Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
cuta har ta wuce gasa ni da kake yi. Ta kai masa
cizo a kirji ya kauce yana dariya. Zumbura baki tayi kuma na dena sonka.
Yana dariya yace babu komai Cutie son da nake miki ya ishemu ai.
Bata kula ba ya sake kara ruwan zafin saboda na robar ya fara hucewa. Kuka kala
kala Hamza ya gani. Da kyar take magana don bakin ya mutu. A hankali tace to ka
dawo ta gabana na rungumeka naji dadi.
Yadda tayi ya bashi tausayi amma yasan abinda yayi mata zaisa taji dadin jikinta.
Zagayowa yayi ta rungumeshi tana kuka yana shafa bayanta. Bai kyaleta ba sai da
tayi kusan minti talatin a cikin ruwan zafin sannan kamar jiya yayi mata wanka. Sai
da ya shiryata sannan ya shiga wankan shima. Kafin ya fito tayi baccin wahala.
Gyara mata kwanciya yayi ya rumgumeta cike da tausayawa. A haka suka yi bacci tana
kwance a jikinsa.
Yau dai bata ji kunyar tashi da asuba ba har Hamza na tsokanarta. Da wuri ta
kammala ayyukanta na gida saboda jiki yayi kwari ta dena tafiya da kyar. Da tayi
zancen zuwa asibiti Hamza yace bazashi ba office zai tafi. Itama baiyi mata izinin
taje ba. Ganin ya dauki zafi yasa bata matsa masa ba. Bata damuwa da bin kwaf akan
matsalarsa da Izzatu. Tare ta gansu tasan idan fushin ya kare zasu daidaita. Kullum
Tala ke kai abincin asibitin.
Cikin 'yan kwanakin nan Zuhra da Hamza sun kara shakuwa sosai. Soyayya yake nuna
mata tamkar wata 'yar yarinya haka yake lallabata. Itama dai ta fara sakewa dashi
amma har yanzu tana jin kunyarsa. Ko kayan bacci tasa sai yayi da gaske yake cire
mata hijab. Ana tashi daga office gida yake tahowa su sha soyayyarsu. Ana haka
Hajiya ta kirashi tana masa fadan kwana biyu bata ganinsa a asibiti meye dalili.
Dama yasan ba son Izzatu suke yi ba, idan ya fadi abinda tayi kuma kara wutar abin
zaiyi sai kawai ya bata hakuri yace ayyuka ne suka saka shi a gaba.
Kwanan Izzatu tara a asibitin sannan aka sallameta. Duk irin nasiha tagari Raliya
tayi kokarin yi mata domin ta samu ta rike igiyar aurenta dake lilo a iska. Itama
ta danyi karatun ta nutsu saboda bata taba tsammanin zai iya shareta haka ko waya
babu ba. Tun safe akayi sallamar ta kira shi a waya yana can jikin Zuhra bai bi ta
kai ba. Sai daga baya yaga missed call ya kira tace an sallameta ne tun safe. Hamza
yace to sai ki tari adaidaita sahu ki taho gida ni motata jiya da kyar ta kawoni
gida. Anjima kadan makanike zai zo ya dauka. Kamar ya kwada mata guduma haka taji
maganar tasa. Adaidaita sahu kuma??? Ita ba don kada tayi karya ba sai ta iya cewa
bata taba shigarsa ba. Motoci uku ne a gidansu kuma duk inda zata indai ba aiki ne
yayi masa yawa ba Hamza da kansa yake kaita. Gashi ko zancen motarta da ta bari a
Kaduna baya yi. A sanyaye tace Baby ko daga gidanku kasa azo a daukeni mana. Saboda
yadda ta bashi haushi ko amsa bai bata ba ya ajiye wayar.
Zuhra na falo tana biyewa yara suna shirmensu Hamza ya fada mata an sallami Izzatu
tayi abinci da ita. Tace Mamanta fa? Gidan kanwarta zata wuce, kisa Tala ta gyara
mata daki kafin ta karaso. Yana gama magana ya shige falonsa. Sakonsa ta fadawa
Tala sannan tabi bayansa dama ta riga tayi girkinta kuma zai isa indai cikin Izzatu
ne ita kadai.
