Advertisements
Chapter 35 Reading Al Adun Wasu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Al Adun Wasu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 36

102K to 105K   out of 106K words

kike yiwa Nana.

Izzatu tace bari ni na goyaka. Junior yace shi dai Zuhra yake so ta goya shi. Tuni
ta cire mayafinta tana kokarin daukarsa su Mama suna hanata saboda cikin jikinta.
Izzatu dai gefe ta matsa saboda duk abinda Junior yake so tana so ya samu.

Likita yace ya haka ina za ku kaishi?

Idanun Izzatu fal hawaye tace don Allah ku bari ta goya shi ko na minti daya ne.

Hamza yace a'a ba'a so ana motsa shi da yawa. Jin haka Izzatu, Zuhra da Junior suka
soma kuka. Likitan yace to ta goya shi amma yanzu zata sauke shi.

Junior har da murmushin karfin hali. Izzatu ta daga shi ta dora a bayan Zuhra dake
durkushe. Iyayensu na kallo amma ansan bazasu hanu ba ko ance su bari.

Zuhra tasa mayafi ta daure shi kadan yayi ajiyar zuciya. Hamza da kowa yana kallon
yadda ya lumshe ido a bayan Zuhra. Likita yace to ya isa haka zamu je wurin
scanning a sauko shi.

Zuhra suka ga tayi kasa gabadaya da durkusa kan gwiwoyinta. Jikinta yayi matukar
sanyi tace Innalillahi....ko karasawa bata iya yi ba ta saki wani irin kuka. Dogon
numfashin da Junior yaja taji bai sauke ba ne ya tsorata ta.

Hamza yayi hanzarin sauko da Junior likitan ya fara duba shi. A raunane ya dago
yace sai dai muyi hakuri....

Izzatu bata ji karshen maganar ba ta fadi kasa a sume. Lokaci guda dakin ya rude da
koke koke. Suka taimakawa Izzatu ta farfado. Suna nan tsaye aka cire masa allurar
hannunsa aka rufe shi da bedsheet. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.

Hamza ya dauko dansa a kafadarsa suka fito. Zuhra ke kuka sosai amma Izzatu
hawayenta ya kafe. Zuciyarta ke zafi kamar ta fashe. Sun zo wucewa idonta ya hango
mata a zazzaune a bakin kofar family planinning unit.

Kamar wadda aka aika ta tafi wurinsu harda yi musu sallama. Tace...kunzo a dakatar
muku da haihuwa ko? To wallahi kuyi a hankali dai. Ni da nafi kowa mahaifa na cire
daga haihuwa uku. Kunga ko shekara ba'ayi ba ga gawar dana can ana fita da ita daga
asibitin. Haihuwa ai kyautar Allah ce.

Kamar wata zautacciya haka take maganar Mama tazo taja hannunta. Matan wurin suka
yi musu gaisuwa. Suna tafiya uku a cikin na layin suka tashi suka ce sun fasa.
Wadda ta fito a lokacin ma ta fara kiran nurse azo a cire mata loop din da aka saka
mata yanzu danta daya kacal. Tuni wurin ya hargitse ranar dai babu wadda tayi
abinda ya kawota duk matan suka watse.

****
'Yan uwa da abokan arziki duk sun zo gidan lokacin su Hamza sun tafi kai Sunusi
Hamza Nasir gidansa na gaskiya.

Kuka kam Zuhra tayi sosai. Lokaci guda sai Allah Ya kawo wa bawa jarabawa domin
gwada imaninsa. Izzatu ce dai idonta har yanzu a soye. Suna zaune ta gama waya da
yayarta Zeenatu ta tashi tayi hanyar kitchen. Ana tambayarta ko akwai abinda take
so bata kula kowa ba taje ta fere dankali cikin dan lokaci tayi faten dankali ta
zuba a plate ta sako cokali ta dawo falon. Inda Zuhra ke kwance jingine da kujera
tana kuka taje ta zauna a gabanta.

