Advertisements
Chapter 28 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 50

81K to 84K   out of 147.7K words

Wakin Hajja su kwaso mata jakunkunan tsarabar da suke ajiye a cikin Wakin. Abinku da an boko wayayyu, masu yin komai cikin tsari, ko wace jaka maale take da sunan mamallakiyarta, kuma saman jakar a rufe yake da wani irin abin maalewa, babu wacce za ta ce ga abinda ke cikin jakar"

ar'uwarta in dai ba buWe jakar aka yi ba.

"Cikin nutsuwa Mummy ta gama rarraba musu tsarabarsu. Ta ara da yi musu godiya sosai, zuwa arfe"

"takwas na dare, gidan ya zama saura su kaWai, bain da suka halarci liyafar duk sun koma gidajensu,"

zukatansu cike da farin cikin tsarabar da Kamal yayi musu.

"Misalin arfe goma da rabi na dare. Kamal ne kwance a gefen katifar Mummy can cikin Bedroom Win ta,"

"hira suke yi a nutse. Yana sake bata labarin yadda yanayin tafiyarsa ta kasance, da irin yadda komai yazo"

"masa a sauae acan Win, da irin nasarorin da ya samu a tafiyar tasa."

Bayan ta gama jera mishi fatan alkhairi da addu'ar Allah ya ara Waukaka sai ta kira sunanshi a nutse. Da

irin salon da ke nuna lallai ko me za ta faWa muhimmiyar magana ce za ta yi mishi.

"""Na'am! Mummyna."""

Ya amsa a tausashe. Yana ara ba ta dukkan hankali da nutsuwarsa.

"""An daWe idan nayi maka maganar aure kana cewa ka dama min wua da nama wajen zaSin matar"

"aure. Tambayarka zanyi, ka samu matar auren ko har yanzu lalube kake a cikin duhu ko kuwa jiran tsammani kake yi?"""

"""Mummy, babu ko Waya gaskiya. Zancen auren ne fa gaba Waya na jingine shi gefe Waya. Ko kin sama"

"min matar auren ne?"""

"Ya tambayeta, da murmushi a fuskarsa."

"""Eh! Na sama maka."""

Ta amsa da dukkan gaskiyarta.

"A nutse ya mie zaune daga kishingiWar da yayi, saboda yadda maganar ta bugi zuciyarsa. Bai taSa Wauka"

"za ta ce ta zaSa masa mata ba, shi yasa a yanzu da ta faWi ta zaSa masa maganar ya bashi mamaki."

"""Wace ce? Mummy wa kika zaSa min? Kin sani ni mai biyayya ga umarninki ne ko da zuciyata ba ta"

"so..."""

"""Babu ma zancen dole a ciki. Shawara ce ba umarni ba. Kaje kayi addu'a, ka nutsu, ka kalli rayuwar"

"Wanka da Allah ya baka a yanzu da can gaba. Zulaikha, ita ce yarinyar da na zaSa maka saboda dalilai masu yawa. In dai kaji zuciyarka ta nutsu da ita, ni kam ina maraba da ita a matsayin sarkuwa, domin na"

"yaba da ita Wari bisa Wari..."""

"""Aunty Zulan Imam kike nufi Mummy? Kina ganin banyi mata tsufa ba? Shekaruna talatin da takwas fa,"

"ni ina mata kallon kamar yarinya ce arama."""

"""Ba wani tsufa da kayi mata, sai dai idan bata yi maka ba, bazan tilastaka ba. Kaje ka huta, kayi addu'a,"

"kayi tunani a nutse. Zuwa nan da sati mai zuwa kazo min da cikakken amsar da ka yanke."""

"""To Mummy. Allah ya tabbatar mana da alkhairi."""

"""Amin ya rabbi."""

"Da haka suka yi sallama ya fice zuwa Wakinsa, zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka yi da"

Mummy.

