Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
kudinki. A kunyace
Zuhra tace ta barshi. Tayi murmushi ta fita bari a kawo muku abinci.
Hamza ta fita ta kira tana rokonsa yazo gida Mummynta tana son ganinsa. Muryarsa a
dashe saboda tsananin bacin ran da yake ciki yace mata ya kusa karasowa gidan. Da
sauri ta koma dakin da ta bar su Zuhra tace mata dan sake gyara fuskarki muje. Anti
Faiza tace ina zaku ake magana bama ganewa? Izzatu tace sirri ne. Kawayenta na
dakin kuwa sun gane suma dariya suke yi. Yan kayan kwalliyar jakarta ta dauko ta
sake shafa hoda da janbaki. Fuskar nan ta fita daban da sauran jikinta saboda
kyallin foundation. Tun a dakin kannen Izzatu da yayarta Zeenatu ke dariya kasa
kasa. Ita kuwa uwar gayya ko a jikinta tace da Anti Faiza yanzu zata dawo su tafi.
Mamaki Hamza yayi yadda gidan ya cika da mutane haka. Yadda yake ji idan Izzatu
bata yi da gaske ba zai iya marinta. Sanadiyar bin al'adun wasu ta janyo masa asara
mai girma. Ita ta tada masa hankali yasa hannu a takardar ba tare da yasan me yake
yi ba. Kuma ta goge masa messages. Tsaki yayi ya shiga gidan ta baya. Wani karamin
falon ya shiga shiga ya kirata a waya. Bata kawo komai a ranta ba jin yanayin
muryarsa. Burinta kawai taga yadda zasu kwashe da Zuhra idan sun hadu. Its Zuhra
zaman jiran da take yi a falo ya fara isarta don ma da mutane.
Da sauri Izzatu tazo da tray a hannunta dauke da juice da soyayyan nama a karamin
plate ta mika mata. Muje ku gaisa ku tafi Faiza duk ta damu. Zuhra ta dan gyara
mayafi ta karbi tray din. Sai da suka je kofar falon duk taji kunya kamar kada ta
shiga. Izzatu ta turata tare da komawa falo tana sanar da mutane su shirya dariya
zata yiwa wata April Fool. Mariya na jin haka ta mike da sauri tace da Ummahani
kila yarinyar nan ce. Na rasa abinda ke damun Izzatu. Bata kara magana ba suka ji
karar fashewar tangaran.
Lokacin da Zuhra ta shiga falon da sallamarta. Hamza ya taso a fusace yana cewa
Izzy kinsan abinda kika jawo min yau? Zuhra tayi saurin daga kai suka hada ido,
bata san lokacin da ta saki tray din ba. Mutumin nan da ya kusa marinta ta gani.
Bakinta har rawa yake tana cewa yayi hakuri ta durkusa tana tsince sauran jug da
kofin da ya fashe. Dama a harzuke yake yace me ya shigo dake falona? Waye ya bude
miki? Duk ta kidime tace Anti Izzatu ce. Zuwa lokacin kofar falon ta cika da yan
gidansu Izzatu har da ita. Sauran mutane ma jin ana daga murya suka zo kallo. Hamza
yace ita Izzatun ce ta bude miki falona tace ki shigo. Zuhra tace eh. Hamza na daga
murya yace ba kece mara kunyar yarinyar nan ba, wato sata kika zo yi. Da sauri ta
girgiza kai tace a'a wurin Hamza nazo.
Daga shi har Zuhra babu wanda hankalinsa ke bakin kofa bare su ga yadda mutane ke
kallonsu. Yan gidansu Izzatu da suka san komai sune suke dariyar yadda jikin Zuhra
ke rawa. Yace Hamza? To nine Hamzan ya akayi? Zuhra tace ba kai Hamzan ba. Kannin
anti Izzatu ne yace yana sona shine yake min tes. Ita tace na zo nan yana jirana
wallahi. Hamza ya runtse idanunsa yace idan na bude baki bace min a wurin nan ba
sai na bata miki rai. A gigice ta juya ta hango Izzatu. Ta karasa gabanta tace yi
hakuri na fasa miki kaya. Amma ni ban gane ba mijinki yace shine Hamza. To waye
kanin naki? Wata irin dariya taji sun kwashe da ita suna cewa APRIL FOOL!!!.