Kwance ta same shi akan doguwar kujera ya dafe kansa da hannu daya idonsa a rufe. A
hankali ta rinka tafiya har tazo gabansa ta durkusa. Gashinta ta janyo daga cikin
dankwali ta matso kusa dashi sosai sannan ta zira masa gashin a kunne tana wasa
dashi. Da sauri ya bude ido ya dagota ta fado jikinsa. Kinci bashi Cutie ya fada
yana karkade kunnensa. Tayi dariya kai dai kaji tsoro kawai zaka wayance. Hancinsa
ya goga a jikin nata yana murmushi...Cutie I love you so much. Ganinki yana sa na
manta damuwata. Mayar masa da murmushin tayi tace I love you too. Amma yanzu ka
tashi muyi magana kaji. Ba haka yaso ba a yadda ta kwanta a jikinsa so yayi su
zauna a haka. Yace idan na tashi kin min alkawarin zan sami duk abinda nake so. A
kunyace tayi hada bakinta da nasa tace harma da kari.
Zama ya gyara ya dorata akan cinyarsa. Ina jinki Cutie. Har wani dan gyaran murya
tayi sannan tace Ya Hamza nasan bani da wani iko akan duk matsalarka da mamansu
Khalifa. To amma abinda yake faruwa yanzu yana iya shafarsu. Idan har iyaye na
fushi da juna yara su kan gane idan sun fara wayo. Jiya Khalifa cewa yayi yanzu
baka zuwa wurin Mummy dinsu saboda tayi maka laifi. Nayi kokarin yi masa wayo nace
kana zuwa. Daga baya yazo yace yanzu nice mamansu ko, ita kuma zata koma Abuja su
dena ganinta. Bansan ya akayi yake irin wannan tunanin ba amma ya kamata ka nuna
masa ba haka bane. Yanzu yaro ne bazai kawo komai ba, amma nan gaba idan ya kara
wayo zai ga kamar baka sonta ne. Daga nan ko kai ko ita zai goyi bayan daya ya bar
dayan wanda hakan bai dace ba.
Hamza kallonta kawai yake yi har ta gama bayaninta. Fuskarsa dauke da murmushin
jindadi, shi kam yaga ranar biyayya ga iyaye. Iska ta busa masa a ido da taga baya
kiftawa. Ya shafa fuskarta, Zuhra ke dabance a mata. Lokacin da ya dace kiyi
farinciki hankalin miji ya dawo gareki gabadaya sai kike tunanin kyautatawa wadda
tayi sanadiyar jefaki cikin kunci.
Zuhra tayi saurin dora yatsanta a bakinsa...Ya Hamza ni bana cikin kunci. Na aureka
ba don ina so ba amma yanzu bana fatan ganin ranar da zamu rabu. Yayi murmushi
Allah Cutie? Kice karatun da na koya miki yayi aiki kenan. Kunya taji ta sunkuyar
da kai, ni ba haka nake nufi ba. Yayi murmushi ni haka nake nufi. In Sha Allah
zanyi kokarin gyarawa kuma. Sai dai sai kinyi min hakuri da kunnenki kika ji abinda
tayi. Zuhra tace babu komai indai zaka gyara itama zatayi da yardar Allah. Hamza ya
jinjina kai, Cutie fada min gaskiya ke bakya jin haushin duk abinda tayu miki?
Zuhra tace tabdi, ya za'ayi naji haushi ta hadani da mijin da babu kamarsa. Tana
fadar haka ta tashi ta gudu tana masa dariya.
******
Mai adaidaita sahu ga gaji da ihun da Izzatu take yi ko yaya suka shiga gargada.
Dama da ganinsa ko ba'a buge yake ba to yana dan tabawa ya kallota ta mudubi
idanunta wuri wuri. Ke Hajiya ya zaki rinka min ihu kamar yau kika fara shiga
adaidaita? Izzatu ta kankame karfen gefen da take tana mai nadamar kin bin mamanta
a wanda ta tafi...ban taba shiga ba wannan ne shigata ta farko. Dan matashin yayi
dariya yace shegiyar karya kice daga turai jirginki ya sauka kawai. Kallon yadda
yake kurdawa tsakanin motoci take yi baki na rawa tace wallahi ba karya nake yi ba
a Canada na girma. Dreban ya kwashe da dariya yace bari na dan shillaki kiji kamar
a jirgin Canadan kike.
Ai bata kara samun nutsuwa ba sai da ya tsaya a bakin gate din gidanta. Gudu yake
yi da ita sosai har wani abokinsa na tambayarsa ina zuwa haka da suka tsaya a
danja yace yau Canada ya nufa. Izzatu taga tashin hankali duk jikinta ya bugu.
Kafarta kamar bazata dauketa ba da suka tsaya a kofar gida.