"A wannan dare, duk irin gajiyar da ke jikinsa bai samu wani wadataccen barci ba. Da ya fara sai ya farka a"

"nutse, zuciyarsa sai hasko masa Zulaikha take yi a sadda ya ganta Wazu babu mayafi, da kuma irin ganin da yayi mata lokacin liyafar nan."

"Babu laifi, ta yi daidai gwargwado. Sai dai abin dubawar shi ne ita za ta iya amincewa da shi a matsayin"

"mijin aurenta kamar yadda Mummy take so? Domin shi fa bai wani iya soyayya ba, ko Aisha a haka suka yi rayuwar babu wani romansiyya ta musamman."

"Wayarshi ya Wauko, ya buWe hotunan status da anwarsa take sakawa na Zulaikha ya fara kallo Waya"

bayan Waya.

"""Uhmmmm!"""

"Yaja nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ajiye wayar gefe Waya."

"Zuzzurfan tunani ya afka a ciki na tunanin makomar rayuwar Wanshi Imam, kamar yadda Mummy ta"

umarce shi. Ya sani ko ya i ko ya so duk tsawon zamani dole ya nema ma Imam wacce za ta zame mishi

makwafin uwa.

"Ada can baya har ya fara tunanin zai iya hauri ya auri Safina ko don saboda Imam, amma sai yaga sam"

babu wata shauwa ko shiri tsakanin Imam da Safina. Idan Imam yaje can gidan yi musu hutu a

"matsayinsu na kakanninshi, duk dawowa idan Imam Win yayi ya dinga mishi orafin Aunty Safina kenan, ya dai fahimci kamar ba ta da hauri da yara. Da wannan dalilin yasa lamarinta ya sane mishi a zuciya."

Ita kuwa Aunty Zulai... shi da kanshi idan ya zauna yana mamakin yadda matsananciyar shauwa ta shiga

"tsakaninta da Imam. Kuma a cikin ananin lokaci haka, Imam bai taSa kai mishi arar Aunty Zulai ba. A"

kullum alkhairinta yake faWa mishi.

"Daga arshe dai, Kamal tattare tunanin komai yayi ya aje gefe Waya. Ya shige banWaki ya Wauro"

"kyakkyawar alwalarsa, ya shimfiWa dadduma ya fuskanci gabas, ya kabbarta sallah don neman zaSin Allah."

"Kwanaki bakwai da Mummy ta bashi yayi tunani, ya shafe su ne cikin yin sallar istikhara ako wane dare."

Kuma cikin hukuncin Allah a kullum al'amarin ara kwanciya yake male-male a cikin ransa. ara samun

nutsuwa yake yi ta musamman.

"Da yake an bashi hutun sati biyu a gurin aikinsa, shi yasa yake ara samun lokacin zaman gida sosai,"

kuma ya mayar da zaman nasa ya fi arfi a Sangaren su Mummy da Wakin Hajjah.

"Ba domin komai ba, sai don ya ara fahimtar wai wacece ma Zulaikha? Don haka a fakaice kuma a"

hankali yake karantar duk yanayinta da Wabi'unta.

Zulaikha kuwa tun tana Wari-Wari da sakin jiki har dai sannu a hankali ta fara sakin jikinta. Saboda ko ta

"janye jikinta shi da kanshi ko Mummy ko Karima ko Hajja sai sun janyo ta, a dole ma ta fara sakin jikinta."

Matsakaitan akwatuna ya kawo musu shae fal da tsaraba ita da Karima. Sai dai kusan gaba Waya kayan

"na turawa ne, ita kuma bata saba saka su ba. Don haka ta nemi guri ta adana akwatin, ba tare da tunanin ranar da za ta iya saka Waya daga cikin kayayyakin ba."

Kwanaki bakwai na cika cif! Da kanshi ya samu Mummy a Wakinta ya sanar da ita ya amince.

"""To Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Sai ka dage kayi oarin neman soyayyarta..."""

