Advertisements
Chapter 5 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 50

12K to 15K   out of 147.7K words

fara ci tana"

"korawa da Maltina. Kafin ace kwabo, ta cinye gaba Waya."

Lumshe idanu tayi tana hamdala a zuciyarta saboda jin yadda a ™an™anin lokaci ta ™ara dawowa cikin

"hayyacinta. Ashe kaso sittin na gajiya da galabaitar da tayi yunwa ce, yanzu kuwa da ta samu mahaWi sai"

ga shi ta dawo hayyacinta sosai tana jin ™arfi a jikinta.

˜ara gyara zama tayi idanunta a lumshe tana shan A.c a zuciyarta kuma tana Istigfari da Hailala kafin ta

ankara ta fara gyangaWi.

"""Wai barci kike yi? Ki tashi ga direba can zai mayar da ke gida."""

Ta ji muryar Bintu bagatatan a kanta kamar a cikin mafarki.

A hankali kuma a nutse ta buWe idanunta ta zuba a cikin na Bintun. Ita ma fuskarta babu walwala ko

"kaWan kamar dai yadda fuskar Bintu yake. Sai kuma ta kawar da idanunta daga Bintu ta maida kan agogo,"

™arfe goma sha biyu da minti goma sha takwas na rana.

Bata ce komai ba sai mi™ewa da tayi tsam ta tsaya tana kallon Bintu.

"A fakaice, Bintu ta harari gefen Innaye, ta ™ara Sata fuska sannan ta nufi hanyar fita. Innaye ta rufa mata"

baya zuciyarta na ™ara cika da tsoron halayen Bintu da sannu a hankali suke ™ara bayyana.

Har suka ™arasa gurin motarta inda direba ke zaune a mazaunin direba bata sake ce ma Innaye komai ba.

Ita ma Innaye bata ce mata cikanki ba.

"Kamar sadda za su zo asibitin, ™ofar baya na motar Innaye ta buWe ta zauna sannan ta mayar da ™ofar ta"

rufe da ™arfi.

'Ta Allah ba taki ba. Duk muguntarki haka za ki ga motar nan ki ™yale ko ™warzane baki isa kiyi mata

ba.'

"Bintu ta faWa a zuciyarta, cike da jin haushin irin bugun ™ofar da Innaye tai ma motar ta."

Dogon tsaki ta ja kafin ta mayar da idanunta kan direba.

"""Bala kayi tu™i a nutse fa. Kana dawowa ka tabbatar ka wanke min motar ciki da waje saboda ™ura da"

"gudun kwasar cututtukan da ban san farkonsu ba bare ™arshensu. Ina fatan ka gane?"""

"""Na fahimta Ranki ya daWe. Sai na dawo."""

Ya amsa a ladabce.

"Baya ta matsa, shi kuma ya tayar da motar, tana tsaye tana kallonsu har suka fice daga cikin asibitin kafin"

ta koma ciki tana sake jan tsaki sama-sama.

******

"""Hmmm! Na ce ba... Au! Ina kwana Baba?"""

A Wan daburce Zulaikha ta sake gaishe da Rabi a karo na uku.

Ba tare da damuwa ko nuna yanayin gundura ba ta amsa gaisuwar da murmushi fal a fuskarta. Haka

"kawai, Zulaikhan burge ta take yi, basu taSa yin wata doguwar magana ba tun da suka zo gidan, amma idan ta je can inda aka sauke su za ta kai musu abinci ta ga irin taSara da shagwaSar da yarinyar ke ma"

mahaifiyarta abin dariya da burgewa yake ba ta.

"Tun bayan shigowar yarinyar, da ajiye tsadaddun kulolin abincin mai gidan da tayi ta gaishe ta a karo na"

"farko, ta lura da yadda yarinyar take saiSi wajen fita kamar akwai wani abu da take so."

