Advertisements
Chapter 2 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 36

3K to 6K   out of 106K words

Umma tace kin
kone ko? Dama cin abinci kin kasa jira ya huce. Zuhra tace hakori na ne yake min
ciwo daga nasa naman a baki. Baba yayi mata sannu. Ta tashi ta mayar da duka naman
gashi ku cinye bakina zafi. Baba yace ki ajiye zuwa gobe mana. Idan ya lalace ai
sai nayi kuka Baba. Ta dauki tuwon bari na kai kitchen bazan iya ci ba. Ta fice
tana fifita baki.

A bakin rariya ta tsuguna ta cinye tuwonta ta wanke baki. Umma tace ya naji shiru
ko bakin ne. Tace a'a almajiri na nema a waje. Wuraren shadayan dare su Umma sun
kwanta Zuhra ta lallabo ta fito falo. Tayi sa'a kuwa ledar naman tana nan kan dan
tebur din da suka ajiye tare da jug din ruwa. Zuhra ta bude ledar a hankali ta sami
yan kasusuwan da basu cinye ba duk ta tsotse don naman yayi mata dadi.

Baba ya taso Umma suka tsaya ta yar kofar jikin tagar dakinsu suna kallonta. Hawaye
Umma take sosai a hankali tace bar mana tayi muci. Baba yace muna tausayinta tana
tausayinmu. Allah Ya albarkaci rayuwarki Fatima. Suka koma suka kwanta.

Da safe Umma ta riga ta tashi. Ta fito suka gaisa ta dauko tsintsiya zata fara
shara. Umma tace kamar na bar ledar naman nan a falo. Zuhra ta dan tsorata sai tace
ai da asuba na dauke saboda beraye. Umma tayi murmushi kawai ta fita tsakar gida.
[9/25, 2:39 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿5


Batul Mamman(Mrs)💖
Kafin karfe tara ta gama duk ayyukan da zata yi. Wanka tayi sannan tayi shirin
islamiyya tunda asabar ne ana yin ta safe. Ta gama shirinta tsaf ta yiwa iyayenta
sallama ta tafi.

A darasi na uku Malama Rabia ta shigo. Ita kadai ce mace da ke koyarwa a islamiyar
tana koya musu Nahawu. Zuhra jira tayi sai da aka kammala darasin gaba daya sannan
tace tana da tambaya. Yan ajin har sun soma dariya sannin halinta. Wata tambayar
idan tayi sai kaji kamar shirme. Ita kuwa sai ta dake, sai an bata amsa tace nasan
ku ma kun karu. Malama Rabia tace ina jinki Fatima. Zuhra tace menene hukuncin
macen da ke karin gashi ko bleaching a musulunci. Malama tayi dan murmushi ai
hukuncinsu a bayyane yake, babu kyau. Zuhra tace ai nima nasan babu kyau ina nufin
akwai wata aya ko hadisi da yayi nuni an hana ko kuwa fatawar malamai ce kawai.
Malama Rabia tace to bari mu fara da maganar karin gashi tunda shi tabbas akwai
ingantattun hadisai a Sahihul Bukhari da Sahihul Muslim da suka nuna anyi hani da
yinsa.

Manzon Allah SAW yana cewa Allah SWT Ya tsinewa mai karawa wata gashi da wadda tace
a kara mata. Ki duba hadisi na 5934 a Bukhari da 2122 a Muslim.

A wani hadisin kuwa, Asma'u bint Abubakar(RA) tace wata mata tazo wurin Annabi SAW
tace masa ta aurar da yarta amma lalura tasa gashin kan yar ya zube. Shin zata iya
saka mata gashi? Sai Annabi SAW yayi kashedi ga mai karin gashi da wadda aka
karawa. Bukhari 5479, Muslim 3962.

Malamai sun dauki karin gashi a matsayin yaudara sannan suka yi hani dashi. Akwai
hadisin Mu'awiyya RA wanda yace Annabi SAW yace karin gashi yaudara ce. Sahihul
Bukhari 3229.

Ta koma ga sauran daliban gaba daya. Ku kanku a ma'aunin hankali kunsan cewa akwai
ha'inci a karin gashi. Banda asarar kudi da kuma warin da yake yi a kan mai sawa.
Sannan duk mai karin gashi bata taba rufe kanta gaba daya domin tayi ne don a gani.
Asali ma a shekarun baya muna ganin mace da karin gashi mun san ba musulma bace.
Sai gashi a hankali mun dauki al'adu da dabiun wasu muna yi. Allah Ya shirye mu
baki daya.

