Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
bazata yanka da wuri ba kada yayi tsami. Man da ta
soya yasha albasa sannan ta duba bata da juice da yawa. Zobo tayi wanda ta dafa da
citta da kaninfari. Ta tace ta saka sugar da lemon tsami sai ruwan cucumber da ta
gurza ta tace. A leda ta kulla ta zuba a fridge saboda jug bazai shiga ba. Tana
sauke mai ne ya tsallo mata a wuya har wuri biyu. Wani uban tsalle ta doka saboda
zafin da taji ta soma karanta ALLAHUMMA AJIRNI MINANNAR saboda neman tsari daga
azabar Allah. Allah Ya kiyayemu, amin. Sanda ta gama komai shadaya da rabi ta gyara
kitchen sannan taje tayi wanka. Riga da zani ta saka tayi irin kwalliyar dazu mara
yawa ta sauko kasa.
Sabuwar wayarta ta dauko sai dai ta kasa gane kan wayar. Tana ta tabe-tabenta taji
sallamar Hajara. Kamar kananan yara haka suka rungume juna suna tsalle. Can Hajara
tace ke dena jijjiga ni kada ki barar da danki ko 'ya. Zuhra ta zaro ido tana shafa
cikin Hajara. Doke hannun tayi to yar duniya meye na shafa min ciki. Kema ina
tunanin akwai fa, ji yadda kika yi haske kika kara cikowa. Zuhra ta kama hannunta
zo ki zauna yau tattalinki zan taya Yaya Sahabi. Ah su Hajara daga aure sai ciki.
Hajara tace ke bana son iskancinki fa. Kema naki yana hanya idan babu in sha Allah.
Ai burina mu shiga labour room tare. Shakiyanci suka yi ta yiwa juna. Daga baya
suka shiga kitchen da Zuhra tace kannen Hamza zasu zo. Hajara ta bude taga
danwake...anya Zuhra kina da kai kuwa? Yan uwan miji zasu zo ki rasa abinda zaki
basu sai danwake? Zuhra tace yayansu ne yace shi suka fi so. Plates suke hadawa da
cups suka ji sallama a falo. Dama Zuhra da hijab dinta a hannu saboda kada suzo da
maza. Kuskuren da mata da yawa keyi kenan. Yan uwan miji maza ko abokansa su zo sai
mu fito babu lullubi ko hijab. Muji tsoron Allah mu kare mutumcinmu. Mota biyu suka
yo duk a gidan nasu suka hadu suka taho tare. Zuhra fuskar nan dauke da fara'a sai
kunyar su Mariya take yi. Suka gaisa da Nura yace zai tafi sai bayan sallar Juma'a
zai dawo. Bajewa suka yi da 'ya'yansu ana ta hira da Zuhra. Ta sake musu sosai kada
ma Adabiyya da Hamida suji labari. Ta tambayi yaran sunayensu suka fada mata.
Karamin dan da Ummahani ke goyo kuwa Zuhra ta goya shi saboda ya hana mamansa
sakewa. Tun yana kuka har yayi bacci. Da taimakon Hajara dasu Adabiyya ta hado musu
abinci. Cikin tabarminta ta shimfida manya biyu. Jidda tace ai ki hada mana a
tray kawai muci tare yafi kara zumunci. Zuhra na murmushi tace haka Ya Hamza ma
yace. Su Ummahani suka hada ido suna dariya. Yaya yaji dadin aure....
Sakewa da jindadin da basu taba yi ba a gidan dan uwansu yau sunyi. Yabo da addua
kam Zuhra tasha a wurinsu. Nura yafi kowa santi da ya dawo aka hada masa nasa
abincin. Bayan sun gama kuma dukkansu sunsa hannu wurin gyara falon da wanke wanke.
Tamkar 'yan uwana jini haka suke jin Zuhra. Sai da sukayi sallar la'asar suka fara
haramar tafiya. Ana haka sai ga Hamza ya dawo daga wurin aiki. Shima yau ya gaji
sosai. Kudi ya kusa kammaluwa zai sallami su Mr Peter ya rabo da kaya. Dadi yaji
yadda ya tarar da kannensa sun cika gidan ana ta hira. Zuhra na tsakiyarsu da goyo
kamar sun shekara tare. Suna ta gaishe shi da yi masa sannu da zuwa ita kuwa kanta
na kasa. Duk kunyarsu take ji, tana kallo yace bari nayi wanka na sauko kafin ku
tafi. Ummahani ce ta dan zungureta Anti Zuhra tashi mana Yaya ya dawo. Indai don
wadannan ne, ta nuna Jidda da Mariya suna dariya...duk ki manta dasu kowacce ta
iya rike miji in fada miki. Zuhra harda rufe fuskarta da hannuwanta. Hajara ce ta
tasheta ta karfi. Zata hau saman Ummahani tace kawo dan nan kada yace zamu bankare
masa kirjin amarya.
