Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
zunguri kofa
saboda yadda ta turo shi gaba. Yace yanzu don Allah idan ke namiji ce kika ga mace
irinki zaki so ta? Tace eh to ya danganta da namijin. Baba yace ni bance sai mai
kudi ba amma dai Zuhra a sami rufin asiri. Ke kadai fa Allah Ya bani dole na so ki
da alkhairi. Dazu kina cin abinci lomarki har tafi tawa. Itama dariya maganar ta
bata. Ta sunkuyar da kai. Baba yunwa naji sosai a lokacin. Yace to abinda zai faru
nayi miki alkawarin waya mai kyau harda kemara indai zaki rinka tsafa.
Alhamdulillah Zuhra tace da karfi tare da fadawa jikin Baba tana godiya. Yace
dagani duk gidannan kinfi kowa nauyi saboda cin ki. Ta mike tsaye tana tsalle daga
yau zaka ga canji Baba. A wurin ta cire hijab da dankwali ta kama zanin zata kwance
Baba yace shiga daga ciki dai yana kawar da kai. Ta wuce da tsallenta kamar karamar
yarinya. Baba yace da Umma kin kula da hannun rigar mamanta kuwa? Dandakuwa.....
Umma tace Baban Zuhra ka fiye gane gane kaima. Allah Yasa canjin ya dore dai. Kusan
minti goma sai gata ta fito da daurin kirji da gashinta buzu buzu. Ta dauko kwandon
wankanta da yar robar shampoo ta wuce bakin rijiya ta debi ruwa bokiti biyu. Suna
nan zaune ta fito bayan kusan rabin awa tayi wanka da wanke kai. Umma tace har kin
danyi haske kuwa. Bata ce komai ba ta shige daki.
Tasha wahalar taje kanta sosai saboda tsabar cikarsa. Ta shafa mai a ko ina ta raba
biyu tayi kitso manya. Ta shafa mai a jikinta da body spray din da Baba ya siyo
mata. Ba wani abu ke sawa bata amfani dasu ba, ita a tunaninta idan basu kare ba
Baba zai ajiye kudinsa yayi wani abin dashi. Tana matukar tausayinsa saboda lalurar
hannu da ta same shi.
Sai da akayi laasar ta fito fes da ita. fuska tasha hoda da janbaki orange, har
girarta ta gyara. Baba kuwa baki yaki rufuwa da ya ganta bayan ya dawo daga
masallaci yace ko ke fa. Allah Yasa ayi gamon alheri a hanya. Umma tace iyayen
zamani ba kunya. Dari biyu ya bata kudin mota tayi godiya ta fita. Tafiyar ma
kokarin daidaita kafarta ta rinka yi kada Baba yace tayi ta maza. Sai da ta fita
Umma tace ba naga ka siyo wayar ba. Yace eh kyaleta muga zuwa kwana biyu sai na
bata. Ki rinka sa ido tana gyara kanta. Ga iya zuwa islamiyya daukar karatu amma
bata damu da tsafta ba.
[9/25, 3:23 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿11
Batul Mamman(Mrs)💖
Su Anti Faiza sun sha dariya da Zuhra ta basu labarin dalilin shigowarta a guje.
Anti Faiza tace lamarinki sai addua Zuhra. Yanzu meye na rashin kunya bayan an baki
hakuri? Zuhra tace yana daga mota fa yake bani hakurin. Ni dariyar da suka yi min
ita yafi bani haushi. Hajara tace to ba dole suyi ba kin kama fuska kinyi mata
zane. Ji girarki kamar an miki fenti. Zuhra tace wai haka Anti? Yau baki ga yadda
Baba yayi murna ba har alkawarin waya yayi min. Daga nan suka cigaba da hira. Anti
Faiza ta sako zancen bleaching tana musu fada. Zuhra tace nima hanata nayi har
malama Rabia na tambaya hukuncin mai yi. Ta zauna tayi musu bayanin yadda suka yi
da malama. Anti Faiza tace ato ni dai nasan kuna tare naji tsoro kada ta koya miki
hali kinsan ance zama da madaukin kanwa.....
Bayan kwana biyu suna cin danmalele a falon Anti Faiza suka ji sallama. Zuhra ta
kwaye zaninta har ana ganin cinyoyinta. Anti Faiza sai fada take mata basu ji
sallamar ba. Abba ne ya amsa sai ga Izzatu ta shigo. Da yake Zuhra na fuskantar
kofa tana shigowa suka hada ido. Sai da ta kware don tsoro sannan ta tashi da gudu
ta shige daki. Anti Faiza cikin mamaki tace sannu da zuwa Maman Khalifa. Ganin
Izzatu na kallon kofar dakin tana dariya tace wata kanwata ce mai shirmen tsiya.