Sai tambayarki ta biyu akan masu shafa mai su canja kalar fatarsu daga baka ta koma
fara. Wasu masu zalamar ma fararen ne suke kara kode fatarsu. To duk wannan yana
cikin nau'in canja halitta wanda Allah Ya hana. Shaykh Ibn Uthaymeen yayi bayanin
canja kalar fata na dindindin kamar bleaching a matsayin laifi kamar masu yin
tatoo(zane da wuta ko abu mai kaifi a jiki) da kankare hakori ayi wushirya. Irin
wadannan laifukan Annabi SAW ya sanar damu tsinuwar Allah ta tabbata ga masu yinsu.
A bangaren lafiya kuwa munsan cewa babu wani nauin bleaching wanda bashi da illa ta
kusa ko ta nesa. Wanda munsan Allah Ya hana mu cutar da kawunanmu. Ga zubar da
mutumci da kimar mai yi a idon wadanda suke da hankali suke amfani dashi. Ga asarar
kudi da sauran abubuwa marasa kyau. Allah Shine mafi sani daga kurakuran da muke
aikatawa. Allah Yasa duk abinda zamuyi mu tsaya a iyakar da Yayi mana. Laifukanmu
kuma Ya Yafe mana.

Gabadaya ajin suka ce Amin. Jikin yan matan duk yayi sanyi saboda ba'a rasa masu
dan shafe shafe da masu dora gashi ko da a jikin acuci ne irin na Hajara. Zuhra
tayi godiya ga Malama Rabia sosai. Duk bayanan da tayi kuwa ta rubuce su a yar
takarda wanda zata nunawa Hajara shaida. Ta so ace Hajarar na nan tayi tambayar.

Daga kofar daki 'yan matan biyu suka ce Mama mun tafi. Ba tare da ta dago kanta
daga laptop din gabanta ba tace Allah Ya kiyaye hanya ku gaishe su. Shiru taji ba
amsa...tana dagowa taga sun tafi. A ranta tace na rasa saurin me yaran nan suke yi
haka.
Hajiya ta fito daga dakin Alhaji taji karar mota. Sauri tayi kada su tafi ta basu
sako su siyo mata a hanya idan suna dawowa. Kayan da ta gani a jikin Adabiyya ne
yasa ta kara sauri tana kwala musu kira. A tsorace Adabiyya mai shirin shiga mota
ta juyo. Hamida tace shikenan mun gama yawo. Ko kadan ba haka suka so ba. Hajiya na
dakin Alhaji suka ki zuwa yi mata sallama. Ita kuma Mama daga bakin kofa suka yi
mata basu bari iyayen nasu sunga kayan jikinsu ba. Hajiya ta fito har wajen rai a
bace tace duk su shigo ciki.

Mama ta fito daga daki tace Hajiya lafiya? Kafin ta bata amsa yaran suka shigo. Ya
Salam...Hamida? Adabiyya? Meye hakan kuma? Hajiya tace kema basu ce miki zasu tafi
ba ko. Nima karar mota naji na fito da sauri ashe rabon idona ya gane min ne.

Hamida yar shekara ashirin da biyu jeans ne a jikinta da top wadda ko rabin cinya
bata rufe mata ba. Duk ta dameta sai tayi rolling da karamin mayafi. Adabiyya mai
shekaru shatara kuwa skirt ne a jikinta amma itama ya matse har shatin pant dinta
ake gani. Shima don tafi yayarta jiki ne ta saka. Sai riga matsatstsiya karama har
da wata belt a samanta an kara tamketa. Da dan karamin mayafinta. Hajiya ta kalli
yayansu Nura. Kai mahaukacin ina ne da kana ganin sun fito a haka kake shirin jan
mota. Ku fada min gaskiya ina kuke shirin zuwa. A tare suka ce gidan Yaya.
[9/25, 2:39 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU🗿6


Batul Mamman (Mrs)💖



Mama tace ni na rasa gane me ake yi a gidan Yayan naku ne? Jiya kunje kun ce aiki
zaku taya Izzatu yau ma kun ce aikin zaku kara yi. Ko packing suke yi ne zasu tashi
bamu sani ba, ta zauna akan kujera kusa da Hajiya tace ni a iya lissafi na ma ai
sai karshen August za'ayi birthday din Nana. Kuma ita ce ta rage anyi na yayyenta.
Hajiya ta tabe baki kina ma kokarin rikewa. Sun mayar da birthday tamkar wata
ibada. Duk shekara sai anyi sau uku a gidan. Allah Ya kyauta.