Ita fa ba saba binsa daki sannu da zuwa tayi ba. A falon ta dan tsaya sannan tayi
sallama tare da cewa in shigo. Daga ciki Hamza yace yes come in. Kwance yake akan
gado amma kafafun na kasa ko takalmi bai cire ba. A tsorace tayi saurin zuwa gaban
gadon, cikin sanyin murya tace...Ya Hamza jikin ne? Harararta yayi sai yanzu kika
ga damar zuwa. Zuhra tace ina? Zama yayi suna fuskantar juna tana durkushe a gefen
gadon. Yanzu mijinki ya dawo ba sannu da zuwa bare ki karbi jakata. Tace yi hakuri,
bai kula ba ya cigaba da cewa kuma na taho daki baki biyoni kin cire min kaya
kinyi min wanka ba. Zuhra ta mike da sauri....eyyeeee Ya Hamza wanka? Ya kashe mata
ido wanka fa. Don Allah kayi hakuri....sai kawai ta soma hawaye. Saurin tashi yayi
ya janyota jikinsa. A cinyarsa ya zaunar da ita tayi saurin rufe ido. Wai meyesa Ya
Hamza ke yi mata hakane yanzu. A hankali yake magana Cutie you scared me. Na kiraki
yafi sau goma baki dauki wayar ba. Dafe kai tayi... ina jin hayaniya ce tasa banji
ba amma kayi hakuri. Kokarin tashi take yi ya sake riketa sosai yana kallon
wuyanta. Cutie me ya sameki a nan ya fada yana dan taba wurin...auchh Ya Hamza da
zafi fa. Cikin shagwaba take magana tana kara narkewa jikinsa ba tare da ta sani
ba. Sorry meye ya sameki? Murmushi tayi masa mai ne ya kona ni da har zanyi kuka
saboda zafi sai na tuna ba karamin lada aka rubuta min ba. Na kone a kokarin
karrama baki... ta washe baki tana murmushi. Hura wurin ya rinka yi yana mata
sannu. Zuhra dai duk tsigar jikinta ke tashi ta dan wayance, 'yan gidanku suna da
kirki duk ina sonsu. Zanyi kewarsu idan na tafi. Tashinta yayi shima ya mike...tam,
zaki fara ko? Ni tashi muje na sallamesu sai na dawo nayi wankan.
Suna saukowa su Mariya suna ta dariya. Hamza yace zan hanaku zuwa gidan nan tunda
gulma kuka zo yi. Cikin raha suka yi sallama duk suka tafi. Dubu biyu ya bawa
Hajara ta shiga mota. Tayi masa godiya sosai. Suna shiga mota mai gyaran inji yazo
ya fara aiki.
Zama Zuhra ta sake yi suka kafa sabuwar hira dasu Hamida sai ga Hamza ya leko yana
kiranta. Tace bari ta sauko sai suyi shawarar abincin dare. A kofar dakinta ta
ganshi ya bude tabi bayansa. A ina su Hamida zasu kwana? Zuhra tace ai tare zamu
kwana a nan dakin kayansu na cikin kwaba. Sai da ya gama dariya sannan yace don
Allah ki dena cewa kwaba sai a zata baki waye ba, wardrobe sunanta. Ta sha kunu sai
kayi ta tsokanata ko? To Cutie kauyancinki ne yayi yawa. Yanzu dai har su Adabiyya
su tafi a dakina zamu rinka kwana tare. Kinga kada suyi tunanin akwai matsala a
tsakaninmu sannan zamu cigaba da lessons dinmu ko. Yana kare magana ya bude wata
drawer inda yaga ta ajiye kayan bacci ya dauko mata wasu riga da wando. Rigar dai
kamar bra ta sama sai ta bude kadan taga kasa. Wandon kuwa ko cinya bai gama rufewa
ba. Zuhra na gani ta kwace kayan daga hannunsa a kunyace, ni gaskiya bazan saka
wannan a gabanka ba. Yace to dauko wadda kike so....ta fara neman wata kenan yace
amma ki kwana da shiri duk wadda kika saka ko kinyi bacci sai na cireta. Baki bude
ya barta ya shiga toilet ya dauko brush dinta. Sannan ya dibi turaruka da body
spray harda man shafawa. Ki karo wasu abubuwan idan kina bukata harda kayan da zaki
saka da safe. Fita yayi ya barta a tsaye ta ma rasa abinda zata yi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #53
