Advertisements
Chapter 38 Reading RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 50

111K to 114K   out of 147.7K words

agogo bayan ta ji ™arar ficewar motarsa daga gidan, ™arfe tara da"

minti goma sha bakwai na dare.

"""Ina my dear yake haramar zuwa a darennan?"""

Ta tambayi kanta a fili.

Lokaci Waya kuma sai tunanin yadda yake yawan yawace-yawace a cikin kwanakin ya faWo mata a rai.

˜irjinta ne yayi kwance-kwance ya buga daram!

"""Na shiga uku ni Bintu? Kar dai ace yawon zuwa club My dear ya tsira abinda ba halinsa ba?"""

Ta sake tambayar kanta hankalinta a tashe. Domin tunanin yi mata kishiya a soyayya balle har ya fara

neman aure abu ne da ko a mugun mafarki bata taSa hasashen zai iya faruwa ba.

******

"A hankali yake tu™a motar, jefi-jefi idanunsa na sauka akan fuskar wayar yana kallon lambar Karima da"

"yayi saving sunanta da ˜urratul-ayni. Kamar bazai kira ba, sai kuma ya danna mata kira, domin a yadda zuciyarsa ke tafarfasa ita ce kawai zaiyi tozali da kyakkyawar fuskarta ya nemi Sacin ran da ke dan™are a zuciyarsa ya rasa."

"Har ya cire ran za ta Wauka sai kuma ta Waga a lokacin da kiran ke daf da tsinkewa. Bayan sallama, shiru"

tayi daga can Sangaren tana jan fasali irinna macen da ake bibiya ana neman soyayyarta. Domin har

"yanzu ba wai ta sake mishi bane, jan zarenta take yi yadda take so shi kuma yana bibiye da ita sawu da"

"™afa, abinda ke ™ara fasa mata kai kenan tana ci gaba da murza kambunta yadda take so."

"""˜urratul Ayn..."""

Ya kira ta a tausashe.

"""Na'am Nurul-™alb"""

Ta amsa shi da wani irin salo da ko a fili ko a waya bata taSa gwada mishi irinsa ba.

Wani zirrrr da ya ji tun daga tsakiyar kansa zuwa babbar yatsarsa yasa shi saurin gangarawa gefen titi tun

"kafin ya buga ma motar gabansa. ˜ara ™an™ame wayar yayi a kunnensa kamar me tsoron kar a ™wace masa. Ya sake yin ™asa ™asa da muryarsa yana jin yadda zuciyarsa ke bugu sauri-sauri da matsanancin soyayyar Kariman. Allah ya sani yana son Karima, irin soyayyar nan mai saiSi da shiga cikin zuciya sannu sannu kafin malallakiyar zuciyar ya ankara ta yi masa mugun kamu."

Idan za a ritsa shi da wu™a shi da kanshi bazai ce ga abinda ke ™ara jansa a afka ma soyayyarta ka'in da

"na'in ba. Lallai sai yanzu ya ™ara yarda so tsuntsu ne, yana tashi haihata-haihata daga wannan bishiyar ya koma wancan. Bazai ce ya daina son Bintu ba, amma fa shi baya jin ta a ransa kamar yadda yake jin Karima."

Da gaske yanzu idan za a bashi Al™ur'ani zai rantse da Allah Karima yake so! Karima yake ™auna!! Da

Karima yake burin yin rayuwar aure na har abada!!!

"""Ina so in ganki ˜urratul-ayn! Yanzu...!"""

Ya sake faWa da murya ™asa-™asa.

Shiru tayi na ´an wasu da™i™u! Ta buWe baki za tayi magana sai yayi saurin katse ta da cewa

"""Kar ki ce min a'a dare yayi don Allah sanyin idaniyata. Ina cikin matsananciyar damuwa, tabbas idan"

"banyi tozali da kyakkyawar fuskarki ba zanyi kwanan ba™in ciki ne a wannan dare."""

"""Me yake damunka Nurul ™alb? Wa ya taSa min kai ?"""

Ta tambaye shi da murya mai bayyana damuwa da damuwarsa.

"""Ke kaWai nake son gani kawai... I'm very sure hankalina zai kwanta idan na ganki. Pls ™urratul-ayn"""

"Ya sake faWa cikin magiya, ba tare da ya amsa Waya daga cikin tambayoyinta ba."

"""Shi kenan! Allah ya kawo ka lafiya. Amma yanzu ina asibiti..."""

"""Ga ni nan zuwa."""

Bai jira ta sake cewa komai ba ya katse wayar. Tayar da motar yayi ya harba kan titi a guje yana jin yadda

zuciyarsa ke tsallen baWaken murnar za tayi tozali da muradinta.