Mama ta ce Nura fada min gaskiya me ake yi. Indai birthday ne an saba yi mun kuma
hakura mun zuba ido. Tunda shima Hamzan bai ji maganar mu su dena ba ai matarsa
bazata ji ba. Shiru yayi har sai da Hajiya ta daka masa tsawa...baka ji ana
tambayarka ne? Adabiyya ta soma kuka dama ita akwai tsoro tace Hajiya party din
wedding anniversary zasu yi na shekara goma da aure. Innalillahi wa inna ilaihi
rajiun shine abinda su Mama ke fada. Hajiya ta mike tsaya tana magana a
hankali...lalacewar Yayanku har ta kai nan? Allah Ya shirya. Daga nan dakin Alhaji
ta koma ta cigaba da gyarawa.

Mama ta dubi yaran. Yanzu don Allah waye ya ce ku saka irin kayan nan? Yaushe ma
kuka siya? Adabiyya tace jiya da muka je ne Anti Izzatu tace kananan kaya zamu saka
yau. Shine muka ce bamu da masu kyau. Sai ta kaimu wani kanti ta siya mana. Mama
tace eh lallai yarinyar nan bata nemawa kanta zaman lafiya a gidan miji. Shirun da
taga munayi don bama son zama iyaye masu sa ido a lamarin gidan 'ya'yansu ne. Amma
wallahi idan na bullo mata ta bayan gida sai ta gane karyar rayuwar turai take yi.
An gayyaci su Mariya? Hamida tace eh duk su biyun. Har Yaya Ibrahim ma an gayyace
shi da Anti Umma. Mama tace suma duk kananan kayan aka ce su saka? Hamida tace bamu
sani ba. Mu da kannenta tace mu saka dai jiya.

Mama tace duk su je su canja kaya tana zuwa. Nura yace harda ni Mama? Ta harare shi
ban sani ba. Dakin Alhaji ta shiga ta tarar da Hajiya a zaune a kan gado tana kuka.
Mama tace haba Hajiya kukan iyaye ga 'ya'yansu bai taba zama alkhairi ba. Hajiya ta
share hawaye da gefen dankwali. To ya zanyi Kaltume? Yaron nan ko kadan ban goyi
bayan zuwansa Canada karatu ba amma Alhaji ya dage. Karshe yaje ya hadu da mata
itama tashin can. Mama tace shekara hudu fa kawai suka yi da babanta yaje aiki.
Hajiya tace to ai dai ta zauna ko. Gabadaya sun dauko wasu al'adu daban da namu.
Wadanda basu dace da addinmu ba. Kina kallo duk shekara sai sunyi party nasu da na
yaransu. Sati kusan uku da suka wuce ba ya kawo mana laces ba wai na Mother's day.
Na Alhaji kuwa na Father's day ai kinga bamu taba gaya masa dalilin bayarwa ba kila
da zaginsa zaiyi ma. Duk wata rana da turawa suke bawa mahimmanci Yaya da matarsa
suna yi. Ko da ba kowanne muke gani ba amma munsan anayi. Su a dole rayuwar turawa
sukeyi. Mama tace kiyi hakuri yanzu zan kira shi a waya yazo. Dole mu sake masa
magana ko mu hadashi da Alhaji. Wannan karon sun wuce gona da iri tunda suna son
batawa yaranmu tarbiya. Hajiya tace Allah Ya shirya mana. Amma don baki ji yadda
raina ke baci ba idan su Khalifa na kirana Granny dinnan. Mama ta kwashe da dariya.
Ai gara naki ma. Nida ake kira Grams fa. Yau da bamuyi boko ba ai da mun sha kunya
tunda sai kiyi musu magana ma amma su amsa da turanci. A dole sai an bambanta su da
'ya'yan yan uwansu.

Sani masinja ya dauki wayar landline din office dinsu da aka kira. Muryar mace yaji
tace matar Hamza ce. Ji yayi tana kuka tace ya fada masa Junior ya fado daga kan
kujera ya karye a hannu. Sani ya tashi da sauri sai ya tuna meeting din da suke yi
mai mahimmanci ne. Har ya koma ya zauna ta sake kira a fada masa yanzu ya taho
gida. Ta kira wayarsa a kashe. Dole Sani masinja ya shiga hall din da ake meeting
din.