Su Hajiya da Umma sai kallonsu suke yi. Izzatu tace Zuhra..

A hankali ta bude ido tace naam.

Ga abinci kici nasan kila rabonki da abinci tun jiya. Idan baki kula da kanki a
wannan lokacin ba matsala na iya tasowa nan gaba.

Sake fashewa da kuka Zuhra tayi.

Izzatu tace dazu kika gama cewa idan muka yi hakuri muna da lada. To kukan na meye.
Jarabawa ce Allah Yayi mana hakurinmu shine ladanmu. Kici abinci ko don abinda ke
cikinki. Idan bazaki ci ba kuma wallahi zan dura miki ta karfi. Bar ganina haka
nima karfi ne dani.

Dan murmushi Zuhra tayi mai ciwo sannan tasa cokalin a ciki ta debi kadan tasa a
bakinta.

Tana ajiye cokalin Izzatu ta dauka itama taci dashi ta sake mikawa Zuhra. Sunyi
haka wurin sau uku matan wurin na kallonsu da tausayawa sai kawai suka kankame juna
suka saka kuka wanda yasa duk wadda ke wurin zubar da hawaye.


*************
Sadaukarwa ga duk wadda ta taba rasa da ko 'ya Allah Ya jikansu Yasa masu ceto ne a
garemu Ya bamu hakurin jure rashin. Amin




Mai turo sakon gaisuwa sakonki ya iso gareni kuma nagode ina miki fatan alkhairi.
AL'ADUN WASU#80

Batul Mamman(Mrs)#




Yau kwanan Junior uku da rasuwa amma kullum jinta suke kamar lokacin aka yita
saboda yaro ne mai shiga rai. Zuhra bazata taba mantawa ba shi ya fara cewa zai
zama abokinta a gidan. Ga Nana idan tayi wasa ta gaji sai ta fara neman shi ko
Khalifa kamar yadda ta saba.

Idan kaga Izzatu dole ka tausaya mata a wannan lokacin. Ta rame sosai duk da cewar
da wuya ka ganta tana kuka. Mafiya yawan lokaci ita ke rarrashin Zuhra saboda ita
akwai raguwar zuciya. Abin kuka baya mata kankanta. Yadda ta koma ya bawa duk wanda
ya santa mamaki tare da zama abin burgewa saboda ta dauki qaddarar da tazo mata
hannu bibbiyu.

Suna zaune a falo Raliya tana kallon Zuhra da Izzatu suna karbar gaisuwa. Wata mata
cikin 'yan gaisuwar tace wace mahaifiyar yaron ne a cikinku? Izzatu ta nuna Zuhra.
Matar ta rinka bawa Zuhra hakuri akan ta rungumi qaddara ta sami lada. Batan san
kukan Zuhra a wannan lokacin ba na rasuwa bane. Tana jinjina yadda Izzatu ta nunata
a matsayin maman Junior ne. Wannan abu akan idon Hajiya akayi da Raliya. Sunji
tausayinsu sosai.

