Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
da gudu da wani mayafi da ta gani a dakin Izzatun domin a
suturta mata jiki. A kasa suka tarar da Tala da Nana zata hada mata tea. Idanunta
ne suka bi Hamza dauke da Izzatu ga jini a jikinta. Zuhra tace mata ta kula da
gidan da yara zasu je asibiti.
Gudu Hamza ya rinka yi cikin dan lokaci suka isa asibitin. Maaikatan asibitin suka
yi masa jagora zuwa emergency inda aka bukaci su tsaya a waje shi da Zuhra. Haka
suka rinka kai kawo a wurin sai gashi an turo Izzatu akan gado an wuce dakin
operation da ita. Hamza ya tambayi wani cikin likitocin menene ya sameta. Likitan
yace bari mu fito zamu yi maka bayani. Ku dai kuci gaba da addu'a.
Sun kusa awa biyu a corridor din babu wanda yake iya yiwa wani magana. Kowa da
abinda yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa. Zuhra ce tayi karfin halin cewa Hamza
ko zai yi waya gida ya sanar dasu Hajiya, jikinsa duk a sanyaye yace ya barota a
gida. Itama Zuhra tace bata dauko tata wayar ba. Suna magana likitan ya fito yace
Hamza ya biyoshi office. Ga mamakin Zuhra sai taji ya kamo hannunta suka tafi tare.
Ko zama basu yi ba Hamza yace don Allah ka fada min halin da take ciki. Likitan
yace to ka zauna mana, Zuhra ya zaunar tare da rike mata hannu gam. Likita yace
kaine mijinta ko? Hamza ya gyada kai. Ya cigaba da cewa to sai dai kuyi hakuri bamu
iya saving din abinda ke cikinta ba.
Bangane ba doctor? Kana nufin tana da ciki ne.
Kwarai kuwa don har ya kusa wata biyu. To matsalar da aka samu shine mahaifar bata
da kwari kwata kwata. Don ita da abinda ke cikin tare suka fara fitowa.
A gigice Hamza yace fitowa kamar yaya?
Ina nufin bari tayi wanda har mahaifarta ta fara fitowa saboda rashin kwarinta.
Shiyasa muka ga dole muyi mata virginal hysterectomy saboda ceto rayuwarta.
Kokari Hamza yake kada ya rasa nutsuwarsa yace kayi min bayani a yaren da zan gane.
A wane hali Izzatu take?
Likita yace yanzu tana bacci saboda anyi mata allurar anasiziya. In sha Allah nan
da kamar awa daya zata farfado. Abinda nake nufi da hysterectomy shine mun cire
mata mahaifa saboda ba karamin lalacewa tayi ba.
Wata muguwar faduwar gaba Hamza yaji wanda hakan yasa shima ya zauna. Zuhra ta sake
kankame hannunsa saboda firgici. Yace doctor kana nufin yanzu bazata sake haihuwa
ba.
Haka nake nufi amma don Allah kayi hakuri bamu fara sanar da kai ba kafin mu
aiwatar da nufinmu. Yanayin da take ciki ne baya bukatar bata lokaci. Idan ta tashi
ita tafi cancanta da ta fadi maganin da tasha ya illata mahaifar haka. Bazamu iya
yanke komai ba sai munji daga gareta. Tashi likitan yayi ya barsu a office din
bayan ya gama yi musu bayani.
Yana fita Zuhra ta rungume Hamza tana kuka. Kayi hakuri Ya Hamza duk laifina ne.
Ganina ne ya bata mata rai har hakan ta faru. Da hannunsa ya share mata hawaye...ki
dena fadin haka Cutie kaddara ce da bata wuce kowa. Amma shima a kasan zuciyarsa
gani yake kamar laifinsa ne tunda Izzatu ta fada masa ranar zata dawo, sai abin ya
zama kamar cin fuska ma.
Sabon dakin da aka kai Izzatu suka je. A nan ya bar Zuhra yace zaije gida ya fada
musu tunda baizo da waya ba.
******
Daga Hajiya har Mama babu wanda labarin yayi masa dadi. Duk sun tausayawa Izzatu.
Mama tace watan cikin nawa? Ni ban san dashi ba Hamza ya bata amsa. Sai a lokacin
ta kula da rigarsa tace ya gyara ta. Kunu da kayan tea suka hada ya daukesu ita da
Hajiya da Adabiyya ya kaisu asibitin sannan ya dauko Zuhra suka tafi gida. Har
lokacin Izzatu bata farfado ba.
Saboda yanayin da suka fita maigadi da Tala suna ganinsu suka fara tambayar ya mai
jiki. Zuhra ce take iya basu amsa tana cewa da sauki. Wanka duk suka yi sannan
Zuhra ta sauko ta hada masa abinci. Da kyar ta samu yasha tea yace zai koma
asibitin. Damuwa ce tayi masa yawa yana tambayar kansa ta ina zai samo kudin
asibitin Izzatu? Bashi da sauran kadarar da zai sayar sai wani fili da ya siya a
Kumo wanda yanzu kafin a samu mai siya ma aikine guda. Shi ko irin budewa yara
account dinnan bai taba tunanin yi ba saboda basu hango rana irin wannan da zasu
fuskanci matsin rayuwa ba.