"Har ta kusa fita sai ta juyo da sauri ta sake gaishe ta a karo na biyu, ko bayan da ta amsa gaisuwar, sai ta"

Wan tsaya shiru ta ™ura mata idanu.

A karo na ukun kuma har ta fita sai ta sake dawowa ta gaishe ta.

"Kamar baza ta amsa ba, duba da yadda Hajiya Bintu ke ta kwakkwafarta a kan ba™in tun ranar da suka zo"

gidan sai kuma ta yanke shawarar yi mata magana ganin yanzu ai Hajiyar ba ta nan.

"""³an matan Mamanta ya aka yi? Gaisuwa Waya biyu ai ya isa ko? Kin ga tun shigowarki na lura kamar"

"akwai maganar da kike so kiyi amma kina ta nu™u-nu™u. Kina bu™atar wani abu ne? Kar ki damu, faWi ko me kike so yanzu in Wauko miki."""

Kamar damar da Zulaikha take bu™atar samu kenan. Da sauri ta ce

"""Ummm! Daman zan tambaye ki ne don Allah. Jiya da rana har kika tafi baki kawo mana abinci ba, kin"

"manta da mu ne?"""

"Šan shiru Rabi tayi kamar tana tunani, sai kuma ta amsa kai tsaye da cewar"

"""A'a! Ban manta da ku ba. Hajiyar ce ta ce ba sai nayi abincin rana ba, ko da na tuna mata da ba™i kuma"

"sai ta ce ba abinda ya shafe ni bane. Ta aike ni can gidansu daga can kuma na wuce gida..."""

"""Da gaske haka kuka yi Baba?"""

Zulaikha ta katse ta da tambayar da yanayin mamaki fal a fuskarta.

"""Eh da gaske, me zai sa inyi miki ™arya? Kin san daman a Sangaren girki abincin da nake dafawa a"

"gidannan na masu aiki ne kawai, sai kuma ba™i idan akwai."

Abincin maigidan ita da kanta take dafawa. To tunda ta ce ba sai nayi ba ai kin ga ba ni da hurumi ko ikon

"da zan ce dole sai anyi ko?"""

"""Uhmmmm haka ne."""

Zulaikha ta amsa a mamakance.

"""Lallai ma!"""

Ta ™ara faWa tana sake jinjina girman al'amarin. Ita daman tun jiya ta san da gangar Bintu ta hana su

"abinci, amma saboda tsananin ™warewarta a ™arya da iya shirya zance sai ta ce bata san ba'a kai musu"

abinci ba.

"""Ba damuwa. Ta yi ma kanta."""

Ta sake faWa ranta a Sace.

Da sassarfa ta kama hanyar ficewa daga kicin Win Rabi ta bi ta da kallo.

A zuciyarta take harhaWa Waya bisa biyu tana hasaso abinda ya faru bayan tafiyarta. To ko dai wannan shi

"ne dalilin da yasa ta ga waWannan tsadaddun kulolin na abincin Oga a hannun Zulaikha? Kulolin da ko gurin wanke-wanke Hajiya ta jaddada mata lallai ta dinga musu wanki na musamman, sannan da an gama wankewa a kife a kwando a saka towel a goge a mayar da su ma'adanarsu, ba tare da an haWa su"

da tarkacen kaya ba...

"""Amma Baba Rabi ita Hajiyar ta faWa miki matsayinmu a gurin maigidannan kuwa?"""

Maganar da Zulaikha tayi ya dawo da ita cikin tunaninta ba tare da ta san sa'adda ta dawo cikin kicin Win

ba.

"""A'a! Bata faWa min ba. Abu Waya dai da na sani ku Win danginshi ne, don Hajiya Bintu ta sha faWin shi"

"ke da ´an'uwa ˜auyawa..."""

"""Ba ´an'uwa ™auyawa kaWai bane. Ita wannan tsohuwar ba™auyiyar da kike ganina tare da ita,"

"mahaifiyarshi ce."""

