Advertisements
Chapter 8 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 50

21K to 24K   out of 147.7K words

ruwan da kake kira da ™azantacce tun kafin a haife ka shi muke sha, muke komai da"

"shi. Kuma kai Win ma kafin barowarka ™auyen ™azantaccen ruwan nan dai kake sha, kuma ya rayar da kai"

"har zuwa girmanka."""

Innaye ta katse shi da Wan murmushi a fuskarta na jin daWin yadda ™arara Wan nata ke nuna damuwa da

lafiyarta.

"˜ara gyara zama yayi yana cigaba da yi mata ™arin bayani, a fuska da muryarsa babu abinda ke fita sai"

matsananciyar ™aunar mahaifiyarsa.

"""Duk da haka dai Innaye. Kin san yanzu abubuwan sun canja ba kamar da ba. Yanzu cututtuka ba su"

"wuyar shiga jikin Wan Adam. Ya zama dole mu dinga ™o™arin kiyaye duk abubuwan da aka tabbatar suna da rawar da suke takawa wajen Wabba™a samuwar cututtuka a jikinmu. Amma idan baki gamsu ba ga Bintu nan, tunda ita likita ce za ta miki cikakken bayanin da za ki fahimta na abubuwan da ya kamata ki kiyaye."""

Ya maida idanu kan Bintu yana jiran tayi ma Innaye ™arin bayani kamar yadda ya nema. Abu Waya da bai

"sani ba shi ne Bintu dai ba baka sai kunne, sai a yanzu ne duk irin cin kashi da tozarcin da tayi ma Innaye tun bayan fitarsu yake dawo mata arai, a tsorace take sosai kar Innaye tayi suSul da bakan furta Waya daga cikin abinda ta aikata mata."

"""Eh! Haka ne My Dear. Uhmmm! Innaye don Allah ki kiyaye. Duk abinda zan faWa My dear ya riga ya"

"faWa, yanzu dai bari in haWa alluran inyi miki in baki magungunan. Ina fatan kin ci abinci?"""

Ta ™arasa da tambayar har lokacin ta kasa Waga idanu ta kalli Innaye cikin ido.

"""Eh na ci."""

Innaye ta amsa idanunta na kallon irin ruWewar da Bintu take ciki. Duk da tayi hasashen me ya Waga

"hankalin Bintu cikin ™an™anin lokaci haka, amma sam bata yi niyyar tona abinda tayi mata ba. Idan tayi"

haka kamar bata gode Allah da ya dube ta ya haWa ta da Karimatu a lokacin da Bintu ta so tozarta ta bane.

Tana kallo Bintu ta haWa allurai har guda biyu tayi mata. Sannan ta Sallo magunguna kala huWu ko wanne

Wai-Wai ta mi™a mata. Hafiz ya buWe Waya daga cikin gororin ruwan da ke cikin Wakin ya zuba a kofi ya

mi™a mata.

Sai da tasha magungunan ta haWiye sannan Bintu ta fice daga cikin Wakin bayan ta basu uzurin za ta je ta

amsa waya. Nan ta bar Hafiz suna cigaba da hira da Innaye ita dai ta cikawa bujenta iska tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Har lokacin bata daina addu'ar Allah ya kulle bakin Innaye kar ya bata ikon

tona asirin tozarcin da tayi mata a asibiti.

"Duk abinda ke faruwa har zuwa ficewar Bintu, da ficewar Hafiz bayan an kira sallar isha'i, Zulaikha tana"

jin su. Ko ™wa™™waran motsi bata yi bane domin ba ta ™aunar tozali da Waya daga cikin fuskokin su biyun.

"""Auta? Wai lafiya kike kuwa?"""

"Innaye ta jefa mata tambayar lokacin da ta yaye rufar da tayi ma kanta, ta mi™e ta zauna akan gadon"

tana mutsuttsuka idanunta kamar wacce ta farka daga barci.