Izzatu tace ai mun taba haduwa. Ta baki labarin an kusa kadeta da mota shekaranjiya
ko? Zuhra daga daki tana lasar hannunta da ya sha manja tace na gama yawo yau.
A falo Anti Faiza tace ba dai Alh Hamza ta yiwa rashin kunya ba? Ke Zuhra fito.
Izzatu tace ba kararta na kawo ba. Ni ta burgeni ne ma. Don baki ga idanunta ba da
ya fito daga mota. Yadda kika san ta saki fitsari a wajen amma duk da haka bata
dena magana ba. Anti Faiza tace ai indai Zuhra ce ta wuce nan. Sai ki fito ki bata
hakuri ta kira Zuhra daga daki.
A sanyaye ta fito ta gaishe da Izzatu sannan tace ku yi hakuri. Hajara tana gefe
tana musu dariya. Izzatu tace ba damuwa. Ai ranar baki ga yadda yaji haushi ba. Har
muka je muka dawo yana mita. Ni da zaki bini gidana ma ai da saka ku zanyi a gaba
ina samun abin nishadi. Zuhra ta kalleta da mamaki. Yanzu nufinki baki ji haushin
duk abinda na fada masa ba? Izzatu tace not at all. Zuhra dai bata gane dangantakar
turancin da tambayarta ba, sai tace da nice wallahi fitowa zanyi daga motar in
saita bakin mara kunya. Hajara ta dan taba Anti Faiza sannan ta kallo Zuhra alamun
ayi mata magana. Izzatu ta ce ni bana son hayaniya nasan he will handle everything
shiyasa na kyale ku.
Maganar ta bawa Zuhra mamaki sosai. Ace wata tayiwa mijinki rashin kunya kice baki
damu ba. Gaskiya ke a mata daban ce....anti Faiza tayi saurin toshe mata baki. To
sarkin shirme ance abinda kika yi babu komai kin dage sai neman jawo magana kike.
Maman Khalifa don Allah kiyi hakuri. Izzatu tayi dariya ke babu komai fa.
Haka suka cigaba da hira Zuhra tana basu labarin Baba na son yi mata aure amma yace
yafi son miji mai ilimi. Ni kuwa indai gida da abinci bani da damuwa. Hajara tace
amma kika ki maikifi? Baki taba tsayawa gabansa bane shiyasa kike magana. Banda
karni babu abinda yake. Anti Faiza tace wai kura ce zata ce da kare maye. Ke da ba
kya minti uku kin gama wanka ai bai kamata ki guji dan uwanki kazami ba. Zuhra tace
baki ji na fada miki Baba zai bani waya bane..ai daga yanzu zan rinka wanka sosai.
Ita dai Izzatu har ranta shirmen Zuhra yana bata shaawa. Dalilinta kenan na zuwa
gidan ranar don idan tana neman Faiza waya take yi mata.
Kwana hudu Zuhra ta yi a gidan suka koma tare da Hajara. Baba ya bata dubu shida
yace ta kaiwa mai koya mata sakar. Cikin dan kankanin lokaci ta fara kwarewa saboda
abu ne da take so. Ga tsafta an dore da wanka. Kwalliyar ce dai har yanzu da sauki.
Baba ya cika alkawari ya bata wayar. Ranar murna ba'a magana. Haka ta rinka shiga
makota tana nuna musu. Mamansu Hajara ma tayi murna. Don duk makotansu sunfi
shakuwa sosai tamkar yan uwa. Tecno ce second hand ya siya a wurin wani dan
layinsu. Da yake suna ganin girman Baban Yara kamar yadda suke kiransa ba karamin
sauki mai wayar yayi masa ba.
Arch Hamza na zaune yana duba wasu takardu a office dinsa Inuwa sakatarensa yayi
sallama ya shigo. Bayan sun gaisa yace ranka ya dade naji baka ce komai ba game da
text da wayar da nayi maka. Hamza yace yi hakuri wasu abubuwan ne suka dauke min
hankali. Izzatu ta fada min komai. Babu matsala nagode. Har kunya yake ji ace
matarsa karya tayi. Inuwa yace ranka ya dade babu matsala? Hamza ya ajiye takardun
ko dai akwai wani abu ne Inuwa? Shi a tunaninsa Inuwa ya gano Junior lafiya yake.
