ita da Aadil su ™arasa yini, idan aka yi sallar magriba sai"

"ya koma ya Wauko ta. A cikin mota bata ce masa za ta zauna ko baza ta zauna ba, shi kuma ganin ta yi shiru sai ya Wauka ta amince ne. Tunda suka shiga gidan, ganin take-takenta yasa shi tunanin baza ta zauna ba. Shi da kanshi a zuciyarsa ya rushe shawarar da ya yanke na barinta a gidan, amma yadda take ciccin magani tana Sata rai abu ne da bai taSa tsammani daga gare ta ba. Sai a yau ya ™ara tabbatarwa da gaske ne Bintu ba ta ™aunar ´an'uwansa, abinda Innaye da ´an'uwansa suka daWe suna yi mishi"

hannunka mai sanda yayi kamar ba ya gani.'

"Ana kiran sallar Azahar, Hafiz da Kamal suka tashi don su je suyi alwala. Zumbur! Itama Bintu ta mi™e a"

"tsammaninta tafiya za suyi, don hankalinta ba shi akan hirar da suke yi bata san sun mi™e da nufin yin"

"sallah bane, ita dama ko gyalenta bata cire ba balle ayi tunanin ta ji daWin zama."

A mamakance Hafiz ya juya yana kallonta

"""Wai ina kike shirin zuwa Bintu? Ki zauna muje muyi sallah mana!"""

"Ganin da Wan sassauci a fuskarsa ba kamar Wazu ba yasa ta yi kwaba-kwaba da fuska, a hankali ta ce"

"""Wallahi ba na jin daWi ne My dear, don Allah muje ka sauke ni a gida sai kayi sallar a can. Aadeel ma"

"na ji jikinshi kamar da zazzaSi."""

"Tsananin haushi da takaici yasa Hafiz kasa magana, ™arin ba™in cikinsa ga Kamal da Zulai duk suna tsaye"

"suna jinsu, ya sani tun Wazu sun fahimci hassada da ™yashi ke Wawainiya da Bintu, a yanzu kuwa daga"

yadda tayi magana ko ™aramin yaro zai fahimci karya ce kawai take shirgawa ba kunya ba tsoron Allah.

"Ya sani idan basu tafi ba, Bintu baza ta taSa nutsuwa tayi yadda yake so a gidan Zulai ba, ta dinga"

"kunyata shi kenan tana zubar mishi da mutunci. Karo na biyu da ya sake ™arewa Bintu kallo, zuciyarsa cike da tunanin irin maganganun su Anty Balira a kan Bintu, da irin abubuwan da take nunawa akan idanunshi tun shigarsu gidan Zulai ayau. Ayar tambayar da ya daWe da Wiga mata a take ta koma alamar"

motsin rai!!

"Ya kasa daina mamaki, ashe da gasken-gaske Bintu ba ™aunar ´an uwanshi take yi ba? Da gaske ne"

abinda ake mishi shaguSe a kanta? A wannan karon lallai idanunshi sun washe.

"""Uhmmm!"""

Yayi ™wafa a fili. Ya ™ara tamke fuska idanunshi a kanta da salon bayar da umarni ya ce

"""Bintu ki zauna inje inyi sallah in dawo."""

Har yayi shiru sai kuma ya ™ara da cewa

"""Na zaci idan da ™auna da soyayya gidan Zulai kamar gidan Mashku yake a gurinki?"""

Ya jefa mata tambayar yana ™ara tsattsareta idanu.

"Da saurin gaske ta taSe baki, ta ™ara da wani zazzare idanu kamar wacce ta ji yayi wani babban saSo a"

maganarsa.

"""Gidan Mashku dai?"""

Ta tambayeshi da mamaki sosai a muryarta. Kafin ya amsa ta ™ara da cewa da cewa

"""Mashkura ™anwata fa? A'ah wallahi! Wannan misalin sam bai ko kusa hawa ba. Kada ma ka ™ara jona"

"min wannan ka-re-ren! In banda ma ™addara me haWo gabas da yamma me zai haWa kifi da kaska?"""

"Tsananin mamaki da takaicin maganganunta yasa shi kasa ce mata komai, sai baki da ya ai hangame"

"yana kallonta, Kafafunshi suka daskare guri Waya kamar an zare mishi laka."

"Ita kuwa Zulai, dariya maganganun Bintu suka bata, a ™asaice, ta saki wata siririyar dariya kafin ta kalli"

"Kamal, da taushin murya sosai ta ce"

"""Abban Imam kar ka makara sallah fa, lokacin yana ™o™arin wucewa"""

Ta sake mayar da idanunta kan Hafiz da murmushi a fuskarta ta ce

"""Yaya mun gode da ziyara, ku gaida gida. In Allah Ya yarda idan na fara fita ni zan zo in muku yini."""