Raliya tace a ranta lallai kowane rashi daga Allah baya rasa alkhairi a tattare
dashi sai dai ba kowa yake ganin wannan alkhairin ba bare ya amfana dashi. Misali
mutane da yawa suna wa'azantuwa da mutuwar wani makusanci su daina akaita barna da
sukeyi a da. Wasu kuma imaninsu ne yake karuwa idan suka yi rashi. Wasu kuma abinda
idonsu ya rufe da basa gani sai su fara fuskantarshi a wannan lokacin. Ga mai
hankali mutuwa ayah ce mai ishara ga barin mummuna da komawa ga kyakkyawa. Rasuwar
Junior tayiwa kowa ciwo amma Raliya tasan shine ta zama sanadin shiriya ga 'yarta.
Saboda irin tarbiyar da suka bawa 'ya'yansu Izzatu ta tashi da irin halin nan na
bature daga ni sai iyalina makusanta wato miji da 'ya'ya. Duk wanda yazo a bayansu
ana iya rayuwa batare dashi ba. Hakan yasa ta kasa fahimtar mijinta a lokacin da
yaso ta gyara halayenta don su zauna lafiya da 'yan uwansa. Sannan kuma 'yan uwan
nasa suma suka ki ta saboda ta kasa barin al'adun da ba nata ba ta shigo musu da
bakin al'amura. Babbar matsalarta kuma shine bata daukar abubuwan da take da
mahimmanci shiyasa ko sun nuna fushinsu sai ta ga kamar hakan ba komai bane. Ajiyar
zuciya Raliya tayi tana addu'ar Allah Yasa ta dore a haka Ya yafe musu kuskurensu
wurin bawa 'ya'yansu tarbiya. Dama haka Allah Yake hukuncinSa. Abinda ka raina baka
dauke shi laifi ba sai yayi sanadiyar bata tsakaninka da mahaliccinka. Abinda kuma
ka raina a matsayin aikin lada sai ya kaika ga rahmar Allah. Allah Yasa mu dace.
Amin

****
Da yake Junior yaro ne gidan baya cika sosai. Hamza yana waje inda yake karbar
gaisuwa daga makota da abokan aikinsa. Cikin masu zuwan ne kawai yaga wani mutum ya
shigo rabin fuskarsa duk a rufe yasa bakar jacket da bakin wando gashi kansa da
hula. A gaban Hamza ya durkusa ya cire bakin glass din idonsa yace Sir I am very
sorry about your loss. May his soul rest in peace.

Ba Hamza ba sauran 'yan office dinsu da suke wurin tuni suka gano muryar Mr Oscar.
Wurin mutum biyar suka yi kansa harda masu zagi. Hamza ya tashi da sauri ya hanasu.

Inuwa sakatare ya harzuka yace haba yallabai Mr Oscar ne fa. Babu wanda zai ce ya
manta halin da ya jefa mu sanadiyar satar da yayi maka. Shine har zai shigo gidan
nan hankali kwance.

Hamza yayi dan murmushi yana rike da hannun Oscar....idan har rashin da mukayi zai
sa yazo gidan nan duk da cewa yasan nemansa nake yi to lallai dole ne nayi hakuri.
Har kun manta abinda ya tara mu a nan? Mutuwa ce fa mai daukar babba da yaro talaka
da mai kudi.... Ya mayar da dubansa ga Oscar....nagode sosai da nuna damuwarka
gareni a wannan lokacin.

Mr Oscar ya soma hawaye yace...Oga nasan nayi kuskure ina neman afuwarka. Ka yafe
min domin nayi nadama. Tsoron abinda zai faru yasa na kasa zuwa na sameka.

Inuwa yace abinda zai faru bai wuce na kira 'yan sanda suyi gaba da kai ba. Shege
arnen banza.

Bata rai Hamza yayi sosai yace haba Inuwa. Kada fushi yasa ka sakawa mai laifi da
tsiya. Ko baka san maganganunka zasuyi tasiri a zuciyarsa ba ya sake tsanar Hausawa
da musulmai....kaga Mr Oscar nasan naji ciwon abinda kayi min amma yau godiya nake
da kazo min taaziya saboda haka kaje kawai.

Cheque Mr Oscar ya dauko daga aljihunsa... Oga kayi hakuri nayi kokarin mayar da
kudin kamar yadda suke amma na kasa. Na yi amfani da miliyan daya da duba dari
takwas kuma bani da hanyar maido maka da kudin nan. Ka bani lokaci ko aiki idan na
samu zan rinka biyanka a hankali.

Godiya Hamza yayi ga Allah sannan yace babu komai kaje na yafe maka. Ba kowa bane
zai iya abinda kayi.

'Yan office dinsu basu ji dadin yafe masan da Hamza yayi ba sai dai kuma Mr Oscar
ya basu mamaki.

