Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
ba Alh Sunusi
mahaifin Izzatu ya kirashi da kansa yace lallai yazo gidan anyi masa masauki ko da
shi kadai ne. To ta yaya zaije gidan shi kadai dole ya tafi da Izzatu. A haka suka
rabu yayi shirin tafiya office.
Da rana da ya dawo a kitchen yaji motsin Zuhra. Yana shiga ya tarar da ita tana
rabon abinci a cikin irin abin take away dinnan. Jallop din shinkafa tayi sai kwai
da ta dafa ta yanka shi bibbiyu take sakawa a abincin. Hamza ya dan dauki lokaci
yana kallonta bata kula ba saboda ta juyawa kofa baya. A hankali yaje ya rufe mata
ido tayi murmushi tace Ya Hamza ka dawo?
Cikin wasa ya bata rai, ya akayi kika gane nine?
Tace da kamshin turarenka mana.
Jera abincin yaga tana yi a wasu manyan robobi yace abincin meye wannan Cutie?
Ta dan kalle shi tayi murmushi...ni banso ka dawo ka tarar ban gama ba. Abincin
sadaka ne zan bawa maigadi yace akwai makarantar allo a nan baya. Nayi da niyyar
Allah Ya baka sa'a kuma Yasa kayi karatun ka gama lafiya. Tana kaiwa nan idonta ya
ciko da kwalla, tunanin rabuwarsu da Hamza na wata biyu ke damunta. Shi kuwa kasa
magana yayi kamar kodayaushe idan tayi wani abin da yafi karfin tunaninsa. Har
abincin sadaka take yi wanda yasan akan yi lokaci lokaci a gidan iyayensa. A take
yayi wa kansa alkawari indai ya sami sarari da yardar Allah Hajji zai kai Zuhransa.
A duniya dai shine kawai abinda zaiyi mata na karshen jindadi a matsayinta na
musulma. Amma a nan kanta ya dafa ya rinka saka mata albarka. Sonta kuwa kullum
karuwa yake a zuciyarsa saboda kyawun halayenta.
Kwanaki biyu a tsakani su shirya tafiya Abuja. Izzatu sai rawar kafa take kamar
farin shiga a zuwa Abuja. A motar Hamza suka tafi da aka gyaro. Zuhra tasha kukanta
a daki Hamza na rarrashi sannan ta fito ta rakasu.
Kwanansu uku suka dawo aka fara shirye shiryen tafiyar Hamza zuwa kasar South
Korea. Kwanaki uku suka rage ya tafi idan kaga Zuhra duk tayi wani iri. Har rama ta
danyi saboda zulumin tafiyar Ya Hamza. Dambun nama ta roki Umma tayi mata saboda
ita idan tayi duk sai rabi ya kone. Ai kuwa Umma tayi mai dadi musamman da tasan na
tafiyar Hamza ne. Da aka kawo yayi ta murna.
Izzatu ma a nata bangaren cake tayi masa kanana mai dadi ta jera a wata roba sannan
ta liketa saboda kada ya bushe. Itama Hamza yayi mata godiya.
Da asuba ana saura kwana biyu ya tafi kuma ranar Zuhra zata fita girki. Tunda ta
idar da sallah take masa kuka. Duk abinda zaiyi mata tayi shiru yayi amma minti
kadan sai ta cigaba. Ya zuba mata ido kawai yana kallonta.
Cutie wai kukan nan na meye? Ba fa yau zan tafi ba.
Ta dago jajayen idanunta...to meye maraba Ya Hamza daga yau kai da ka sake
kwana...sai tayi shiru kanta a kasa
Ya share mata hawaye kina tunanin zanyi wata biyu bamy hada shimfida ba ko? Gashi
ke kuma kina son kwanciya a jikin mijinki.
Rufe ido tayi a kunyace...ni ba haka nake nufi ba.
Hamza yayi dariya yace ai ba sai kin fada ba na sani. Addua kawai nake bukata daga
gareki. Kinga jiya munfi awa daya ina nuna miki yadda ake whatsap saboda haka
zamuyi ta hira kullum kinji ko. Idan kika yi kwalliya kullum ki turo min hotonki na
gani.
Ta gyada kai wani hawayen na taruwa a idonta...Ya Hamza yau kada kaje ko'ina har
sai lokacin da zan fita girki. Don Allah ka zauna dani.
Hannunta ya kama ya tasheta daga kan gadon. Muje har breakfast tare yau zamuyi.
Manne jikin juna suka sauko saboda asabar ce su Khalifa basu da makaranta. Sai
karfe goma zasu je islamiyyar safe.