"Daga shi har ita sun san ta fada ne kawai, ba zuwan za tayi ba. Ita kuwa a ranta tuni ta gama kudurtawa"

nan da shekara biyar masu zuwa idan muna raye ba lallai su ga keyarta a cikin gidansu ba.

"Ya kasa amsa ma Zulaikha, sai Wan murmushi da ya sakar mata. Ya Waga hannunshu da™yar ya cusa a"

"aljihu, ya ™irgo dubu ashirin ya aje mata a gefen hannun kujera. Bai saurari godiyar da take masa ba yaja kafa jiki a sanyaye ya fice daga falon, Bintu ta bi shi a baya tana saSe da Aadil a kafaWa, ko arzikin sallama su Zulai basu samu daga bakinta ba."

"Sai da suka isa gurin mota sannan Hafiz ya lura da Kamal na biye da su a baya, sallama yayi mishi a"

"mutunce kafin ya wuce masallaci. Kunya duk ta cika Hafiz, saboda irin rashin kirkin da matarsa ta zuba a gidan ™anwarsa kuma a gaban mijinta. Shi kuwa Kamal da yake wayayyen mutum ne, ko a fuska bai nuna ma Hafiz rashin jin daWin abinda ya faru ba ba."

"Hafiz ya tayar da mota kenan sai ga wata motor tana ™o™arin shigowa, a dole ya dakata har sai da"

"wancan motar ta shigo, ta samu gurin perking kafin ya fara ™o™arin fita da motarsa."

"Kamar an ce ya kalli wancan motar da ta shigo, karaf! Idanunsa suka faWa cikin na Karima da take zaune"

"a mazaunin direba, da waya ma™ale a kunnenta tana magana tana sakin murmushi akai-akai. A gefenta Imam ne gishingiWe akan kujera yana barci."

Akan idanunshi Zulai ta fito daga cikin gidan da saurinta da bayyananniyar murna a fuskarta ta ™arasa

"gurin motar Karima, buWe ™ofar mai zaman banza tayi, ta rungumo yaron cikin tsananin kauna da kulawa"

"ta Wauko shi cak ta fito da shi daga cikin motar, a lokacin ita ma Karima ta fito, suka wani kashe hannu da"

Karima alamar da ke nuna amincin da ke tsakaninsu.

Bai san cewa ya saki baki da hanci yana kallonsu ba sai da Bintu ta taSa shi tana tambayar lafiya? mai

yake kallo?

"""Karima ce fa ´ar gidan Mummy Saudah, baka santa bane ko akwai wani abu ne a tsakaninku?"""

Ta ™arasa tambayar ™arshen da salon da ke bayyana zargi ™arara a muryarta.

"Bai ce mata komi ba, ya cigaba da jan motar a sanyaye suka fice daga gidan."

"A cikin mota haka ta cigaba da mita kamar cin ™wan makauniya, duk dai akan kallon da ya ™ure Karima"

"da shi kamar bai taSa ganinta ba. Shi kuwa ta tafasa sauke bai ce mata ba sai da suka ™arasa gida, sannan ya fara sauke mata kwandon bala'i da tashin hankali irin wanda bai taSa mata ba, duk dai akan irin wula™anci da tozarcin da tayi masa a gidan Zulai. Da irin yadda take wula™anta danginsa a Soye amma a"

gaban idanunsa sai ta dinga nuna mishi tana ™aunarsu.

"Itama da yake a wuya take haka ta biye mishi yana faWa tana faWa, kamar za su ba hammata iska. Daga"

karshe ma da abin ya kai ta ma™ura haka ta nannaWo wani murgujejen zagi ta laulayawa ™auyensu da kafatanin mutanen da ke rayuwa a ™auyen.

"Šif! Ya Wauke wuta na wasu ´an da™i™u, kafin ya farfaWo ya nuna kanshi da yatsarsa manuniya, fuskarsa"

Wauke da matsanancin mamakinta ya ce

"""Bintu! Ni kike kallon tsakiyar idanuna ki zagi ™auyen da na fito da duk mutanen cikinta? Har da ni da"

iyaye da dangina fa kenan? Kika cewa iyayena da dangina kucakan ™auye? Masu datti dangin ™azanta da

"dauWa? Ashe dangina ba danginki bane?"""

Dogon tsaki ta ja babu alamun nadama ko kaWan a fuska da kalamanta ta amsa da

"""Allah suturi bu™wui in ji kishiyar mai mageWuwa. Can ga su gada wallahi, wannan tarkacen ba da ni ba."

"Kaje dai can ka ji da danginka kai da suka zame maka dolen dole ba ni ba. Kuma zancen gaskiya ka ma nisantani da su da tarkacen da ya kwasosu, don tuni na daWe da fahimtar yadda ba sa ™aunata ko kaWan. Daga yau kar in ™ara ganin ™afar wani ya tako min gida. Tunda nayi kawaicin da kawar da

36 / 50