A'a babu komai, dama wannan maganar ce kawai. Daga nan ya fita. Tunda Oga bai damu
da yanayin contract din ba gara ya dena damun kansa kawai. [9/25, 3:29 PM] +234 803
040 6305: AL'ADUN WASU 🗿12
Batul Mamman(Mrs)💖
Da daddare yana bacci yaji kamar ana taba shi. A tsorace ya tashi ya lalubi fitilar
gefen gado. Zaune ya ganta ta dora pillow a cinyarta. Sweetheart ka tashi muyi
magana game da birhtday din Nana. WHAT??? Shine abinda ya iya fada a hasale. Izzatu
tace maganar birthday din Nana nace. Ya nuna mata agogo Izzy kinga time fa, uku
saura na dare. Ta dan kwanta a jikinsa kullum ina son mu tsara komai baka dawowa
gida da wuri. Jikinsa ya janye sannan yace saboda haka sai ki tasheni da tsakar
dare? Haba Izzy! Tashin miji ayi magana a irin wannan lokacin ai sai a film. Indai
maganar kirki ce ai ido biyu ake yinta. Ni naga irin haka is normal tsakanin
couples. Idan abu na damun daya sai suyi discussing at night. Kasan kuwa na sake
ganin yarinyar da kuka yi fada saboda ka watsa mata ruwa. Ashe kanwar Faiza ce. A
wannan lokacin Hamza ji yayi tamkar ya saka ihu. Fuskarsa ko kadan babu annuri yace
yanzu Izzy ki tasheni a tsohon daren nan saboda zancen birthday sannan ki ce kinga
yarinyar nan? Did I ask you? Gobe meeting gareni da sassafe kuma na fada miki. amma
sai kika zabi yanzu ki hanani bacci kuma ki bata min rai. Kallonsa kawai take
yi....yau me ya sami baby dinta yake irin wannan fadan. Shi kuwa Hamza banda bacin
ran gani yayi dama ta samu na bin umarnin Mama a soke maganar party. Yace ki manta
da maganar wani party don an dena. Kina iya dafa abinci ki kawo a kai asibiti ko
makarantar allo sadaka. Wannan karon ita ce nata ran ya baci. Wace irin magana kake
yi ne? Yarinya duk na gama sa mata rai. Har kayan da zata saka ranar duk na gama
siya. Hamza yace indai kaya ne ko gobe ma ki saka mata. Izzatu ta soma hawaye kada
kayi min haka Hamza please. Yace meye na daga hankali, shekara biyu zata yi ai ba
wayo gareta ba. Hawaye take sosai ya rungumeta yana rarrashi. Tace indai don na
tasheka ne kayi hakuri amma kada kasa yan gidanmu suyi min dariya ko aga kamar baka
da kudin ne. Bai san haka suka daukaki abin ba sai yanzu. Yace na gama magana Izzy
no more parties. Ki duba a family dinku mai bukatar taimako sai mu bashi jari. Su
Mama basa son abinda muke yi kuma nima na fahimci kuskurenmu. Ai ture shi tayi ta
tashi tsaye. Dama nasan zugoka aka yi tunda ka fara magana. Na rasa meyasa 'yan
gidanku basa sona. To wallahi sai anyi ko kana so ko baka so. Hamza yace ni kike
fadawa haka Izzy? Yau daya don na hanaki abu shine zaki nuna min ban isa ba. Ba
tare da ta bashi amsa ba ta fice daga dakin harda buga kofa.
Kansa ya rike ya zauna a bakin gado. Lallai yayi sakaci da har abin ya kai haka.
Dole ya nemi yadda zai gyara gidansa don a zauna lafiya. Cikinsa ne ya murda alamun
yunwa. Yau kamar sauran alhamis Izzatu batayi girkin dare ba. McDonald's tayi musu
order. Soyayyan dankali aka kawo musu da kaza harda Tala da maigadi. Ko kadan Hamza
bai koshi ba sai dai an saba irin haka wanda tun kafin suyi aure yayi mata
alkawarin ware rana daya a sati kada tayi girkin dare zasu rinka ci a waje ko ayi
order a kawo musu gida. Tashi yayi ya bita dakinta sai dai a rufe yaji dole ya koma
ya kwanta. Da kyar ya iya bacci saboda yunwa.