"A can Sangaren Karima, narai-narai tayi da idanu tana kallon Hibba haWe da cewa"

"""Na shiga uku Hibbah! Mijin Aunty Bintu ne fa...!"""

"""And so what?"""

Hibba ta katse ta haWe da gallah mata harara.

"""Wani lokacin ke dai banza ce Wallahi Karima. Na rantse da Allah da tuntuni na san da wannan labarin"

"da tuni kun daWe da wuce wannan matakin. Sai me don mijin Bintu ne? Haramun ne? Uban me kuka haWa da Bintun da har kike shakkar auren mijinta?"""

Taja dogon tsaki ta sake gallah ma Karima harara a karo na biyu sannan ta cigaba da cewa

"""Dama ace Bintun wata mutuniyar arziki ce shi ne har za ki Wan ji wani War don mijinta na son ki. Na"

zaci ke kika bani labarin irin yadda Bintun take wula™anta iyaye da danginsa don sun kasance ™auyawa? Kuma baya ga haka ma ko asibitin nan nazo gurinki ai ina ganin yadda take wula™anta ku Nurses tana daka muku tsawa don kawai ta™amar ita likita ce. Don haka ki aje wata Bintu a gefe Waya ki rungumi

masoyinki da gasken-gaske.

"In dai har za ki ji shawarata, ki bashi dukkan goyon baya Wari bisa Wari. Tunda kika ga Mummy ita da"

"kanta ta zaunar da ke tana faWa miki kyawawan halayen Hafiz Win, alamun da ke nuna ta yi na'am da al'amarin Wari bisa Wari kawai dai ba ta son yi miki tilas ne."

"Yanzu dai duk ba ma wannan ba, tashi ki shiga bayi ki wanke fuskarki kizo in miki kwalliya sama-sama"

"don kar ya ganki garau-garau duk kin jigata da aiki..."""

"""Don Allah ki bari Hibbah, ni ba wani kwalliya da zanyi..."""

Ai ko kafin ta rufe baki har Hibba ta finciki hannunta taja ta da ™arfi suka fara tafiya zuwa banWaki.

"""Wallahi baki isa ba. An faWa miki namiji irin Hafiz da sanyin jiki ake samun hankalinsu? Ko don kina"

ganin Allah ya kashe ya baki? To in faWa miki ko kina da kyau sai kin ™ara da wanka kamar yadda ba'a

"bori da sanyin jiki."""

A ™asa da mintuna goma sha biyu Hibba ta yi ma Karima sassau™ar kwalliyar da ya ™ara fito da ita fes! Ta

tsiyayi humrah ta shafa mata. Don saboda tsabar sabo da gayu da gwalli duk inda Hibba za ta saka ™afa a cikin jakarta akwai komai da za ta bu™ata na kwalliya. Ko don ya kasance sa'na'arta ne oho!!!

"Kamar yanzu dai, ™anwar Hibban aka kwantar a asibitinsu Karima, mahaifiyarta ita ta yini da mare lafiyar"

ita kuma Hibba za ta kwana da ita. Duk da sanin jinya za ta je asibiti hakan bai hana ta zuwa da kayan kwalliya da Waya daga cikin kalolin humrar da mahaifiyarsu take sayarwa ba. Ashe rabon tayi ma Karima

amfani da kayan kwalliyar ne.

"Karima aikin yamma tayi, tun tuni ya kamata ta tafi, amma ganin Hibba ya saka ta zama tana rage mata"

"dare, bayan ta kira Mummy ta faWa mata ba sai an turo mata direba ba, direban gidansu Hibba zai dawo da ita gida."

Hira ne yayi hira har Allah ya matsi bakinta take ba Hibbah labarin irin naci da matsanancin son da Hafiz

ke mata. Bayan ta gama zage ta tas kan irin wasa da dama Waya da Allah ya jefo mata sannan ta Suge da

bata shawarwarin yadda za ta sauke duk wani izzah da aji ta ™ara ru™o wuyan Hafiz Win ™am! Ta yadda

"bazai taSa gigin barinta ba. Suna cikin wannan tattaunawar ne Hafiz ya kira ta a waya, shi ne fa har ta"

fara gwada masa kulawa da soyayya wanda da can ba ta wani nuna masa saboda tsoron abinda zai je

yazo idan zancen soyayyarsu ya koma kunnen Bintu.

