Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
suka ji shigowar
motar Alhaji.
Ana magariba Hamida ta zuba musu tuwon a katon faranti. Suna ci yan matan na zuba
mata santi. Ita duk kunyarsu take ji ta kasa sakin jiki taci sosai. Bayan sun gama
Mama tace su rakata falon Alhaji ta gaishe shi. Tuna ranar da ta fara zuwa gidan
tayi kunya ta kamata ta rufa katon mayafinta ko fuskarta baa gani. Tana durkusawa
ta gaisheshi ya fara miko mata rafar kudi dubu goma. Tayi saurin daga kanta yayi
mata murmushi wannan tukwicin ciyar da dan tsoho ne. Itama murmushin tayi Hamida
tace Alhaji mun tayata fa. Yayi dariya kin tayata hira dai. Daga shi har Hajiya da
Mama duk sun mata karba mai kyau suna ta yabon iya girkinta. Wannan kuwa a wurin
Ummanta ta koya. Da zasu koma dakinsu Adabiyya ta dauko turaren ta mika masa gashi
inji Baba. Allah Sarki mal Bashir harda wata wahala banda 'ya da ya bani. Ina fata
babu wata matsala dai tsakaninki da Yaya da Izzatu. Tace babu komai nagode.
Ledar kayan da Umma ta bata ta bawa Adabiyya ta kaiwa su Mama. Tasha addua sosai a
wurinsu. Da Hamza ya dawo falon Alhaji yaje. Suna hira ya bude food flask din yaga
akwai sauran tuwo a ciki. plate din Alhajin ya jawo ya zuba yaci harda karawa.
Alhaji yace Kaltume kiyiwa danki magana ya bar min na dumame. Hamza na dariya yace
yau tuwon yayi dadi amma ba jagwalgwalon su Adabiyya bane ko. Mama tace me ka mayar
min da 'ya'ya ne. Don kasan matarka ce ta dafa kake mana santi. Cak ya tsaya da
shan miyar da yake da cokali yana kallon Mama. Hajiya tace yau kowa yasan sabon
hannu yayi mana girki sai yabonta ake yi. To Hamza, ga abinci da dadi ga kyankyamin
Zuhra da yake. Amma dole ya yaba mata don ba karya ta iya girki.
Da zasu tafi Mama atampa Super Exclusive ta bata mai kyau, Hajiya kuma ta bata dubu
biyar. Sai godiya take musu kamar ta ari baki. Su Adabiyya suka yi mata alkawarin
zuwa su kwana biyu da weekend don duk cikin satin zasu gama jarabawa. Adabiyya na
level two Hamida na level one a jamia. Hamza sai mamakinsu yake basa son zuwa
gidansa a iya saninsa.
Ba karamin dadi taji ba yadda suka karbeta a gidan. Suna isa gida ya rufe ko'ina
yace mata sai da safe. Yana son yaba mata yadda ta kyautatawa iyayensa amma wata
zuciyar ta hana shi. Abinda su Hajiya suka bata ta nuna masa yace to Allah Ya saka
da alkhairi. Kema an fada min abinda kika kai musu nagode. Taji dadin godiyar tasa
ta tafi dakinta zuciyarta fes.
Da sassafe ta farka ta gyara wake ta bawa maigadi ya kai mata markade. Haka kawai
taji kosai take son yi. Waken ba dayawa ta hada ba tunda nata ne ita kadai amma
tayi yadda maigadin zai samu don tana ta tunanin me yaci jiya da rana da kuma dare.
Tafi kowa sanin yunwa ba dadi.
Kunu ta dama da tsamiya ta dan saka lemon tsami sannan ta soya musu kosan. A dan
karamin jug din roba ta zubawa maigadi nasa kunun sannan ta sami wata robar ta zuba
masa kosai da yaji. Nata kuma ta kwashe daga mai ra barshi ya tsane kafin ta kaiwa
maigadin. Tana juyowa taga Hamza har sai da taji tsoro. Ya gama shirinsa zai tafi
wurin aiki. Gaisheshi tayi tace zan mikawa maigadi abinci. Hanya ya bata ta wuce ya
tsaya yana kallon kosan. Yana jin yunwa amma bazai ce tayi abinci dashi ba duk da
jiya yaci kuma ya yaba. Kamar ya fita daga kitchen din sai ya dawo bari yaci yaji
ko ta iya kosan. Izzatu bata yi tace abincin talakawa ne. Daya ya jefa a baki yaji
dadi harda dan kurbar kununta dake cikin kofi. Gaskiya da dadi, a hankali ya dawo
ya dan leka falon yaga bata taho ba. Da sauri yazo ya dauki wani harda saka yajin
da ke wata yar roba ya kuma sawa a baki duk da akwai zafi sannan ya dauki biyu a
hannu. Ko taunawa bai fara ba Zuhra ta dawo tayi mamakin ganinsa a kitchen din tace
ashe baka tafi ba. A ransa yace me zaisa ta dawo yanzu. Gimtse baki yayi yace uhmm.