Batul Mamman(Mrs)#
Tunda suka yi maganar nan Zuhra take bata rai ko dakin nasa bata je ba . Ya ma
za'ayi yace tasa wannan kayan duk ya gane mata jiki. Ta fasa kwana a dakin nasa ma
a falon zata kwana a kan kujera. Sun gama girki sannan suka yi sallar Isha. Bayan
sun idar tana daura dankwali Hamida tace Anti Zuhra meyasa bakya saka relaxer a
kanki gashi kanki yana da yawa, irinsa yafi kyau. Adabiyya ta taba gashin don Allah
ki fadawa Yaya gobe ya barmu muje salon din bayan layin nan. Baki ga yadda suka yi
suna ba kuma duk musulmai ne matan wurin. Hamida tace ni da bikin Zayya munje har
lalle suke yi mai kyau. Don Allah Anti Zuhranmu ki tambayar mana. Zuhra tayi
murmushi nifa bana son Antin nan haka kawai bayan inajin duk kun girmeni. Nan aka
fara fadar shekaru Adabiyya ta girmeta ita kuma ta girmi Hamida. Duk hirarsu Hamza
yana tsaye a bakin kofa yana ji ya dawo daga masallaci. Zuhra ta sake tana ta hira
amma tun bayan dawowarsa bai sami damar kebewa da ita ba. Abincinsa ma a falonsa na
kasa ya gani. Gyaran murya yayi sannan ya shigo...kun hadu kun cika gida da hira ko
sallama bakwa ji. Hakuri suka soma bashi Zuhra ta kawar da kai. Hakan baiyi masa
dadi ba don ba na kunya bane, da gani fushi take yi. Tunanin dalilin fushin yake yi
amma ya kasa ganewa. Kiranta yayi sannan ya shige falonsa. Kanensa na zaune bare ya
tambayeta a nan.
Da ta shiga falon gani kawai tace ta dan durkusa a gefen kujera. Lallai ya tabo
Cutie dole ya bata hakuri. Yi yayi kamar bai gane tana fushi ba yace tashi ki zubo
mana abinci yunwa nake ji. Ni naci da su Hamida ta bashi amsa a takaice. Sai ya dan
kashingida to shikenan ki barshi na fasa ci nima. Kallonsa tayi da mamaki a
fuskarta ba yanzu kace kana jin yunwa ba. Ya kada kai tunda kinci ba tare da kin
jirani ba shikenan, am not hungry anymore. Duk sai bata ji dadi ba. A hankali ta
dan matsa kusa dashi, Ya Hamza nayi maka laifi ne? Yadda take maganar yasan kuka
take shirin yi masa. Yace a'a naga kema kina ta bata rai shiyasa na dena jin
yunwar. Sunkuyar da kanta tayi sai hawaye...hankalin Hamza ya tashi ya sauko kasan
ya matso kusa da ita. Yanzu Cutie me nayi miki kike kuka....cikin kukan tace ba
kaine kace sai na saka wannan kayan ba dazu, kuma da nayi fushi baka rarrasheni ka
bani hakuri ba. Tasa hannu ta share hawayenta kuma shine yanzu kake fushi dani don
Mala'iku su rubuta min zunubi. Zama yayi yana kallonta har ta gama bayanin sannan
ya soma murmushi yi hakuri my cute baby ashe fushin duk laifina ne. Kiyi hakuri
dazun ma wasa nake miki. A take ta washe baki kamar ba ita take kuka ba...da gaske
ka yarda nasa rigar mutumci? Ya dafe kai wato wadancan ba na mutumci bane. To ki
saka duk wanda kike so kinji. Yanzu dai bani abinci sai muyi shirin bacci. Tana
tashi yayi ajiyar zuciya Zuhra akwai iya rigima. Ji yadda take masa kuka lokaci
daya kuma ta dena kamar ba ita ba.
Bayan yaci abinci ta koma suka zauna kallo ita da su Adabiyya. Shiru shiru Hamza na
jiranta a dakinsa taki hawowa har shadaya da rabi. Duk sai ya damu so yake kawai ya
ganta. Gajiya yayi da jira ya sauko ya tashe su suje su kwanta dare yayi. Zuhra na
ganin ya tafi tace akwai TV a dakina muje muga karshen film din. Adabiyya tace wane
karshen film kuma ki tafi ki kwanta Anti Zuhra kada kisa Yaya ya kora mu gida da
sassafe.