Ko da bata gane me suke nufi ba amma dariyarsu tayi mata ciwo sosai. Hawaye kawai
take yi ko gani bata yi sosai yadda hawayen ke zubo mata tace Apre..me? Kanwar
Izzatu ta sake cewa April Fool. Da wannan fuskar taki kike tunanin yin saurayi dan
gayu. Ina ji kuna hirar da matar da kuka zo. Anti Faiza tace Izzatu wai me yake
faruwa ne. Na zata kuskure kikayi da kika ce a nan kanin naki yake jiranta. Ba sai
kiyi musu bayani ba. Da kyar Izzatu ta tsayar da dariyarta tace ni nake yin text
din.
Hamza kallon Izzatu yake yi tana dariya ita da yan uwanta. Sauran mutanen wurin
kuwa kadan ne abin ya basu dariya. Sauran tausayin Zuhra suke yadda rashin sani
yasa ta fuskanci wulakanci. Anti Faiza ta rungumo Zuhra wadda bata san inda take
jefa kafafunta ba. Sautin dariyar da aka yi mata kawai take ji a kunnuwanta. Izzatu
ta cigaba da cewa april fool nayi mata na rinka tura mata text din soyayya. Ta zata
saurayi tayi har ta amince. Ta dafa kafadar Zuhra ta sake cewa april fool. Kada ki
damu it was just for fun.
Saukar mari taji mai kamar wuta a kumatunta kafin Hamza yace kowa ya fice masa daga
gida. Mata suka tsaya kallonsa ya daka musu wata tsawa. Ba shiri suka fara bacewa.
Izzatu na dafe da kumatu ta juya taga ba Hamza, Zuhra da Anti Faiza.
Anti Faiza jan hannun Zuhra kawai take yi har suka fita daga gate din gidan.
Ummahani ce tayi musu horn Mariya na gaban motar suka ce su shigo. Anti Faiza tace
su tafi kawai. Mariya tace kiyi hakuri ku shigo kada a rinka kallonta kinga an fara
fitowa..
Anti Faiza tana ta cewa su tsaya zasu sauka a hanya amma Ummahani taki tsayar da
motar. Mariya tace ki kwantar da hankalinki zamu kaiki inda za'a bi muku hakkinku.
Anti Faiza ta cije lebe tana kallon yadda Zuhra ke zubar da hawaye tace Allah zai
isar mana ku ajiyemu kawai ba sai munje wurin yan sanda ba. Ummahani tace gidansu
Hamza zan kaiku. Ni matar kaninsa ce, wannan kuma kanwarsa ce. Sai a lokacin Zuhra
tace ku ajiye mu don Allah. Mariya ta juyo ta kalleta. Dole Zuhra ta baka tausayi.
Wannan karon Izzatu ta wuce gona da iri. Kiyi hakuri mun kusa zuwa gidan. Anti
Faiza tace kunga bama son wani wulakancin ku barmu kawai. Ummahani bata tsaya ba
sai a cikin gidan don tayi saa an budewa Alh Nasiru gate zai fita kenan suka shigo.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/25, 3:40 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿
21
Batul Mamman(Mrs)💖
Ummahani na tsayar da motar Mariya ta fita da sauri ta tari Alhaji. Su Anti Faiza
kuwa fita suka yi daga motar suka yi hanyar gate zasu fita. Muryar dattijo suka ji
yace don Allah su tsaya. Kuka Zuhra ta cigaba tana jan hannun anti Faiza. Mariya ta
zo gabansu tace don girman Allah ku tsaya. Ba yadda zasuyi dole suka biyo bayanta.
Amma duk yadda aka yi Zuhra ta kafe bazata shiga cikin gidan ba. Kukan da take yi
yasa Alh Nasiru yace Anti Faiza da ke mata fada ta kyaleta. Sai a lokacin Zuhra ta
kalli dattijon. Ko ba'a fada ba tasan shine baban mijin Izzatu saboda sunyi kama.
Da sauri ta durkusa har kasa tace ina wuni? Lafiya kalau ya amsa fuskarsa dauke da
murmushi. Kallonta yake yadda take goge hawaye da majinar fuskarta da dankwalin
kayanta. Sannan ta nade kanta da jikinta da katon mayafi.
Suna nan tsaye Mama da Hajiya suka fito tare da Mariya. Hajiya tace yanzu Mariya ke
fada min munyi baki kuma wai sunki shigowa. Anti Faiza da Zuhra suka gaishe su.
Mama ta ce ya naga bakuwar na kuka Allah Yasa lafiya. Alhaji yace Mariya ta dan
soma fada min. Ku daure mu shiga ciki. Mama ce tazo ta kama hannun Zuhra ta tayar
da ita suka shiga cikin gidan ba don tana so ba.
