Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
[9/25, 2:37 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU🗿1
Batul Mamman(Mrs)💖
Bismillahir Rahmanir Rahim
Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu
yara suka fara binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa
baya rabo da yar tsarabar da zai kawo musu. Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga
tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu sakamakon zarton da ya fada kai har ya
tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka ce hannun ya mutu
dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. Da
dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya
mikawa yaran. Suna ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka
hada ido da wani matashi a layin. Da sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka
kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade jikinsu. Baban yara barka da
yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba Sani. Yanzu
don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas
so kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza
kai. Kayi hakuri in Allah Ya yarda bazamu sake ba. Yayi murmushin takaici Allah Ya
bada ikon denawa. Kuna ta batawa kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda
mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. Na tabbatar babu wanda zai so nan
gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa. Sani ya dan yi
murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin
ya murde. Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta
kuce gado ne. Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu.
A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. Mal Bashir ya dauko
naira dari ya mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan
Baban Yara? Darin da ka bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi
zata je karbo sakamakon jarabawarta. Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a
wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau daya banga fitowarta ba. Mal
Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama.
Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai
ta tashi da gudu ta shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa.
Ummanta ta soma fada ke lafiyarki kuwa. Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan.
Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi
hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji sallamar ba. Takalmansa
ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya
matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin
sallama ta tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin
jikinsa. Yace da Umma ta karbo sakamakon jarabawarta kuwa?Umma tana kwashe
yakuwarta ta ce bana jin amma ga wasu takardu can akan taga wanda Hajara ta kawo
mata dazu. Mal Bashir ya tashi ya dauko a sanyaye...ai tunda ta gudu yasan bana ma
bata kitsa abin arziki a makaranta ba.
Ai kuwa yana budewa yaga abin haushin da yasa rai da gani. Ta 48 tayi cikin su 52.
Ransa ne ya sosu. Ya rasa yadda zaiyi da yarinyar nan. A fusace ya tashi ya tafi
kofar bandakin. Zuhra me kike yi ne ya tambaya da daga murya. Daga ciki ta ce ehem
ehem! Ya sake bugawa idan ba so kike na bude ki ba gara ki fito tun wuri. Zuhra ta
gwammace ta yini a bandaki da ta fito ta sha fadan Baba. Ta sake cewa ehem..... ya
ce bari na fita tunda mun koma wasan buya da ke. Sai da ta kara kusan minti biyar
sannan ta fito duk ta hada gumi. Ta dubi Ummanta, wai yau da Baba ya kamani
bansan....saukar rankwashi taji a tsakar kanta ta durkushe a kasa tare da rike kan
ta soma kuka.
[9/25, 2:38 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU🗿2
Batul Mamman(Mrs)💖
Baban Yara yace idan baki rufe min baki ba sai na kara miki. Da kuka Zuhra ta mike
tsaye tana turo baki ko saboda rankwashin nan ba dole na kasa kokari ba. Idan kana
taba min mandula oblongata dina haukacewa zanyi nan gaba kadan. Baban Yara yace
kece mandular ai. Nan kika fi kauri dama. Kin iya haddace 'yan kalmonin turanci
kizo kina barazana dasu kamar wata wadda tasan abinda take yi. Zuhra dai kuka ta
cigaba da yi har sai da Umma tayi mata tsawa. Wallahi idan kika tara min makota
yau jikinki sai yayi tsami. Jin haka ta soma tsalle tana kara kukan. Baban Yara
yace bari na dauko wayar chaja na yi miki mai dalili. Ai kamar anyi ruwa an dauke
haka ta hadiye kukan.