"""Soyayya kuma Mummy? Sai kace wani aramin yaro?"""

Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

Dauwa tayi mishi da an yatsunta kafin ta amsa mishi da

"""A'a kai ka yanke ma asa cibiya saboda tsufa Baban Imam! To ina tabbatar maka idan baka nemi"

"soyayyarta ba baza ta taSa aurenka ba, kana zaune garin kallon ruwa kwaWo zaiyi maka afa. An faWa"

"maka irin waWannan kyawawan yaran masu nutsuwa ana sake da su ne? Uhmmm! Ka zauna nan dai, sai dai kaji wufff! Wani ya yi awon gaba da ita..."""

"""Haba Mummy... wannan fa kamar kina min baki ne. Bayan kuma ke da kanki kika kwaWaita min"

"aurenta a raina."""

"""Eh! Duk da haka kuma ai ban ce zan tilastata ta so ka ba. Idan kana son ta ka zubar da duk wani girma"

"ka nemi soyayyarta, na faWa maka."""

"Da haka suka rabu da Mummy, ya fice daga Wakin yana tunanin shi ta ina ma zai fara?"

Bayan Sata hankalin dare da yayi yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin kwarkwanta notikan Autar

Innaye cikin kwanaki alilan. Mataki na farko da ya fara bi shi ne karSan lambar wayarta ta hannun Karima.

"""Yaya?"""

"""Lafiya kuwa?"

"""Allah yasa dai anwar tawa ba laifi tayi ba?"""

Ta jera mishi tambayoyin a firgice.

"""Kin shiga uku da sa'ido Karima. To tambaya zanyi mata akan Imam."""

"Har za ta sake jefa masa wata tambayar, wani Wan tunani da tayi kuma yasa ta sakin murmushi. Katse"

"kiran tayi, cikin asa da minti Waya ta tura mishi lambar Zulaikha, a asan lambar ta ara da"

"""Allah yasa mu ji alkhairi Yayana."""

"Dariya kawai yayi, ya amsa addu'ar a fili amma bai mayar mata da martani ba."

******

Sannu a hankali cikin kwanaki alilan shauwa mai arfi ya shiga tsakanin Abban Imam da Umman Imam.

"Kamar yadda Zulaikha take kiranshi shi ma yake kiranta, amma arfin shauwar tasu ta fi a waya, gurin"

"chatting da kuma kiran da yake yawan takura mata da shi da cewar ya kira ne suyi hira, yana gidan ko ba ya gidan."

"A cikin kwanakin ya hana ta da zuciyarta sakat! Duk inda ta bi da tunaninsa maale da ita, saboda yadda"

"yake yawan sakota cikin al'amuransa. A cikin hirarrakin da suke yi, cikin hikima ya bata labarin kaso saba'in cikin Wari na rayuwarsa."

Yanzu har an kai matakin da idan ya tafi gurin aiki kafin ya dawo zai kira ta ya faWi abincin da yake so ta

"dafa mishi. Ita kuma bata taSa ce mishi a'a ba, yana dawowa zai tarar da abinda yake so an jera mishi a"

"dining Win Sangarensa. Sai dai ba ta taSa yarda ta etara iyakar addininta wajen mu'amala da shi, a"

"taaice ma, ta fi sakewa da shi suyi hira sosai ta waya, a fili ba aramin kunyarsa take ji ba."

"Tana zama a inda yake suyi hira ne kaWai idan su Mummy suna gurin, duk yadda yaso su dinga keSewa ta"

"i bashi damar hakan. Shi kuwa bai takura ta ba, ko a hakan ma ya gode, kuma kan tafe kan isa watarana jariri ango ne."

******

Duk yadda ya so ya yakice tunaninta a zuciyarsa ya kasa. Ga wani matsanancin ciwon kai da yake ta

"addabarsa tun da asubah. Har ya Wauki jakarsa ta zuwa wurin aiki ya ajiye, ko takalmin afarsa bai samu"

"sararin cirewa ba ya faWa rub da ciki a kan gado, afafuwansa na lilo a asa."