Suna shiga dakinta taga Hamida ta shiga wanka Adabiyya ta cire kaya ta daura tawul
tana jiranta. A ranta Zuhra tace ashe kowa na wankan dare banda ni. 'Yan sauran
kayan bukatarta ta dauka tayi musu sai da safe. Tana sallama falon nasa ta ganshi
zaune ga laptop a gabansa ya zurfafa yana aiki, TV kuma a kunne ana news a BBC.
Zama tayi a wata kujerar tace masa sannu da aiki. Hannu ya daga alamar amsawa ya
cigaba da abinda yake yi. Remote ta dauka ta canja tashar zuwa film din da suke
kallo kafin ya tashe su. Wurin minti shabiyar tana zaune, idonsa yana kan aikin
gabansa yace Cutie tashi kije kiyi wanka. 'Yar shagwaba ta soma yi masa ka bari a
gama don Allah. Dago kai yayi yana kallonta to babu komai bari na gama aikin gabana
sai nayi miki. Bata jira ya kare zancen ba ta shige cikin dakinsa harda murda key.
Girgiza kai yayi yana dariya. Tunda tare zasu kwana ai bashi da damuwa.
Sai da ta gama gyara jikinta tsaf ta tuna bata dauko wasu kayan baccin ba. Wadanda
ya dauko ta gani akan gadon ta dauk tasa. Kayan sunyi mata kyau sosai ta saka hula
sannan ta dauki hijab dinta mai hannu dogo har kasa ta dora a kai. A haka zata
kwana a can gefen gadon idan yaki yarda ta koma falo. Tsoro take kada ya sake
rungumarta irin na daren jiya ko ma yayi mata kiss irin yadda yayi da safe. Lips
dinta ta dan shafa tana murmushi ashe kiss dinma ba kazanta bane. Ji tayi Ya Hamza
ya kara shiga ranta sosai. Tunanin me kike yi haka harda murmushi Hamza ya fada
yana rufe kofar dakin da mukulli. Hantar cikinta ce ta kada saboda tsoro murya a
sarke tace bari na koma falo na kwana. Dan hararta yayi kina son muyi fada ne? Ta
girgiza kai yace to sami wuri ki kwanta ni sallah zanyi. Kafin ya fito daga alwala
ta shimfida abin sallah biyu a inda take tunanin nan ne gabas. Kallonta yayi tayi
masa murmushi nima nayi alwala ai. Zuhra batasan komai tayi kara shiga ransa take
yi ba. Dadi yaji mara misaltuwa da yaga ta tsaya akan abin sallah tana jira ya
tayar. Da Izzy ce sai dai ta kwanta yayi ya idar da nafilarsa ko ta bijiro masa da
bukatarta a lokacin. Sunyi kusan minti arbain da biyar suna sallah sannan ya idar
yayi musu addua. Zuhra na ninke abin sallan tace Ya Hamza karatunka dadi wallahi.
Yace nagode kinyi min addua kuwa? Yana kallo da hijab din ta kwanta tace sosai ma.
Sai da ya kashe fitila suka kwanta kowa na nasa gefen Zuhra tace Ya Hamza ina son
tambayarka amma kada kaji haushi na. Idan na bata maka rai kayi hakuri. In sha
Allah raina bazai baci ba yi tambayarki. Sauke numfashi tayi da karfi...na kula tun
satin da ya wuce wani lokacin sai ka zauna kayi ta tunani. Har ina tsoron ko duk
saboda ni ne sai naga kuma kamar abin yafi karfin matsalar aurena da kayi ba'ason
ranka ba. Idan bazaka iya fada min ba ma babu komai zan tayaka addua kullum. Amma
kasan wani lokacin idan ka dan fadawa wani matsalarka sai kaji nauyinta ya ragu. Ko
jibi idan su Khalifa suka dawo sai ka fadawa mamansu. Tunda ta fara magana yake
kallon inda take kwance. Zuhra daban ce shine kawai abinda yake tunani. Har tana
lura da damuwarsa duk yadda yake kokarin boyewa. Shiru yayi ya kasa magana saboda
yadda ta tsaya masa a rai. A hankali ya fara yarda da cewa bazai iya rabuwa da
Zuhra ba. Ji tayi yayi shiru tace Ya Hamza nayi maka laifi ko? Ka yafe min. Babana
ne yace ana son mata da miji su rinka yiwa juna addua. Naga ko dai a yaya muka yi
aure kai mijina ne yanzu shine nake son yi maka addua. Har yanzu bai yi magana ba
sai ma haushin kansa da yake ji saboda yadda ya kuntata mata harda sa ranar saki.