Kayan kwabin fanke Zuhra ta debo ta fara kwabawa. Hamza taji ya tsaya a bayanta ya
zira hannu a robar da take kwabin yana wasa da hannunta sannan yana bin wuyanta
yana kissing. Gabadaya aikin gagararta yayi cikin kankanuwar murya tace Ya Hamza
don Allah ka bari na gama. Koma can gefen ka tsaya.
Yi yayi kamar yayi fushi yace ba ke kika ce kada na barki ba yau. Ni babu inda zani
ya fada yana sake rumgumarta ta baya. Muryar Junior ce tasa ya saketa ba shiri da
ya shigo kitchen din yana murza ido.
Maama fanken zaki yi min don Allah?
Zuhra tayi murmushi tace kaga har na gama kwabawa sai mu dan jira ya tashi ko.
Rungumeta yayi daidai kafarta yace Maama kinfi sona akan Daddy shiyasa kike dafa
abinda nake so.. nima idan na girma ke zan fara siyawa mota da jirgi kafin Mummy da
Daddy.
Hamza ya bude baki
yana kallonsa. Lallai yaran zamani kun iya sa ido. Kai yanzu har kasan so? Ya fada
yana daga Junior sama suna dariya.
***********
Wannan shafin naki ne Maman twins. Gaisuwarki ta riskeni ina fata nima tawa ta iso
gareki. Godiya mai tarin yawa tare da fatan alkhairi. Allah Ya albarkaci zuria.#
AL'ADUN WASU ##73
Batul Mamman(Mrs)##
Jirginsu Hamza shabiyu da rabi na dare zai tashi shiyasa ya yanke shawarar barin
gidan karfe goma domin ya sami damar zuwa gidan iyayensa yayi musu sallama.
Sai da ya dawo daga masallaci bayan sallar isha sannan yaci abinci kadan yaje yayi
wanka. Gidan duk yayi wani iri saboda kowa na tunanin tafiyar Hamza. Ya shirya
cikin kananan kaya yayi kyau sannan ya dauki rigar sanyi a hannu saboda banda
sanyin jirgi ya bincika ana sanyi sosai a South Korea. Ya gama shirinsa tsaf suka
sake wata sallamar da Izzatu sannan ya fito zaije dakin Zuhra. Gabansa Izzatu tayi
saurin tarewa ta daure fuska....Baby ina zaka je kuma?
Shima tasa fuskar a daure saboda bata masa lokaci da yake ganin zata yi yace zanje
sallama da Zuhra mana.
Yana soma tafiya ta rike masa hannu....bafa zan yarda ba. Yau girkina ne saboda
haka bai kamata kace zaka wata sallama da Zuhra ba. Ba tare zamu airport din ba?
Sai kuyi sallamar a can.
Dan rufe idonsa yayi sannan ya bude a hankali....Izzy kada kisa mu rabu da bacin
ran juna. Zanyi tafiyar wata biyu har zancen wani girki zai taso? Kije ki fito min
da jakar kayana, idan bazaki iya ba ki jirani a kasa ina fitowa zamu tafi.
Bai kara saurararta ba ya tafi dakin Zuhra. Zaune ya ganta akan kujera tana sharar
hawaye. Ta gama shiryawa ta saka wani katon hijab tana jira Hamza ya fito su tafi.
Tana ganin ya shigo tayi saurin goge hawayenta ta mike tsaye...Ya Hamza har ka
fito?
Murmushi yake yi yana kallonta. Na fito Cutie, wato baki dena kukan ba ko?
Kamar yace yi wani kukan ta soma wani sabo. Ya dauki lokaci yana bata hakuri da
rarrashi duk ta hanyar da yasan zai dauke mata hankali. Da kyar tayi shiru tana
fada masa irin yadda zata yi kewarsa idan ya tafi. Wayarsa ya dauko yana daukarta
hoto tana ta rufe fuska wai bata yi kyau ba.
Yace gara na dauki fuskar a haka nasan cewa idan na tafi kullum zaki tuna dani
kamar yadda zan tuna dake.
Jin haka yasa ta dauke shi itama sannan suka yi wani tare. Suna cikin haka suka ji
wani mahaukacin bugun kofa. Yasan aikin Izzatu ne dama yana sane ya kulle kofar
dakin don ba karamin aikinta bane ta bude su. Sai da ya sake yiwa Zuhra kyakkyawar
sallama sannan suka fito tare fuskokinsu dauke da murmushin da ya kona ran Izzatu.