Takardun jarabawarta da aka hada da report card din ya soma dubawa. Wasu har zero
ta ci. Maths(lissafi) tace arbain da takwas, Arabic tace casa'in da hudu sai Hausa
ta taci sabain da daya. Dama sune darrusan da suke dan taimakawa bata daukar ta
karshe gaba daya. Sai ko rubutu da ta iya mai kyau idan ka gani zaka dauka na wata
mai kokarin ne. Yana dubawa yana tsaki sai daga baya ya kula da yadda take rubuta
suna. Kansa ya rinka girgizawa kawai don takaici. Ko shi da iyakarsa aji hudu a
secondary ga shekaru sun mika amma yasan idan suka shiga aji shi da yar tasa sai
yafi ta kokari. Zo nan ya yi mata tsawa. A hankali ta ja kafa ta je ta tsugunna a
can gefe. Yanzu kin tabbatar duka takardun nan naki ne? Nawa ne Baba duba sunan da
rubutun mana. Yace ai na duba. Wasu ki rubuta Zuhra Bashir wasu kuma Fatima Bashir
don tsabar rainawa malamai hankali. Yana cigaba da dubawa yayi karo da wata.
Takalminsa ya raruma ya kwada mata. Ya daga takardar yana nunawa Umma. Kinga
wulakancin yar nan wai Fatima Basiru. Ya nuna kansa nine BASIRUN??? yadda yayi yasa
ta soma dariya Umma tace Allah Zuhra zanci mutumcinki. Ana miki fada kina wa mutane
dariya don shakiyanci. Zuhra ta kara matsawa gefe tana sharar hawaye to ba haka
naji su Kawu Sabiu da Innar Ajingi suna kiranka ba. Baba ya cije lebe saboda
takaici. Da kika ji sun fada ba sunan gida bane?. A nan wa kika taba ji ya kirani
Basiru? Tace to yi hakuri wallahi daga yau na dena. Ki ma kara ya fada yana tattare
takardun. Yana yi yana mita. Yarinya sau nawa ana miki repeating gashi kin kusa
shekara ashirin. Amma kanki kamar kifi, nasan duk ajin kece mamansu ko. A'a Baba ga
Hajara, ka manta ajinmu daya. Yace ina fa zan manta...an tara dakikai biyu a aji
daya. Baku da aiki sai cin awara da wainar flawa. Zuhra da baki baya shiru tace to
ba kai kake bani kudin ba. Umma tace kaga ka dena kula yarinyar nan sai jininka ya
hau.
Takardun ya miko mata jeki ki ajiye min a dakina. Ni ina ta kokarin hada kudi na
biya miki kudin WAEC saboda kada a rufe amma naga kamar asara zanyi. Sau biyu kina
qualifying din nan amma kin kasa hada credit uku. Zuhra tasan yadda babanta ya damu
tayi karatu amma duk yadda ta dage a cewarta ko kadan bata ganewa. Zama tayi kusa
dashi kaga Baba kawai ka kaini makarantar koyon sakar nan. Har na tambayo matar
tace a wata biyu zata koya min sau uku a sati zani. Kuma a dubu shida. Ai kaga yafi
sauki akan WAEC din. Ta nuna kanta ni da ka ganni bani da abinci a boko. Kan baya
dauka yadda kasan an zuba dusa a kwakwalwar haka nake. Shi din ma ya kusa dariya
sai ya dan dake. Tashi ki bani wuri ni. Ko damuwa ba kya yi yan ajinku zasu tafi
makarantun gaba ke kina son koyon saka. Ta dan tura baki to ya zanyi Baba. Suma fa
duk harkar ta koma satar amsa. Idan sakar ma bazata yiwu ba kawai kayi min aure ka
huta. Shi da Umma a tare suka yo kanta suna mata fada. Da gudu ta tashi tayi hanyar
waje tana dariya tare da jan mayafin Umma a igiya.