Maigadi ne ya kwaso mata kayanta ta shiga ciki tana jan kafa. Tana shiga falon
idonta ya dire akan Zuhra zaune a kan ledar cin abinci ta dora Nana a cinyarta ga
Junior da Khalifa duk sun zagaye tray suna cin abinci. Zuhra ta dago kanta a dan
tsorace tace mata sannu da zuwa. Ko bi ta kanta bata yi ba tace where are your
table manners kids? Yaushe kuka fara cin abinci a kasa kuma a tray? Khalifa yace
zumunci yake karawa. Izzatu ta dakawa Tala tsawa, daukesu ki zubawa kowa plate
dinsa su koma dinning table. Tala ta ruga kitchen a ranta tana cewa shikenan mun
shiga uku.
Sai a lokacin Izzatu ta karewa abincin kallo tace meye wannan kuke ci a wulakance.
Zuhra taji babu dadi. Farar shinkafa ta dafa sannan tayi miyar alaiyahu. Jajjagen
attaru da albasa tayi sai tumatir kadan ta soya da manja ta zuba alaiyahu wanda ya
tsane ruwansa sannan ta dafa kwai ta sakawa kowa. Tala na zuwa da plate din Hamza
ya fito yace ta mayar ko kallon Izzatu baiyi ba ya koma falonsa rai a bace. Zamansa
kenan wayarsa tayi kara ya dauka.
Mutumin yace shine sakataren ministan tsara birane. An turowa Hamza sakon email ana
bukatar ya karanta ya turo reply kafin gobe. AL'ADUN WASU #70
Batul Mamman(Mrs)#
Hamza.
Hamza..
Hamza....
Shigowar Izzatu falon nasa tana kwala masa kira yayi daidai da faduwar wayarsa daga
hannunsa saboda yadda kiran nata ya dan razana shi. Ya fuskanci kamar da gayya Izzy
ke zuwa a lokacin wani abu mai mahimmanci ta wargaza komai. Sunkuyawa yayi ya dauki
wayar ya mayar da batir zai kunna tazo ta tsaya rai a bace. Yanzu Baby don kayi
aure shikenan ni ban isa ba a gidan nan? Menene dalilin da zaisa ka hana Tala
rabawa yara plates kamar yadda na saka ta?
Hamza ya fasa kunna wayar kada ya bude email din Izzatu tayi abinda zai kasa
fahimta ya bayarda amsar da bata dace ba. Sai da ya zauna sannan yace...daga yanzu
da kika shigo gidannan zaki ga changes wadanda suka sha bamban da abinda kika saba
dasu. Duk wanda baiyi miki ba ki fara magana dani kafin kice zaki gyara shi.
Maganar yara na cin abinci a tray nima jiya haka muka yi dasu duka. Once in a while
dai family suyi sharing plate yana kara saka shakuwa a tsakaninsu. Yanzu ki taimaka
ki tafi daki kiyi wanka ko abinda ranki yake so kafin nazo na sameki. Yana kaiwa
nan ya fita ya wuce dakinsa.
Wayarsa ya kunna ya duba email din. Gayyatarsa akeyi zuwa workshop da za'ayi a
Lagos na kwana hudu. Daga litinin zuwa alhamis, a ranar juma'a kuma za'ayi musu
gwaji a fitar da mutum biyar da suka yi nasara a turasu Korea course na wata biyu.
Jin abin yayi kamar a mafarki ya sake karantawa. Su goma aka zaba su halarci
workshop din. Idan ya amince zashi akwai inda zai danna alamar ya amince sai su
turo masa da kudin jirgi. Hatta hotel din da za'a sauke su a kwanakin da zasuyi duk
an tanada. Hamza dai ya rasa bakin magana sai cewa yaje IKON ALLAH. Shi bazai iya
tuna lokacin da ya tura application na halartar workshop din ba. Inuwa sakatare ne
ya fado masa yayi saurin kiransa. Bayan sun gaisa yake sanar dashi abinda ke
faruwa. Inuwa yace Alhamdulillah, ranka ya dade ai kusan wata biyu kenan da naga
tallan abin a labaran NTA sai kawai na bude website dinsu na cike maka tunda naga
abin na architects ne. Banyi tsammanin zamu sami nasara ba shiyasa nayi shiru da
zancen.
Hamza yace Allah Mai iko da daukaka ni bansan me zance maka ba Inuwa. Allah Ya saka
maka da mafificin alkhairi.
Inuwa yayi dariya ranka ya dade ai bazan taba biyanka alkhairin da kayi min ba a
rayuwata. Ban gama karatu ba ka bani aiki kuma ka cigaba da biya min kudin
makaranta har na kammala. Allah dai Ya sanya mana alkhairi a wannan aikin Ya bamu
sa'a.