Zuhra na kallon yadda ya zurfafa a tunani ta dan dafa kafadarsa. Ya Hamza kaine fa
kake cewa kaddara ce abinda ya faru. Don Allah kayi hakuri. Idan ka bari damuwa
tayi maka yawa waye zai rarrasheta idan ta farfado? Murya a sanyaye yace babbar
damuwata yanzu inda zan samo kudin asibitin Izzy. Kinsan halin da nake ciki bansan
inda zan samo kudin ba indai ba kudin kamfani zan dauka ba. Zuhra tace idan ka
dauka aikinku zai sami rauni. Kuma kace har kun kusa kammala daya. Ta mike tsaye
ina zuwa....
Bata dade ba ta dawo da wata karamar leda mai kyau a hannunta. A tafin hannun
Hamza ta ajiye ledar yace koma meye ki rike kayanki zansan yadda nayi na sami
kudin. Ko bashi ne sai na nema. Idonta fal hawaye tace yanzu ka gwammace ka nemi
bashi akan ka karbi abinda kake da iko dashi? Wannan abin da na baka kai ka siya
fa? Idan ka karba ai ba yana nuna gazawarka a matsayin namiji bane. Jarabawace
Allah Ya dora maka.
A hankali ya bude ledar ya ciro wata yar roba mai murfi. Sarka ce da dankunne da
zobe na gwal a ciki. Saurin rufewa yayi ya dora mata a cinyarta. Cutie ki dauke
kayanki bazan sayar miki da sarkarki ba....abinda ya kasa fada shine ko pant bai
siya mata ba a lefenta. Komai Alhaji ne yayi. Hannuwanta biyu tasa ta rike
kumatunsa tana kallon fuskarsa mai dauke da tsantsar rashin kwanciyar hankali.
Tunda nake ban taba saka gwal ba a rayuwata don an sayar da wanan bazanji komai ba.
Duk irin wadannan abubuwan dama ai saboda rana irin yau ake tanadin su. Ni a abinda
su Baba suka koya min wannan shine aure. Taimakon juna a lokacin bukata batare da
mun fita waje mun tonawa kanmu asiri ba. Su Alhaji ne baka son sanarwa halin da
kake ciki to ni din da na sani ka bani damar taimakonka mana. Sarkar da hannunta ya
hada ya rike sosai sai kawai taga hawaye ya fito daga idonsa. Lallai rayuwa bata da
tabbas, babu wani yanayi da bawa zai tsinci kansa yace wannan yanayin zai tabbata a
ciki har ranar busa kaho. Yau kana da arziki gobe waninka ne. Wa zai taba tunanin
akwai ranar da Architect Hamza Nasir Hamza zai karbi taimako a hannun Fatima
Bashir? Yarinyar da ko certificate din shaidar tayi secondary school bata dashi,ga
kazanta ga rashin wayewa. Ikon Allah kenan, kada ka taba raina bawa domin baka san
abinda Allah yayi masa na arziki ba. Arziki kuwa ko da ba na kudi bane. Hawayen da
Hamza yake yi ya karyar mata da zuciya ta soma kuka. Haka suka rungume juna na
tsawon lokaci. Daga baya Hamza yace ta tashi su koma asibiti tace a'a yaje kasuwa
ba'a rasa masu bude shago ranar lahadi ya sayar. Ita kuma zata kara yin saka zuwa
la'asar ko bai dawo ba zata yi girki ta tafi asibitin da kanta. Sai da ya kwashe
kusan minti biyar yana kissing dinta sannan ya fita. Bai san da yaya zai gode mata
ba. Tunda ya shiga mota har ya isa kasuwar ALHAMDULILLAH yake ta nanatawa saboda
godiya ga Allah da Ya azurta shi da mace tagari a lokacin da rayuwarsa take tsaka
da rushewa.
A dalilin mugun tashin da dollar tayi wanda muke ta addu'a Allah Ya yafe mana Ya
kawo mana sassauci sai da Hamza ya sami dubu dari uku da tamanin da hudu a matsayin
kudin sarka, dankunne da zobe. A haka ma don mutanen sun kula kamar a matse yake da
ya sayar.
A hanyarsa ta tsallaka titi ya koma motarsa yaga wata tsohuwa tukuf itama ta rasa
yadda zatayi ta tsallaka. Da a lokacin da yake Hamzansa ne mijin Izzatu ita kadai
baya jin zai iya yadda hannunsa ya taba matar. Amma yanzu ya koyi darasin zaman
duniya. Hannun matar ya riko tana tafiya da kyar har ya tsallakar da ita titi.