Shima mamakin yayi yadda Hamza yayi saurin yafe masa yace..Oga haka duk musulmi
suke da saurin yafe laifi?

Hamza yace a'a amma haka musulunci yace mu rinka yafiya ga wadanda suka cutar damu.

Mr Oscar yace indai kuwa haka ne to na yarda wannan addinin naku akwai adalci. Zan
iya zama musulmi dan uwanku yanzu?

Wani cikin mutanen wurin ya tuna lokacin da Umar Farouq Mukhtar ya musulunta a
masallacin unguwarsu. Yaji ance yaron har ya auri wata yarinya Ruqayya wadda tayi
sanadiyar musuluntarsa. Kabbara suka yi abin alkhairi ya samu aka musuluntar da Mr
Oscar.

****
Daga ranar aka gama zaman makokin duk 'yan uwa suka koma gidajensu. Wata Juma'ar na
zagayowa Hajiya ta dawo gidan. Ita da bata zuwa gidan 'ya'yanta sai da dalili mai
karfi shiyasa suka yi mamakin ganinta.

Ibrahim ne ya kawota ya zauna a falo saboda Hamza baya nan. Izzatu da Zuhra basa
kasa Tala tace mata suna sama Zuhra ce bata jindadi.

Waya Izzatu ta saka a speaker tana magana ga kofin tea a hannunta Zuhra ta kwabe
fuska kamar zatayi kuka. Izzatu tace...Baby har yanzu taki shan tea din fa. Ga
idonta ya cika da hawaye. Ni tsorona kada ta haifa min baby mai kuka.

Daga office dinsa Hamza yace kyaleta idan na dawo dura zamuyi mata irin na jiya.

Zuhra tace don Allah kuyi hakuri. Zan sha da kaina.

Hajiya tana tsaye a kofar dakin Zuhra tana jinsu. Zuciyarta cike take da farinciki
mara misaltuwa. Sallamarta ce tasa Izzatu tayi saurin kashe wayar duk suka gaisheta
suna yi mata sannu da zuwa. Hajiya da fara'arta ta amsa tace su zauna wurinsu tazo.

Izzatu tace bari na kawo miki abinci Hajiya.

A'a dawo ki zauna nagode.

Zuhra Hajiya ta kalla tace ki shanye tea din sannan muyi magana ko.

A yadda Hajiya ta tsareta da ido dole ta karbi kofin ta fara sha. Izzatu tayi
dariya bari na dauko miki bread kada ruwan tea ya kulle miki ciki.

Kamar tayi kuka haka ta rinka tura bread tana kurbar tea kamar magani. Sai da ta
shanye tea din sannan Hajiya ta bukaci su bata hankulansu tana son yi musu magana
ne. A nutse ta fara magana duk su biyun sun sunkuyar da kai kasa suna
sauraronta....

Nasan zakuyi mamakin zuwana gidan nan a wannan lokacin duba da cewa ba abu bane da
na saba yi. Yanzun ma dole ce tasa ni zuwa domin akwai shawara da nake son baku.

Tun kafin rasuwar Sunusi nake kula daku a asibiti har zuwa kwanaki ukun da mukayi
muna karbar ta'aziyya a gidannan. Tabbas canjin da nagani a wurinku ya sanyani
matukar farinciki. Nagode Allah Yayi muku albarka. Sai dai akwai kalubale a
gabanku. A lokacin da kishiyoyi basa zaman lafiya idanuwa basu fiye zama a kansu ba
dama shaidanun mutane burinsu su ga ana tashin hankali. Amma daga yanzu da mutane
suka kula yanayin zamanku ya canja to 'yan gulma da hada fada daga danginku ko na
mijinku zasu kawo muku farmaki. Da sunan soyayya wata zata wargaza muku farincikin
da kuke kokarin ginawa. Abubuwa da yawa sun faru a iya zamanku a gidan nan tun daga
lokacin aurenki Izzatu har zuwa yanzu da kuka zama ku biyu. A da can ki sani mu ba
kinki mukeyi ba sai dai halayen da kika zo dasu ne bama so. Munyi kokarin ganin kun
canja tun a baya sai ya zamana shima maigidan naku ya biyewa irin wadannan bakin
al'adun. To babbar matsalar da kika fuskanta shine duk inda ake aure to idanu sunfi
yawa akan mata. Komai munin halin miji indai matarsa tana da kyawun hali sai kiga
ba kasafai ake damuwa da halinsa saboda mace ita ce gida kuma da ita aka fi hulda.
Haka komai kirkin namiji idan matarsa bata kyan hali to nan ma gabadaya gidan
za'ace basu da hali saboda ita mace ita take nuna irin gidanta a waje.