[9/25, 2:39 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU🗿3
Batul Mamman(Mrs)💖
Mal Bashir Ibrahim mutumin Ajingi ne ta jihar Kano. Su biyar ne maza a gidansu
shine na biyu. Mahaifinsu manomi ne kuma yana kiwon shanu da tumaki. Da farko sun
fara karatu har ya kai aji hudu a makarantar gaba da firamare sai babansu ya matsa
akan basa samun lokacin taimaka masa a gona. Shi a son ransa duk su hakura da
karatun. Ko kadan Bashir baiji dadin hakan ba, sai da ya hakura shi da wansa da mai
bi masa suka koma gona. Sauran biyun suka cigaba. Akayi rashin saa autanma ya dena
zuwa don shi yafi son kiwo. Wanda ya karasa kuma kan nasa kamar na Zuhra. Ba wani
sakamakon kirki ya samu ba. A halin yanzu ma masinja ne a wani company. Mal Bashir
ya dawo birni shima aikin kafinta a nan ya hadu da Atine yar kwanar Diso ya
aura.sun jima basu sami haihuwa ba gashi yana da son 'ya'ya ,sai daga baya aka
haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Mal Bashir kuma sunan Atine shiyasa suke
kiranta Zuhra.
Zuhra na fita gidansu Hajara ta nufa tana ta mita ta jawo mata fada a gida. Da
sallama ta shiga sai dai babu kowa a tsakar gidan. Daga dakinsu Hajara ta ji an
amsa ta shiga. Kwalliya Hajara take yi anyi wankan yamma tana shirin fita unguwa,
mudubi ne a hannunta tana zana gira. Zuhra ta sakar mata dundu a baya...shegiya kin
hada min zafi a gida kin zauna kwalliya. Hajara na sosa bayanta suka ji muryar
mamanta. Ta shigo dakin haba Zuhra sau nawa za'a hanaki zagi ne? Zuhra ta sunkuyar
da kai tana hararar Hajara. Mama tace idan na sake ji Allah da yayanku Lawal zan
hadaki. An kwana biyu ba kiji bulala ba shiyasa kika dawo da yi mana zagi. Zuhra
tace don Allah kiyi hakuri na dena daga yau In sha Allah. Mama tace da kin kyautawa
kanki sannan ta fita. Hajara ta cigaba da kwalliya suna hira tace ke ni fa Sahabi
ya dage sai nayi karatu. Yace zai rinka yi min lesson kafin a fara WAEC don har ya
biya min kudin a wata makarantar. Zuhra tayi dariya zaiyi asarar kudi da lokaci
kenan. Baki fada masa kina sahunmu bane? Bana son wulakanci wallahi tunda na
fahimci yana son nayi karatu na soma dagewa. Wannan karon mutum shida na doke harda
ke. Zuhra ta daga hannu alamar jinjina kaga su Fropesa Hajara kenan. Hala irin su
Ligan dinnan zai nema miki. Kanwar Hajara da ke tsakar gida sai dariya ta leko ta
taga...Yaya Zuhra kin fiye abin dariya. Wai Ligan...Legal ake cewa. Zuhra ta hade
fuska tace in ba tsoro ba ki shigo dakin nan ki fada mana kiga yadda zanyi dake.
Marar kunya kawai. Hajara ma dai dariyar take ta dauko dankwali zata daura. Sai da
ta daura wani dakal dakal din mayafi karami. Ta daure shi da ribbons har biyu
manya sannan tayi dauri. Daga karshen daurin ta zaro wani ribbon din mai gashi dogo
daga jikinsa ta makala taga ya zauna sosai sannan ta tura shi a jaka. Duk abinda
take idanun Zuhra kyam a kanta. Tace Hajara gashin doki kika koyi sawa? Da sauri
Hajara ta toshe mata baki. To sarkin karadi kada ki fada da karfi sai na fita zan
saka. Zuhra tace wallahi babu kyau kuma kema kin sani. Ga acuci kin dora wannan
wari ma ya isheki. Hajara tace ke ba yau zan saka ba fa. Yanzu ma gidan Anti Faiza
zani tayata aikin abincin da zasuyi a makotansu. za'ayi party ne a gidan. To gobe
zansa idan zaa wurin party din. Zuhra tace happy bazday tuyu zasu yi? Oho nima ban
sani ba. Tace dai yan gayu ne a gidan. Zuhra tace duk da haka bani gashin na kona
ko na fadawa Mama.