Amin Hamza yace sannan ya ajiye wayar. Addu'ar tsohuwar nan da suka hadu a kasuwa
ya tuna yayi murmushi. Lallai Allah shine mai bayarwa ga wanda Yaso a lokacin da
Yaso. Duk wannan abu a dalilin canjin ra'ayi da ya samu ne ya kyautatawa Zuhra.
Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace a suratul Rahman " Hal Jaza'ul Ihsani Illal
Ihsan"...babu wani sakamako ga kyautatawa sai kyautatawa.
Hamza ya gyara alakarsa da matarsa wadda ya aura domin ya wulakanta. Ya bata damar
zama wata jigo a rayuwarsa gashi tun ba'aje ko'ina ba yaga sakamako mai kyau a
lokacin da yake cikin halin matsi da takura. Sai gashi komai yazo masa da sauki
tunda ba'a taba rasa abinci a gidansa ba. Da duka mutane zasu zama masu kokarin
kyautata alaka da sauran mutane da hakika zamu ga taimakon Allah a cikin dukkan
al'amuranmu. Ya Allah Ka taimaki Nigeria da shuwagabaninta da dukkan kasashen da
musulmi ke ciki. Amin
Sallah Hamza yayi raka'a biyu yayi godiya ga Allah SWT sannan yayi addu'ar samun
nasara. Baiyi saurin fadawa kowa ba yana jira sai dare ya fara sanar da Zuhra amma
kafin nan ya fita zuwa gidansu. A nan ya fadawa su Alhaji wayar da ya samu. Alh
Nasiru yayi murna sosai tare da yi masa fatan alkhairi. Su Hajiya ma duk sunyi
farinciki suka yi masa addua. Yana fitowa bai biya ko'ina ba sai gida.
*****
Izzatu ta sauko falo tana tafiya tana rangwada jiki. Tun daga sama take jin hirar
Zuhra dasu Khalifa. Tana saukowa ta zauna daga can gefe ta fara kiran yaranta daya
bayan daya. Abinka da da da uwa duk sai suka koma wurinta suna bata labaran
abubuwan da suka yi lokacin da bata nan. Ko kadan Zuhra bata nuna damuwa ko bacin
rai ba sai da ta tashi suka hada ido da Izzatu ta jefa mata muguwar harara. Bata
tanka mata ba ta tashi ta shige kitchen zuciyarta babu dadi. Ita dai tana tsoron
zaman da zatayi da Izzatu.
Da ta gama abinci ta zubawa su Junior a plates daban daban yadda taga Izzatu tana
so sai dai bata same su a falo ba. Tala ta tura ta kirasu suzo suci abinci. Ko da
taje dakin Izzatu ta fadi sakon Izzatu cewa tayi taje ta dafa musu indomie guda
uku ita da yaran. Khalifa ya tashi Mummy ni dai abincin Maama zanci. Indomie uku
bazamu koshi ba. Junior ya tashi nima haka Mummy kizo muje tare akwai dadi ya fada
yana jan hannunta. Izzatu ta fizge hannu tace Zuhra ba mamanku bace nice mamanku.
Ita bata sonku, so take Daddy ya koremu mu bar mata gidan ita kadai. Khalifa yayi
shiru alamar tunani...ni dai Maama tana sona da gaske. Amma bari naje na tambayeta
dama tace duk wanda yake fadar abu ba mai kyau ba akan wani idan baya nan jirgin
aljannah a Kano zai barshi. Ran Izzatu ya baci tace idan ka sake min zancen jirgin
aljannah sai jikinka ya gaya maka. Kuma duk ku sami wuri ku zauna ko na zane ku.
Babu musu suka zauna suna mata kuka. Juyawa tayi taga me Nana take yi a gaban
dressing mirror taga bata nan. Da sauri ta tashi ta fita, ta sama ta hangota Zuhra
na bata abinci. Ta girgiza kai wannan yarinya da shegen cin abinci take, bata san
lokacin da ta fice daga dakin ba. Dole ta kula da abinda Nanan take ci saboda kada
tayi kiba sosai.
Tala ta kawo indomie haka su Khalifa suka ci ba don rai yana so ba. A dakin nata
suka yi bacci Izzatu tasa Tala ta kaisu dakinsu.
Zuhra dai tasan duk neman rigima ne yasa Izzatu ta hana su Khalifa cin abincinta.