"""Lafiya ™alau. Kawai dai ba na jin daWi ne."""

Ta amsa fuskarta ba walwala.

"""Wallahi Innaye duk na ™osa mu koma gida."""

Ta sake faWa fuskarta na bayyana gaskiyar maganar daga zuciyarta ne.

Da™i™u talatin Innaye ta Wauka tana karantar yanayinta. Irin shirun da Auta tayi tun bayan da ta idar da

"sallah, ta san ba haka kawai bane. Amma tunda bata faWa mata komai ba sai bata matsa mata da tambaya ba, don wani sashe na zuciyarta na tunanin ko don maganar auren da tayi mata Wazu ne ya canja yanayinta? Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ce"

"""Ki kwantar da hankalinki. Kamar gobe ne za mu koma gida in sha Allahu."""

*****

"Duk da kasancewarta cikin mutane masu nauyin barci, irin numfarfashin da Innaye take ja sama-sama"

tana saukewa a wahalce ya fi ™arfin a ce ta gagara farkawa.

"Bayan ™arfin nishin kuma kusa da kusa suke kwance. Tun tana jin nishin kamar a mafarki, har dai daga"

baya ta tabbatar ba mafarki take yi ba don haka ta farka a firgice.

"""Innaye? Inna lillahi... Me yake damunki?"""

"Ta jera mata tambayoyin a ruWe. Kafin ta amsa da saurin gaske ta mi™a hannu ta taSa wuyan Innayen,"

matsanancin zafin da taji yasa tayi saurin Wauke hannunta a gaggauce.

"""Subhanallahi... Jikinki zafi sosai Innaye... ZazzaSi kike yi ne? Bari in kira Yaya."""

Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ta yun™ura za ta sauka akan gadon a galabaice Innaye ta

ri™o hannunta.

"""Dare... dare ya yi... ki ™yale.. shi zuwa safe."""

"Tayi maganar da™yar, da yanayin da ke bayyana tana cikin mawuyacin hali."

"Tafin hannun Zulaikha da ke cikin nata ta sake ri™ewa sosai, ta ja hannun a hankali har zuwa kan goshinta,"

a jiga ce ta sake cewa

"""Kaina ciwo sosai kamar zai faWi, ki kama min Auta."""

Ta sake faWa a wahalce.

Kasancewarta mai saurin kuka tuni har hawaye ya wanke mata fuska. Ta matsa sosai kusa da Innaye ta

Wauki kanta ta Wora akan cinyarta.

"Kamun kai tayi mata kamar yadda ta bu™ata, bayan ta gama sai ta cigaba da tofa mata duk irin addu'ar"

da ya zo bakinta.

Ko da ta Waga idanu ta kalli agogon da ke ma™ale a bango cikin Wan madaidaicin hasken da suke bari a

"kunne idan za su kwanta. Sai taga ™arfe uku na dare saura minti takwas, sai a lokacin ita da kanta taga"

rashin dacewa kiran Yaya Hafiz a wannan tsakiyar dare.

"Duk irin barcin da ke idanunta tuni ta neme shi ta rasa, a ta™aice ma idanunta bushewa suka yi, idanunta"

biyu tana hawaye tana tofe Innaye da addu'a har zuwa lokacin da ladanin unguwar ya kwaWa kiran sallar farko.

"A wannan dare, ta shiga cikin gagarumin tashin hankali ne irin wanda bata taSa shiga ba a rayuwarta."

Tun da tayi wayau bata taSa ganin Innaye cikin ciwon da ya jigatar da ita ya fitar da ita a hayyacinta cikin

™an™anin lokaci irin haka ba.

Ko wannan ciwon da take yi har ya zama sanadiyyar da yasa suka baro garinsu zuwa Abuja bai mata

"tsanani haka ba. Bata taSa tsammanin Innaye za ta kai asubahi a raye ba, ta gama fitar da rai da cewar Innaye za ta cigaba da rayuwa, saboda yadda numfashin ma a wahalce take ja tana saukewa da™yar. Amma da yake rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke sai ga shi cikin hukuncin Allah ana tayar da"

i™amar sallar asubah wani nannauyan barci yayi awon gaba da Innaye.