Zulaikha ta faWa idanunta ciccike da hawaye. Kafin Rabi da ta buWe baki tayi magana ta cigaba da cewa

"""Ita ce ta sha wahalar na™uda ta haifo shi zuwa wannan duniyar. Ni kuma da kike gani kamar ba kowan"

"kowa ba, ™anwarsa ce da suka fito ciki Waya. Saboda Allah da Annabi idan da adalci ya kyautu ace an"

"hana uwar da ta sha wahalar haihuwa da rainon Wanta abincin da shi wannan Wan nata ne yake nemowa da guminsa?"""

"Kamar an buWe famfo, haka hawaye ke kwaranya a idanunta. Ita kuwa Rabi, tunda ta buWe baki ta kasa"

"rufewa, balle har ta iya ™arfin halin amsa tambayar da Zulaikha tayi mata. Allah ya sani bata taSa tsammanin Innaye mahaifiyar Oga Hafiz bane, duk ga tsammaninta ta fi tunanin ko dai wata Gwaggwansa ce daga ™auye."

"Babbar hujjarta kuwa shi ne, duba da yadda daga Hajiya Bintu har Alhaji Hafiz al'amarin tsohuwar basu"

"Wauke shi da wani gagarumin muhimmanci ba. Hujja ta biyu kuwa shi ne, babu wata kamanni ta musamman tsakaninshi da Innaye, Wan gara-gara ma Zulaikha, suna yanayi a fisge..."

"""Ban ™ara sanin haka duniya take da faWi da tarin abin mamaki Wauke da mutane mabanbanta ba, sai"

"da Bintu ta shigo cikin ahalinmu. Ko da muke ´an ™auye, bamu taSa tsammanin akwai wani tazara na musamman tsakanin Wan birni da na ™auye ba, ko kuma banbanci tsakanin talaka da mai kuWi. Duk a tunanina mu da ku bayin Allah ne da babu wanda ya fi wani a gurinsa sai wanda ya fi tsoronsa... Amma a yanzu na samu ™arin ilimi, ya zama dole mu cigaba da raSewa a ™auyenmu don rayuwar birni da"

"mutanen birni sun fi ™arfinmu ta ko wane Sangare."""

"Tana gama faWin haka ta fice daga cikin kicin Win da sauri, lokaci bayan lokaci take kai hannu saman"

fuskarta tana share hawaye.

Ta fito tsakar gidan kenan da nufin zuwa can Sangarensu aka wangale get Win gidan. Kamar baza ta

"waiga ba, sai kuma ta juya sannu a hankali tana kallon motar da ta shigo. Ganin motar Bintu ce yasa ta ware idanu tana kallon motar da kyau domin ganin ta ina Innayenta za ta fito?"

"Kallo Waya za'a yi mata, a fahimci jikinta a sanyaye yake sosai."

Zulaikha yarinya ce mai shekaru goma sha bakwai. Amma irin yarannan ne da tun suna ™anana suke da

masifar wayau da manyancen iya magana. Ko don ta rayu a hannun Dattijuwa Innaye ce? Allah masani.

Ganin fitowar Innaye daga cikin mota ita ma da nata yanayin sanyin jikin yasa tayi ™o™arin watsar da nata

damuwar ta ™arasa gurin Innaye da sauri.

"""Innaye? Me yake faruwa? Jikin naki ne?"""

Ta jera mata tambayoyin da hanzari fuskarta na bayyana damuwa da tashin hankali. A lokaci Waya kuma

tana Wan tattaSa jikin Innayen domin jin ko akwai zafi?

"Hannayenta Innaye ta kamo ta ri™e, da murmushi a fuskarta ta amsa da cewa"

"""Jiki Alhamdulillah Auta. Kawai dai na gaji ne. Amma babu komai, muje ciki."""

"""To Ma sha Allah! Allah ya ™ara lafiya."""

Ta amsa tana jin kwanciyar hankali kaso hamsin cikin Wari na damuwarta.