Babu ruwanta tunda 'ya'yanta ne fatanta Allah Yasa sun koshi da indomie din da aka
dafa musu. Wurin karfe tara ta tashi daga falon ta koma dakinta. Dama bata yi
gangancin zuwa dakin Hamza ba don tasan ko ba'a fada ba Izzatu ya kamata taje ta
kwana dashi. Abincinsa ta ajiye a dinning table sannan ta tafi.
****
Da murnarsa ya shigo gidan yau zaiyiwa Zuhra kyakkyawan albishir. Ganin bata falo
yasa ya zauna ya ci abincinsa sannan ya tafi yayi wanka. Idan yayi tunanin Cutie
dinsa sai yayi wani shu'umin murmushi. Yasan tana daki ana gyara jiki bata yarda
tazo dakinsa ba wanka saboda sai ya yi mata fin karfi yayi mata da kansa. Air
freshner ya fesa a dakin yana mamakin yadda akayi yau har ya dawo bata fesa ba. Shi
da kullum idan ya dawo dakin sai sanyi da kamshi.
Wata hadaddiyar rigar bacci Izzatu ta saka mai kyau. Ta gyara jikinta tana zuba
kamshi ta fito ta rufe daki. A ranta ta kudurce idan har Zuhra na dakin to sai dai
su kwana su uku don bazata fita ba.
Duk abubuwan da yake kafin ya kwanta ya gama ya koma falonsa yana duba karin bayani
game da workshop din da aka gayyace shi. Ba karamin project gwamnatin tarayya zata
bawa wadanda suka yi nasara ba. Hankalinsa na kan aikinsa yaji an rufe masa idanu
ta baya. Shiru yayi ya shaki kamshin wanda a take ya gane mai shi. Da sauri ya cire
hannuwanta daga idonsa ya kalleta fuskarsa babu fara'a. Lafiya, kika shigo min daki
a daren nan?
Murmushi tayi don tasan har yanzu Hamza na fushi da ita. A hankali zata karkato da
hankalinsa gareta har ya gane abinda tayi domin inganta rayuwarsu ne ba don ta
kuntata masa ba.
Ta sunkuyo zata yi kissing dinsa yayi saurin kawar da kansa gefe. Yanzu Izzatu bata
burgeshi ko me zata yi abubuwan da tayi masa kawai yake tunawa.
Fuskarta kamar zata yi kuka tace Sweety ya kamata ka manta da dukkan abinda ya faru
mu sake gina rayuwarmu kamar da. Nasan nayi maka laifi ina rokonka ka yafe min.
Wani irin kallo yake mata na rashin gamsuwa da abinda take fada....zancen na yafe
miki kema kinsan ba abu bane da zai iya faruwa lokaci daya. Mu bar wannan zancen
ma, na fada miki duk irin asarar da kika janyo min amma baki ce komai ba. Duk wata
kadara da kika san ina da ita na sayar. Motata ce kawai ta rage da taki. Wace
gudummawa zaki iya bani domin ganin mun cigaba da running din gidan nan kamar yadda
muka saba?
Izzatu tayi saroro tana kallonsa. Ita bata dauki abin serious ba lokacin da ya fada
mata. Tayi ajiyar zuciya...nima bani da wani kudi yanzu duk nayi amfani dasu a
wurin biki. Amma zanyi kokarin taimaka maka da gyaran tawa motar. Sun kira maigyara
yace zata ci kamar sixty thousand.
Hamza yayi murmushi tare da girgiza kai. Izzatu kenan, ita nata taimakon a kanta
zai kare kenan. Yace to babu komai a hakan ma nagode.
Taji dadi ta sami wuri kusa dashi ta zauna...nasan wannan problem din is not
permanent amma zanyi kokarin ganin mun rage kashe kudi sosai. Abinci da kake siyo
mana every thursday sai ka rinka siyowa a wurin da bai kai na da tsada ba,
sannan...
Bai bari ta karasa magana ba ya tashi..bari naje na rufe gidan ina zuwa. Ko sake
kallonta baiyi ba ya fice ya barta zaune. Gani yayi idan ya cigaba da zama ransa ne
zaiyi ta kuna a banza. Ita a irin nata hankalin duk abinda ta lissafa gani take yi
ba karamin taimako tayi masa ba kenan.
Babu wani rufe gida da zaiyi domin ya rufe tunda ya dawo. Dakin Zuhra ya nufa yaji
dalilinta na kin zuwa dakinsa yau.
*****
Kwance take a kan gado amma sam bacci yaki zuwa. Tunanin Ya Hamza take yi, yana can
yau tare da Izzatu. Hawaye taji ya cika mata ido zuciyarta na zafi. Yanzu duk irin
yadda yake bata kulawa haka zaiyiwa Izzatu?