Alhamdulillah tunda har Allah Yasa idanuna sun gane min irin zaman da kuke yi yanzu
ina so don Allah ku zauna lafiya. Ku yafewa juna abubuwan da suka gabata ku rike
juna da zuciya daya. Idan ance ki zauna da kishiya da zuciya daya wata zata ji
tsoron cutarwa daga kishiyar to ki sani duk abinda tayi miki na cuta kuma tayi
nasara dama Allah Ya kaddara hakan sai ya faru. Kada tsoron muguntar kishiya yasa
kema ki zama muguwa. Ni da Mama ba karamin toshe kunne da hakuri da juna yasa muke
irin wannan zaman da kuke gani yanzu ba. Dole sai anyi hakuri sosai.

Idan mace taki kwantar da hankalinta kina ji kina gani watarana miji zai sakeki
kuma ya barwa kishiya 'ya'yanki ko ta rike ko ta cutar dasu idan baki da karfi dole
kiyi hakuri daga inda kike kina jin labari mara dadi game da 'ya'yanki. Ko kuma rai
yayi halinsa kishiyar nan dai da bakya so ki bar mata 'ya'ya da mijin baki daya.
Kunga kenan har gara ki fahimceta ku zauna lafiya ko don gaba. Allah Ya kara rufa
mana asiri Ya baku zaman lafiya. Shima zanyi masa nasa fadan na yin adalci
tsakaninku.

Tunda Hajiya ta fara magana Izzatu da Zuhra ke kuka.

Izzatu tace Hajiya mungode kuma don Allah ku yafe min. Kema Zuhra ki yafe min duk
abinda nayi miki. Tun daga april fool har bayan auren.

Zuhra ta share hawaye na yafe miki nima ki yafe min. Banyi wani kokari na daidaita
ku ba saboda ina jin haushin abinda kika yi min.

Hajiya dai tana kallonsu tana jindadi. Addu'a ta sake yi musu sannan ta tafi duk
yadda suka so taci abinci ta ki.

*****
Hamza na tuki yana murmushi shi kadai. Yadda gidansa ya koma yasa shi jindadi. Tun
kafin rasuwar Junior dama babu wadda ke kwana a dakinsa. Yau zai bukaci su daidaita
yadda zasuyi. A son ransa dai Izzatu yake son ta fara karbar girki saboda wasu
dalilai nasa. Tun ana zaman makokin ya fada mata ya mayar da ita. Siyayya ya tsaya
yayi musu ta kayan kwadayi sannan ya wuce gida.

Da sallama ya shigo falon Nana da Khalifa suna masa sannu da zuwa. Zuciyarsa ce
tayi masa zafi da ya tuna da Junior. Allah sarki rayuwa.

Zuhra da Izzatu suna hira suma suka yi masa barka da zuwa. Bakinsa ya kasa rufuwa
don jindadi. Sai da yaci abinci ya basu tsarabar da ya kawo musu.

Wurin goma da rabi na dare ya bukaci ganinsu a dakinsa. Kowacce tayi wanka tayi fes
da ita. Kusan tare suka shigo yana zaune a tsakiyar doguwar kujera yayi murmushi to
sai ku sakani kawai a tsakiya irib yadda matan Alhaji suke yi masa.