Architect Hamza Nasir Hamza ya juyo a fusace yace meye haka Sani? Manyan baki
gareshi turawa masu son hadin gwiwa da kamfaninsa na zane da ginin gidaje da hotels
da sauran manyan gine gine. Sani masinja yace ranka ya dade uwargida ce ta bugo
tace Jiniya ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Hamza ya tashi da
sauri....what? Ya dubi bakinsa yace da turanci kuyi hakuri dana ne ya karye a
hannu. Sun tausaya masa suka ce zasu dawo a karasa meeting din. Amma ya daure yasa
hannu a takardar shaidar amincewarsa da sharudansu. A gaggauce ya karanta ba tare
da ya fahimci kalma ko daya ba yasa hannu a duka biyun. Daya tasu dayar ta
kamfaninsa. Sunji dadin amincewarsa sosai suka tashi. Yana ta sauri a hanya wayar
Mama ta shigo. Ya dauka a gigice a zatonsa Izzatu ce. tace Yaya kana ina ne? Mama
ke ce? ina hanyar zuwa gida. Tace to maza kazo ina son ganinka. Yace Mama Izzatu
bata kiraku bane? Junior ne ya karye a hannu. Yana hango wani dan sanda ya nufo
motarsa saboda yana amsa waya yana tuki da gudu yaja motar kafin a bada hannu har
ya kusa karawa wani. Mutane suka bishi da zagi da bakaken maganganu.

Mama ta dubi Hajiya tace bamu ga ta zama ba wai Junior ya karye a hannu. A tare
suka fito daga dakin suka kiran Nura yazo ya kaisu gidan Yaya. Hamida tace Mama me
ya faru? Junior ne ya karye a hannu. Yanzu yayanku yake fada min. Adabiyya tace ba
gaske bane. Jiya ne Anti Izzatu tace bata san da yadda zata sa Yaya ya baro office
da wuri ba. Partyn surprise take son yi masa. Bai san komai game dashi ba. Ana haka
wata makociyarsu da aka bawa aikin meatpie ta shigo take cewa danta ne ya karye
kuma ya kwana da zazzabi shiyasa bata aiko ta karbi kayan yin meatpie din ba. tana
fita ne shine Anti tace ta sami idea din abinda zata fada masa. Hajiya ranta ya
kara baci. Mama kuwa ashar ta dannawa Izzatu saboda yadda zuciyarta ke mata zafi.
Ta kalli su Hamida duk sun saka material ne da mayafansu manya tace Nura ya kaisu
amma ya fadawa Yaya tana son ganinsa komai dare.

Sai bayan fitar bakin sakataran Hamza yana hada takardu ya duba wadda ya saka hannu
a kai. Jikinsa ne ya fara rawa ya soma salati. Wani cikin yan office din yace
menene. Inuwa Sakatare yace ai bana jin oga ya karanta takardar nan da kyau. Ta
nuna ya amince ya karbi kudin da suka bashi saboda haka nan da wata shida duk ribar
da aka samu tasu ce. Daga wani wata shidan kuma sai su rinka raba ribar gida uku.
Su kaso biyu shi kuma daya.
[9/25, 2:41 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿7