A gida aka bar yaran wurin Tala saboda dare ne. Kowa yana fadar me Daddy zai siyo
masa na tsaraba. Suna zuwa gaban mota Izzatu tayi saurin shiga gaba. Dama Zuhra
bata yi tunanin shiga ba saboda tasan ba ita ke da girki ba. Kafin su je gidansu
Hamza taga kayan takaici kala kala. Hannun Izzatu a cinyar Hamza yana tuki. Ko ta
sakala hannun a wuyansa ta wani kwanta a jikinsa. Yayi mata magana har ya gaji.
Baya son abinda zai batawa Zuhra rai. Da suka je gidan Izzatu ta zauna kwam sai
Hamza ya bude mata kofa. Hakan ya bashi damar tsayawa bawa Zuhra da ta fito hakuri.
Don bata son ya tafi da baccin rai shiyasa ta nuna masa babu komai. Izzatu ta gaji
da jiransa ta bude ta fito suka shiga ciki.
Duk kannen Hamza sun zo yi masa sallama. Mota uku suka yi zuwa airport wasu a tasa
wasu a ta Ibrahim da Nura.
Sai da zai shiga ciki Izzatu ta soma kuka duk ana jinta ta rungume shi tana cewa
zatayi missing dinsa. Tamkar ya tona kasa ya rufe kansa saboda kunyar kannensa dake
wurin. Ibrahim barin wurin yayi saboda bacin rai. Sai da Hamzan yayi mata tsawa
sannan ta kyale shi tana kallon yanayin Zuhra wadda ranta ya gama baci. Abinda yake
gudu dai sai da ya faru sun rabo da Cutie dinsa ranta babu dadi. Key din motarsa ya
bawa Izzatu yace su tafi gida ita da Zuhra don yasan ta kware a tuki.
Bayan ya shige ciki motocin su Nura da Ibrahim ne suka fara yin gaba sannan Zuhra
da Izzatu suka tafi wurin motar Hamza. Da Izzatu ta bude ta shiga sai tayi saurin
danna central lock ta rufe Zuhra a waje. A take hankalin Zuhra ya soma tashi ga
dare ta fara buga glass tana yiwa Izzatu alama da ta bude mata. Glass din ta sauke
kadan tace....naga babu abinda baki iya ba shiyasa kullum Hamza yake yabonki to
wannan yabon ya kaiki gida. Daga nan ta fige mota tayi gaba ta bar Zuhra a tsaye.
Wayarta ma Hamza ya jona mata chaji tana cikin motar. Zuciyarta ke wani irin bugu
saboda tsananin bacin rai. A rayuwarta bazata taba mantawa da Izzatu da ire-iren
wulakancin da take mata ba. Kukan ma ta kasa ita daga airport din ma bata san
hanyar da zata bi taje gida ba gashi tasan ko ba'a fada ba shabiyun dare ta kusa.
Wani irin tsoro ne ya ziyarci zuciyarta ta fara addu'o'i. Jiki a sanyaye ta fara
tafiya hanyar da tasan zata kaita bakin gate ta fita. Motoci kadan ne suke wuceta
tana tafiya a gefen titi. Ga irin yanayin da muke ciki na raunin tsaro babu wanda
ya tsaya yayi yunkurin taimaka mata. Itama ko an tsaya bazata shiga ba saboda
tsoro.
Shabiyu saura minti uku Izzatu ta shiga gida. Maigadi ya tareta yana mata sannu da
zuwa. Cike da nishadi ta shige ciki saboda ta gama tsara abinda zata fadawa Hamza
idan Zuhra ta kai kararta. Rantsewa zata yi motar Ibrahim ta ga ta shiga shiyasa ta
taho. Dama shima Ibrahim din ta tsane shi saboda tun farkon aurenta ta kula baya
sonta. Kai tsaye dakinta ta wuce ta tafi ta kwanta hankali kwance.
Shiru Tala bata ga shigowar Zuhra ba tana son bata canjin kudin kulu da ta aiketa
saboda bayan asuba take son tafiya garinsu zata je tayi sati biyu kamar yadda Hamza
ya bada umarnin ta je. Gajiya tayi da jira ta fita waje maigadi har ya kwanta ta
buga masa kofa ya fito ta tambayeshi ko yaga shigar Zuhra ciki. Yace shima yayi
mamaki amma Izzatu ita kadai ta dawo.
Har Tala ta juya zata koma ciki sai dai hankalinta bai kwanta ba. Da yake da waya
ta fito sai ta gwada kiran Zuhra. Karar wayar suka ji daga cikin mota saboda a
gefen motar suke a tsaye. Nan da nan Tala da maigadi suka shiga tashin hankali.