A falo suka zauna Zuhra da Anti Faiza suka rakube jikin kujera. Mariya ta bada
labarin abinda idanunta suka gane mata a gidan Yaya. Mama da Hajiya sai salati
suke. Ita kam Hajiya har kunya taji ace wai Hamza danta ne kuma na fari ma. Alhaji
ya dubi su Zuhra yace ko zaku yi mana bayanin yadda abin ya samo asali. Nan Zuhra
ta soma basu labari. Tana yi tana kuka. Su Ummahani sunji tausayinta sosai. Alhaji
yayi murmushin bacin rai Mariya ku tashi ku kaisu gida. Sai ku gane mana gidan. In
sha Allah anjima zamu zo gidan nayi magana da mahaifinki. Amma kafin nan don Allah
kada ki sanar dasu komai. Zan gyara matsalar in sha Allah. Mama ta matsa kusa dasu
ta rike hannun Zuhra ki yi hakuri kinji 'yata. In Allah Ya yarda Alhaji zai share
miki hawaye kuma zai hukuntasu daidai da abinda suka yi miki. Zuhra ta gyada kai ni
dama dariyar ce ta fi bani haushi. Anti Faiza tace to ba an baki hakuri ba. Tashi
mu tafi. Bayan sun fita Mama tace Hajiya ya kika yi shiru? Hajiya tace hmmm to me
zan ce? Kina kallo kullum lamarin gidan yaron nan kara lalacewa yake. Wai april
fool sai kace wasu kasurguman kafirai. Na rasa yadda ake suke kwakulo duk wata
al'adar banza suna dabbaka ta. Alhaji yace ku kyale ni dashi. Alkawari ne
tsakaninmu akan idan haka ta sake faruwa zan hukunta shi.....wani murmushi kawai
Alhaji Nasiru yayi. Sai na nunawa yaron nan nima ina riko da namu al'adun nagari.
Izzatu ta rike kumatu ta soma kuka. Ita Hamza zai mara a gaban mutane. Sai a
lokacin ta kula kowa ya watse sai yan gidansu da mamanta. Da sauri ta nufi wurinta
zata rungumeta, sai taga maman tata ta matsa. Izzatu ta zaro ido meye ma'anar
hakan. Raliya mahaifiyar su Izzatu ta kalli 'yarta fuskarta na nuna alamun rashin
jindadi tace Izzatu that was extreme. Ban taba nuna damuwata ba idan kuna wasanku
ke da yan uwanki. Kuma ni mutum ce da ta yarda a bar yaro ya sake yayi abinda ransa
yake so. Amma ban yarda da cin zarafin wani don nishadi ba. Me yarinyar tayi miki
haka da har zaki kirawota har gidanki ki mayar da ita laughing stock(abin dariya) a
gaban mutane? Hawaye ne ya cigaba da sauka daga idanun Izzatu tace Mum har me nayi
mata? Kawai ba'a fahimceni bane amma yi nayi don ayi dariya. Raliya tace kada ki
manta yarinyar nan nan mutum ce kamar kowa. Ya zaki ji idan kika sa rai da abu
kamar soyayya sai kawai ace miki wasa ne har a biki da dariya? ta dubi sauran
'ya'yanta ku tashi mu tafi. Laifinmu ne ni da Dad dinku da muka dora ku kan al'adun
da basu dace da society dinmu ba. Gashi mun dawo Nigeria kina ta samun matsala da
inlaws dinki. Izzatu na kallo duk suka fita jiki a sanyaye.
Share hawayenta tayi ta hau sama. A hankali ta bude kofar dakin ta hango Hamza
zaune a kan kujerar gaban madubi ya dafe kansa. Karasa shiga tayi ta tsaya a
gabansa, ka kyauta Hamza. You slapped me for no reason. A yadda ya dago kansa sai
da ta razana ta matsa baya da sauri. Gani take wani marin zai kai mata. Har wani
huci taga yana yi saboda yadda ransa yake a bace. Izzy kinsan abinda kika yi kuwa?