Da kyar Hajara ta bata ribbon din. Za ta fita Zuhra tace ke kamar kwailin kike ko,
kinga fuskarki kuwa? Sai yanzu na lura. Hajara ta dora hannu a ka. So kike dai Mama
taji tayi fada kike wani daga murya. Kuma bleaching ake cewa ba kwailing ba kalmar
ko dadin ji babu. Tana murmuahi tace wani mai na samu mai dan kyau na gyaran fata.
Kinsan tunda biki ya matso gara na shafa na dan washe. Zuhra dai tabe baki
tayi...wallahi Hajara ki kiyaye sabon Allah. Ga acuci, ga bleaching ga karin gashi.
Shi Sahabin zaki ha'inta da farin karya ko danginsa. Naga dai duk a unguwar nan
kuka tashi to meye basu sani ba.
Karasa hada jakar tafiyarta tayi tace to malama zuhra idan kin gama waazin ki zo ki
rakani bakin titi. Kuma wallahi kika fadawa su Mama sai munyi fada. Zuhra tace mun
dade bamuyi ba...ni akan irin wannan ba sai dai aji kanmu ba. Lokaci guda kika
tsiri irin wadannan abubuwan kawai don zakiyi aure. Hajara tace to in kinji haushi
kema ki fitar da miji mana. Ran Zuhra ya soso ta dan yi murmushi miji dai Allah ke
bayarwa. Kuma da yardarSa idan na tashi aure sai na sami miji na gani na fada. Daga
nan tayi tsaki ta fita Hajara na kiranta tana bata hakuri. A tsakar gida suka tarar
da Mama tace har anyi fadan ne kajin Mama? Ku zo nan...suna harare hararen juna
suka durkusa gaban Mama. Tace duk naji abinda kuke fada. Ke Hajara akan an fada
miki gaskiya kike gayawa yar uwarki magana ko? Duk canjin halin da kika koya yan
kwanakin nan ina lura dake. Shiru nayi so nake farin naki yafi haka yawa sannan
nasa yayyanki maza suci ubanki a gidan nan. Zuhra ta kwalo ido....lah Mama kema
zagin kike yi. Mama tace ban kuma ce kiyi ba, nima kuskure ne. Ta cigaba da yiwa
Hajara fada kije gidan Yayar taku ki dawo zanyi maganin rawar kan nan naki. Ita ma
ba kyaleki zata yi ba kin sani sarai. Idan na sake jin kuna fada kuma ni daku ne.
Ki wuce ki rakata ta hau adaidaita tace da Zuhra. Sum sum suka tashi suka fita.
Zuhra ke rike da jakar kayan amma har suka je titi ko tari basuyi wa juna ba. Sai
da adaidaita sahun ya fara tafiya Hajara ta leko tana dagawa Zuhra hannu. Itama
dagawa take tana tambayarta yaushe zaki dawo. Hajara tace sai yanzu zaki tambaya?
Kwana goma zanyi.....Zuhra harda dan hawaye ta koma gida. Irin wannan fadan sun
saba yin shi da Hajara. Sai dai suna sake haduwa zancen ya wuce kenan.
[9/25, 2:39 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU🗿4
Batul Mamman(Mrs)💖
Hajara na sallama gidan yayarta ta hadu da babban dan Anti Faiza Abba zaune a bakin
kofar gida. Hannunsa ta gani a nade alamun gyaran karaya ko gocewar kashi. Yana
ganinta ya rungumeta A dan tsorace tace Babana me ya sami hannunka? Yace fadowa
nayi daga kan babur din Baba. Ba dai hatsari kukayi ba ko ta tambayeshi suna shiga
cikin gidan. Yace a'a jiya ne da daddare na hau sai na fado. Anti Faiza na jin
muryarsu ta fito tana mata sannu da zuwa. Tace kafin ki fara korafi jiya abin ya
faru ni kuma bana son tadawa Mama hankali sai ya dan ji sauki. Hajara tace ba komai
Allah Ya sauwake. Sauran yaran uku suka zo suna mata sannu da zuwa. Mai bin Abba ce
ta kalli Hajara da kyau sai tace Anti Hajara kinga fuskarki tayi fari, kafarki kuma
baka. Ko kema mai bleaching ce irin ta fim dinnan....