Washegari saboda tana fushi bai sami breakfast ba. Da yayi magana tace ta dena
girki sai ya janye maganar party. Shi kuma yace ta bashi atm card dinsa na wurinta
maganar soke party babu fashi. Baram baram suka rabu. Har mamanta ta kira a waya
ta fadawa tace kada ta damu idan bata da kudi ne zata turo kaninta ya kawo mata.
Hamza gani yayi an cigaba da shirye shirye. An siyo katons din lemo da ruwa. Ga
gifts duk an gama hadawa a wata jaka mai hoton Nana duk an ajiye a store. Ya sake
wa Izzatu magana tace ai ba kudinsa bane. Maganar Mama ya sake bi ya kwashe yaran
ya kaisu gidansu.
Su Hajiya sunyi mamaki da farinciki ganin Hamza yaji maganarsu. Aka sa Ibrahim dasu
Mariya suka kawo nasu yaran. Tuni su Khalifa suka saki jiki cikin yan uwansu. Idan
suna Hausa sai ka rantse daga turai suka dawo. Kwatakwata basu iya sosai ba ,sai
turanci. Nana kuwa dama bata iya magana sosai ba. Tunda suka zo ta likewa Adabiyya
take kiranta Anti Adab.
Izzatu tayi mamaki da ta dawo daga supermarket ta tarar yaran basa nan. Tala ce ta
sanar da ita sun fita da daddynsu. Sai dai tasha takaici da ya dawo shi kadai yace
a can zasu kwana. Tasan saboda maganar party ne. Tayi ta rokonsa da koke koke duk
a banza. Har zaunar da ita yayi yana mata nasiha amma ta kafe. Shi kuwa yace indai
zata iya zuwa gidansu ta dauko yaran shikenan. Bata san gatse ba ta tafi ana sauran
kwana biyu sai dai ta tarar duk sun tafi Kumo. Babu kowa a gidan sai maigadi. Kuka
kam ranar ba'a magana. Izzatu tayi fushi sosai da Hamza tare da alkawarin sai ta
rama duk ranar da dama ta samu.
[9/25, 3:31 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿13
Batul Mamman(Mrs)💖
Fada sosai Hamza da Izzatu suka yi sai da kyar ya samu ya rarrasheta suka daidaita.
Amma kudirin ramuwa yana nan a ranta, dama kawai take jira.
Kusan wata biyu suna zamansu lafiya. Architect Hamza na kokari wurin cigaba da
kulawa da iyalinsa. Su Hajiya ma yana wadata su da abubuwan bukata. Hatta kawunsa
da aka kora aiki sai da ya aika masa da dubu dari. Hajiya taji dadi sosai har waya
tayi masa abinda bata yi sai da dalili saboda dan fari ne tayi masa godiya. Wannan
wayar tasa shi jindadi mara misaltuwa. Shiyasa ya cigaba da yin abinda zai
kyautatawa iyayensa. Itama Mama taji dadi ya dauki shawararta don Izzatu bata nuna
musu bacin ranta game da tafiyarsu Kumo da 'ya'yanta ba.
Zuhra an gama koyon saka Baba ya kukuta ya siyo mata injin saka tsoho ne ma amma
bai lalace ba. Tayi murna sosai shiyasa sakarta ta farko shi da ummanta ta fara
sakawa rigunan sanyi masu kyau da kauri har uku uku. Duk da suna tsokanarta taki
karatu amma sakar tayi kyau sosai. Umma ta bata shawarar duk lokacin da aka bata
kudi ta sayi kulu tayi sakar ta ajiye kafin lokacin sanyi tunda ya kusa sai tq
sayar.
Wata rana Hamza ya fita zuwa gidansa da suke shirin komawa tun safe saboda aikin
yazo karshe. Gida ne da ya tsara komai na ginin da kansa sannan kamfaninsa ke
ginin. Izzatu tana kitchen yayarta dake aure a Alaska ta kirata a waya. Suna hira
ne Izzatu ke tambayarta ina yaranta. Zeenatu tace sun fita da babansu siyan kayan
da zasuyi amfani dasu na HALLOWEEN. Izzatu tace kai sis har kin tuna min lokacin da
muke siyan namu da Daddy. Gaskiya ba karamin missing America nake yi ba. Zeenatu
tace ba kinga dan fillo duk kin rude ba. To amma meyasa bakiyi a nan? Hmmm kinsan
yan Nigeria da kauyanci kada ma yan kauye suji labari. Gidadancinsu yayi yawa...ko
kin manta yadda muka yi da inlaws dina game da birthday din Nana? Zeenatu tayi
dariya haba Juliet din Romeo duk soyayyar taku har zakiyi korafi. Ba haka bane sis,
abin ya bani haushi sosai. Amma gaskiya zamuyi halloween this year. Ba don yana
wani aiki ba ai da dole mu taho sai muyi celebrating tare. Zeenatu tace muma zamu
taho nan da December a gida zamuyi new year.