"Minti Waya, biyu, sai ta kara kunnenta a hancin Innaye don ta ™ara tabbatar da barcin take yi ko dai ba"

barcin bane? Sai da ta tabbatar barcin ne kafin ta iya kwantar da kan Innaye a hankali bisa filo ta sauka daga kan gadon.

"˜afafunta duk sunyi tsami, idanuwanta sun kumbura sunyi tulu-tulu saboda kuka. Jikinta a sanyaye ta"

shige banWaki domin Wauro alwala.

"Ko da ta idar da sallah, bata tsaya yin Azkhar kamar yadda take yi duk bayan sallar asubahi ba tayi addu'a"

"a gaggauce ta sake hayewa kan gadon tana Wan tattaSa jikin Innaye. Cikin hukuncin Allah kuma sai taji zazzafan zazzaSin ya sauka gaba Waya, har ma wani zufa ne ya Wan tsattsafo akan goshinta."

Gefen hijabin da ke jikinta tasa ta goge ma Innaye gumin tana sauke nannauyan ajiyar zuciyar samun

"nutsuwa. A nan kan gadon, ta cigaba da Azkhar har zuwa sadda wani daddaWan barci ya kwasheta."

Sallamar da Hafiz yake ta dokawa a ™ofar Wakin shi ya farkar da ita a firgice daga wani mummunan

"mafarki da take yi a daidai lokacin. Karaf idanunta suka faWa kan agogo, ™arfe bakwai da minti arba'in da"

biyu na safe.

"Izuwa lokacin, Hafiz ya gaji da sallamar da yake ta yi yana ™arawa ya shiga cikin Wakin don ganin lafiya"

suke kuwa?

Idanunsa cikin nata ya zabga mata harara.

"""Don tsabar iskanci kina ji ina ta doka sallama kin ™i amsawa?"""

"""Yi ha™uri. Barci nake yi, sallamarka ce ta tashe ni. Ina kwana?"""

"Ta jera mishi maganganun cikin sanyin murya, kamar dai ba Zulai ba da yasan ta bala'in raina shi."

Irin yadda ta amsa mishi har sai da yasa shi ™ara kallonta sau Waya. Sai yaga ta sunkuyar da kanta ™asa

"tana wasa da yatsun hannayenta. TaSe baki yayi, ya ™arasa cikin Wakin har kusa da gadon idanunsa akan Innaye da har lokacin take barci."

"""Wani irin barci Innaye take yi haka? Ina fatan dai lafiyarta ™alau?"""

Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba. Babban dalilin da yasa shi yin tambayar kuwa shi ne

"barci bayan sallar asubahi ba Wabi'ar Innaye bace, ko lokacin azumi ita ba ta komawa irin barcin nan na bayan sallar asubah."

Zama take tai ta tasbihi da istigfari har gari yayi haske sosai tayi sallar walha. Ko za ta kwanta sai bayan

"ta idar da sallar walha, tara da rabi zuwa karfe goma na safe."

"""Ba ta da lafiya. Kwana tayi da zazzaSi mai zafi a jikinta kamar baza ta wayi gari ba..."""

"""Bakinki ya sari Wanyen kashi. Sakarya kawai wacce bata iya magana ba. Kawai don ta kwana da zazzaSi"

"a jikinta sai ki ce kaman baza ta wayi gari ba?"""

Nan ya cigaba da zazzaga mata faWa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kawai don ta ce Innaye

kamar baza ta wayi gari ba.