Ta dan sha kunu ita a dole bazata nuna masa ta yarda tayi laifi ba. Don kawai nayi
april fool shikenan sai ya zama laifi. Har ka manta babu shekarar da bama yiwa
juna. Last year kaya ka kawo min wai na fadar kashiya. Sai da na gama yarda nasha
kukana sannan kace april fool. Shi inda ya dosa daban da abinda take fada. Saboda
tashin hankalin da yake ciki ya manta da wani wasan april fool da tayi. Wannan
last year ne, har kin manta nace mun dena duk irin wadannan abubuwan. Tace ban
manta ba amma ai wannan ba na kudi bane. Ya rasa yadda zaiyi da ita. Kinga sami
wuri ki zauna kin tsaya min a ka. Bakin gado ta zauna tana fuskantarsa. Izzatu ya
kira sunanta..... naam. Kin taba goge min text da Inuwa ya turo ranar wedding
anniversary dinmu? Dan tunani tayi tace eh, amma na karanta farkon sakon na kuma
fada maka abinda nagani. Shine duk ka wani daure min fuska har da mari. To wallahi
bazan hakura ba. Ta fadi maganar ne tana tashi. Bata ankara ba taji ya janyota iya
karfinsa ya hadata da bango. Da sauri yake numfashi don ji yake kamar zuciyarsa
zata iya bugawa. Idanunsa duk sun kankance. Sai a lokacin Izzatu ta ji tsoro tayi
tunanin tambayarsa abinda ya same shi. Kafin tayi magana yace daga yau idan kika
sake daukar min waya sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. A dalilin wayar
karyar da kika yi kika ce Junior ya karye da deleting text dina da kika yi karayar
arziki na iya samuna. Ga mamakinta hawaye ta ga ya zubo daga idanunsa, abinda bata
taba gani ba. Nan da nan ta rikice, babyna ya zamuyi idan ka talauce? Zamu sami
abincin da zamu ci ko sai Daddyna ya taimaka mana? Gashi kayi min alkawarin zaka
canja min mota. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya ke nanatawa. Zancen ace ransa
ya baci da maganarta ma bata lokaci ne. Izzatu dama baki da hankali??? Tace bangane
ba. Ya daga murya ya soma fada... ina fada miki matsalata kina zancen canjin mota.
To hell with canjin motar taki. Ya dauki kujerar gaban madubin yayi wurgi da ita.
Wani irin bakinciki yake ji wanda yake tunanin idan ya taba Izzatu kila sai dai ta
kwana a asibiti. Ba talauci ba ko me zai sameni tare zamu zauna. Kin jawo min
tashin hankali kala kala kinga ina rabuwa dake shine yanzu zan fada miki halin da
zamu iya fadawa kiyi zancen damuwarki ta banza. Gefe ta koma don gaba daya ta
tsorata da Hamza. Mutum ne wanda da wuya kaga bacin ransa. A hankali ta soma
matsowa kusa dashi zata bashi hakuri sai wayarsa tayi kara.
Ita ma wayar ji yayi kamar ya kwadata da kasa sai yaga Alhaji ne yake kiransa. Yana
dauka Alh Nasiru yace ana saukowa daga masallaci kazo ina nemanka. Sai kawai ya
kashe wayar. Hamza ya rike wayar yana kallonta...Allah Yasa ba gulmar abinda ya
faru dazu Mariya ta kai gida ba.
[9/25, 3:41 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿22
Batul Mamman(Mrs)💖
Daga masallaci gidansu ya wuce ya baro Izzatu tana ta aikin kuka a gida. Lokaci
daya duk ya birkice mata abinda bata saba gani ba. Allah Ya sa su Khalifa ta hadasu
da Tala suna dakinta suna cin abinci duk wannan tashin hankalin da ake yi.
Baiyi mamakin ganin motar Ibrahim ba don yasan kullum sai yazo gidan. Yana ta
sallama yaji shiru ba'a amsa ba. Kande mai aikinsu ce ta fada masa suna dakin
Alhaji.
Sallama yayi ya shiga ya tarar dasu suna ta hira. A ransa yace babu wanda yasan
matsalar da yake ciki. A lokacin da yake jindadi bai kyautatawa iyayensa yadda ya
kamata ba saboda haka yanzu bashi da dalilin tada musu hankali ya fada musu halin
da kamfaninsa zai iya shiga. Mama na ganinsa ta washe baki ta soma guda. Murmushin
yake yayi yace Mama alkhairi muka samu ne? Kwarai kuwa Yaya in sha Allahu alkhairi
zamu samu. Ya karasa ciki ya gaishe da iyayensa. Ibrahim ya miko masa hannu suka
gaisa suna tambayar juna aiki da iyali. Bayan sun dan nutsu Alh Nasiru yace bayan
magriba in Allah Ya yarda zamu je gidan surukan naka. Hamza ya kalli Ibrahim da
alamar tambaya. Alh Nasiru yace da kai nake Yaya. Ni kuma Alhaji, wani abin ne ya
faru? Mama ta katse shi cike take da murna tace babu komai. Rabon da ta sake masa
sosai tun kafin ta karye a gidansa. Alhaji ya ce bani hankalinka nan Yaya. Duk aka
yi shiru ana sauraronsa. Dazu Mariya da Ummahani sun zo gidan nan da yarinya tana
ta kuka akan cin zarafin da kuka yi mata kai da matarka. Hamza yace wallahi Alhaji
ban san da abin ba sai da naje gida. Yau har marin Izzatu nayi akan abinda tayi.