Kallon rashin yarda tayi masa ko akwai abinda kake so? Uhmm uhmm ya amsa bakin nan
a rufe. Ya rasa yadda zaiyi da kosan bakinsa. Daukar plate tayi ta juye kosan ta
dauki kofin kunun tace to adawo lafiya ta fice ta barshi a tsaye. Sai a lokacin ya
saki numfashi sannan ya sami damar tauna da hadiye kosan bakinsa. Ficewa yayi ya
shiga mota ya cinye sauran biyun sannan ya goge hannu ta tissue. A mudubin motar ya
kalli kansa....Hamza kaji jiki, satar kosai a cikin gidanka. Murmushi yayi ya ja
motarsa.
[9/25, 3:55 PM] #+234 803 040 6305#: AL'ADUN WASU #42
Batul Mamman(Mrs)#
Iyakar karfinta tasa tana neman kwace hannunta amma rikon da yayi mata ba na wasa
bane. A haka ya jata suka je dakinsa ya dauko kwalin tissue sannan suka koma nata
dakin. Iyakar tsurewa Zuhra ta gama don bata san abinda zaiyi mata ba sai magiya
take yayi hakuri. Yana jinta ya share, sai da suka zo gaban dressing mirror dinta
ya jawo stool din ya zaunar da ita. Numfashinta har wani sama sama yake don
fargaba. Har tausayi ta bashi sai ya dan sassauta murya tare da daidaita fuskarsa
da tata har suna jin numfashin juna...ke, rufe idonki. Ji tayi kamar zuciyarta zata
ballo kirjinta ta fito, ba dai hada bakin da ya gama da Izzatu zaiyi da ita ba. Ita
ko a litattafan hausa idan tana karantawa ta tsani ace anyi kiss. Turawa dai marasa
kunya suyi abinsu amma ita duk yar kazantarta kyankyamin haden bakin nan take yi.
Kokarin tashi tayi ya rike kafadunta ya sake zaunar da ita. Kawai sai ta saka masa
kuka...don Allah kada kaci amanar matarka. Kamar yau ne zata dawo kuyi abinku.
Tissue yake zarowa daga kwali yace me zamuyi? Kanta a kasa tace sumba mana. Bai san
lokacin da ya soma dariya ba. Kece sumbar ai....ya nuna bakinta Allah Ya kiyaye
nayi kissing wannan dan bakin. Ina miki kallon saliha ashe kema idonki ya bude
kinsan kiss. Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta don kunya yasa hannu ya sauke su.
Rufe ido nace. Ba musu ta rufe...tissue ya ninke ya soma goge mata girarta. Yana yi
yana kallon yadda ta bata rai harda turo baki. Bai bar abinda yake ba yana yi yana
kallonta. Ya gama da girar ya koma saman idanunta da lips dinta. Takaici duk ya
isheta kwalliyar rabin awa an goge mata ita. Hannunta ya sake kamawa ya kaita kofar
toilet. Jeki kisa sabulu ki wanke fuskarki. A tsiwace tace bayan duk ka goge min
kwalliyata. Daga hannu yayi zai dalle mata baki ta tafi da sauri. Ke dawo ki ajiye
mayafin kada ya jike. Kamar bata ji me yace ba sai da ya maimaita da dan fada fada.
A hankali ta warware shi. Idanunsa a kanta, dole ta rufe jiki da katon mayafi irin
wannan matsatsiyar riga. Doguwar riga ce mai kyau duk ta fito da surar Zuhra. Ta
wuyan rigar kirjinta ya dan fito. Tana daga hannu ta ajiye ya hango
hammatarta......fal gashi.