"Hannunsa ya laluba ya janyo filo guda Waya ya Wora kansa, sannan ya sake Wauko wani filon ya kifa a"

"kansa. Lumshe idanu yayi, a zuciyarsa yake ta addu'ar Allah ya kawo barci ya Wauke shi ko na awa Waya ne."

"Cikin hukuncin Allah kuma sai addu'arsa ta karSu. Barcin ya Wauke shi, amma irin rikitaccen barcinnan"

"mai tafe da wasu irin birkitattun mafarkai. Kamar dai yadda ya faru da shi cikin dare, wani al'amari da tun bayan rasuwar marigayiya da ya tattara batun aure ya ajiye gefe Waya bai sake faruwa da shi ba sai"

yanzu.

"Yanzu Win ma kuma akan Zulaikha, Aunty Zulan da duka-duka tsawon lokacin da ya san da wanzuwarta a"

"duniya basu taka kara sun karya ba. Haka ya farka a firgice, ko da ya fahimci abinda ya sake faruwa a karo na biyu tsakanin daren jiya zuwa yanzu wani matsanancin kunya ne ya lulluSe shi."

"Filon da ya Wora a kanshi ya janye ya rungume tsam-tsam a irjinsa, ya janyo lallausan bargon da ke ajiye"

"a gefen gadon ya lulluSa har kansa. ara matse filon yayi, zuciya da gangar jikinsa cike da wani irin matsanancin shaui da son aure arara."

"Shi kaWai, ya kwaSe fuska kamar zai saka kuka. A hankali ya ce"

"""Na shiga uku, Allah na tuba ka yafe ni. Wannan yarinyar za ta lalata ma Mummy Wa."""

"Shi kaWai, yayi ta juyi akan gadon yana ara jin yadda sabon al'amarin ke ara amsuwa a dukka sassan"

jikinsa. Ga kansa da yake matsanancin ciwo har lokacin bai sassauta masa ba. A jejjere yake ta sauke

"ajiyar zuciya. Dayar ya yunura ya mie ya nufi banWaki, ko da ya tsaya a gaban madubi, sai yaga idanunsa sun yi ja sosai."

KaWa kai kawai yayi hannunsa Waya dafe da mararsa yana tafe a hankali har ya shige banWaki. Ruwan

"sanyi ya sakar ma kansa da tsammanin zai samu sassauci a yanayin da yake ciki, ashe bayan tiya akwai wata cacar, yana gama yin wankan kuma ya fara rawar Wari. Alamun zazzaSi na shirin kawo masa farmaki."

"Dayar, ya iya janyo Waya daga cikin rigunan wanka masu kauri da suke ajiye a banWakin ya saka a jikinsa,"

ya lallaSa a hankali ya fice daga bayin. Kan gadon ya sake komawa ya udundune jikinsa gaba Waya da

"bargo, haoransa sai haWuwa suke gaf-gaf."

Ya Wauki tsawon lokaci a cikin wannan hali yana ta jan duk addu'o'in da suka zo zuciyarsa. Hankalinsa a

"tashe, ga shi ya kasa miewa tsaye balle ko waya ce ya Wauka ya kira cikin gida a kawo mishi Wauki."

"Sannu a hankali kuma sai barci ya fara fisgarsa, haka yayi barcin a jigace, da yake akwai bashin barci a"

"idanunsa fiye da awa Waya yana barci sannan ya farka. A lokacin kuma zazzaSin ya sauka, zufa ya lulluSe gaba Waya jikinsa."

"Hamdala yayi sannan ya janye bargon daga jikinsa ya mie tsaye, gurin kayansa ya nufa ya Wauki wasu"

"kayan marasa nauyi ya canja. Ko da ya kalli agogo, arfe goma sha Waya da kwata ne na safe."