Haka suka kama hanyar zuwa Sangarensu suna ri™e da hannun juna cikin kulawa. Babu mai cewa komai

"a cikin su biyun, ko wacce da tunanin da take yi a zuciyarta."

"Suna ™arasawa ciki, ta zaunar da Innaye a gefen gado ta sa hannu ta zare mata hijabin jikinta."

"""Sannu Innaye. Allah ya ™ara lafiya. Ai dole ki galabaita, jiya fa duk farkin barcin da zan yi sai in ga"

"idanunki biyu. Ga shi yau da sassafe baki samu komawa barci ba kuka fice zuwa asibiti. Ko kinyi barci ne acan asibitin?"""

"""Barci kuma Auta?"""

"""Eh mana. To ba naga akwai gadajen da ake kwantar da marasa lafiya ba?"""

Ta amsa tana tura baki da murmushi a fuskarta.

"""Eh haka ne! Amma ai ana kwantar da waWanda jikinsu yayi tsanani ne. Ni kuwa kin ga har yanzu da"

"sauran ™arfin jiki a tattare da ni..."""

"""Amma Innaye kin ci abinci bayan an gama gwajin da aka ce za'a miki kafin ki karya?"""

Ta katse ta da sauri bayan ta tuno sun fita daga gidan Innaye bata karya ba.

"""Uhmmm!"""

"Ta ja numfashi ta sauke a kasalance. Kamar baza ta ™ara yin magana ba daga wannan ajiyar zuciyar, sai"

kuma ta ce.

"""Auta! Wato da gaske ne duk lalacewar al'umma ba'a rasa na kirki. Yau ba don Allah ya haWa ni da wata"

"yarinya ´ar arziki wacce ta san ya kamata ba da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Wata kila, da"

"sai dai matar gidan ta dawo ta sanar da ku babu yadda nake, an kwantar da ni ranga-ranga a asibiti. Amma da yake ko cikin lalatattu ba'a rasa na kirki sai Allah ya agaje ni da taimakonsa na gaggawa a lokacin da banyi tsammani ba. Alhamdulillahi! Je ki tara min ruwan wanka inyi sai in alwala, ga shi can"

"ana kiran sallah a masallaci..."""

"""Me ya faru da ke a asibitin Innaye?"""

Zulaikha ta tambaye ta tana jin babu daWi sosai a zuciyarta. Daman tun bayan ficewarsu take ta ji a ranta

lallai a rashin kirkin Bintu za ta fa iya wula™anta Innaye ganin babu idanun kowa a kansu.

"Ganin wayar Innaye ajiye a gefen gado yasa ranta ya ™ara jagulewa, tayi tunanin da akwai waya a"

"hannun Innaye, idan ta ga abinda bai gamshe ta ba za ta iya kiran Yayansu yaje asibitin ya Wau mataki."

"""Maimaita abinda ya wuce sam ba shi da wani amfani Auta. Balle kuma kin san hali na abu idan ba na"

"alkhairi bane ban cika son maimaita labarinshi ba..."""

"""Don Allah ki faWa min Innaye."""

Tayi maganar kamar za ta saka kuka.

"""Bazan faWa miki ba Auta. Domin jin babu abinda zai ™are ki da shi. Nasihar da zan miki a wannan gaSar"

"Waya ne rak! Mu mutanen ™auye ne, can ™auyen, can ne duniyar da muka buWi idanu da ita. Kuma kaso casa'in da biyar cikin Wari na mutanenmu acan suke farawa kuma su ™are rayuwarsu."

A mafiyawancin lokuta duniyar sauyawa take yi. Idan Allah yayo ki cikin masu tsawon rai yanzu kika fara

"rayuwarki, ban san ko kina daga cikin WaiWaiku kuma tsirarun da Allah ya ™addari za su tsallake"

"™auyenmu suyi rayuwa a wani guri na daban ba. Idan Allah ya ™addara miki haka, ki ji tsoron Allah. Kar ki kuskura don wani ni'ima da Allah yayi miki ki wula™anta mutanen ™auye, ko ki wula™anta na ™asa da ke."