Isowar Hafiz harabar asibitin ya yi daidai da isar Dr. Raudha aminiyar Bintu na ™ud-™ud cikin asibitin. Ita a

"ranar aikin dare take da shi. Mamaki ne ya kamata don ta san Bintu aikin safe tayi, tunanin ko wani abu yazo karSa ma Bintu a cikin asibitin yasa tayi watsi da mamakin ta cigaba da latsa waya tana ™o™arin danna kiran lambar Mamanta har Hafiz ya shige cikin asibitin akan idanunta."

Tsayawar da tayi amsa waya a cikin mota yasa tayi kyakkyawan ganin da yasa wayarta ya suSuce daga

"hannunta ya faWa kan cinyarta. Bata ko bi ta kan wayar ba ta cigaba da kallon Hafiz da Karima da suka jero suna takun da ke bayyana ™arara masoya ne su biyun. Kamar ita ce Bintu, saboda wani ba™in ciki da kishi da ya rufe mata idanu, a haukace ta yun™ura za ta buWe motar ta fita sai kuma tayi gaggawar saka ma kanta linzami."

"Wayarta ta rarumo da sauri, bata bi ta kan muryar mahaifiyarta da take ji yana fita a cikin wayar ba ta"

"katse kiran a gaggauce, hannunta har rawa yake yi gurin lalubo lambar Bintu ta danna mata kira, amma"

wani abin ba™in ciki da takaici shi ne wayar Bintun a kashe take.

Cikin ™asa da sakan hamsin sau huWu tana gwada kiran Bintu na'ura na faWa mata wayar a kashe take.

Baki da hanci buWe zuciyarta tumbatse da maWaukakin mamaki ta cigaba da bin su Hafiz da kallo har suka shige cikin motarsa shi da Karima. Tsoro ne sosai ya ™ara kamata ganin yadda Hafiz ya buWe ma Karima ™ofar da za ta shiga yana kashe ta da lallausan murmushi. Idan ma ba idanunta ne ke mata gizo

"ba, sai taga kamar har wani Wan du™awa Hafiz Win yayi ma Karima alamun girmamawa."

Ita kuwa Karima sai wani rausaya take yi tana rangwaWa haWe da fari da idanu. Ko rantsuwa tayi babu

kaffara akan idan ba matsananciyar soyayya ba ce a tsakaninsu babu yadda za ayi ta gansu a cikin wannan yanayin.

"""TaSWijan! Namiji! Namiji!! Mugu Wan masara ana goyonka kana gemu... Don ubanki Bintu ki buWe"

"waya in baki labarin kaWan daga cikin sakayyar da Hafiz zai miki kan irin alwashin da kika daWe kina sha akan shi ya fita daban a cikin maza."""

"Ta yi maganganun cikin masifa kamar za ta ci babu, a lokaci guda kuma tana cigaba da gwada kiran"

lambar Bintu. Wanda har lokacin na'ura ke sake tabbatar mata wayar a kashe take.

Ita kaWai a cikin motar take masifa tana zage-zage kamar za ta ci babu. A Lokaci guda kuma tana shan

alwashin kaloli mabanbanta na cin uban Karima da za suyi ita da Bintu gobe a ofis idan an wayi gari.

"""Kuga min shegiyar yarinya sumumu-kasau ashe ™asungurmar munafuka ce? Ko da yake ai maganin"

"Bintun ma da ta sakarwa uwarta Hajiya Sauda fuska, ai ga sakayyar sakin fuska nan ta fara gani. Tana"

"niyyar wanke zu™e™iyar Wiyarta ta bashi ya aura."""

Tana wannan masifar har bata san lokacin da motar Hafiz ya bar harabar asibitin ba. Waigawa kawai tayi

taga inda motarsa take ba shi sai filin gurin.

"Ta ja tsaki ya fi sau hamsin, duk yadda mahaifiyarta take ta biyo bayan kiran wayarta ta kasa Wauka. Duk"

da magana ce mai muhimmanci suke yi. Ta sani a yadda take fusacen nan ko ta Wauka baza ta iya mayar da hankali su cigaba da magana ta nutsuwa ba.

"A ™arshe sai kashe wayar tayi, ta figi jakarta da wayar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin asibitin. A"

zuciyarta take ™udurta yadda za ta ci uban duk wata nurse budurwa da ta tarar da ita a bakin aiki a

wannan daren.

"'Munafukai, Algungumai, duk bakinsu Waya matsiyata. Ashe bayan kwarkwasa da gwalli da suke yi ma"

Likitoci maza har mazajen likitoci mata basu bari ba. Duk za su ci ubansu Waya bayan Waya.'

Da wannan ™udurin ta ™arasa cikin asibitin zuciyarta cike da addu'ar Allah ya haWa da ´anmatan nurses

"Win asibitin, musamman waWanda ta san sun fi shiri da Karima."