Tace bari naje na tambayi Maman Khalifa ko ba a gida zata kwana ba.
Maigadi yace ashe baki da tunani ban sani ba? Tare ya kamata su dawo amma basu dawo
ba kuma duk munsan ba da ita maigida zaiyi tafiya ba. Ni a tawa shawarar ki kira
wani a gidansu Yallabai kiji ko a can zata kwana tunda ya fada min da bakinsa can
zai fara zuwa kafin yaje iyafot din.
Da yake a rude take a take tace bata da numbar kowa. Har ta soma kuka tana tunanin
ko wani mugun abin ne ya sami Zuhra. Daga baya ta tuna jiya da safe Hamida ta kira
wayarta saboda bata sami ta Zuhra ba. Sai da suka rinka bin nambobin da aka kira a
wayar wajen shida gashi babu kudi sosai sannan suka yi sa'ar samun ta Hamida.
****
Hamida da Adabiyya suna ta hira basu ji wayar da wuri ba. Tala har ta hakura sun
kira wasu nambobin biyu sai ga kiran Hamida ya shigo. Ita duk ta tsorata ganin daga
gidan Yaya aka kira da wannan daren. A tunaninta ko babu lafiya Zuhra ta kirata da
numbar Tala. Jiki na rawa Tala ta dauka tace kiyi hakuri na kiraki a tsohon daren
nan. Dama tambayarki zanyi ko a nan gidanku Maama zata kwana ko gidan iyayenta?
Hamida tace bangane ba Tala. Kina nufin Anti Zuhra bata dawo gida ba? To ina Anti
Izzatu?
Tala tace tana dakinta munga ita kadai ta shigo kuma ga wayar Maaman a motar
Yallabai an jona ta da wani abu. Sautin kukan Hamida Tala ta jiyo tasan lallai ba
lafiya ba.
Ko ajiye wayar bata yi ba ta tafi dakin Mama ta tarar bata nan. Dama tasan Hajiya
na falon Alhaji tun da suka dawo daga airport a nan suka gansu suna hira. Falon ta
nufa da gudu tana yiwa Adabiyya bayanin abinda Tala tace. Sallama tayi ko amsawa
basu jira anyi ba suka daga labulen suka shiga falon. Alhaji ne da matansa suke ta
hira yau basu kwanta da wuri ba.
Hajiya ta daka musu tsawa tana son jin dalilinsu na shigowa a haka. Cikin kuka
Hamida ta fada musu wayar da suka yi da Tala. Babu wanda hankalinsa bai tashi ba a
wannan lokacin. Alh Nasiru ya dauki waya ya kira Ibrahim ya sanar dashi sannan ya
tafi dakin Nura ya taso shi. Ko hula babu a kan Alhaji suka fita da Nura. Airport
din zasu fara dubawa kafin suje gidan iyayenta.
*****
Hadari ne yake hadowa garin yayi duhu sosai sai fitilun cikin airport na gefen
titi. Iska da kura sai kada Zuhra suke tana tafiya idonta sharkaf da hawaye. Banda
Izzatu hatta Hamzan haushinsa take ji. Don me bai tabbatar da ta tafi ba ya shige
ciki. Kullum Umma na fada mata maza basa son macen da tafi kawo kara amma wannan
karon suna yin waya da Hamza idan har ta isa gidanta lafiya kenan zata fada masa.
Dole ayi mata iyaka da Izzatu idan ba haka ba kuma lallai zasu daku. Ko a unguwarsu
babu mai takalar Zuhra dambe don da gaske karfi gareta.
Ajiyar zuciya tayi da ta ga ta kusa isa bakin gate sai dai tun kafin ta isa ta fara
jin ana daka mata tsawa. Nan take ta gigice ganin sojoji sunfi biyar a kanta da
bindigogi.
*****
Sanarwar karshe akeyi cewa jirgi zai tashi kowa yasa seat belt kuma a kashe waya.
Ran Hamza a bace ya kira Zuhra yafi sau ashirin bata dauka. Izzatu kuma da suka
sake sallama tace Zuhran na dakinta. Ya tabbatar idan yace ta kai mata tata wayar
kuma bazata kai ba. Dole ya hakura ya kashe wayar. Sauran mutum hudu da zasu tafi
tare duk ta Abuja suka tashi da kyar ya sami alfarmar tashi ta Kano saboda
iyalinsa. Yayi yunkurin kashe wayar sai ga text ya shigo. Da sauri ya bude ya zata
Zuhra ce.
(Sir idan kana da lokaci gobe ka kirani.