Batul Mamman(Mrs)💖
Alhaji Nasiru Hamza dan kasuwa ne mazaunin Kano amma asalin iyayensa mutanen Kumo
ne na garin Gombe. Sana'ar siyar da shanu da tumaki ya fara wadda a hankali har ya
fara fitar da fatar dabbobin kasashen waje yana sayarwa. Shiyasa ma aka fi saninsa
da Nasiru maifata. Halima wadda suke kira Hajiya ya fara aure yar kanwar babansa.
Sun fara zama a Kumo kafin kasuwancinsa ya bunkasa ya dawo Kano. Lokacin ta haifi
danta na fari Hamza suke kiransa da Yaya. Suna zamansu lafiya da mijinta. Kuma suna
yawan zuwa gida ganin iyayensu. Hamza na da shekara biyu ta haifi Ibrahim sai
Mariya. Alh Nasiru ba karamin soyayya yake nunawa yaransa ba. Yana da amini kuma
abokin kasuwanci Alh Sabiu. Kowa ya sansu tare hatta iyalinsu suna mutunta juna.
Matan Alh Sabiu biyu. Kaltume ce uwargida sai Sahura. Kaltume bata taba haihuwa ba
a shekarun da sukayi da mijinta. Tana dai karatu a lokacin. Ita kuwa Sahura
'ya'yanta shida. Da kamar gaske suke zaman lafiya. Sai daga baya Sahura ta rinka
daukar zigar yan uwa da kawaye ta fara yiwa Kaltume habaici da gorin haihuwa. Tun
bata kulawa har dai ta fadawa mijinsu akan ya yiwa Sahura magana sai cewa yayi ai
ba matsayinsu daya ba. Idan taji haushi ta haihu mana. Da kadan kadan suka juya
mata baya. A lokacin tayi shawara ta sanar da Halima halin da take ciki lokacin
tana da ciki na hudu. Ita kuma sai ta fadawa mijinta. Ko kadan Alh Nasiru baiji
dadin faruwar hakan ba. Ya zaunar da abokinsa yayi masa nasiha. Sai dai duk a
banza. Wata rana Kaltume zata tafi makaranta ta shirya ta rufe dakinta sannan ta
leka dakin Sahura tace ta fita. Tana dawowa da yamma ta tarar da Alh Sabiu da
Sahura har da wasu makota a kofar dakinta. wasu samari ne suke kokarin balle
kofar. Kaltume duk ta rude ta tambayi abinda ke faruwa. A madadin amsa sai mari da
duka da Alh Sabiu ya rinka kai mata. Sahura na kuka tace muguwa saboda baki haihu
ba shine zaka kashe min nawa 'ya'yan. Tunda kika fita nake neman Ihsan banganta ba.
Sai dazu kawai naji kukanta a dakinki. Ba yadda banyi ba na kasa budewa, tun tana
kuka har muka ji shiru. Ta cigaba da kuka ina jin ma ta mutu Alhaji. Shi kuwa sai
dukan Kaltume yake har sai da aka bude dakin. A kwance suka tarar da Ihsan yar wata
takwas. Sahura tace ai kawai ta mutu ko ta suma. Alhaji Sabiu ya cire babbar
rigarsa yana ta dukan Kaltume. Babu mai hanashi har Allah Ya kawo Alh Nasiru. Yayi
ta rokon abokinsa amma sam yaki dena dukanta. Alh Nasiru ganin babu yadda zaiyi ya
ja hannunta. Sahura tace shikenan Alhaji dama tunda yake kare mata kwartonta ne. Ji
yadda yake rike mata hannu a gabanka. Alh Sabiu yace ko Sahura, to ke Kaltume na
sakeki saki uku in kin gama idda ki auri kwarton naki. Kai kuma Nasiru bani ba kai.
Da haka abokan suka rabo. Ashe mukulli Sahura ta sata na Kaltume ta durawa yarta
maganin bacci ta kaita dakin.

Halima taji tausayin Kaltume sosai barin ma da aka rinka yadawa a gari abokin
mijinta ne kwartonta. Gashi ya gujeta bayan aurenta ya mutu. shi kanshi sai da abin
ya shafi kasuwancinsa. Sai da ta kai ko makaranta ta dena zuwa. Har yan uwanta wasu
suna kyamarta. A wannan halin ne Halima ta bawa mijinta shawarar ya auri Kaltume
domin ta tsira da mutumcinta. Da kyar Kaltume da Alh Nasiru suka yarda. Bayan anyi
auren saboda Halima ta lura Kaltume na son 'ya'ya ta dauki Hamza da Mariya ta
kayansu ta mayar dakin Kaltume. Wannan abu ya kara musu zaman lafiya sosai. Kaltume
har kullum bata yiwa Halima kallon kishiya sai yar uwa. Haka suka zauna lafiya
Halima ta haifi Jidda. Daga nan Kaltume ita ta sami ciki ta haifi Nura da Adabiyya.
Sannan Halima ta haifi auta Hamida. Gidansu abin sha'awa saboda kan 'ya'yan a hade
yake. Daga baya asirin Sahura ya tuno Alh Sabiu yaji tana bawa yarta labari. Har
gida yazo bawa Kaltume hakuri domin ya gane bai kyauta ba. A yanzu ma dai komai ya
sukurkuce musu shi da Sahura don yaran babu wani mai abin kirki gasu har su
shadaya.

Tun daga farkon layin gidansa yake hango motoci. Hankalin Hamza ya sake tashi
sosai. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake fada. Shikenan Junior ya
rasu.........jikinsa duk a mace yayi parking din motarsa daga can baya ya fito. Sai
kawai ya kasa karasawa gidan. Kifa kansa yayi a saman motar. A wannan yanayin
Ibrahim ya iso. Yana neman gurin parking don layin ya cika ya hango yayansa a tsaye
ya kifa kai. Ibrahim ya fito da sauri da matarsa Ummahani da yaransu uku.

Hannu yasa ya taba Hamza a kafada. Hakan yasa ya juyo da sauri. Muryarsa a raunane
yace ashe kuma kunji. Ummahani tana gaishe shi yace mata shiga ciki Umma ai
dukkanmu mukayi rashin. Ibrahim yace rashi kuma Yaya? Nifa tun jiya Izzatu tace
muzo da yara yau. Nayi tunanin irin partyn da kuka saba ne

2 / 36