Saurin kawar da kansa yayi. Yaso shagala da kallon jikinta sai gashin da ya gani ya
dawo dashi. Gaskiya lamarin Zuhra akwai gyara. A inda ta barshi ta dawo ta same shi
yace ta sake zama a kan stool din. Wani lotion mai kamshi yasa kadan a hannunsa
saboda zafin gari ya shafa mata a fuska. Daga shi har ita wani yanayi suka shiga
yadda yake shafa mata fuskar. Bayan ya gama ya dauko hoda ya shafa mata. Sai ya
duba lip gloss light brown ya sa mata a baki. Har abin taje gira yasa ya kwantar
mata da gashin girar sosai. Ita kanta sai taga tafi dazu kyau duk da tana son saka
janbaki da eyeshadow. Kallonsa take yadda ya iya sarrafa kayan kwalliyar mata.
Da ya gama mikewa yayi yana dan sosa bayansa da ya kage saboda ya jima a duke.
Hararta yayi saura kice min dan daudu, kuma ko kice kinyi kyau bare kuma godiya.
Murmushi tayi tace nagode. Shareta yayi ganin ta fara dariyar shakiyanci bari naje
na shirya ki canja kayan nan kafin na fito ki saka mai zani.
Wata atampa mai adon pink da fari ta saka wrapper skirt da riga. Duk Hajara ke kai
musu dinki kuma sunyi sa'ar tela. Pink din mayafi ta saka da farin takalmi da yar
jaka fara mai kyau. Sake kallon kanta tayi a mudubi tayi murmushi. Mutumin min nan
yana da kirki idan yaso. Amma banda wayon ya tabani meye zai goge min fuska da
kansa. Tana zancen zuci taji wani kamshin turare mai dadi. Hamza ne sanye da yadi
ruwan madara mara nauyi. Ya gyara fuskarsa ya rage gemu da gashin baki. Sai ya kara
haske da yi mata kyau. Shima kallonta yayi ta canja kayan yace better...Zuhra tace
best. Ta dan daga gira...nima fa na iya turancin nan. Good, better, best waye bai
iya ba. Dariya ta bashi ita kuwa ko a jikinta tabi bayansa suka fita.
Da kansa ya bude mata gaban motar ta zauna ya rufe. Yana tayar da motar ya kunna
AC, ko minti biyar basu yi da fara tafiya ba ta soma gyangyadi. Dan bugun
kujerarta yayi, kinji sanyin AC ko, to idan kika yi min bacci jefar dake zanyi a
titi na huta. Gyara zamanta tayi tace amma dai wasa kake yi ko? Gabansa yake kallo
ki yi baccin sai mu gani wasa ne ko gaske. Waje ta koma kallo. Da shirun ya isheta
tace Allah Sarki su Nana suna hanya ko. Kaduna babu nisa sosai tun dazu suka isa ya
bata amsa. Daga nan motar tayi tsit ko rediyo bai kunna ba.
Motar na shiga layinsu Zuhra yara suka fara binsu ana ga Zuhran baban yara. Hannu
bibbiyu ta rinka daga musu. Har su Anas da Sani kowa ta gani sai ta daga hannu.
Haka kawai Hamza sai abin bai masa dadi ba. Tana dagawa Munkaila mai shagon kusa da
gidansu hannu Hamza yace kika kara daga hannu sai na dalle miki baki. A islamiyya
ba'a koya muku kamun kai bane. Turo baki tayi to kuma sai ka hanani zumunci da
mutane. Rai a bace ya juyo sai dai ko motar bata jira ya kashe ba ta fice da gudu.
Umma na kwance a falo taji an fado mata a jiki. Tana kokarin tashi Zuhra ta soma
kuka. Umma tace to meye haka kuma. zuciyarta cike take da farincikin ganin yarta.
Baba da ke daki fitowa yayi da jin muryar Zuhra. Shima makale shi tayi tana kuka.
Umma tace wai kukan na meye ne? Hamza ne ya shigo dauke da manyan ledoji guda biyu
yace kukan shagwaba take yi Umma. Baba ya tarbe shi, har kasa ya durkusa ya
gaishesu tare da ajiye ledojin a gaban Baba. Umma tace kai kuwa baka gajiya da
wahala. Duk zuwa sai kayi dawainiya. Dan sunkuyar da kansa yayi albarkarku muke
nema Umma. Zuhra mamaki tayi wai dama yana zuwa gidansu. Kawai sai taji ya kara
girma a idonta. Zata yi kokarin dena yi masa rashin kunya.