Hankalin Zuhra ya tashi da lalube take mika hannu saboda dakin yayi duhu sosai sai
sautin AC, Ya Hamza kayi magana mana, Ya Ham....hannunta ne ya kai jikinsa ya
janyota ya rungumeta sosai suka kwanta. Kanta akan kirjinsa da yake a bude bai
balle maballan ba yaji saukar hawayenta. Saurin dagata yayi duk ta dukunkune jiki
da hijab yace Cutie kukan me kike yi? Har da sheshsheka tace ba kaine kayi shiru ba
na zata wani abu ne ya sameka. Hijab din jikinta yake kokarin cirewa tana rikewa a
raunane yace Cutie kin damu dani ne haka. Da muryar shagwabarta tace kaifa Yayana
ne yanzu wanda yake min kirki bana so muyi fada har mu rabu. Ta rike hijab din a
jikinta don Allah kada ka cire min kunya nake ji. Kyaleta yayi ya rungumta a haka.
A hankali ya bata labarin da babu wanda ya sani sai kalilan a kamfaninsa. Amma bai
fada mata duk Izzatu ce take yin sanadiyar faruwarsu ba. Har mamakin kansa yake
yadda ya iya budewa Zuhra kazamar yarinyar nan mara kunya cikinsa. Muryarta a kasa
saboda labarinsa yasa ta kara yin kuka tace Ya Hamza ka godewa Allah da duk wata
jarabawar rayuwa. Kaga ni bana sonka aka yi mana aure amma dana hakura na barwa
Allah sai gashi ka zama mai kirki har ina sonka sosai a matsayinka na Yayana. Allah
baya dorawa mumini abinda yafi karfinsa. Kuma yarda da qaddara yana karawa mutum
imani da kusanci da Allah. Kada ka taba jin tsoron talauci Allah shine mai
azurtawa. Zan rinka tayaka addua har Allah Ya kawo karshen komai. Hawaye ne suka
cika masa ido ba na komai ba sai na karin imani da maganganun Zuhra suka saka masa.
Abu daya ya kudurce a ransa zaiyi iya kokarinsa ya koya mata sonsa domin a halin
yanzu baiga wanda ya isa ya rabashi da ita ba sai Allah. Idan abin nan da yake ji
soyayya ce da bai taba tunanin zai yiwa wata ba bayan Izzatu to lallai ya amince
har ransa yana son Zuhra. Ita kuwa duk da kunyar da take ji saboda yanayin
kwanciyarsu ta hakura saboda yadda take jin tausayin Ya Hamza.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/2, 9:57 AM] #+234 803 220 0468#: AL'ADUN WASU
#54
Batul Mamman(Mrs)#
A hankali ta dan bude idonta sai taga haske a cikin dakin. Bude idanun tayi
gabadaya ta kalli agogo. Karfe bakwai harda minti tara. Subhanallah ta fada tana
kokarin tashi daga kan gadon. Rabin jikin Hamza duk ya danne mata hijab tayi
kokarin janyewa ta kasa. Tana son taba shi ta tashe shi amma haka kawai take jin
wata irin kunyarsa. Baccinsa yake hankali kwance. Karewa fuskarsa kallo tayi tana
ayyana irin kamaninnsa da dukkan kannensa. Duk Alhaji Nasiru suka biyo shiyasa kana
ganinsu kaga 'yan gida daya. Sajensa yafi komai daukar hankalinta kuma yana karawa
fuskarsa kyau da kwarjini. Ga wani tausayinsa da yake ratsata saboda labarin da ya
bata da daddare. Shagala tayi da kallon mijinta tana tunanin yadda zata ji ranar
da zasu rabu. Idonsa a rufe yace irin wannan kallo Cutie sai na zata irin son nan
kike yi min, in ba ni ba sai rijiya. Saurin tashi tayi zata gudu saboda kunyar da
taji ya kamata tana kallonsa hijab dinta ya shake mata wuya. Tashi yayi yana mata
sannu. Kinga maganin masu kwana da miji da hijab kenan. Kan Zuhra dai yana kasa ta
kasa kallonsa ya tashi ya shige toilet yayi alwala. Bayan ya fito itama tayi suka
yi sallar asuba tare da salatul duha tunda gari ya waye.
Sai da suka gama azkar sannan yace