Gaban Hajara ya fadi, Anti Faiza ta bar raba kayan wanki da take yi tace bazaki
make mata baki ba kina jin abinda take fada. Nabila ta ce Allah ki kalli kafarta da
fuskarta ki gani. Anti Faiza ta taso zata kaiwa Nabila duka sai taga Hajara na jan
siket dinta tana kara rufe kafa. Anti Faiza tace su fita tana mata wani kallo. Gaba
daya cikin Hajara ya duri ruwa. Tun kafin ta tambayeta tace wallahi Mama tayi min
fada dazu kuma bazan kara yi ba. Anti Faiza tace da kina hauka ne kika fara shafe
shafe. Ta fizge jakar kayan Hajara ta zazzageta a wurin tana duba kayan tana fada.
Hajara a hankali ta gode Allah da Zuhra ta karbi ribbon din mai gashi a jiki. Anti
Faiza kuwa ta kare mata tas sannan tace ke da Zuhra kuke yi ko? Hajara tana matsar
kwalla tace a'a ni kadai ce. Ba wani nan, abokin barawo ai barawo ne kuna tare wata
rana zata koya ne. Ta fara laluben wayarta. Zan kira Umma ince a turo min ita ko
zuwa asabar ne in ja muku kunne da babban baki. Ba don hannun Abba ba ai gidan
zani na hada ku. Wato kun girma zaku nunawa duniya baku da mafadi. Ita dai Hajara
sai bada hakuri take.
Bayan kwana biyu Zuhra na zaune kan karamar kujera a kofar kitchen Umma na ciki
tana duba miya da yar karamar fitilarta gwamnati ta gaza. Zuhra ta rike ciki ta
fara waka.
Dan kanzo
Iya ko dan dago dago
Iya yunwa bata da hankali
Iya yunwa taci mutum tara
Iya.....
Umma tace Zuhra ko in miko miki kwano ne? Ta washe baki Umma kin gama girkin. Umma
tace a'a wai da ki tafi makota bara. Baki Zuhra ta turo tana rike ciki ni shiyasa
bana so kice zakiyi girki Umma musamman tuwo sai ki dade. Miyar nan tun kafin
magariba kika dora gashi har an idar da isha. Umma tace ni kuma kinga bana son
danyen girkin nan naku. Sai ayi tuwo da miya cikin rabin awa. Suna magana Baban
Yara ya shigo. Zuhra tana matse ciki tana masa sannu da zuwa. So take yasa Umma ta
kada miyar haka. Dariya yayi musu ya shige ciki. Ga mara juriyar yunwa , ga mai
dadewa a girki.
A falo suka zauna suna ci. Da yake ba wuta Zuhra kasa jira tayi nata tuwon ya huce
tasa mafici tana fifitawa tana ci. Ta cika baki da tuwo tace Ummana kin iya girki
sosai sai dadewa. Umma tace bazaki yaba min ba sai kin hada da mita. Wannan mijinki
sai yayi da gaske wurin noma. Baba yace to dai kada ki takurawa babata. Ya fito da
wata leda daga aljihunsa. Ya danne ta da dungulmin hannunsa sannan ya bude da dayan
ya dauko gasashshiyar kaza. Umma tace yau dadi zamu ci BabanZuhra. Yace Ya'u ne ya
siya shine ya debar min yace na kawowa Zuhra. Dadi ya kamata taje ta durkusa a
gabansa. Cinya ya dauko mata da fikafiki biyu. Ta karba da murna ta koma wurin
zamanta.
Kamar ance ta daga kai ta hango hannuwan iyayenta a gefen kwano suna kokarin raba
wuya su ci. Duk zumudin da take a lokacin wani daci taji a wuyanta. Hawaye ya sauko
mata tayi saurin gogewa. Ta dan gutsiri naman kadan tace washhhh.