"Je ki tara min ruwan wanka, kafin in fito ki je cikin gidan ki samu mai aikinnan ta baki abinci ki kawo min,"

"idan kuma babu, ki zo ki haWa min shayi."""

Duk wasan da ke tsakaninta da Innaye a wasu lokutan kamar jika da Kaka. Ta san irin lokacin da take

"tubure mata da ´an rigingimu, ta kuma san lokacin da take Waukar abinda ta faWa da muhimmanci."

"Don haka a wannan gaSar, duk yadda ta so jin abinda ya faru a asibitin sai bata ™ara cewa komai ba. Ta"

"mi™e tsam, ta shige banWaki ta tara ma Innaye ruwan wanka a bokiti."

"Ko da ta fito, sai ta tarar Innaye har ta gama shirin shiga wankan, don haka bata sake Sata lokaci ba ta"

fice zuwa cikin gidan da wani irin taku na musamman. Zuciyarta cike da sa™e-sa™en yadda za ta canja

tsarin zamansu a gidan kafin su bar garin Abuja.

"Su ba wula™antattu bane, don haka bazai yiwu Bintu ta cigaba da Waukarsu a wula™ance ba. Ba maula"

suka je gidan ba balle ace za'a dinga ba su sadda aka so a hana su sadda aka ga dama.

Idan Bintu tana da ´anci a gidan lallai su ma suna da shi. Da wannan daliln kuwa ko da tsiya ko da tsiya-

"tsiya za ta ™watar musu ´ancinsu, idan Yaya Hafiz yaga dama, yayi ™uli-™ulin kubura da ita. Amma tsakaninta da matarsa ba sau™i ba sau™a™awa, shege ka fasa, Wan halak sai yanka."

"Tana waWannan tunane-tunanen har ta ™arasa cikin falon gidan, watsar da tunanin komai tayi ta buWe"

idanu sosai tana kallon irin ™ayatattun kayayyakin da aka yiwa falon kwalliya da su. Duk da ba sanin

"kayayyaki masu tsada tayi ba, ido ba mudu bane amma ya san kima."

"Kuma da ganin kura za ta ci akuya, ko da ganin kayayyakinnan ma™udan kuWaWe suka ja ba ´an kaWan ba."

"Haka kawai, ba tare da sanin dalili ba sai hoton gidansu na can ™auye tun daga soro har zuwa falo da"

"uwarWakin Innaye ya faWo a cikin idanunta. Babu mahaWa ko kusa, amma da ta tuna nisan tazarar da ke"

tsakanin rayuwar birni da na ™auye sai ta ajiye tunanin komai ta ™arasa cikin kicin Win.

"""Baba Rabi an gama abincin ne?"""

Ta tambaya da yanayin fuska kadaran-kadahan bayan sallama ™asa-™asa da tayi a ™ofar kicin Win.

"""Ba'a gama ba Auta."""

"Ta amsa da sauri cikin girmamawa, domin maganganun da yarinyar tayi Wazu kafin ta fice daga kicin Win"

tana kuka sun tsaya mata a rai.

Da wannan dalilin yasa ta ™uduri aniyar in Allah ya yarda ta Sangarenta dai baza ta sake yin wani abu da

"zai nuna wula™antarwa ga tsohuwa da yarinyar ba, duk da daman dai tana yin komai ne don guje ma kuskurewa UwarWakinta. Don ta ™ara warware ma Zulaikha yadda tsarin girkin abincin ke tafiya sai ta cigaba da cewa"

"""Kin san yanzu ranar ta fara Wagawa, kuma a ™a'idar da Hajiya Bintu ta tsara zuwa uku na rana ne zan"

"dinga raba abinci. Shi yasa na tsara komai yadda aikin zai dinga tafiya kan lokacin da ta tsara..."""