Mr. Oscar)
Rasa abin yi yayi ba don yana cikin jirgi ba ai yanzu zai kirashi yaji abinda zai
fada masa. Addu'ar abin hawa da ta tafiya Hamza yayi ya kashe wayarsa zuciyarsa
tana tunanin me ya sami Cutie dinsa.
****
Kneel down sojojin suka saka Zuhra suna ta turancin da pidgin ta kasa gane abinda
suke fada. Kuka take yi kamar ranta zai fita saboda tsabar fargaba. Wani cikin
sojojin ya harare katon hijab dinta yace ta cire shi da Hausa. Zuhra ta sake
kankame jiki tace bazata cire ba. Saita ta suka yi da bindigogi suna fada...ki cire
hijab mu tabbatar babu komai a jikinki idan ba haka ba a wurin nan zamu harbe ki.
Wasu cikin sojojin har sun fara ja da baya saboda kin cirewa da tayi. Wani yace me
ya kawoki nan? Bakinta har hardewa yake ta fada musu abinda tazo yi. Dariya suka yi
suka karyata ta. Suka bata umarni na karshe ko ta cire hijab dinta ko a harbe ta.
Can gefe wasu sojojin ke ta buga waya ga manyansu suna sanar dasu abinda ke faruwa.
A haka Zuhra tana kuka tana rokonsu ta kama hijab din ta cire gashi kanta ko
dankwali babu dadinta ma doguwar riga ce ta atampa a jikinta. Rigar duk ta matse ta
sama rabin kirjinta a waje. Idon wasu ya kai nan tayi saurin rufewa tana kuka
sosai. Ta saddakar mutuwarta tazo amma har abada bazata taba yafewa Izzatu ba. Shi
kanshi Hamza idan har wani dalili yasa ta tsira to ta bar gidansa kenan.
Motoci biyu ne suka iso kusan a tare sai ga motar 'yan sanda guda daya. Tun kafin
su tsaya Alh Nasiru ya hango Zuhra a durkushe. Idanunsa suka kada suka yi ja saboda
bacin rai. Wannan cin kashi da aka yi mata da me yayi kama, me zai fadawa Mal
Bashir? Ibrahim ko kashe tasa motar baiyi ba ya fito da sauri amma da ya karaso
sauke idonsa yayi saboda bazai iya kallon matar dan uwansa a wannan yanayin ba.
Nura kuwa mai raunin zuciyar da tafi ta Hamza kuka yake yi kamar wani yaro.
Duk fitowa suka yi sojoji na tsayar dasu 'yan sandan suka taho suka fara yi musu
bayanin report din da Ibrahim ya kai musu. Shaida suka nema domin gaskata zancen
'yan sandan. Nura ya duba wayarsa yayi sa'a akwai hoton ranar yinin Zuhra da suka
je daukota daga Ajingi shine ya nuna musu. Duk da haka sai da suka bukaci washegari
a kawo wani na'uin shaidar ko wacece Zuhra.
Alh Nasiru da kansa ya dauko hijab din da akayi wurgi dashi ya dora mata a kanta.
Kasa tashi tayi ya dagata da kansa. Sai a lokacin ta kara sa kuka mai sauti.
Ibrahim ya kalli sojojin yace mace mai hijab sunanta musulma ba 'yar ta'adda ba da
zaku wulakanta ta haka.
A baya Alhaji ya zaunar da ita ya shiga gaba. Ibrahim ma binsu yayi a baya suka
tafi gida.
Jugum jugum haka su Hajiya suka zauna a falo. Ana shigo da Zuhra Hajiya ta ajiye
kunyarta taje ta rungumota. Zuhra ta kankameta tana kuka kamar mai ban tausayi.
Cikin kuka tace Hajiya ai ba laifi bane idan ban yafewa Maman Khalifa ba ko? Kowa a
wurin yaji tausayinta. Ga masu tayata kuka su Adabiyya suna yi.
Da kyar falon ya sami nutsuwa har ta fada musu abinda ya faru. Alhaji ya bata
hakuri sannan yace ta kwantar da hankalinta zuwa gobe zasu san abin yi. Ruwa mai
zafi Mama ta sa aka dafa mata tayi wanka amma taki cin komai. Dole suka kyaleta ta
kwanta cike da tunani kala kala.
[10/22, 4:49 PM] #+234 705 352 3457#: AL'ADUN WASU #74
Batul Mamman(Mrs)#
Gudu take yi a wani daji kafarta ko takalma babu ga gumi da ya wanke mata jiki.
Sautin harbi take ji amma ta rasa daga ina yake fitowa. Tana cikin gudun ta hango
wani gida a tsakiyar