Bayan kwana biyu da wayarsu zancen halloween ya tsayawa Izzatu a rai. Lokacin da
suna Canada da iyayenta suna celebrating tare sa sauran turawa. Nan da nan ta fara
shirye shiryen yadda zasuyi nasu a gida. Hamza ta tambaya kudi don ya dena bata atm
card dinsa. Tunda tace kaya zata siya bai hanata ba saboda rigimarsu ta party ta
wuce. Washegari ta debi yara suka je manyan shopping malls din Kano da kyar ta
sami abinda take so ta dawo rai a bace. Me zaayi da Nigeria abinda bai taka kara ya
karya ba sai ka nema ka rasa. Washegari Khalifa ya tashi da zazzabi dama mura yake
suka fita wannan siyayyar. Abu kamar wasa sai da suka kaishi asibiti da daddare,
sai da safe aka sallamesu bayan an gama kara masa ruwa. Da suka dawo ne wurin karfe
takwas ya kira Mama ya sanar da ita.
Ranar ta dace da talatin da daya ga watan october wadda a irin wannan ranar ne
turawa suke yin halloween. Izzatu bata fadawa Hamza ba domin bata dauki abin a
cikin irin wadanda ya hana ba tunda ba gayyato mutane zata yi ba. Ita da 'ya'yanta
zasuyi abinsu a gida. Bayan Hamza ya fita tasa Tala tayi musu wanka ta koma
kitchen. Ita kuma ta dauko musu kayansu da ta siyo ta saka musu. Harda Khalifa mara
lafiya. A ka'idar wannan rana ta halloween wadda take da sunaye da yawa harda Day
of the Dead ana yin abubuwa masu yawa. Nasara mabiya addinin kirista suna
celebrating wannan rana ne domin tunawa da matattunsu. Kamar waliyai, manyan masu
bauta da shahidansu. Ana saka kaya na ban tsoro a ranar kamar riga mai alamun jini,
fuskar shaidanu, yin shigar da baza'a gane mutum ba, tsorata mutane a gidajensu ko
waje, zuwa wuraren ban tsoro kamar makabarta, tsohon kango ko gidan da babu mutane.
Kai hatta horror films(fim na ban tsoro) ana gani a wannan ranar ko ka ziyarci
malamin duba da sauran abubuwan firgici dai. Haka halloween yake ko kadan bashi da
alaka da musulunci. Amma wani lokacin musulmai yan uwammu idan suka sami kansu
cikin yahudu da nasara sai kawai su dauki al'adunsu suna ado dasu ba tare da sunsan
ainihin dalilinsu na girmama ranar ba. Zama a kasar waje ba shine dalilin da zaisa
mu dauki dabiar nasara wadanda suka bata da yahudu wadanda Allah ke fushi dasu ba.
Allah Ya tsare mana imanimmu. Amin
Izzatu ta sakawa Khalifa da Junior kayansu. Rigace mai dogon hannu da dogon wando
duk sun dame musu jiki ga kuma fuska wadda aka fitarwa hudar idanu da wurin
numfashi. Kayan bakake ne. Idan daga nesa ka hangosu zaka rantse kwarangwal ne
saboda zanen kayan da yanayinsu. Bayan ta shiryasu ta daukesu hoto ta turawa Hamza
a waya. Daga nan taje ta dauko na Nana. Su kuma jajaye ne harda safar hannu mai
alamar farata zako zako. Fuskar(mask) kuwa kamar ta aljanu harda kaho biyu a sama.
Nana tana ta dariya Izzatu ta gama shiryata ta daukota zasu fito falo sai Nana tace
Mummy poo. Izzatu ta san halin Nana bata kashi a pampers duk yadda za'ayi da ita.
Dole ta cire mata ta zame mata wandon ta dorata a po ta tafi kitchen duba girki don
shabiyun rana ta wuce. Junior da Khalifa suna falonsu suna kallon cartoon.
Tana kitchen taji sallamar su Mama. Da sauri ta fito tana musu sannu da zuwa. Duk
su biyun rungume su tayi yadda ta saba. Hajiya sai dan yake take don wannan halin
na Izzatu na bata