Zuhra ta rike baki ...sai na fadawa su Hajiya.

Yace ke kuma daga magana sai ki fassara mutum. Izzy ai ba haka nake nufi ba ko? Ya
fada yana kallonta.

Dariya tayi sannan tace zaka ga fassara mutum idan kaji mun maimaita abinda ka
fada.

Zama suka yi suka saka shi a tsakiya yace mata kun iya sharri. Dama wani albishir
nazo muku dashi amma tunda abin naku yazo da haka na fasa.

Magiya suka shiga yi masa har ya fada musu cewa ya sami kwangilar zane daga
gwamnatin tarayya kuma an biya shi kudin aikinsu. Sannan Mr Oscar ma ya dawo masa
da wani bangare na kudinsa. Sunji dadi sosai suka yi masa addua. Daga nan suka dan
taba hira sannan Zuhra ta tashi ta tafi daki bayan sun amince Izzatu ce zata fara
karbar girki.

Tun daga wannan rana zaman lafiya ya kara samun wurin zama a gidan Hamza. Cikin
kudin da ya samu ya nemi shawararsu akan ya sayi mota daya ya daukar musu dreba ko
ya sayawa kowa daban tunda Izzatu ta amince ya sayar da tata. Guda daya suka nemi
ya saya musu nan gaba idan ya sami hali kowa sai ya saya mata.

****
Wata rana da daddare Zuhra na kwance Hamza na yi mata tausa saboda kafafunta duk
sun kumbura. Tun bayan rasuwar ta zama yau da lafiya gobe babu. Hamza yana kallonta
tana lumshe ido yace Cutie kin tuna sarkar da kika bani na sayar lokacin da Izzy
bata da lafiya?

A hankali ta gyada masa kai don har bacci ya fara daukarta.
Wata karamar leda ya ciro daga aljihunsa ya saka mata a tafin hannu. Sai a lokacin
ta bude ido tace menene wannan Ya Hamza?

Murmushi kawai yayi ta tashi zaune ta bude. Sarka ce da dankunne da zobe na gwal
mai matukar kyau. Dadi ya kamata ta rungume shi tana masa godiya. Wani kallo tayi
masa tace ina fata ba biyana kayi ba?

Ko kadan Cutie. Abinda kika yi min sakayyarki na ga Allah. Wannan kyauta ce kawai.
Na bawa 'yar uwarki ita ma.

Zuhra tace to Allah Ya saka da alkhairi Ya kara budi.

****
Yau ta kama asabar sun tashi da sanitation din gida. Izzatu da Tala ke aikin harda
Khalifa. Zuhra kuwa an hadata da zama da Nana, Izzatu tace kada ta tashi sun yafe
mata aikin.

Tana zaune taji mararta ta fara ciwo kadan kadan. Da yake tasan watan cikin bakwai
sai bata damu ba. Yinin ranar haka tayi ta fama da dan ciwo amma bata fada ba. Sai
dare har ta fara baccin ciwo ya tasheta. Tun tana daurewa har ta soma kuka. Da kyar
ta iya zuwa dakin Hamza ta kwankwasa kofa.

Cikin bacci Hamza yaji kamar ana kiransa. Juyawa yayi yaga Izzatu tana bacci. Sake
kiran akayi da karfi wannan karon ya tabbatar Zuhra ce. Shi da Izzatu suka taso
yana bude kofar ya sameta a tsaye ta kasa daga kafa.

Daga shi har Izzatun sun rude ya daga Zuhra ya sauka kasa da ita Izzatu na bin
bayansu. Koda suka isa asibitin likita ya tabbatar musu haihuwa ce Allah Yasa suna
da dakin da aka ajiye yara bakwaini da dole sai dai su tafi Aminu Kano ko asibitin
Murtala.

Ga fargaba ga ciwo Zuhra ta rinka kuka. Dama Hamza yana ta tsoron

35 / 36