******

Wannan gwaggwaSar canjin bazata da aka samu bagatatan a cikin tafiyar soyayyar da a farko shi kaWai

"yake kiWansa kuma yake rawarsa ba ™aramin faranta masa zuciya yai ba. Tuni ya manta da Bintu, Sacin ran da ta cusa mishi da duk wani abu da ya shafe ta."

"Ba ma kamar yadda minti Waya biyu a hirar da suka gabatar da Karima sai ta ambaci Innaye, ko kuma ta"

"ambaci kirkin ´an'uwansa. A cikin hirarsu har ta bashi labarin haWuwarta na farko da Innaye, da yadda jininsu ya haWu farat Waya. Amma ko da wasa bata bashi labarin yadda Bintu ta wula™anta Innaye a"

wancan lokacin ba saboda gudun tayar da husuma tsakanin ma'aurata.

"Sun yi hira na awa Waya cif bayan isarsu gidan Momy Sauda. Kamar bazai tafi ba, sai da Momyn ta kira"

shi a waya tayi mishi tatas kan cewa baza ta yarda da irin wannan rashin adalcin tun yanzu ba.

"""Allah ya huci zuciyarki Mummy. Zan tafi yanzu, sai da safe. Gobe idan Allah ya kaimu da yamma zan"

"zo..."""

"""Kar ma ka fara Hafiz, hira sau biyu a sati ya isa. Ga waya nan ku dinga magana, shi Win ma ban yarda ya"

"wuce sau uku a rana ba. Ina fatan ka fahimce ni?"""

"""Na fahimta Mummy."""

Ya amsa a ladabce.

Har ya kama hanya zai fita ta kira shi.

"""Da alama dai kun daidaita da ™anwartaka. Zan tuntuSeta yau da dare saboda gudun yin kitso da"

"™war™wata. Idan ta tabbatar min da amincewarta kayi ™o™arin zuwa Fa™o cikin satinnan ka sanar da iyayenka halin da ake ciki, idan sun shirya ko zuwa watan gobe sai ka turo kawai ayi mai gaba Waya a wuce gurin. Nima nan zan sanar da iyayenta maza, tunda an fahimci juna kuma da sanayya ta ko wane"

"Sangare to gaskiya babu wani amfanin Sata lokaci. Ko kana da wani shiri ne da kake bu™atar jinkiri...?"""

"""Ba ni da wani shiri Mummy."""

Ya katse ta da matsanancin farin ciki bayyane a fuskarsa.

"""Ai ni Wallahi ko gobe ne a shirye nake a Waura auren kawai a wuce gurin. Na gode Mummy. Allah ya"

"™ara girma."""

"""Amin ya rabb! To ina fatan Bintu dai ta sani?"""

"Ta sake jefa mishi tambayar, tare da ™ure shi da kallo tana ™o™arin karantar yanayinsa."

"Šan shiru yayi yana sosa ™eya, amma har lokacin fara'ar da ke fuskarsa bata Sace ba. Can kuma sai ya ce"

"""Gaskiya bata sani ba Mummy... Amma zan faWa mata. A daren nan ma in sha Allah zan sanar da ita."

"Gobe idan naje Fa™o sai in sanar da su Baffa."""

"""To madallah! Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama mafificin alkhairi. Ni dai don Allah ina"

"ro™onka alfarma... A matsayinka na miji, kasan irin kalaman da za kayi amfani da su gurin faWa ma Bintu al'amarin. Tsakani da Allah kishiya babu daWi, amma tunda umarnin Allah S.W.T ne ba mu da yadda za muyi. Ka bi ta sannu a hankali, cikin tausasan lafuzza da ™an™an da kai. Sannan ka nusar da ita auro"

"Karima ba shi ke nufin soyayyarta ya ragu a zuciyarka ba..."""

"A matsayinta na Babba, haka ta sake Sata wasu lokutan tana nusar da shi irin tausasan hanyoyin da zai bi"

wajen sanar ma Bintu zai auri Karima. Bai bar gidan Mummy ba sai ™arfe sha Waya na dare. Zuciyarsa cike taf da farin ciki.

Yana tu™i a hanyarsa ta komawa gida sai wa™e-wa™e yake saboda murna da yayi masa yawa. Ya ma rasa

"wa ya kamata ya kira ya fara yi ma wannan daddaWan albishir Win? Har ya Waga waya zai kira Zulai, sai ya ga dare yayi sosai. Sai kawai ya buge da kiran Ibrahim abokinsa Wan gidan Abba Lurwanu yayi mishi"

albishir.