"Mai ya shafa sama-sama ya fesa turare. Ya yaye zanin gadon da ke shimfiWe akan gadonsa ya canja wani,"

sannan ya sake hayewa kan gadon ya kwanta bayan ya Wauki wayarsa.

Har ya lalubo lambarta zai kira sai kuma ya yanke shawarar bari ya fara dubawa ko tana Online.

"wawarar magana yake so suyi guda Waya, tsakanin jiya zuwa yau irin abubuwan da suka faru da shi sun bashi tsoro, bai san idan ya cigaba da jan lokaci yana lallaSata me zai iya faruwa a gaba ba."

Gara kawai ya fito fili ya faWa mata halin da zuciyarsa take ciki game da ita. Yana da kyakkyawar yainin

"in sha Allahu za ta fahimce shi, za kuma ta bashi damar da yake buata, ayi komai a gaggauce a wuce"

gurin kafin shaiWan ya jefa shi a halaka.

"""Hi Beb!"""

"Ya fara tura mata, zuciyarsa cike da fatan tana kusa da wayar, ya sani in dai taga saonsa za ta amsa"

mishi a gaggauce.

"Minti biyu tsakani ya tsura ma suna da lambarta idanu kafin yaga ta buWe saon, nannauyar ajiyar zuciya"

ya sauke lokacin da yaga alamun tana typing daga can Sangaren.

"""Abban Imam! Ya aiki? Fatan ka isa Ofis lafiya?"""

"""Ban fita ba fa, ba ni da lafiya Wallahi. Har na Wauki jaka kawai na ajiye na koma na kwanta."""

"A arshen saon, ya ara da hoton kan gwaigwai (Emoji) mai nuna alamar shagwaSa, da mai nuna zama"

"abin tausayi, da mai kuka ya tura mata."

"Mamaki ne ya Wan kamata, domin tun sassafe suka yi waya, bayan gaisuwa da tambayar yadda ta wayi"

"gari ya tabbatar mata a ranar bazai karya a gida ba. Zaiyi sammakon tafiya Ofis ne, akwai wasu"

"muhimman ayyuka da bai arasa jiya ba, yau zai arasa ya tura su Lagos."

Da damuwa a fuskarta kamar yana gabanta ta ce

"""Subhanallahi! Me yake damunka Abban Imam?"""

"""Ke ce!"""

"Ya amsa mata kai tsaye, ba tare da wata kwana-kwana ko Soye-Soye ba."

Da mamaki sosai ta tura mishi da kan gwaigwai na zare idanu. Sannan ta ara da rubuta mishi

"""Ni kuma?"""

"""Eh"""

"Ya sake amsawa, sannan ya tura mata da alamar zuciya mai motsi."

"""Allah sarki ni... Me nayi kuma?"""

"Ta aika mishi da tambayar. Acan Sangarenta, sake gyara kwanciya tayi akan katifar Hajja tana ara rie"

wayar am-am a hannunta. Ta rasa dalilin da yasa duk cikin mutanen da take mu'amala da su lamarin

Abban Imam na musamman ne a zuciyarta.

"Ko a waya idan suna magana, ko kuma idan suna chatting, irin yadda yake riritata, yana nuna mata ita"

"Win ta musamman ce. Yana mata raki da shagwaSa-shagwaSa kamar wani Imam, ita kaWai ta san irin yanayin da take ji a jikinta. Bakinta bazai taSa iya fasalta irin yadda take ji ba, shi yasa ako wane lokaci cikin jin kunyarsa take. In dai ba akwai su Mummy a gurin ba gaskiya ba ta jin kunya zai barta ta iya"

sakewa da shi suyi magana ko da na minti biyar ne kacal.

"Amma a waya, ko kuma ta kafar sadarwa, tunda ba ganin idanun juna suke yi ba shi yasa har take iya"

sakewa da shi suyi hira haka.