Hajiya ta tabe baki sai kace kayi wani abin arziki. Ai ba laifinta bane ita kadai.
Alhaji ya cigaba da magana...kasan akwai alkawarinmu na ka amince da duk hukuncin
da zan dauka a kanka idan irin haka ta sake faruwa ko? Tuni Hamza ya gano inda
Alhaji ya nufa..muryarsa har tana sarkewa yace don girman Allah Alhaji kada kace
nema min auren yarinyar nan zaka yi. Kayi min wani hukuncin ba wannan ba. A rana
daya abubuwa sai samunsa suke yi. Ba don kada ya nuna karayarsa ba babu abinda zai
hana shi fashewa da kuka. Alhaji yayi yar dariya. Dadina da kai akwai hazaka gashi
har ka gano inda na nufa. Kamar yadda kuka sawa yarinya rai cewa bayan magariba
zaka je gaishe da mahaifinta to tare zamu ayi mai gaba daya. La'ila ha
ilallah...Alhaji kayi hakuri. Idan kaga Hamza a lokacin shima sai ya baka tausayi.
Yana cikin wannan matsalar ina shi ina aure. Auren ma da wannan kucakar yarinyar
mara kunya. Muryar Alhaji ce ta katse masa tunani. Wallahi idan har kaki yarda da
auren nan daya hukuncin da zan iya yanke maka shine na zare hannuna daga dukkan
abinda ya shafeka. Babana ba fa kai kadai na haifa ba, kuma kaine na fari amma
matsalar gidanka ta isheni. Sam ka kasa rike matarka. Hamza yayi shiru yana jinjina
kalaman mahaifinsa. Can dabara ta fado masa yace Alhaji nayiwa Izzatu alkawarin
bazan taba yi mata kishiya ba. Alhaji ya tashi yana cirw babbar rigarsa yace ashe
auren zobe kuka yi bamu sani ba. To kada ka damu yanzu ma alkawarin naka bai tashi
ba tunda ba kai ka nemi auren ba. Ita da kanta ta nema maka. Mu nan karashen aikin
ta barmu dashi kawai. Ka tashi ka tafi gida ka saka manyan kaya don bazamu gidan
surukai da kai a haka ba ka wani ci zanzaro.
Ko kazar da kwai ya fashewa a ciki zata fi Hamza kuzari. Daga kafa yake kamar ba'a
jikinsa take ba. Ko da ya koma gida dakinsa ya shiga ya rufe. Izzatu tayi bugun har
ta gaji. Bai fito ba sai da aka kira magariba. Yayi wanka ya canja kaya. Ba don
kuncin da zuciyarsa ke ciki ba sai ka zata sabon ango ne....kodayake ya kusa zama
angon!
Masallaci ya fara zuwa yayi sallah sannan ya wuce gida. Alhaji da Ibrahim ya gani a
shirye suna jiransa. Mama har bakin mota ta rakosu tana musu fatan alheri. da ta
shiga gida Hajiya tace wato duk gidannan kinfi kowa farinciki da wannan abin. Mama
tayi dariya Hajiya bazan taba manta abinda Izzatu tayi mana ba. In Allah Ya yarda
yanzu Yaya zai san yayi auren yar da ta dace da addini da al'adarsa.
Yadda Ummahani ta kwatanta masa haka Ibrahim ya bi. Hamza yana gaba kamar ruwa ya
cinye shi. Alhaji da Ibrahim sai hirarsu suke yi. Daga bakin layin suka ajiye motar
Ibrahim yace daga nan na manta kwatancen, Yaya ya ma sunan yayartawa? Wata muguwar
harara Hamza yayiwa Ibrahim kafin yace zanci.....Alhaji yayi gyaran murya don yasan
karshenta zagi Hamzan zaiyi. Yau ya zama a lallaba auren zamani. Ibrahim dai dariya
yayi sannan ya kira Ummahani ta tuna masa sunan. Da tambaya suka sami gidan domin
ba wuyar ganewa.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/25, 3:42 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN