Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
na kawo su don kada ace
ina raba zumunci. Amma wallahi barnar kudin naka tayi yawa. Hamza yace ina maganar
party Ibrahim. Junior ne ya rasu. Baka ga mutane da yawa ba. Ummahani na kokarin
bude gate Junior ya bude tare da wasu yaran. Sun sha sababbin kaya. Hamza ya kura
masa ido sannan ya dubi Ibrahim. Ibrahim yace kai wa ya fada maka ya rasu? Hamza a
rikice yace Izzatu tayi waya Office tace a fada min ya karye a hannu. To ina zuwa
naga motoci nayi tunanin ya rasu ne. Ibrahim yayi tsaki cike da bacin rai yace
Allah Ya kyauta ni na tafi. Zuciyarsa na kuna yaja motarsa yayi gaba. Ace babban
mutum kamar Yaya dan shekara talatin da bakwai ya bari mace na karanta masa yadda
zasuyi rayuwa. Kodayake ba laifinta bane. Tare suke yin komai. Daga nan Ibrahim
gidansu ya tafi.
A hankali Hamza ya tura karamar kofar gate din ya shiga. Kawai sai ji yayi mutanen
wurin sun ce SURPRISE!!! farfajiyar gidan ya gani ya sha kwalliya an jera kujeru da
tebura. Ga fitilu suna ta haskawa an kunna inji. Kida aka kunna yana tashi a
hankali. Bai gama tantance abinda ke faruwa ba Izzatu taja hannunsa suka shige
cikin gida. Muje ciki ka canja kaya. Suna shiga daki ta rungume shi. ....HAPPY
ANNIVERSARY MY BABY.
[9/25, 2:51 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿8
Batul Mamman(Mrs)💖
Hamza ya yiwa Izzatu kallon rashin fahimta. Izzy me yake faruwa ne? Kince Junior ya
karye but it seems lafiyarsa kalau. Fari tayi masa da ido irin yadda tasan yana
kara dauke masa hankali, sai a lokacin ya kula da kayan jikinta. Wani irin yadi ne
mai matukar santsi aka yi mata doguwar riga wadda ta dameta daga sama har gwiwa
sannan ta bude sosai. Ga wani abu kalar takalminta da sarka anyi mata dauri. Tamkar
wata amarya ta fito. Jikinta mai kyau ne ba kace ta haifi 'ya'ya uku ba. Tana lura
da yadda yake binta da kallo tayi murmushi. Dama nayi ne kawai don ka dawo gida
akan lokaci. Na gama komai na shirya mana anniversary dinmu na shekara goma. Ya
shafi gefen fuskarta amma Izzy ba kya ganin abin ya danyi yawa. Ki ce dana ya karye
kinsan zan tsorata. Kiss tayi masa a kumatu to yi hakuri daddyn Junior. Kaga ana
jiranmu a waje.
Tare suka fito rike da hannun juna. Sunyi matukar kyau sosai ga yaransu suma sun
sha ado. Babban shekararsa biyar suna kiransa Khalifa mai sunan Alhaji Nasiru. Sai
Junior mai shekara uku sunan baban Izzatu gareshi Sunusi sai kuma Nana(Halima) mai
neman shekara ta biyu. Sunan Mama yaso saka mata sai dai Maman taki saboda Ibrahim
da Mariya duk sunyi mata takwarori.
Hajara tana ta binsu da ido duk inda suka yi ana ta gaisawa da daukar hotuna. Ga
masu rabon abinci suna ta yi su ma. Tace kai Anti Faiza ina ma Zuhra tazo muci son
ran mu. Ji kaji kamar su suke kiwonsu. muma dai Allah Ya bamu kudin nan muji dadin
rayuwa mu rinka party duk shekara. Mariya tace ba amin ba kanwata. Anti Faiza da
Hajara suka juya suna kallonta. Hajara tace kinji min mata da bakinciki. Faiza ta
kai mata duka to shashasha baki san mutum ba zakiyi rashin kunya, yi hakuri baiwar
Allah. Ko ba'a fada ba daga shigar Mariya an san tana da kudi. Murmushi Mariya tayi
ba komai ke dai kiyi adduar arziki mai albarka ba na party ba. Daga nan ta tashi ta
hada kan 'ya'yanta sukayi waje.
Haka aka cigaba da taro har wurin karfe takwas na dare. Nura ne suna shirin tafiya
dasu Adabiyya yazo ya fadawa Hamza sakon Mama kan cewa tana son ganinsa a yau. Sai
bayan fitarsu ya duba agogonsa. Subhanallah ya fada da karfi tare da mikewa. Izzatu
tace yaya akayi? Ya nuna mata lokaci. Kinga har lokacin isha yayi bamuyi magriba
ba. Ta dan tura baki idan an watse ba sai muyi ba. Bana son a fara shiga ciki ne
azo a bata min toilets. Hamza yace ni dai bani key please. Ta dan daure fuska Allah
bazan bayar ba. Kana shiga mutane zasu fara bin bayanka. Ya girgiza kai yana
murmushi Izzy baki da dama. Wani famfo ya zagaya a bayan gidan yayi alwala sannan
ya fita masallaci. Duk lalacewar lamarinsa bai tashi da tarbiyar sakaci da sallah
da gangan ba.
Ana gyaran wurin jamaa sun watse sauran kadan Hamza ya fito zuwa gidansu. Izzatu ta
bashi manyan kuloli cike da abinci, nama da snacks. Ga katon din juice da na ruwa
ya kaiwa su Hajiya.
Kula daya ya dauko maigadi ya biyoshi da sauran. Da sallama ya shiga babban falon.
Mama da Hajiya ne a wurin sai Jidda da ta biyo su Nura tana jiran mijinta. Duk suka
amsa sallamarsa sannan Mama tace maraba da Mungo Park. Turus Hamza yayi ya kasa
furta gaisuwar da yake shirin yi musu. Hajiya tace Jidda tashi mu shiga ciki uwa da
danta zasu gana. Dama zamanta a wurin ta kara tunzura mama da bayanin abinda ya
faru a wurin partyn. Hamza yayi murmshi da wuya kaga fuskarsa a hade sai dai idan
yana cikin tashin hankali. Mama nasan nayi laifi ko baki fada ba. Amma wallahi nima
bani da masaniyar wannan party din. Surprising dina tayi nima. Mama tace ai naga
alama. Zaka ce iyayenta basu da labari ne? Ka hado kuloli ka kawo wa mayunwatan
iyayenka abinci ko. To duk ka kwashe abinka bama so. Yace Mama ita da kanta ta bani
na taho dashi. Tace kaga ni ba wannan ke gabana ba kaji ko. Yanzu don Allah Yaya
yaushe zaka san ka girma? Wace irin rayuwa ce kuka daukarwa kanku kai da iyalinka.
Kanka aka fara zuwa kasar waje karatu ne da zaka dauko al'adun da ba naka ba kayi
ado da su. Sau nawa muna yi maka fada ni da Hajiya akan birthday partyn da kuke wa
yaranku duk shekara amma ka share. Irinsu valentine dinnan ma duk kuna yi ko? Shiru
Hamza yayi don yau kam ya san ya batawa Mama rai. Tace ba tambayarka nake ba. Yace
munayi. Ta cigaba da fada....duk wani dan iskan day da yahudu da nasara ke
girmamawa kaima ka girmama. Ka iya kashe kudi mai tsoka ka shiryawa yara party
kawai don suji dadi. Irin sadakar nan ta abinci ko kudi kuwa sai karshen ramadan.
Baka tunanin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki yanzu.
Alhamdulillah muna da rufin asiri ci, da sha da sutura babu wanda Alhaji baya
saukewa amma ai ihsani yana da dadi ko. Ko kasan duk wata sai Ibrahim ya kawo buhun
shinkafa gidannan sannan ya bamu dubu biyar biyar ni da Hajiya. Ya san ba kudin ko
abincin muka rasa ba. Amma yana neman albarkar iyaye. Mariya da Jidda suma suna
nasu kokarin da dan abinda sukeyi. Duk cikinsu kafi kowa morar Alhaji kuma ka fisu
kudi amma daga kai sai iyalinka. Kawaici kawai mahaifinka yake maka irin na
bafillatani amma ko kadan baya jindadi. Shin ka taba zama ka tambayeshi a halin da
kamfaninsa yake ciki? Ko ka tambayi Hajiya me take bukata ko da ba na kudi bane?
Hamza ya girgiza kai a hankali. Mama bata san cewa tana fadan ma hawaye take yi ba.
Tace to girma ya kama babanku. Ibrahim lecturer ne amma daga wurin aikinsa yana
zuwa kamfanin taya shi aiki. Nura yanzu yake ajin karshe a jamia amma tun yana
level one yake zuwa. Hamza yayi mamaki wai Nura har ya kai level four yanzu sai dai
bai nuna ba kada fadan ya karu. Ita kuwa Mama cigaba tayi da fadanta. Yan uwanku na
Kumo makusanta. Ina nufin yan uwan Hajiya da na Alhaji kasan halin da suke ciki? Ko
kasan a rage maaikatan banki harda kanin Hajiya. Hamza ya dago kai wanne? Tace
Nafiu. Gashi yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha uku. Watansa kusan bakwai ba
aiki. Akan Nafiu Hajiya ta soma kukan rashin taimakon da kake yi. Maganganun sun
ratsa Hamza sosai. Ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci. Mama tace ni dai
lahirarka nake duba maka Yaya. Rayuwarka nema take ta sauka daga turbar addini.
Har yau ban manta yadda Izzatu tasha maganin hana haihuwa ba wai sai ta gama
karatu. Allah ne ma Yaso kuna da rabon haihuwar daga baya. Ka tashi ka je ka bawa
Hajiya hakuri ka tafi dare yayi. Hamza yayi godiya sosai tare da sake bata hakuri.
Har ya kai bakin kofa tace Yaya....naam ya amsa. Nasan saura baifi sati biyu ba
birthday din Nana. Kwana hudu kafin ranar ka dawo dasu nan. Wallahi ka sake
celebrating birthday a gidanka zaka ga fushina sosai.. Allah Yayi muku albarka
[9/25, 2:51 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿10
Batul Mamman(Mrs)💖
Zuhra ta shigo layin gidan Anti Faiza sai ta hango mai tsamiyar biri yana turawa a
baro. Tsallakawa tayi bangaren da yake zata siyo. Dama tana ta tunani yar tsarabar
da zata kaiwa su Abba.
Hamza da Izzatu suna mota suna hira tana fada masa Inuwa sakatare ya kira yaji ya
jikin Junior fa. Dariya sukayi yace kin mayar dani makaryaci dai. Khalifa ne ya
hauro daga baya ya dawo gaba ya zauna kusa da Izzatu. Ta juya ta harari maiaikinta.
Ke Tala garin yaya kika bari ya taso har ya dawo nan. Oya Khalifa koma wurin
zamanka. Ko kulata baiyi ba yace daddy ka kawo na tayaka driving. Hamza yace not
today Khalifa kaga anyi ruwa jiya titin babu kyau. Kuma akwai mutane a nan. Khalifa
yace ko sau daya ka bari na dana. Izzatu ta kama shi zata mayar bayan mota yasa ihu
tare ta riko wuyan Hamza. Iyakar karfinsa yasa yana jan babansa. Garin ya cire
hannun Khalifan ya dan dauke ido daga kan hanya.
Tana tura ledar tsamiyar birin a jaka taga mota ta yo kanta. Hantar cikinta ta kada
ta rasa ina zata yi ma. Gabadaya ta rude kafafunta sun kasa daukarta. Da kyar Hamza
ya iya tsayar da motar bayan ya shigar da ita cikin wani ruwa da ya kwanta a gefen
titi. Har fuska ruwan ya watso wa Zuhra sannan ta zame ta fadi a zaune cikin ruwan.
Karshen bacin rai kam taji shi a lokacin. Musamman da ta hango mai tukin da yaro
suke kicikici da sitiyarin motar. Da sauri Hamza ya tura Khalifa wanda yake ta kuka
cinyar Izzatu ya sauke glass din motar yana duban Zuhra. Leko da kansa yayi zai
bata hakuri sai dai akayi rashin sa'a kwalliyar fuskarta ta bashi dariya. Izzatu da
Tala ma da suke cikin motar sai da suka yi saboda yadda lebenta ke daukar ido. Ita
kuwa Zuhra haushi ya kara kamata. Hamza ya dan daure amma fuskarsa dauke da
murmushi yace don Allah kiyi hakuri kinji. Yaro ne ya rike sitiyarin Allah Ya
kiyaye ban tabaki ba dai ko? Zuhra ta tsuke baki ban sani ba...don tsabar wulakanci
kayi min wanka da kwatami sannan ka wani kame a mota kana tambayar ko ka tabani.
Hamza ya dan sha kunu jin abinda ta fada yace to naji kiyi hakuri don Allah. Ya
zaro kudi a aljihunsa ya mika mata dubu biyar. Gashi ki sayi sabulu. Ganin ya tayar
da motar ta kama hannun gefen inda yake zaune ta soma masifa. Amma kai baka da
mutumci wallahi...tana kallonsa tana kallon kudin. Kudinka me zasu min. Malam ka
fito ka duba ko naji ciwo ka kaini asibiti. Izzatu ta dan leko kiyi hakuri kinji,
kinga yaron da ya jawo, ta dungure Khalifa. Maganar Zuhra ta bawa Hamza haushi yace
idan bazaki karbi kudin ba sauri nakeyi. Kin samu na tsaya zaki rinka yi kin
rashin kunya. Zuhra tace anyi din, nace anyi din kuma Allah Ya isa abinda kayi min.
Ka wani makale a mota kai mai kudi ko. Yadda take magana ya sake bawa Izzatu
dariya. Haka kawai yarinyar ta burgeta. Hamza kuwa harararta yayi sannan cikin
fushi ya fito daga motar. Tun kafin ya karaso tsoro ya cika mata zuciya. A gabanta
ya tsaya ta daga kai ta kare masa kallo. Tabdijam...da kyar in kanta zai kai
kafadarsa ma. Ta hadiyi yawu da kyar. Mutumin duk da bashi da kiba amma dai baya
sahun masu rama, gashi da tsaho. Idanunta suka kawo ruwa don kallon da yake mata ba
na wasa bane. Idan ya dake ta kuwa ya daki banza. Ya dan rage sautin muryarsa ke
kinga nayi kama da sa'anki ne? Ta girgiza kai. Yace to ina baki hakuri sai ki rinka
yimin rashin kunya. Izzatu ta dan bude kofa tace babyna ka taho mu tafi kawai.
Zuhra ta zaro ido ta kara kallonsa....baby kuma? Katon gardi da kai a kiraka baby.
Lallai an cuci kalmar nan al'quran. Ran Hamza ya sake baci ya daga hannu zai
mareta. Tace kana tabani zanyi suman karya a wurin nan sai mazan can sun taru. Kuma
in fada musu abinda kayi min. Daga kai yayi ya kalli kofar kantin da ta nuna yayi
murmushi yace bismillah. Zuhra ta dan ja da baya da gaske nake fa...shima ya kara
matsawa gabanta ai ban hanaki ba. Ta tabbatar dai ba wasa yake ba kawai sai tace
Allah Ya isa da karfi ta kwasa da gudu.
Binta yayi da ido sannan yayi tsaki. Idan ya sake ganin yarinyar nan sai jikinta ya
gaya mata. Shi zata yiwa Allah Ya isa har sau biyu. Yayi kwafa ya shiga mota.
Izzatu sai dariya take. Yarinyar kamar wata clown. Ita fa gani take tayi kwalliya
karshe ko? Hamza yayi tsaki yanzu duk abinda ta fada min bai dameki ba Izzy sai ki
rinka dariya. Tace ai abin naku ne da ban dariya. tayar da motar yayi don idanun
Izzatu suna ga yarinyar da ke gudu ba maganar da yake ba. Tana kallo har Zuhra ta
fada gidan Faiza....
[9/25, 2:52 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 🗿9
Batul Mamman(Mrs)💖
Tunani ne duk ya ishi Hamza har ya isa gida. Tabbas ko makaho yasan kasarmu tana
cikin matsi a wannan yanayin da muke ciki. Sai fatan Allah Ya kawo mana sauki. Amma
a haka duk shekara basa rasa dalilin yin taro a gidansu. Duk da hakan ba ra'ayinsa
bane tun farko amma ya goyi bayan Izzatu akan duk abinda take yi. Dole ne kuma ya
nuna mata kuskuren rayuwar da suka daukarwa kansu ko don inganta tarbiyar
'ya'yansu. Kila mutane suna ta zaginsa bai taba tunanin haka ba sai yau. A haka ya
isa gida zuciyarsa duk ba dadi. Izzatu ta gama gyaran dakin yana ta kamshi ita
kanta ta yi kyau sosai tace ya shiga yayi wanka.
Inuwa Sakatare ya karanta takardun gabansa yafi a kirga. Yana son sanar da ogansa
amma yana tunanin kada ya zama ya nuna rashin damuwa akan lalurar Junior. Daga
karshe dai text ya tura masa wanda ke dauke da cikakken bayani dangane da
yarjejeniyar dake tsakaninsu da turawan. Kusan minti goma ba reply sai kawai ya
kira wayarsa. A lokacin Hamza na wanka. Izzatu na kallo har wayar ta tsinke aka
sake kira har sau hudu. Tayi tsaki ta dauka. Bata son abinda zai bata romantic
night din da ta tsara musu ita da mijinta. Gashi baya yarda da kashe waya komai
dare. Inuwa ya gaisheta ya tambayi jikin Junior tayi dariya kawai tace da sauki.
Yace na turowa Oga sako ne nake son tambayarsa ko ya gani. Izzatu tace yana wanka
amma zan sanar dashi. Inuwa yayi godiya yace sai da safe. Har ta ajiye wayar ta
dawo ta dauka. Tasan halin Hamza kafin ya kwanta sai ya duba sakonnin wayoyinsa mai
bukatar reply ya tura. Ita kuwa daren yau na tunawa da ranar aurensu ne. Bata
bukatar duk abinda zai dauke masa hankali. Duba sakonnin mail dinsa tayi duk ta
bude su a matsayin an karanta haka ma na whatsapp. Text kuwa banda na Inuwa duk
sauran na etisalat ne da mtn. Gabadaya ta hada ta goge harda na Inuwan saboda daga
farkonsa taga an rubut RANKA YA DADE YA JIKIN JUNIOR......iya nan ta gani ta goge
ta saka masa wayoyin a chaji. A tunaninta text din dubiya ne. Da ya fito ya duba
wayar babu wani abu mai mahimmanci sai kawai suka yi shirin kwanciya....
Zuhra ta dawo daga islamiyya tana ta zumbura baki. Sallamar ma a ciki ciki tayi.
Umma tace waya taba uwar masu gida? Jakarta ta jefar a kan tabarma ta cire hijabin
ta kwanta. Umma yunwa nake ji kamar naci babu. Baba ya fito daga bandaki da buta a
hannu yace Allah Ya rabamu da babu. Shine zaki wani kwanta kina turo baki. Ji don
Allah kamar ba mace ba. Kin wani kwanta a kasa. Ji gaban rigarki ma kamar manja. Ya
taba kitsonta da tsagar har ta bace don tsufa...yanzu kan nan yaushe rabonsa da ki
wanke shi? Wai wa zan samu ya aureki a haka? Ba kwakwalwar karatu ga rashin jure
yunwa. Gaki ba wani kyan azo a gani ba. Da nayi kudi ne ma sai a aureki ko don
nauyin aljihuna. Zuhra ta soma shura kafafu Umma kinji Baba ko? Ai dai kai na biyo
wallahi. Yace wa? Ni? Haba yarinya don kinzo na fara tsufane. Tambayi Ummanki
lokacin da nake matashi yadda mata ke bina. Umma tana wanke shinkafa tana musu
dariya. Zuhra tace har tafiyarmu iri daya fa. Baba yasa dariya ai kuwa da kinji
kunya ace budurwa kamarki tana tafiyar maza. Maganin farinjini zan nema miki. Tunda
karatun yaki sai ayi auren. Maganarsa ta sake tunzura Zuhra har ta soma hawaye tace
Umma ina kama dake ko? Umma ta rike baki tace ta ina? Ni duk gidanmu babu mai kyau
na. Ke kuma da Babanki kike kama. Kaga Sima yar gidan Malam Basiru. Dariya sosai
suke yi mata tana ta kuka. Ta tashi ta shige daki. Baba yace kinga kin batawa uwata
rai ko. Umma tace don na tayaka?. Amma maganar gaskiya rashin saurayin Zuhra na
damuna. Maikifin bakin layi ne kawai yake zuwa kuma tace bata son shi. Baba yace
nima abin na damuna. Bata son kula da tsaftar jikinta ne kuma da laifinki. Umma
tace akan ta tsefe kanta har dukanta nayi. Lokaci na bata zuwa wani satin tana
bacci zan sa mata almakashi kowa ya huta. Baba yace wallahi ban yarda ba. Da nayi
saa ta gado irin gashinki mai dan tsaho kuma sai ki aske. Ba gidan Faiza zata ba
bayan azahar...Umma tace can zata je. Baba yace to kice ta tafi da kaya ko biyu ne
ta kwana. Kinsan halin Faiza ko taki ko taso sai tayi tsifar nan. Zuhra na jinsu
daga daki ta leko ta taga na fasa zuwa gidan Anti Faizar. Umma tace kunfi kusa ai.
Sai da ta gama cin abinci ta sha ruwa sannan ta dauko hijab ta saka da kullin
kayanta a dankwali tace Umma zan tafi. Baba ya harareta a haka Zuhra... Islamiyya
fa kika je ko wanka bakiyi ba ki ka saka kaya. Ji hijab din ko guga babu. Ke ko
irin gayun mata baki iya ba. Ki dan saka kayanki a yar leda zaki kulle a dankwali.
Yarinyar nan da a kauye muka tashi bana jin zaki taba wayewa. Gaskiya Umman Zuhra
bakya kyauta min. Kin bar min yarinya ta zama borar karfi da yaji. Umma tace ai
kana gidan kana ganin yadda nake fama da ita.
Baba yace zo ki zauna kinji Fadimatu. Ta zauna bakin nan kamar ya