"Ita dai Zulaikha shiru tayi mishi, a madadin ta ce wani abu ma sai ™ara sunkuyar da kanta ™asa tayi"

idanuwanta na tsiyayar da hawaye. A zuciyarta take ™ara tunanin irin rijiya da bayan da Innaye ta

"tsallake jiya, duk da tana yarinya kuma ba'a taSa yin mutuwa a gabanta ba ta san bata yi kuskuren cewa irin zazzaSin da Innaye tayi jiya kamar baza ta wayi gari ba."

"Amma tunda ba a gabanshi aka yi ba dole tayi mishi uzuri, ta san babu ma amfanin yi mishi ™arin bayani"

don bazai fahimce ta ba. Tana jin shi har ya gama zazzaga masifar da yake yi ya fice daga Wakin a gaggauce yana jan tsaki.

"Zuciyarsa cike da Sacin ran kalmar da Zulaikha ta faWa. Shi yasa sam ba ya shiri da yarinyar, bata iya"

magana ba. Wasu lokutan haka take sakin maganganu kamar ta ci kashi.

"Bai daWe da fita ba ya dawo cikin Wakin, Bintu na biye da shi cikin shirinta na fita aiki, sai Sata fuska take"

yi kamar anyi mata dole.

"Amma ko da Hafiz ya juya yana nuna mata Innaye da yi mata ™arin bayanin kwana da tayi da zazzaSi, sai"

tayi saurin daidaita fuskarta zuwa yanayin jimami da tausayawa.

"Duk abinda take yi, ™asa-™asa Zulaikha ke kallonta zuciyarta cike da mamakinta. Tana sane ko gaishe ta"

"bata yi ba, don har lokacin Sacin ran cin mutunci da tozarcin da tayi mata jiya bai bar zuciyarta ba."

A tausashe Bintu ta kalli Hafiz tana mishi ™arin bayani bayan ta Wan tattaSa jikin Innaye sama-sama. A

"lokacin ita ma Innaye ta farka, ta buWe idanunta a jigace tana rarraba idanu a tsakaninsu."

"""Sweetheart, ka kwantar da hankalinka. Daman dole za'a sami irin waWannan ™ananun matsalolin."

"Magunguna da alluran da na kawo mata masu kyau ne sosai, don haka a karon farko dole ta fuskanci irin waWannan matsalolin, tunda a iya tsawon rayuwarta bata taSa amfani da magunguna masu kyau da ™arfin waWannan ba. Cikin ™an™anin lokaci za ta daina fuskantar zazzaSin, magungunan kuma za su"

"fatattaki duk wani typhoid da maleria da yake jikinta."""

Da damuwa sosai a fuskarsa ya ce

"""Yanzu babu wani taimako da za'a iya mata ta daina fuskantar zazzaSin? Ki dubi fa yadda idanunta suka"

"yi zuru-zuru zazzaSin dare Waya kawai."""

"""I'm sorry to say gaskiya babu. Haka nan za muyi ha™uri ta cigaba da shan magungunan. Ka san kuma"

"jiki-jiki, kowa da yadda magani da allura ke aiki a jikinshi. Ita wannan alamun shi ya bani tabbacin magani da alluran sun karSe ta, kuma fa ba lallai yau tayi zazzaSin ba. Ka kwantar da hankalinka pls."""

"Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Innaye, a tausashe ta fara gaishe ta da jiki."

"""Sannu Innaye. Allah ya ™ara sau™i. Yanzu dai Zulai ki kamata zuwa bayi a wanke mata baki tayi break"

"fast, sai inyi mata allura kafin in fita. In sha Allah za ta samu sauki sosai."""

Ta ™arasa maganar idanunta na kan Zulaikha da har lokacin ta ™i yarda ta Waga fuska su kalli juna cikin

ido.

Ko kafin Zulaikha tayi yun™urin Waga Innaye da ko magana bata iyawa har Hafiz ya tarairayota zuwa

jikinsa a tausashe ya zaunar da ita.

"""Sannu Innaye. Allah ya baki lafiya."""

"Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa amsawa, sai raba idanu take yi tsakanin shi da Zulaikha da suke ta"

jera mata sannu kamar za su ari baki.

TaSe baki Bintu tayi ta fice daga Wakin bayan ta ba Hafiz uzurin bari taje ta ™arasa shiryawa kafin Innaye

ta gama.

"""Zanyi wanka... Sai inyi sallah."""

Innaye tayi maganar a hankali sosai yadda har basu ji abinda ta ce ba sai da Hafiz ya kara kunnensa

daidai bakinta.

"Zaunar da ita yayi a gefen gadon ya jingina mata filo, da rawar jiki ya shige banWaki ya sirka mata ruwan"

wanka. Har cikin banWakin ya kai ta ya umarci Zulai ta taimaka mata tayi wanka da alwala kafin ya fice daga banWakin.

Can Sangarensu ya koma a gaggauce. Šakinsa ya shige ya sauya kayan jikinsa saboda yamutsewar da

"yayi a dalilin hidimta ma Innaye, bai Sata lokaci ba ya fice daga cikin Wakin ya wuce kicin. Tsaye yayi yana Wan tunanin abinda ya kamata yayi, sai kuma ya buWe kayan karin kumallon da Bintu ta shirya mishi a cikin basket zai wuce da shi Ofis ya Wauko Waya daga cikin kulolin da ya siyo ma Innaye ya sake musu gaba Waya. Jikinsa sai rawa yake yi, bai ce ma Bintu da take tsaye tana kallonsa komai ba ya fice daga"

kicin Win.

"Duk abinda yake yi tana tsaye tana kallonshi ranta a Sace, ta kasa ce mishi komai saboda ™uncin zuciya."

Bayan fitarsa a fili take ™ara Allah wadarai da zuwan Innaye gidanta. Domin a zuwansu ne ta ga abubuwa

mabanbanta da bata taSa tsammanin za ta gansu daga Sangaren Hafiz Win ba.

Tun bayan zuwansu kwanaki biyu kawai ta Wauka tana yi musu abinci a mutunce kuma sau uku a rana. A

"rana na uku ta sakar ma mai aikinta Rabi ragamar komai na su, aka koma basu dafaffen abinci sau Waya a rana."

Ita da kanta ta Webi kayan tea da flask da kofuna ta kai musu can Sangaren da suke. Sannan ta zauna

cikin gwari-gwari tayi musu bayanin da ta Wauki tsawon da™i™u tana tsarawa a zuciyarta.

'Innaye ga waWannan kayayyakin. Kayan tea ne wadatacce da za ku dinga amfani da su gurin karyawa a

"iya tsawon kwanakin da za kuyi a gidannan, idan sun ™are kar kuji komai a faWa min. Sannan a Sangaren abincin rana da yamma, na faWa ma Baba Rabi ta dinga dafa komai a wadace tana zubo muku isasshe a"

kula wanda zai ishe ku cin rana da dare.

"Kuyi ha™uri, kun san yanayin aikina ba na zama bane, a mafiyawancin lokuta ni da My dear abincin dare"

ko na safe kawai muke iya ci tare cikin nutsuwa saboda yanayin aikinmu na da banbancin lokuta.

Ko a cikin kwanaki biyunnan da kuka ga na samu lokacin kula da ku sosai hutu ne na samu a gurin aiki.

"Yanzu kuma hutun ya ™are, ina fatan za ku fahimce ni kuma kuyi min uzuri.'"

"A lokacin, daga yadda Innaye tai ta saka mata albarka tana ™ara ™arfafa mata gwuiwa akan aikinta na"

ceton rayukan al'umma ya tabbatar mata Innaye ta gamsu da maganganunta Wari bisa Wari.

Shi kuma Hafiz kasancewarsa irin mazajennan masu sakarwa matayensu ragamar komai bai taSa

tuhumar ko me za ta ko ta aikata ba. Ko da yaga an daina kai ma su Innaye abin karyawa sai dai sun™in

biredi kawai bai taSa tambayarta dalili ba.

"Ko yanzu ba ta tsammanin zai nuna mata wani Sacin rai, amma irin wannan Sare-Saren jikin da yake yi"

akan tsohuwar shi ne abinda yake ™ona mata zuciya. A ganinta ba komai zai ™ara janyo mata a gurinsu ba sai ™as™anci da rashin godiya akan duk abinda za ta musu nan gaba.

'Saboda Allah in banda salon zubar da mutunci da niyyar janyo mata tozarci kayan karin kumallon da ta

hana idanunta komawa barci ta shirya musu ita da shi shi ne zai juye nashi gaba Waya ya kai musu?' Dogon tsaki taja Sacin ranta na ™ara hauhawa.

"Ta daWe a gurin tana sa™e-sa™e kafin ta wuce ta cigaba da shiryawa, duk bayan mintuna take jan tsaki"

™asa-™asa idan ta tuno abinda ya faru. Haka nan ba don ranta na so ba ta sake raba nata abincin gida

biyu ta zuba mishi rabi a kulolinsa.

"Ko da Hafiz ya koma cikin Wakin, a kan dadduma ya tarar da Innaye tana sallah a zaune. Ita kuma"

Zulaikha tana tsaye jikin gado tana gyara shimfiWar gadon.

"Kusa da Innaye ya zauna, ya buWe kulolin abincin ya fara zuba mata. Lafiyayyen alalen dankalin turawa"

"ne da miyan ganye, a gefe guda kuma ga kunun gyaWa da aka dama shi da madara, yayi fari kar gwanin"

ban kyawun kallo a idanu. Sai ™amshi yake fitarwa.

"Šauri biyu ya zuba alalen dankalin a faranti, ya sa cokali ya buWa cikinsa yadda zaiyi saurin shan iska."

Kunun gyaWar ma Wan madaidaici ya zuba a kofi ya saka cokali yana jujjuyawa don kunun yasha iska da sauri.

Ya du™ufa kan abinda yake yi har bai san Innaye ta idar da sallar ba sai da ya jiyo muryarta ™asa-™asa ta

kira sunanshi.

"""Hafizu?"""

"""Na'am Innaye. Kin idar? Sannu ya jikin naki?"""

Ya amsa yana kallonta a tausashe.

"""Jiki Alhamdulillahi Hafizu."""

Ta sake amsawa da sanyin murya sosai. Sai kuma ta mayar da idanunta kan Zulaikha da itama ta tsaya da

gyaran gadon da take yi tana kallonta cikin kulawa da tausayawa.

"""Sannu da ™o™ari Auta. Jiya ban bari kinyi barci ba. Allah yayi miki albarka."""

"""Amin Innaye. Allah ya ™ara miki lafiya da nisan kwana."""

"""Amin ya rabb!"""

Hafiz yayi gaggawar amsawa tun kafin Innaye ta amsa. Ta buWe baki za tayi magana ya riga ta da cewa

"""Innaye kiyi shiru haka nan. Kin ga jikinki babu ™arfi, ki karya sai ki sha magani, Bintu za tayi miki allura"

"kafin ta fita aiki."""

"""To"""

"Ta amsa a sanyaye. A zuciyarta take ji kamar ta ce mishi a dakata da magani da alluran, amma da ta tuno"

irin bayanin da ta ji Bintu tana yi mishi Wazu sadda ta farka barci sai bata furta abinda yake zuciyarta ba.

A baki yai ta bata abincin yana ba ta kunun tana kurSa a hankali har sai da ta kawar da kanta alamun ta

™oshi.

"""Ki daure ki ™ara ko kaWan Innaye, kin san wasu magungunan rashin isasshen abinci a ciki yana sa su"

"wahalar da mutum."""

"""Na ™oshi Hafizu. In dai ba so kake in amayar da wanda ya shiga cikina ba."""

Ta faWa tana

8 / 50