"Kamar yadda ya zata, Ibrahim Win yayi murna sosai da sosai. Don yana Waya daga cikin ´an adawar Bintu,"

"masu nusar da shi tun a baya ire-iren kura-kuran da Bintun ke aikatawa amma sam idonsa ya rufe, ba ya ji ba ya gani saboda soyayya da ya rufe masa idanu."

"""Shi kenan! Ka ga yanzu za'ayi balancing, idan su Aunty Balira sun zo za su samu gurin da za a tarbe su"

"da haba-haba babu wula™anci, tozarci, ko kyara."""

"""˜warai kuwa Ibbu"""

Suna magana a waya Ibrahim Win yana ™ara bashi shawara kan kar ya kuskura ya haWa Bintu da Karima

gida Waya har ya isa cikin gidanshi. A lokacin sha biyu saura ´an mintuna. Sallama yayi ma Ibrahim da

cewar za su haWu bayan ya dawo Fa™o su ™arasa maganar ya katse wayarsa.

"Yana shiga cikin falo ya tarar da Bintu zaune a kan kujera, idanunta ™yam akan ™ofar shiga cikin falon"

"tana jiran ganin ta inda zai Sullo. SaSanin Wazu da ya barta sanye da kayan barci, yanzu ta ci kwalliya ne"

cikin wata ´ar Singilar rigar mama da wata yaloluwar Wan kamfai. Fuskarta da kwalliya raWau kamar wacce take shirin zuwa gurin perty.

"Ko kusa baiyi mamakin ganinta ido biyu ba, don yana daga cikin Wabi'arta da ke faranta mishi rai duk inda"

ya je in dai yana garin Abuja to Bintu ba ta taSa kwanciya tayi barci sai ta jira ganin dawowarsa gidan lafiya.

Abu Waya da ya Wan bashi mamaki shi ne tattausan murmushin da ta fara watso mishi tun daga inda take

"zaune, sannan ta mi™e tsaye cikin yau™i da lan™wasa, ta fara tafiyar mage tana wani yayyarfe yatsu tana"

"karkaWa mishi ™irji, lokaci guda tana haWawa da fari da idanu har ta ™arasa inda yake tsaye ™yam yana"

kallonta.

"Iya duniya aka ce ya fi iya mota, kamar dai ba Bintu ne suka rabu tana kuka shi kuma ya fita da Sacin rai"

"mai tsanani ba. Hannu ya buWe mata yana mayar mata da martanin murmushi, ita kuma a slow motion"

ta shige cikin ™irjinsa. A tare duk su biyun suka sauke nannauyar ajiyar zuciya.

"Basu tsaya a nan ba, kamar mayunwata haka suka kamo bakin juna suka fara tsotsa tamkar sun samu"

"alawa. Tun daga nan bakin ™ofa, al'amura suka fara kankama, duk su biyun suka watsar da fushi da Sacin ran juna suka cigaba da ™o™arin faranta rayukansu."

Daga bisani dai can-cak Hafiz ya Wauki Bintu suka haura sama.

*******

"Hafiz ya riga ya karanci Bintu kamar yunwar cikinsa, ya sani tunda tayi al™awarin yaye Aadil a washe"

"garin ranar asabar, babu abinda zai sa ta fasa aniyarta."

"Ya kuma sani tun da ta ambaci Ummanta ne za ta yaye shi, to tabbas gurin Ummanta za ta kai shi sai dai"

duk abinda zaiyi ya daWe baiyi ba.

Da wannan dalilin yasa shi gwada mata babba babba ne. Kuma wanda ya riga ta kwana dole ya riga ta

"tashi, duk sammakonta, shi a tafe ya kwana."

"Suna idar da sallar asubah a masallaci, ko da ya koma gida ya tarar da ita har ta idar da sallah ta koma"

"barci. Da wannan damar yayi amfani gurin aiwatar da shirinsa a gurguje, ko da ya shiga Wakin Aadil, ga manyan jakunkuna nan har guda uku ta sha™e da kayan sakawarshi da duk wasu abubuwan bu™atarsa. Don haka Wauka kawai yayi ya fice da su ya zuba a boot Win motarsa. Šakinsu ya koma inda Aadil Win ke kwance can gefe guda a gadonsa yana barci cikin nutsuwa. Bismillah yayi sannan yasa hannu a nutse ya"

Wago yaron ya rungume a ™irjinsa yana Wan jijjiga shi don kar ya farka.

SaWaf-saWaf ya fice daga Wakin don kar ya tashi Bintu. Kuma wani ikon Allah shi ne duk yadda ta kasance

ba ta da nauyin barci har Hafiz ya samu nasarar ficewa daga gidan Bintu ko ™arar motarsa bata ji ba.

"Sai

38 / 50