Hira sosai suka yi da Baba ita kuma suka shige daki da Umma. Duk dadi ya kama Umma
taga kamar Zuhra ta nutsu. Zuhra tace sai bayan hutu zaki dauko Safara'u ne? Umma
tace eh ance sun kusa fara jarabawa. Zuhra tace yace daga nan gidansu zamu je. To
me zaki kaiwa surukan naki? Sai a lokacin tayi tunani ya kamata ace ta kai wani abu
tunda yana yiwa nata iyayen. Umma bata jirata ba ta fita kitchen. Kayan kamshi da
kayan kadin da kanwarta ta aiko mata da yawa ta zuba a leda ta bata. Da zasu tafi
bayan sunyi sallar laasar Baba ya bata wani turare mai kyau yace ta kaiwa Alh
Nasiru. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/26, 12:31 AM] #+234 803 244 1205#:
AL'ADUN WASU #46
Batul Mamman(Mrs)#
Ba shiri ya saketa, yana yarfe hannu. sake bude baki tayi zata yi ihu a hankali
yace ke nine....ajiyar zuciya tayi da karfi sannan tace da tsoratani kazo yi kake
min sanda a daki? Kaima baka da fitila ne? Dukan da tayi masa ya kulle masa ciki
gashi ta dame shi da surutu. Da waya na shigo karama bansan inda kika jefar min da
ita ba. Yayi kokarin dukawa ya lalubi wayar yaji zafi a cikin....auchhhh. Zuhra
tayi saurin matsawa kusa dashi menene ta tambaya a tsorace. A duhun ya harareta
naushi na fa kikayi a ciki ga cizo sai kace wata yar dambe. Duk hanyar mugunta kin
sani. A wahale take jin muryarsa na fita ta mika hannu tana sannu taji ta taba
cikinsa....kamar wadda aka tsikara tayi saurin janye hannun tana cewa yi hakuri.
Shima hakan yaji amma bai so ta dauke hannunta ba. Dakin yayi shiru na dan
lokaci...Hamza ya kasa gane dalilin da yasa ko yaya jikinsa ya taba na Zuhra sai
abin yayi affecting dinsa sosai. Dan gyaran murya yayi bazaki tayani neman wayar
ba? Kamar jira take ta durkusa tana rarrafe tana shafa hannu a kasa. Abu taji ta
taba tayi saurin janyowa ashe hannun Hamza ne shima yana duddubawa. Da yake da
karfinta taja shi kuma baiyi tunanin hakan zai faru ba sai ya fada kanta. Bakon
yanayi duka suka tsinci kansu a ciki. Kunya kamar Zuhra ta nutse a wurin, kamshi ne
mai dadi yake fita daga jikin Hamza.
Yana fadawa ya gane daurin kirji ne a jikinta...a hankali ya soma yi mata magana.
Nifa bana son daurin kirji don Allah ki dena. Wai ita yake hadawa da
Allah....saurin dawowa tayi hayyacinta ta fara kokarin ture shi. Yana ji ya sakar
mata nauyinsa yana mata dariya.....wai kema kina son jin dumin mijinki shine kika
janyoni. To saboda ina tausayinki bazan miki fada ba mu kwana a haka. Wayyo Allah,
karshen kunya Zuhra ta gama ji. Har wata in'inar karfi da yaji ta fara.
Al'Quran....Al'Quran ba...ba haka bane. Ko kadan bashi da niyar tashi don ya soma
jindadin tsokanarta yace to yaya ne? Abinda kika ga munayi da Izzy kike so nayi
miki? Wani karfi ne yazowa Zuhra ta dage ta ture shi. Tana ji yana dariya ita kuwa
sauran kadan ta soma kuka. Bata dade da matsawa ba yaga wayar ya dauka ya kunna
tare da soma haska dakin.
Can bakin kofa ya ganta ta takure harda jan bargonta ta rufe jiki. Koda ya matso
harda dan hawayenta. Kusa da ita ya koma me kuma nayi miki kike min kuka? Sai da ta
dan matsa sannan tace ba kaine kace wai...wai...wai....kwafa tayi ta kasa karasa
maganar. Dariya shagwabarta ke bashi, dazu fa aljani kika kirani banyi kuka ba sai
kece mai arhar hawaye zaki min kuka daga wasa. Kin kallonsa tayi saboda kunyar
ganinsa babu riga. Yace kinga fito daga bargon nan kisa rigar bacci bana son daurin
kirji. Tana kumbura baki tace ni a haka zan kwana. Mikewa yayi to ya rage
naki...wai ma kinyu wanka kuwa kafin ki kwanta. Tsami nake ji a dakin nan....dama
zuciya na kusa ta fara kuka wallahi bana tsami. Yace to kinyi wankan..tsakaninki da
Allah. Rufa tayi har ka sannan tace banyi ba. Rufe bakinta ke da wuya ya janye
bargon gaba daya tana kuka ko kulata baiyi ba. Lokaci daya ya yankewa kansa
shawarar abinda zaiyi ya taimaka mata kafin su rabu.