Godiya ta rinka yi masa tare da addua. Harda dan kukanta tace ba don kai ba sai
nayi kusan minti shabiyar ina kokarin tsallaka titin nan. Magani na karbowa dana
yana fama da lalurar asma. Ta dauki wata leda da magani ta nuna masa. Hamza ya
tausaya mata yace baki da wasu yaran ko jikoki da zasu je miki? Tayi murmushi, shi
kadai ne dani. Bayan shekaru shabakwai sai yanzu matarsa take da tsohon ciki. Idan
abin ya tashi ita take zuwa amma yanzu bazata iya doguwar tafiya ba. Yana ganin
kansa a wani yanayi ga wadanda suka fishi. Kudin aljihunsa ya shafa ya sa hannu ya
kirga dubu goma ya bawa matar. Hannu na rawa ta karba tana ta kuka...Allah Ya
albarkaci rayuwarka data iyalinka, Allah Ya rabaka da masifun zamani, Allah Ya baka
arziki na halali daga inda baka taba tsammani ba. Yaro nagode, nagode. Hamza na
tsaye har ta shiga adaidaita sahu sannan shima ya tafi zuciyarsa kamar an cire masa
wani nauyi. Hakika sadaka maganin masifa ce kuma waraka daga bacin rai.
Asibitin ya koma ya tarar Izzatu ta farfado. Raliya ya kira a waya ya sanar da ita
halin da Izzatu ke ciki. Cikin kidima tace gobe zata taho in sha Allah. Tana ajiye
wayar ta kira kanwarta Larai ta fada mata asibitin da suke.
Tsananin bacin rai da kishi yasa Izzatu kuka tunda ta farfado. Yanayin da taga
Zuhra da Hamzanta shi kadai yake mata yawo a ka tunda ta bude ido. Su Mama kuwa sai
tausayinta suke yi a nasu tunanin bakincikin bari da cire mata mahaifa da akayi
take yi. Cike da tausayi Hamza yake mata sannu amma ko kallonsa taki yi. Su Mama
sai suka dauke kai kamar basu kula da abinda suke yi ba. Adabiyya tace Yaya ina
Anti Zuhra? Yace zata taho girki yasa bamu fito tare ba.
Basu dade ba kuwa sai gata da kwandon abinci. Bata tashi daga kan sakarta ba sai da
tayi mai yawa ta yadda abin da ya rage mata saura kadan. Itama ko kallo bata ishe
Izzatu ba duk da halin ciwon da take ciki. Sauran 'yan uwan Hamza suma duk sun zo.
Zuhra ma ta kira Baba ta fada masa Izzatu na asibiti yace zasu zo washegari tare da
Umma.
Anti Larai kanwar Raliya tazo tare suka karasa yinin sai dai ta baro maigidanta
babu lafiya saboda haka bazata iya kwana a asibitin ba. Dole aka yanke shawarar
Adabiyya da Zuhra su kwana da Izzatu. Ranta inyayi dubu ya baci amma ko tashi
bazata iya yi ba shiyasa dole ta hakura. Shabiyu saura na dare su Zuhra suka fita
suka bashi wuri ya dan zauna wurinta. Sai lallabata yake tana kuka ita bazata zauna
da wadda tayi sanadiyar zubar mata da ciki ba. Da kyar ya lallabata yace gobe shi
zai kwana. Haka suka rabu ranta a bace. Itama Zuhra yayi mata sallama sannan ya
tafi gida.
********
Wasu matasa ne su uku duk da bakaken kaya harda abin rufe fuska suka shigo cikin
kauyen da gudu da cikon na hudun a kafadar wanda yafi sauran girma. A kofar wani
katon family house suka ajiye na kafadar wanda yake ta zubar da jini sakamakon
harbinsa da aka yi a cinya suka gudu. Da yake tsakar dare ne babu wanda ya kula
dasu. Sai can wasu maza biyu suka zo wucewa a buge suka ga mutum a kwance a kasa.
Da har zasu gudu sai daya ya haska shi da touchlight, da sauri ya karaso giyar da
yasha ta fara barinsa yace sa dayan kazo mu taimaka masa Felix ne kanin Mr Oscar
miloniya.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU #67
Batul Mamman(Mrs)#
Cikin hanzari suka burkito fuskarshi suna ganinshi duk suka razana "mr.oscar yau
kaine ahaka?
Afili hakkin hamza yafito,mr.oscar yana kuka yanacewa kutaimakeni na cuci hamza
mutuwa zanyi wayyo Allah na.
Nidai nawa tunanin kenan,kekuma wannene naki
Gabadayansu ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Da sauri Hamza ya koma dakinsa
ya dauko wata doguwar riga ya sakata gaba a baya ya dauko Izzatu. Zuhra ma hijab ta
burma ta bi bayanshi da gudu da wani mayafi da ta gani a dakin Izzatun domin a

Bashir?