"[2/6, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: ""Kin hana ni nutsuwa Beb! Kin hana zuciyata samun nutsuwa tun"

"sa'adda na fara yin tozali da kyakkyawar fuskarki. A yanzu kuma Wan barcin da nake samun yi raba da rabi ma kina neman hana ni. Don Allah ki barni in huta mana Beb."""

"urum! Doguwar saonsa ya faWo cikin wayarta. Jikinta na Wan rawa ta buWe, domin ko da ta ji shi shiru,"

kusan mintuna biyar bai ba ta amsa ba. Tayi tunanin ko ya sauka ne.

A yanzu da saonsa ya shigo da sauri ta buWe don jin laifin me tayi masa? Ko da ta gama karanta dogon

"saon, jikinta ne gaba Waya ya Wauka Wummm! Sannu a hankali ta Wora lumshe idanunta."

Sai a yanzu ta ara zurfafa tunaninta akan irin yanayin da take ji akan Abban Imamu. Duk da a iya tsawon

rayuwarta bata taSa faWawa cikin kogin son wani mahaluki a faWin duniya ba. A yanzu kam ko rantsuwa tayi babu kaffara wannan yanayin da take ji a jiki da zuciyarta ba komai bane face alamomin So.

"""So dai?"""

Tayi ma kanta tambayar a fili tana mamaki.

"""So kuma? Wa ake so ko kuma wa yake so?"""

Hajja da fitowarta kenan daga banWaki zancen da Zulaikha tayi ya dira a kunnenta tsulum ta saka bakinta.

"""Hajja ba fa magana nayi ba... zancen zuci ne kawai ya fito fili. Wani labari nake karantawa a facebook"

"ya Wauki hankalina."""

Ta amsa ma Hajja da sauri tana oarin buWe wayarta da taji arar sao ya sake shigowa.

"""Beb! Baki ce komai ba... Ki agaza ma an Mummy kar kiyi kisan kai... Da gaske nake yi fa..."""

Saon da Abban Imam ya ara turo mata.

"Lura da tayi shauin da take ji na Soyayyar Abban Imamu zai iya saka ta yanka ihu a Wakin Hajja, sawunta"

a likkafa ta sauka akan gadon.

"""Hajja ina zuwa, ki gama shiryawan zan dawo yanzu in lallaSe miki kan."""

Ta fice da sauri tun kafin Hajja ta amsa.

"Sai da ta shige Wakinta, ta mayar da ofar ta rufe, ta jingina da jikin ofar sannan ta iya ba shi amsa"

"""To ni me zan ce? Ni dai babu ruwana... Kar ma ka bari wani ya ji wannan wasar da kake min."""

"""Wallahi, Summa tallahi ina son ki Zulaikha."""

Ya tura mata da sauri saonta na isa gare shi.

"""Da gaske nake yi, ina bala'in son ki."""

Ya sake tura mata.

"""Don Allah, don girman Allah kar ki ce min bakya so na."""

A karo na uku ya sake tura mata.

"""Na sani akwai tazarar shekaru masu Wan yawa a tsakaninmu, amma na miki alawarin zan so ki, in"

"riritaki, in shagwaSa ki, in ji da ke, har ma fiye da saurayin da kike tunanin aura."""

Saon shi ya sake sauka a karo na huWu.

"""Ki taimakeni Beby ki so ni, ko da rabin son da nake miki ne. Ke ni ko bakya jin so na a yanzu, ki bani"

"dama don girman Allah in koya miki so na. In Allah ya yarda baza kiyi da na sani ba."""

"Tsananin yadda maganganunsa suka kassara mata sassan jiki, yasa bata san sa'adda ta zame zuwa asa"

"ba. Saboda jin afafunta tayi kamar an zare mata duk wasu asusuwa da suke cikinsu. Ta karanta saon, ta ara maimaitawa, a karo na

28 / 50