"""To madallah!"""

Zulaikha ta katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta.

"""Yanzu ya za'ayi? Me za ki samar ma Innaye mai Wan sau™i? Daga asibiti ta dawo kuma ta bar gidannan"

"ko karyawa bata yi ba."""

"""Assha! Jikin ya motsa ne? Allah ya ™ara mata lafiya. To ko dai za'a haWa mata Tea ne? Domin ya saSa"

"ma ™a'idar Hajiya Bintu girka wani abu daban saSanin wanda za'a dafa gaba Waya..."""

"""Wai wace ce kuma Hajiya Bintu da kike ta sako min sunanta a cikin maganganun da muke yi? Ya ina"

"miki maganar mahaifiyar Maigidannan ta fita bata karya ba kina min zancen wata Hajiya Bintu da ta tsinci mai gidan a sama da ha™waransa talatin da biyu? Dan Allah ki aje maganarta gefe kiyi abinda ya kamata. Ko Indomie ce da ™wai ki dafa mata yanzunnan, idan kuma baza ki iya ba kina tsoron saSa umarnin wacce kike ma aiki, ki kunna min abin girkin ki nuna min inda kayayyakin abincin suke, ni sai in"

"dafa mata da kaina. Ko da nake ´ar ™auye kin san dahuwar indomie dai ba za ta gagareni ba."""

Zulaikha tayi maganar tana ™ara harhaWe girar sama da ™asa. Zuciyarta cike da haushin Baba Rabi yadda

take ma Bintu wata irin biyayya ta musamman kamar wacce ta girme mata a shekaru.

"""Anya...?"""

Baba Rabi ta faWa cike da taraddadi da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Sai kuma ta ™ara da cewa

"""Ko da yake, shi kenan. Bari a dafa mata, Wan bani mintuna goma kacal. Je ki dawo, yanzu zan gama"

"dafa mata."""

"Gefe guda taja ta tsaya tana bin duk inda Baba Rabi tayi da idanu, akan idanunta ta kunna Gas Win girki,"

"daman shi kaWai ne take ga baza ta iya amfani da shi ba a kicin Win. Tana biye da ita har ta buWe store, ta Wauko duk abinda za ta bu™ata sannan ta fito ta kulle. Abu na biyu da taga yadda ake kunnawa ayi amfani da shi blander ne, don haka ta kura idanu sosai taga yadda ake anfani da shi."

"Tana kallon komai tana k'ara kwasar ilimin yadda ake amfani da kayan girkin 'yan birni, har zuwa lokacin"

da Baba Rabi ta gama dafa lafiyayyiyar indomie da ta ji kayan had'i. Ta soya kwai guda hudu kamar

"yadda Auta ta umarce ta, sannan ta kwashe komai a kula Mai kyau sabanin Wanda ake zuba musu abinci ta mika ma Auta."

"Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke lokacin da ta karbi abincin. Ta haske Baba da wani lallausan murmushi, a"

tausashe ta ce

"""Na gode, Allah ya biya ki da alkhairi."""

"""Amin ya Allah. Ki gaida Innaye, Allah ya kara sauki."""

Baba Rabi ta amsa bayan ta mayar mata da martanin murmushinta.

"Ko da ta koma can bangarensu, akan darduma ta tarar da Innaye, hannunta da casbaha tana ja amma"

tana gyangyad'i. Sallamar da tayi ma bata amsa ba sai da ta ce

"""Innaye barci kike yi?"""

"Firgigit! Tayi ta farka, ta bude Baki za tayi magana wata k'atuwar hamma ta k'wace mata."

"""Sannu Innaye. Kiyi ha™uri, na barki kina jira na ko? Ba'a gama dafa abincin gidan bane shi ne nasa aka"

"dafa miki Indomie..."""

"""WaWannan siraran taliyar Auta? Kin san dai ko a gida ke ce kike ™wazzabar a siyo miki ita gurin Isa

5 / 50