Kan gadonta ya jefa bargon sannan ya shiga toilet dinta. Babu komai sai sabulun
wanka da omon wanki da wanke toilet. Ficewa yayi ya barta a duhun baiyi magana ba.
Ga tsoro tana ji ita kadai amma bata son binsa.
Bayan kamar minti biyar ya dawo da wata fitila mai haske wadda tafi karamar wayar
tasa. Shima a babbar bashi da chaji sosai. Wani abu ta gani a hannunsa kamar
toothpaste tace ina da makilin fa. Wannan ba makilin bane yar kauye zo nan. Baya ta
dan matsa tace yi hakuri. Fitilar ya ajiye a kan dressing mirror dinta sannan ya
jawota ya zaunar da ita kamar ranar da yayi mata kwalliya. Duk ta tsargu da daurin
kirjinta, shi kuwa ya saka kayan bacci marasa nauyi yanzu. Yana zaunar da ita ya
kama hannunta duk da yadda yaji ya daga. Allah Sarki Zuhra sai hawaye...ashe dazu
bata ga komai a kunyar da Hamza yake shirin bata ba. Kokarin sauke hannunta tayi ya
sha kunu zan matseki idan baki tsaya ba. Kuma kinga mu kadai ne a gidan babu mai
taimakonki. To me zaka yi min? Yace sa ido ki gani bana son surutu kuma ki hadiye
kukan nan. A hankali take hawaye tana gani ya bude abinda ta zata makilin ne ya
zuba a wani abu kamar cokali mai dan fadi ya soma shafa mata a hammata. Ji tayi
kamar cakulkuli ta soma dariya....girgiza kai yayi kina da matsala, daga kuka sai
dariya. Bata dena dariyar ba har ya gama yace ta bar hannunta a bude. Dayan hannun
ya daga ya shafa a nan ma. Wurin minti biyu yana dube dubi a dakin har yaga inda ta
ajiye turaruka da body spray din lefenta. Tace wai a haka zan zauna ne? Sai da ya
dauko wurin kala biyar sannan ya dawo ya dauki yar robar da tisssue a hannunsa ya
kwashe duka gashin. Zuhra ta wage baki ....lahhhh kaga gashin ya cire. Hamza
murmushi kawai yayi..yar kauye bata san shaving cream ba. Fes ya share mata sannan
ya mika mata shaving stick har uku. Shiga toilet kiyi shaving sannan kiyi wanka ina
jiranki a nan. Ya Salam yau Hamza so yake ta tona rami ta boye kanta don kunya.
Kasa shiru tayi tace can kasa wai yau kunya kake son sani ji? Bata san yaji ba yace
yes idan baki wuce ba zanzo nayi miki da kaina. Fitilar ta dauka da sauri ta shige
harda murda key. Murmushi Hamza yayi ya dan matsa kofar toilet din...kada ki fito
sai kinyi wanka sau uku. Ki tabbatar jikinki ya fita sosai don zan duba. Idan baki
fita ba na iya yiwa kazamai irinki wanka. Kuma kiyi brush sosai. QTo an hada Zuhra
da aiki, sai da tayi amfani da duka shaving sticks din wurin gyara jikinta sannan
ta shiga dirzar jiki. Allah Ya kiyaye ta bari yayi mata wanka. Sau biyar ma tayi
harda goge kafa da abin kaushi duk da kafar tata bata da matsala. Brush da
toothpaste kuwa sun san Hamza na dakin don sun sha aiki. Katon tawul tasa ta goge
jikinta sai taji wani dadi da iska na shigarta. A hankali tace na gama. Yana kwance
akan gadon nata yace to fito mana. Lallai ma a hakan? Rigar bacci yake duba mata
amma sai yace to meye ya rage da zaki boye min. Shiru yaji bata fito ba ya dan
kwankwasa, bude ga riga ki saka.
Dan kadan ta bude kofar ta zura hannu. Wata rigar bacci ce mai kyau amma cotton
mara nauyi ta wuce gwiwarta ma da karamin hannu. Yace ki goge jikinki sosai kafin
ki saka. Dama ta goge ta saka ta yafa tawul din ta fito. A kan stool din yake zaune
yace tunda yau akwai zafi sosai ba sai kin shafa mai ba. Har gabanta ya karasa ya
cire mata tawul